← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 176

Sashe 12

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba tare da ta kalli Turaki ba tace,"mun gama magana da Baffa, shima ya amince da hakan, so i do not want to hear anything different... ina ce dama saboda kuɗi kake musu aikin ko?, to mahaifinka ya tara maka arziƙin da har jikokinka ba zasu yi talauci ba, no need of any job, ka zauna a gida kamar mace, kaci ka sha ka kwanta...bautar company ta ƙare, dan ba zan yarda kaci gaba da yi musu aiki ba su na neman hanyar da zasu kashe min kai saboda kawai kana da gaskiya, ba zan lamunta ba...i won't let anyone kill my son come what may!, aikin ai ba dole ba ne, ko da ace bamu da cin yau balle na gobe, rayuwarka da lafiyarka ta fiye min wannan tsinannan company ɗin".

Ba shi da ta cewa a yanzu, dole ne zai yi shiru har zuwa sanda zata sakko ta huce before yay Comprehending nata. bai san reason ɗin da ya sa ta ke tunanin accident ɗinsa yana da alaƙa da wasu ke son ganin bayansa ba.

"hannun da sauƙi?". Ta tambaye shi tana kallonsa with so much Sympathising na uwa.

Ya amsa,"ehh sosai ma".

"Allah ya ƙara maka lafiya...tsakanina da wanda ya nemi ya cutar da kai kuma Allah ya isa ban yafe ba, tunda ba wani ya haifa min kai ba".

Shi dai bai ce komai ba, ta kalli dining ta kalli Nihal da ta shigo tace,"ki zubo pepper soup".

ta wuce dining ta zubo ta kawo mata, ta karɓa sannan ta miƙe ta isa kujerar da Turaki yake, ta kalli mug ɗin da yake aje kan table ɗin gabansa tace,"yaushe kasha wannan?".

Yace,"ina gama sha kina shigowa".

bata ce komai ba ta ɗebo ppper soup acikin spoon ta kai bakinsa, ba son ci yake ba sam amma babu yanda ya iya haka yay ta karɓa har sai da ya cinye tas, tana tambayarsa ko zai ƙara yay saurin cewa,"a'a".

kansa ya kwantar jikin kujerar ya lumshe ido, Hajiya Madina na waya da wani Asp akan Case ɗin accident da Turaki yayi har 2times, cikin idanuwan Turaki kuwa hoton yanda yay accident ɗin ke haska masa, abunda ya ɗaure masa kai, the samething da wancan, ko da yake gwara wancan yaga motar da ke binsa a baya wadda ya tabbatar da attacking nasa ta ke son yi, Amma wannan kam kawai ji yayi burki ya tsinke masa, kuma before he notice anything stearing ya ƙwace daga hannunsa, kamin ganinsa ya ɗauke gaba ɗaya yana tunawa da motarsa ce ɗaya akan titin sai farar motar da ta duki tashi ya ƙarasa gangarawa bakin bishiya, wanda sanadin buguwar kansa da glass kenan kuma sai farkawa yay ya gansa a hospital.

Fatansa ɗaya Allah yasa motar da ta buge shi mutanen ciki basu sami matsala ba, saboda ba laifinsu ba ne, shi ne wajen yayi ƙoƙarin kama stearing ya shiga gaban motar ita kuma tayi saurin kaucewa. Amma Maama ta dage kan motar na sa ne ta hankaɗa shi.

yamma liƙis Boɗejo ta shigo parlon, babu kowa, tayi tsaki ta nufi hanyar stairs tana mita. Akan wanne dalili ne ma su duka zasu yashe su wani haura sama after all sun san hawa saman wahala yake yi ma ta.
Ƙofar bedroom nasa a buɗe yake, daga bakin ƙofar ta tsaya tana kallon ikon Allah, sai kace wani gwal ko tauraro, yana zaune kan gado sun wani baibaye shi, basu san da zuwanta ba sai da ta shiga ta zauna kan stool ɗin da ke fuskantarsa.

tace,"wai baka ji sauƙi ba ne har yanzu?, mutum sai kace mace".

murmushi yayi bai ce mata komai ba. ta ɗan harare shi tace,"ashe an kwance maka ƙaton rawanin?".

