← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 176

Sashe 150

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tai lamo da kanta a kafaÉ—arsa tana cewa,"kamar ma kar na koma ai, family É—in ku suna da kirki sosai".
"ni ma haka suke ta ce min wai nayi sa'ar mata me hankali da mutunci, anyway yanzu dai faÉ—a min when zaku dawo?".

ta ce,"to ka zauna anan mana kaima".
"kije ki faÉ—awa Mum hakan".

suka miƙa yana manneta a jikinsa,"7days yayi yawa Fulani Nah, ki faɗawa Mum hakan".

ta ce,"7days yayi kaÉ—an Turaki, ina so zanje inga Ummi nah, kaga babu nisa daga nan".

bai ƙara cewa komai ba ya kama hannunta suka fita, lokacin Baffayo har ya tayar da mota, yay ma ta side hug yace,"please don't stress your self wajen yin aikace-aikace da zuwa gaishe gaishe, dan gidan nan da kike ganinsu aiki suke kamar injina. fita indai ba'a mota ba ne kice da Mum ba kya jin daɗi".
ta gyaÉ—a masa kai kawai tana jin babu daÉ—i, sam bata so ya tafi.

ganin hawaye a fuskarta yasa shi cewa,"ko in faÉ—awa Mum ba kya son zama?".

ta girgiza kanta alamar a'a tana riƙe hannunsa.
sai yaji ta ba shi tausayi sosai.
"daina kukan Fulani Nah bana son hawayenki". ya faÉ—a yana share ma ta hawayen.

sai ya ɗaga waya yana kiran babbar ƴar gidan Inna me su na Hamida, tana zuwa ya ce da ita,"ki kula min da ita kinji, less hayaniya a inda zata zauna please, tana son bacci ki kula da haka, sai an bata abinci tukunna take ci if not zata zauna da yunwa, bata da cikakkiyar lafiya, so duk wanda zai zauna kusa da ita ki tabbatar is not addicted to ɓatawa mutum rai".

tace,"insha'Allahu za'a kula me sunan tsoho".
yay murmushi yana maida kallonsa ga Fillo, wacce ta maƙale hannunsa tana hawaye, ya sunkuya yana ɗora kumatunsa kan leɓenta yace,"ummm 1 peck".

abin da bata taɓa yi masa ba, kuma shi ma bai tsammaci zata yi ɗin ba, tai masa peck a kumatu tare da kissing ɗinsa a goshi tana faɗin,"i will miss you".

"i will miss you too, take care...bye bye".
ta É—aga masa hannu tana faÉ—in,"bye". ya sauke ajiyar zuciya,"ba ki min adu'a ba".

tasa hannu akan ido irin yacca yara ke kuka tace,"Allah ya kai ka lafiya, Allah ya tsare hanya, Allah ya kare ka da kariyarsa".

ya amsa da,"amin, thank you so much". kafin ya iya sakin hannunta ya wuce mota, ita kuma taji wani kuka ya taho ma ta but sai ta danne shi saboda Hamida, su na shiga ciki ta wuce É—akin Hamida ta kwanta akan gado.

wajen ƙarfe goma na dare sun kwanta ita da Hamida sai ga Nilfat ta shigo ɗakin, ta kunna fitila ɗakin ya gauraye da haske, Fillo ta buɗe idonta don ba baccin take yi ba.

"au ashe baccin naku ma bai yi nisa ba, mijinki ne ya kira waya".
ta ƙaraso tana bawa Fillo wayar, sai taji wani daɗi ya ratsata, tun ɗa zu take ta tunaninsa, ta kasa ko baccin har Hamida tazo ta kwanta tayi nata, infact jinta take kamar mara lafiya, ta karɓi wayar tana kallon Nilfat da zata fita tace,"ki tsaya ki karɓi wayar".

ta ce,"wala, ba tawa bace ai ta Baffayo ce, yace da safe ya karɓa".
ta fita tana rufe musu ƙofar, daidai da shigowar kiran Turaki wayar.
tana ɗagawa ta saka kukan shagwaɓa,"tun ɗa zu sai yanzu ku ka je?".

"am sorry Fulani Nah, na dawo ne na tarar Maama babu lafiya, yanzu muka dawowa ma daga asibiti".

"subhanallah, me yake damunta?".
"Bp ɗin ta ne, but da sauƙi, ko in kai mata wayar?". ya tambaya jin ta damu sosai.

ta É—aga kai kamar yana ganinta,"ehh".
yana zuwa É—akin ya tarar Maama tayi bacci, Fillo tace da safe ya faÉ—a ma ta tana yi mata sannu sosai.

ya ce,"insha'Allah, tun É—azu na kira Mum amma sai na kasa cewa ta baki. ba kiyi bacci ba ko tashinki aka yi?".
"ai na kasa yi".
"why?".

tayi shiru ta kasa cewa komai.
ya ƙara cewa,"why?, tell me".
"i am missing your warm body that makes me fall asleep".

taji murmushinsa me sauti ya fito.
"sorry Fulani Nah, just close your eyes and go to sleep, I will come to your dreams, then you sleep like you used to".

a shagwaɓe ta ce,"promise?".
ya ce,"insha'Allah".
ba su jima su na wayar ba yace ta kwanta zai je Baffa na kiransa.

ta sauke numfashi tare da ce masa,"don't forget to Perform Ablution and recite Al'qur'an before you sleep".

ya ce,"i will not forget, good nite".
sam bata so wayar tasu ta ƙare, ta danne kukan kewarsa gudun karta ɗaga hankalinsa ta ce,"good nite, sweet dreams, please you take good care of your self".
"insha'Allah".

da ƙyar dai suka iya yin sallama, Fillo ta tashi ta kashe fitilar sannan ta dawo ta kwanta tayi lamo, ba don tana jin zata iya baccin ba, zuciyarta ta cika fal tare da tunaninka kala-kala, har ɓarawon bacci ya ɗauketa.
[9/7, 01:30] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*55*
kiran sallar farko a kunnen Fillo, tana buɗe ido ta ganta a inda saɓanin Mafarkinta ya nuna ma ta.
ta ɓata fuska tana jin kamar tayi kuka, wayar Baffayo da ke gefen pillow ta ɗauko, adu'arta ɗaya Allah yasa babu pin a jiki, cikin sa'a kuma tana dubawa taga babu, don haka da sauri ta shiga message tayi typing text kamar haka.

