← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 176

Sashe 83

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daga cikin gida kuwa Gimbiya Ilham na zauna tana ta bin Hadiman dake kaiwa da komowa wajen kimtsa kayayyankin da suka shigo da shi. sai taji suna tafiya da zaman kaɗaicin da ta ke ciki, dan Turaki tuni ya fice daga gidan ko sallama ɓata haɗa su ba.
can kuma sai taji parlon ya karaÉ—e da wata uwar guÉ—a kamar gidan zai tsage, ta rumtse idonta for the first time da hawayen farin ciki ya sakko mata tun kawota, ko ba komai tasan duk wannan abin da akeyi na murnar ta kai budurcinta gidan miji ne.
Boɗejo ta fito daga bedroom ɗin da suka kwana riƙe da farin bedsheet ana haskawa mutane ɓacin da yay dan su shaida, ta bawa Jakadiya Hanne tana barin wajen da rawa.

ta isa wurin Ilham ta rugumeta tana ƙara sakin wata uwar guɗa ta musamman, sai kuma kowa yayo kanta ana cewa,"barka Gimbiya, sannu Gimbiya, sannu sannu, Allah ya huce gajiya, ubangiji ya kawo albarkar ɗaki, sannu. Fulani Azima na cewa agaisheki, a gaisheki, ayi miki gaisuwa irin gaisuwar da babu mahaluƙin da ya taɓa samunta".

daga nan Boɗejo da Inna Falmata suka kamata sukai cikin ɗaki da ita. bayan an yiwa Gimbiya Ilham gashin ruwan ɗumi mai kyau, sannan aka haɗa ruwan lalle da turare Boɗejo tayi mata wanka da shi, aka fito da ita sai zuba masifaffan ƙamshi take yi. duk wannan hidima dai da akeyi Boɗejo ƙwafa kawai take jerawa tana tunanin irin rashin mutumcin da zata yiwa Turaki tunda yasa ƙafa ya bar ɗanyan amarya ita ɗaya kamar mayya.

kwalliya aka yiwa Ilham ta gani ta faɗa, tayi azaban kyau, aka fito da ita a lulluɓe da alkyabba fara tas me adon red ajiki, babu ta inda ake ganinta harta ƙafarta kuwa dake sanye cikin wani half conver na sarauta, akan cushion na babban parlon gidan aka zaunar da ita tayi zama irin na masu mulki, Mutum uku daga dangin mahaifiyarta suka zo suka ɗaga hular alkyabbar nata ana fasheta da turare me bala'in ƙamshin gaske, suna yi ana tafi ana busa shantu ana rera mata waƙa na son barka da kawo budurcinta lafiya lafiya, after sun gama bajakolin fesa turaren sai wasu bayi guda biyu suka zauna kusa da ita gefe da gefe suna mammatsa mata ƙafafunta.

acan ɗaya ɓangaren kuwa Turaki na fita gida ya wuce, kaitsaye part ɗin Baffa ya nufa don zatonsa ko suna can suna breakfast, sai dai ko da yaje duk basa can Baffan ma bai tashi ba, dan haka ya taho side ɗin Maama, time duk sun zauna zasu yi break fast, kallo ɗaya Maama tayi masa tasan baici abinci ba, hakan yasa ta miƙe ta shiga kitchen ta dama masa kunun gyaɗa shap shap ta soya irish, duk da cewan akwai soyayyan irish ɗin amma tasan ba zai ci ba.
sai after break fast ɗin ne Maama ta zaunar da Turaki a ɗaki tai masa nasiha sosai akan yanda zai zauna da matar da ba sonta yake ba, ta nusar da shi in har yay haƙuri ya kyautata mata to tabbas zai ga ribar hakan, tunda har yayi biyayya Allah ba zai barsa haka ba.

