← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 176

Sashe 167

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

An halicce mu ne domin mu bautawa Allah, wannan yana É—aya daga cikin dalilan da yasa ake jarabtar mu.
tabbas an halicce mu ne domin mu bautawa Allah, kuma dukkanmu mun yi alƙawarin yin haka kafin a aiko mu a duniyar. Jarabawa hanya ce a gare mu don cika wannan alƙawarin.
jarrabawa ita ce hanyar da Allah ya ke bambanta mu, domin tana taimakawa wajen bayyanar da imani da rashin imani.

Allah yana jarrabar mu, ya tsarkakemu ya kuma wanke mana zunubai. jarabawa gwaji ce ta maye gurbin wani mummunan bala'in, tabbas da munsan musibun da Allah yake kare mu, da ba za mu taɓa rasa sallah ba, kuma ba za mu taɓa son ɗauke goshin mu daga sujjada ba.
Gwaje-gwajen da ke ɓata mana rai na iya zama nau'i na kariya daga wani abu mafi muni da wataƙila ya same mu.
Allah yana so ya tsarkake mu, daga soyayyarsa da rahamarsa, domin mu samu ba Aljanna kaɗai ba, har ma da mafi girman darajar Annabawa da salihai. Gwaje-gwaje su na fallasa kurakuran mu da kasawarmu, kuma sanin hakan yana ba mu damar mai da hankali da himma wajen gyara waɗannan ɓangarori na halayenmu.

Allah yana jarrabar wanda yake so. Annabi(SAW) yana cewa: "Duk lokacin da Allah ya nufi mutum da alheri, sai ya sanya shi cikin tsanani".[Bukhari].
me yasa?, domin idan bawan ya amsa jarabawarsa da haƙuri, da gamsuwa da hukuncin ubangiji, hakan yana kusantar da bawa zuwa ga Allah, Kuma Allah yana son masu haƙuri.

Ibn Al-Qayyim (rahimahullah) ya ce idan aka yi mana jarrabawa, muna fuskantar zaɓi guda biyu; muyi haƙuri ba rashin haƙuri ba.
muke sauraren Alqur'ani da yawaita ambaton Allah saboda wadatar zuci, domin karanta alƙur'ani yana ba da wadar zuciya, addu'a don neman taimakon Allah, da ƙarfinsa, da samun sauƙi daga jarrabawa.

mu tunatar da kanmu jarrabawar da Annabawa suka yi, sun ba mu kyawawan misalai na juriya. mu tuna cewa kowanne mutum guda ana gwada shi ta hanyoyi daban-daban. mu tuna babu wani abu a cikin wannan rayuwar da ke dawwama, don haka jarrabawar za ta ƙare insha Allah.
domin ko acikin alƙur'ani Allah yace,"Lallai ne tare da kowane wahala akwai sauƙi".

ubangiji ba ya ɗaurawa wani rai face abin da zai iya ɗauka, Allah ya amince da mu, don haka mu ma muna buƙatar mu amince da iyawarmu ta cin jarabawa.
Allah yasa mu da ce!.

ƙarfe goma na safe a lokacin, Ilham ta fito daga ɓangarenta tare da wata yarinya da ba zata wuce shekara 8 ba. yarinyar ƙanwar Fulani Azima ce, aka bata ita kafin akaita makaranta, kasancewa yarinyar ta gama primary a halin yanzu.
yarinyar na riƙe ne da jakar Ilham, tabi bayanta zuwa baƙar motar da taga ta shiga, sabuwar motar da me martaba ya bata kyautarta.

a san da suka iso bakin gate domin fita, a sannan ne Fillo ke baro wajen Baba Me gadi da turtsetsen cikinta, da lokacin haihuwarsa kawai ake jira.
Ilham ta zuge glass su na gaisawa da Fillo, da siririyar dariya a fuskarta tace da ita,"kin ga kuwa yacca kika koma?, Allah each and every day cikin nan kumbura ki yake ƙara yi".

Fillo na kallonta tace,"ban da sharri dai".

"Allah babu zancen sharri, jiya da muka ci dinner ba ki kumbura haka ba".