_I don’t just miss you, i miss the warmth in your breath, depth in your eyes, the touch of your fingers, and feeling your hands on my waist. I miss you truly and deeply._

after ta gama rubutawan kuma sai ta kasa sending, ta tsaya tana tunani, kunyar turawar takeyi, ta zuro ƙafafunta ƙasa daga kan gadon kamar wacca zata yi kuka, har sai da Hamida ta buɗe ido ta tambayeta,"Asiraawo lafiya?".

"yi haƙuri na tashe ki, ji nayi kamar wani abu na bina ne, ashe zaren jikin rigata ne".
Hamida tayi murmushi kawai tare da komawa ta kwanta, don ita kanta ta fahimci tana cikin kewar mijinta ne, duk da tana da nauyin bacci but tana jinta sai faman juyi take.

Fillo ta tura text É—in sannan ta wuce toilet ta yo alwala ta fito, har ta idda sallar asuba bata ga reply É—in Turaki ba kamar yanda tayi tsammani. duk sai taji babu daÉ—i, may be ko text É—in ne bai yi masa ba, ko kuma abin da ta tura É—in ne bai dace ba, duk sai taji ta kasa komawa baccin da yake so ya É—auketa.

da safe wajen ƙarfe tara after sun gama breakfast, taji su na waya shi da Mum har take tambayarsa jikin Maama, tai ta jin kamar tace da Mum ta bata wayar, kewar muryarsa take yi kamar ta shekara dubu ɗari bata ji ba.
kuma bayan sun gama wayar da Mum a tunaninta ko zai kirata a wayar Baffayo sai taga har ƙarfe tara bai kira ba, sai taji kamar ta fara fushi da shi, but haka ta ƙara ɗaukar wayar ta ƙara tura masa text.
_The thought of you makes me smile, but the distance we share makes my heart ache. I am missing everything about you. I wish you were here Turaki._

ta tura da yaƙinin cewa a wannan lokacin zai dawo ma ta da reply tunda dai tasan yanzu wayarsa na hannunsa, but sai ta ƙara jin shiru, idonta ya ciko da ruwan ƙwalla ta ƙara tura masa text.
_kuma ba zan dawo gidan ba._

tana turawa ta É—auki wayar ta fita ta kaiwa Baffayo, har ya tambayeta ta gama ne tace masa ehh ko ya kira ma ba sai ya kawo ma ta ba.
ta koma ciki ta shirya kamar yanda Mum ta umarceta don za su fara zagayen gaishe-gaishen Æ´an uwa.

to acikin kwana biyu dai Fillo sai taji tamkar an sakata a kurkuku, mugun bala'in kewar Turaki take yi, har wata rama tayi ka rantse bata da lafiya, duk dare in zata kwanta sai tayi hawaye, ta riga ta saba da kwanciya a jikinsa, wannan ƙamshin jikin nasa, wannan ɗumin jikin nasa da ɗumin iskar bakinsa me ƙamshin min, wannan cairing ɗin nasa da soyayyarsa.

tun ranar da suka zo bata ƙara jin muryarsa ba, yau da safe ya kira Baffayo ya kawo mata waya amma da ta karɓa sai ta kashe kiran, yay ta kira taƙi ɗagawa ita alallai tayi zuciya tun da ranar nan duk yana kallon messges ɗinta bai yi ma ta reply ba.
wasa wasa dai sai taga ina ba zata iya yin har 7days ba, gida kawai take so ta koma, wurin Turakinta, tana missing late-night talk É—in su, tana kewar precious smile É—in sa, she want nothing except his presence around her, being away from him in this 4days she feels like being caged for a lifetime in misery.

a daddafe ta iya kwana biyar ɗin da suka yi, tuni ta fara cutar ƙarya me zafi ta yanda dole su tarkata su koma gida, hakan kuwa akayi, da Mum taga jikinta yay worst sosai musamman da taga kamar har da iskokinta dole suka ɗauko hanya a ranar.
sai ga su ƙarfe biyar na yamma sun sauka, don jirgi su ka biyo saboda Granny tace ba lallai Fillon ta iya jurar zaman mota ba, kuma su na dira a gombe taji ta warware daga cutar da ta fara kamata.

Zaytuna ce tazo ta É—auke su a airport, duk tunaninta gidanta za'a wuce da ita but sai taga sun yi gidan su Turaki, ba haka ta so ba sam, yacca ta so ta koma gida ko da ace bata same shi yana nan ba, to da ya dawo ya zama yay tozali da ita.

san da taga Maama sai da gabanta ya faÉ—i, ashe ciwo take yi sosai dan duk ta rame, ta faÉ—a kamar ba ita ba.
sai taji ta kasa riƙe hawayen tausayinta a lokacin da Maama ta rungumeta tana yi musu sannu da zuwa tana sanya ma ta albarka.
Chapter 150 · 0% Book details