tace,"Me Babban suna ko ni zan iya zaɓa maka Ilham matsayin wacce zaka aura, saboda yarinya ce me hankali da tarbiyya, ita kaɗai ta fita zakka acikin yaran Mai Martaba, to nasan dan ka aureta ba faɗuwa kayi ba ka sami uwar ƴaƴa ta gari. but ni ta yanda akazo da lamarin aurenne ya ɓata min rai, shiyasa duk naji na tsani auren wallahi, to amma ya zamu yi tunda ubangiji ya shirya faruwan hakan tuni. adu'ata Allah ya baku zaman lafiya ya kauda fitina tsakaninku, ya kuma baku ikon fahimtar junanku ta yanda ɗaya ba zai cuci ɗaya ba".

sannan ta ƙara cewa,"ka dai ji me nace maka ko?". ya ɗaga kansa kawai tabbacin yaji, dan bai jin zai iya magana.
suna zaune da ita suna ta hira kiran Boɗejo ya shigo wayarsa, yana kallo yay banza da kiran, da ya ƙara shigowa ya kashe wayan gaba ɗaya yana jan tsaki tare da kwanciya kan gadon Maama. ita dai tana kallonsa amma ko kusa bata yi magana ba, saboda tasan irin ɗacin da yake ji a zuciyarsa, and beside ta lura kamar yana da wata damuwa acan ƙasan ransa, sai dai bai faɗa mata amma tasan duk runtsi zata sa ni.

miƙewar Maama kenan zata shiga toilet taji an banko ƙofar ɗakin, kallon wajen da zatai taga Boɗejo a fusace ta shigo, ta bi Turaki dake gadon idonsa a rufe ta ƙarasa wajensa tana ta zazzaga masifa kamar zata bankawa ɗakin wuta. Hajiya Madina kam dama tana ganin itace ta shige toilet ta rufe ƙofa, haushin duk wanda ke da sanya hannu akan lamarin aurenan take. bata fito a toilet ɗin ba sai da taji Boɗejon ta fita, ta fito a ranta tana jin haushin irin zagin da Boɗejo ta dinƙa mata ita da Turaki, cikin ranta tana jin ina ma ace akwai ƙasar da babu wanda ya sa ni sai ita, da ba abinda zai hanata ɗauke Turaki a gobe ta kaishi can yaje ya huta na kwana biyu ko zuciyarsa tayi sanyi.

acan gidan Turaki dai sabon biki ne ya tashi, dan yana zuwa ya tarar da danginsu da dangin Fulani Azima an cika gidan sai tashin busar algaita ta ko'ina, ta dole BoÉ—ejo ta shirya shi har da cewa wallahi idan baiyi wasa ba sai tayi masa wankan da kanta. ya fito cikin dakakkiyar shadda fara da ta saje da alkyabbar Gimbiya Ilham, yayi azababben kyau har yafi na ranar É—aurin aurensa. kamar dai wancan kwanakin haka yau fuskarsa duk babu walwala har akai taron aka gama, sai da BoÉ—ejo ta tabbatar sun gama cika al'adarsu sannan hankalinta ya kwanta.
jama'a sunci sun sha an bar arziƙin abinci a inda yake, bayan kammalawa Inna Falmata ita tayi jawabin godiya ga duk waɗanda suka zo da kuma tarin adu'oi wa ma'auratan, daga nan kuma sai aka shiga ɗaukar hutuna kamar hauka, kowa burinsa bai wuci yay short vedio yana hasko gidan ba ta yanda duniya zata gani ta shaida gidan arziƙi.

ƙarfe biyar na yamma Turaki ya wuce police station kan sabon report da ya shigar tun a ranar da ya dawo, suka kuma tabbatar masa da cewar suna kan yin bincikensu, bai dawo gida ba sai 6 kuma ba gidansa ya wuce ba wurin Maama ya wuce, inda yaje ta tarar ta wuce wajen Kaka anzo ance tana can ta suma.