Fillo tayi murmushi ta ce,"in ace ana mayar da cikin jikin wani ai ke zan mayarwa, ke ma ki É—anÉ—ana, ko da yake kwana nawa ne Allah na tuba, ina daga balcony zan ke hango ki a field kina aikin patrol".

Ilham tayi dariya sosai tare da cewa,"Allah dai ya raba lafiya, ni ban ma fidda ran ba za ki haihu ba a yau".

sai kuma ta nunfasa ta ce,"zan je gida ne, an yi min waya jikin Mami ya ƙara tashi".

jikin Fillo yay sanyi tana me tunawa da halin da suka riski Fulani Azima a shekaranjiya da suka je dubata.
cikin sanyin murya tace,"Allah ubangiji ya bata lafiya, ko in je in shiryo mu tafi tare?".

"a'a ke da kike fama da kan ki, na faɗa miki bana fidda ran ba za ki haihu ba a yau, ƙila ma sai dai ai min waya ace Baby ya sauka. ɗa zu da asuba ai ina tayi miki dariya ta window".

Fillo ma tayi dariyar ta ce,"hmmm aikin mijinki ne, haka kawai duk ya jigatar da ni da safa da marwa, ke kinji yanda ƙafafuna ke ciwo kuwa. ai ana kaiwa gobe sai dai kuga na kai kaina asibiti sun yanka ni sun ciro muku yaran ku".

"da kanki ma za ki haihu insha'Allah, bari na tafi sai na dawo".

"to a dawo lafiya, ki yiwa Mamin sannu don Allah".

motar Ilham ta bar compound É—in gidan, ita kuma Fillo ta shige part É—in ta.
a ɗaki ta sami Turaki zaune yana rubutu a takarda, tun safe yake aikin rubuce rubucen office, tayi wurgi da hijab ɗin jikinta akan gado, kafin ta nemi waje ta zauna ta miƙe ƙafafu.

"Jannaty please come and massage my legs, Allah ciwo suke min sosai".

ya ɗago ya ɗora idanuwansa akanta, matuƙar tausayinta ya kama shi, in ace yana da ikon da zai fito mata da Babies ɗin nan babu abin da zai yi masa shamaki da hakan, ya ƙagu ta haihu haka ko don ta huta.
ya tattara takardun a gefe tukunna ya taso, kafin ya zauna a gabanta ta dakatar da shi da faÉ—in,"sorry ba ni riyon kayan su Maama".

ya ce,"me kuma za kiyi da shi?".
tayi masa wani kallo kafin tace,"kaji min mutum, me ake yi da gyara?, yau tun tashina ban gyara musu ba".

sai yay zamansa kawai, ta ɓata rai tana faɗin,"zan yi maka kuka". ta faɗa a shagwaɓe.
ya ɗago ido ya kalleta, sarai ya san zata aikata hakan, don haka ya miƙe yaje ya ɗauko ƙaton riyon da ke ɗauke da uban kayan Babies a ciki, ya ajiye zai zauna ta ƙara dakatar da shi.

"diary ɗi na". ya rufe ido tare da karyar da kai, zai yi magana tayi kalar tausayi tana haɗa hannayenta ta ce,"yi haƙuri Baban Ƴan biyu, ai don Allah nace".

sai da ya lakuce mata kumatu kafin ya fita ya bar É—akinsa zuwa nata É—akin, san da ya dawo tana waya da BoÉ—ejo wacca ta kira tana tambayar lafiyar jikin nata.
ya zauna kawai ya shiga matsa mata ƙafafun, yana tsokanarta da lukutar gombe, bayan sun gama wayar da Boɗejo ta harare shi tare da fizgar diary ɗin tace,"ka duba min sirrina ko?".