Samha tace,"rawani kuma?".

tace,"ehh ko za kice min ba haka bane, wadda ba zan faÉ—i ra'ayina ba sai dai nata".

Samha tace,"yo ni wani abu nace BoÉ—ejo, gyara ne fa kawai nake miki...idan wani yaji sai yay zaton rawanin sarauta kike nufi, alhalin ba haka bane...mene haÉ—in bandage da rawani fisabilillah?".

BoÉ—ejo tace,"to banga damar cewa bandage É—in ba...ina ce ba da ke nake maganata ba".

Samha bata ce komai ba, Turaki yace,"wai babu wani maganin da akeyi ne irin wannan ciwon ya warke kusa?".

Boɗejo tace,"lokacin da muka sameka a asibiti rai a hannun Allah ban bada shawara ba ne?, kaje ka tambayi ita Madinar, sai da nace a kira Waziri ya saka maka hannu a gocewar ƙashin nan sai ce tayi inaa ita ba haka ba, gwara asibiti suyi hoto su gano matsalar, yo ni kuwa me zan ƙara cewa wanda ya wuce nayi shiru tunda bani na haifa ba".

Turaki yay shiru, ta ƙara cewa,"ƙarafun da asibitin suka danneka da su ba suyi tasiri ba ne da kake neman wani magani na daban?".

Yace,"sunyi mana, naji sauƙi fa kawai dai ba yanda ya kamata ba...kafaɗar ce bana iya motsata".

tace,"ba sauƙin kenan, ni ai sai dai nace Allah baka lafiya, amma ba dai bada shawarar inda ya kamata akai ka a sama maka lafiya ba, ko kuma maganin da zaka sha...tunda ita Madinar ta ɗauki dukkan yardarta ta ɗora akan bature, yo bature ko gaibu".

Zaytuna tace,"BoÉ—ejo asibiti ai ba gaibu bane, yama fi saurin taimakawa lalura".

BoÉ—ejo tace,"to ko na asibitin ko na gidan duk wanda akayi ni dai fatana Allah ya ba shi lafiya".

Sai kuma ta kalli Turaki tace,"yo kai me ka yiwa mutane suke neman rayuwarka?, gaka dai da kyan hali kuma ni ban san dalili ba, Muhammadu ka faɗa min gaskiya ko dai kana aikata wani mugun abun a ɓoye bamu sa ni ba?".

Ya É—ago ido ya kalleta zai yi magana Hajiya Madina ta shigo É—akin, a cikin wayar da ke kare a kunnenta cikin tsawa tace,"just do as i said! thats all, i don't want that your blabaring".

ta ƙarasa bedside drower ta zauna tana dire wayar da ta katse a gefen Turaki, tasa hannu ta ɗan matsa kafaɗar Turakin, yay saurin rumtse ido tare da yin,"ashhhh". Ya faɗa cikin dauriyar zafin ciwon da yaji.

"still dai?". ta tambaya. Shi kuma ya É—aga ma ta kai.

Hajiya Madina tace da Boɗejo,"babu wani mugun abu da yake aikatawa, gaskiyarsa ce tayi yawa, saboda yaƙi bada haɗin kai akan wani cuta da mutanen da ke son haɗa partnership da company nasu, bcox hakan zai jawa company ɗin asara babba. shine yasa suke so su kashe shi dan samun biyan buƙatarsu".

Baki buɗe Boɗejo ke sauraronta, tana yin shiru tace,"yo ina dalili anan, wallahi sai ya bar musu aikinsu babu dole, dama kai ka ɗorawa kanka ba ce akayi dan kayi karatu dole kaci ribarsa ba, an tara an ajiye muku, ba ku kaɗai ba har ƴan gabanku, to mene kuma na cewar sai anyi aiki a ƙarƙashin wani?, ina su waye masu bibiyar rayuwar taka?".