*Kidnappers.*
ga duk wanda ya san Fillo a yanzu zai iya rantsewa ba ita bace, saboda yanda ta fita a hayyacinta, abinka da mara ƙiba, kallo ɗaya zaka yi mata ka zubar mata da hawaye saboda yanda ta fige, idanuwan nan sun ƙara ɓurmawa ciki.

zaune take akan ƙasan simitin wajen an ɗaure ƙafafunta da igiya, haka ma hannayenta an ɗaure su ta baya, yanda fuskarta tayi jawur da yanda jini ke fita daga bakinta kaɗai zasu shaida maka irin azababben dukan da ta sha a iyakar yau.
ƙaton mutumin dake gabanta ya ƙara buga mata bindigar hannunsa a fuskarta, take bakinta ya ƙara fashewa kanta ya lanƙwashe.

cikin burkitacciyar hausarsa yace,"muddin baka daina yi mana gardama ba, to wuya yanzu ka fara shanta. in bakayi wasa ba sai mun kaseka ayau É—in nan".

da ƙyar Fillo ta miƙar da wuyanta ta ɗago tana kallonsa da idanonta guda ɗaya da bata iya gani sosai da shi.
kallonsa take yi tana hango ranar da suka tsareta suka ce ta bayar da lambar wanda za'a kira, lambar Amir kaÉ—ai ta haddace a duniyarta kuma bata tunanin zata iya bayar da shi, saboda tsoronta kar ya cutu da jin halin da take ciki.

sai da tayi da gaske tukunna ta iya haɗa lambar Yami ta bayar dan ba wani haddaceta tayi sosai ba, kuma sai da aka gwada lambar kusan sau uku duk ba correct ba sai ana huɗun Allah ya taimaketa kiran na shiga taji muryar Yami a sanda aka ɗaga, da wannan ta samu ta kuɓuta daga wahalar da suke bata.

kuma tun a ranar da aka kawo kuɗin suka ƙirga suka ga harda ƙarin dubu ɗari biyar akai amma hakan bai yi musu ba suka ce fiye da wannan suke so, idan bata manta ba tana jin shi ƙaton na cewa,"wato iyaye naka suna sonka sose, tunda har gashi suna ƙara mana kuɗi akan wanda muka nema. wannan ya nuna mana sewan sun tara kudi da yawa, don haka ba zamu sake ka ba sai an cika mana kudi ya zama miliion goma".

tunda taji ance ƙarin dubu ɗari biyar tasan Amir ne kaɗai zai yi hakan duk da bata san ta yanda akayi su Kaka ma suka sami wannan kuɗin ba. dan a ranar da suka kira waya aka sawa su Kaka muryarta tana cewa azo a ceceta, the first abinda Kaka ta faɗa mata shine,"ki daina kuka Fillo, kiyi ta adu'a kinji za ki kuɓuta, banda ƙarfin da zan kawo musu amma Amir zai zo ya tafi dake kinji".
ta sa ni a irin son da Amir yake mata zai ƙara fiye da haka ma in har ace yana da shi, kuma tun a ranar ta ƙara jin Amir ya sami wani waje na daban a tare da ita, in ace da sonsa ya ragu da 85%, to a yanzu wannan son nasa zata ce ya ƙaru da morethan 1000%, saboda shi ɗin mai sonta ne kuma me ƙaunarta, dan haka a duniya bata da wani wanda ya fishi.

dukan cikinta da akayi da ƙafa shi ya dawo da ita daga duniyar tunani. ta saki kukan da bata jin zata iya riƙe shi, ta shiga ambaton Allah a fili da kuma zuciyarta. ta buɗe bakinta wanda leɓenta suka riga suka zama ganda tace,"ku kasheni kawai, dan Allah ku kasheni ko na samu na huta. kunce sai an ƙara muku kuɗi an ƙara still kuna faɗin bai isheku ba, na faɗa muku bamu da wani gata sai Allah, dan Allah dan Annabi ku kasheni kawai".
Chapter 83 · 0% Book details