"oho ke kika sani, ni me zan duba acikin diary ɗin da ake ɓoyewa kamar ana ƙulla munafurci a cikinsa, to ta ina ma zan iya gane watsaltsalun rubutun lukutar Gombe?, rubutun da ba iyawa aka yi ba".

dariya tasa Fillo dakatawa daga rubutun data fara,"oho dai duk abin mutum ba zai ga me ke ciki ba, ah tou! sirinmu ne ni da Æ´aÆ´ana"

"sirri ko munafurci?, yara tun basu zo duniya ba an fara koya musu hali mara kyau, ni dai gaskiya nake faÉ—a miki ki sauya hali, wannan ba halin zama mother ba ne".

ta ƙara yin dariya,"magana ce bata isheka ba sarkin ƴan sa ido, sirrin uwa da ƴaƴa ne dai ba zaka gani ba".

ta faɗa tana yi masa gwalo, sai ya sakar mata ƙafa suka shiga kokawa akan sai ya karɓi diary ɗin, ta ƙwalla ƙara babu shiri ya ƙyaleta yana aikin zaro ido da jera mata tambayoyi a hargitse.

"menene ya faru Angel?, na bige miki wani wajen ne?".

ta kashe masa ido É—aya da cewa,"kasan idan baka daina takura min ba zan kaiwa Ilham jinginar ka, ka kwana dubu saba'in baka ganni ba".

"Allah ya baki haƙuri yallaɓiya ranki shi daɗe me girma uwar gida, da ki hora ni da rashin ganinki ai gwara ki zane min ɗuwawu na kasa zama, rashin ganinki ai azaba ne a gare ni".

"idan na mutu fa?".
sai ya ɗago yana kallon fuskarta da ta ƙara kyau yace,"ban hana ki yi min zancen mutuwa akan ki ba".

"Allah ya baka haƙuri ranka ya daɗe".
ta faÉ—a da murmushi a fuskarta.
bayan ta gama gyaran kayan Babies ɗin take ba shi labarin irin satar kayan da akayi ranar zaman sadaƙar bakwai ɗin Hajiya Madina.

"Daddyn Maama ka san me?, ina sabon less É—in da na É—auki zaninsa nace za'a É—inkawa little Maama riga da shi?, to wallahi har da shi aka É—auke, daga in É—auko in ajiye kan gadon Mum in shiga toilet, ai kuwa na jera Allah ya isa babu adadi, saboda les É—in nan Maama na sonsa".

yace,"Allah ya kyauta, rashin tsoron Allah ne duk yake saka sata a gidan mutuwa, Allah ya shirya masu yi kawai".

ta amsa da amin kafin ya kamata ta yunƙura su miƙe tare, toilet suka shiga domin yin wanka, acikin banɗakin sai da aka ɓata tsawon awa guda ana shan soyayya, sannan suka fito suna dariya, ita tana faɗin idan ya ɗauketa a yanda take yanzu ƙasusuwansa duk sai sun ɓalle, yayin da shi kuma ke faɗin ya sani, hannun lukutar gombe tsaf zai ɓalla shi ya ɓalle gaba ɗayansa..

kamar kullum yauma suka shirya kansu, ita ta saka wata ƙatuwar bubu da ta ɗauka acikin kayan Maama, kuma rigar sai tayi mata kyau sosai, saboda girman cikin jikinta sai awon yayi daidai da ita.
"amma dai ba zaka jima ba ko?".

amon muryarta ya fito a lokacin da take ɓalle masa maɓallin rigarsa.
ya ce,"No yanzu zan dawo babu jimawa, takardun nan kawai zan kaiwa Khaleel, don't be lonely, am always with you, ina cikin nan".

ya faɗa yana pointing saitin zuciyarta. tayi wani kalar murmushi tana kamo fuskarsa cikin tafukan hannunta biyu ta ce,"ina sonka mijina, ina ƙaunarka".

"ni ma ina yi miki tsananin so matata, Allah yayi miki albarka, yasa ki haihu da ranki da lafiyarki".

"amin amin Daddyn little Maama".
furuncin nata ya saka shi yin murmushi me faɗi, tare da duƙawa ya ɗage rigar jikinta ya yiwa cikin kiss, sannan ya ɗago suka yi kissing juna.

da ƙyar ya iya sakinta yaje yana tattara takardun cikin sauri, ita kuma tana bashi labarin cewa,"Jannaty ka san me?".

ba tare da ya juyo ba yace,"ban san may ba sai dai june".
Chapter 167 · 0% Book details