"BoÉ—ejo ai zar...". Hajiya Madina ta dakar da shi daga abunda zai ce. tace da BoÉ—ejo,"zasu shigo hannu ne tunda Æ´an sanda na kan bincikensu".

Boɗejon tace,"dole ma a binciko ko su waye, dan babu wanda zai yi kasadar shiga rayuwar jinin Sarki Sulaiman Dukko bai fuskanci tsatstsauran hukunci ba...ɗan babban alƙali kuma jikan sarki, a nemi aga bayanka sannan a zuba ido, hakan ba mai yiwuwa bane...aiki kuma ka barshi har gaban abadan".

Hajiya Madina tace,"abun da nace nima kenan, to matsalar yana jin sauƙi abin da ya faɗawa uban akai za'a zauna".

Baɗejo ta muskuta tace,"ina ce ai na isa ko?, to bari Dukkon ya dawo ya sameni...wallahi sai dai idan bana numfashi amma wannan aiki dai ba zaka koma shi ba, can suje su ƙarata da duk irin asaran da zasu yi, ai ma'aikatar bata ubanka bace balle asarar ta shafeka".

Hajiya Madina ta jinjina da kai da jin daÉ—in hukuncin BoÉ—ejon. sai dai jin sabon furucinta shi yay saurin dakatar da ita daga shafa masa magani da ta ke yi.

"aure ma zaka yi, ka wartsake kaje ka nemo matar aure ka kawo mana, cikin ƙaramin lokaci ba da daɗewa ba, abun yayi yawa ace kamarka baka da aure, ga mata da yawa nan a dangi, Allah dai ya baka lafiya".

Shirun Boɗejon ya haɗe da walƙiyar wani haske a idon Hajiya Madina, hoton abubuwa da dama suka bayyana acikin hasken. Ta san dai tayi ƙasa da idonta, amma bata san lokacin da murfin idonta ya rufe ya buɗe ba, wucewar sakan 1,2,3, wani abu da ita kaɗai ta barwa kanta sa ni ya dira a tsakiyar zuciyarta.

Da daddare Baffa yana dawowa Boɗejo ta same shi da kanta a ɓangarensa, tace zuwa tayi ta faɗa masa Muhammadu ya bar zuwa aikin da yake yi acan Habuja, Baffa da yaso yayi ƙoƙarin fahimtar da ita akan hakan ma da ke faruwa da shi hanya ce ta matakin nasara a rayuwa, kuma ai mutanen ba zasu taɓa samun nasara ba tunda Allah na tare da mai gaskiya a ko yaushe. tace ita dai indai ta isa Muhammadu ya daina zuwa aikin can tunda ba aljanna ake rabawa a wurin aikin ba.

****
*8:00am.*

Fillo na zaune a uwar ɗaki da ƙur'ani a hannunta tana karatun suratul yasin, taji daɗin jikinta sosai tun aduar da Amir yay ma wancan ranar, da ya je gida haka ya jido mata ruwan adu'oi daga wurin mahaifinsa ya kawo mata, ruwan adu'ar da suka zama na shanta yanzu, shi yasa yanzu sumul ƙalau ta ke jinta kamar bata yi wani ciwo ba.

ta rufe qur'anin da ta kai ƙarshen sura, ta tashi ta koma kan katifarsu ta kwanta, idonta na kallon rufin ɗakin.
tasa hannu tana shafa kusa da ita wurin kwanciyar Kaka, ji kawai tayi ruwan hawaye ya cika idanuwanta ba tare da ta san da zuwansu ba.

tun ƙarfe shida da rabi Kakan ta fita aiki cikin gida, ita ba wai fitar sassafen bace ke damunta, tunda a nan ɓangaren ma ƙarfe shida suke fita, to amma ai anan tana ganin gimlawarta da jin muryarta, amma can idan ta tafi sai dare zata ƙara ganinta.
Chapter 12 · 0% Book details