Sashe 111
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
saboda manyan yayyansa da ke can taraba dole aka fasa kaisa a ranar akace a bari sai gobe, a washegari da safe kuwa ƙarfe takwas na safe gida ya cika maƙil da ƴan'uwan Hayyo maza da mata, lokacin har anyi masa wanka jira ake babban wansu yazo ai masa sallah.
lokacin da aka ɗauko gawar Hayyo za'a fita da ita a lokacinne mutane da dama da basu sami damar kuka ba suka saki nasu, saboda bala'in tausayin Fullo wacce ke ta kuka tana kiran a bar mata Abbanta dan Allah, sai da ƙyar Ammi ta iya ruƙota Hajiya Madina ta ƙwace hannunta daga kan makarar da ta yiwa mugun riƙo, sannan ne aka samu aka fita da gawar Hayyo daga parlon, kuma lokacinne Fullo ta yanke jiki ta faɗi bayan ta ƙwalla wata razananniyar ƙara da ta amsakuwa a gidan gaba ɗaya.
aljanun da ba'a santa da su ba suka tashi....
*Vote, Comment and Share.*
[9/3, 19:37] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*43*
*Taraba Satate, Wurkum district, Late Alhaji Aminu BarkinÉ—o Residence.*
tafkeken gida ne me irin ginin gidan sarauta, sai dai ginin irin na zamanin da ne bana yanzu ba, but an ɗan sabunta shi ba kamar yanda yake ainihinsa ba. ƙofar gidan na marigayi tsohon Hakimin Wurkum danƙare yake da jama'a kace ɗaurin auren wani babban mutum ake ko kuma za'a ƙara yin naɗin sarauta ne.
daga cikin rumfar tempol ɗin da akayi, Maudo ne zaune akan kujera yasha rawani yana amsar ta'aziyya daga bakunan mutane da dama, shi ne Babban ɗa a wurin marigayi Alhaji Aminu Barkinɗo, kuma shine wanda ya zauna a hannun mahaifiyar Hayyo a lokacin da ta na raye, domin shi tasa mahaifiyar ta rasu, kuma tun bayan rasuwar mahaifin nasu ya maye gurbin kujerar tasa har zuwa wannan ƙarni da muke ciki.
daga cikin gidan, ɗumbin mutane ne ƴan gaisuwa ke ta hada-hadar shige da fice a ƙaton tsarkargidan da yay kusan filoti biyu, kana kallon yanda aka kakkasa ɓangare ɓangare zaka san family house ne.
wata farar tsohuwa tukuf ta fito daga wani ɗaki tana dogara sanda, sai da suka ƙaraso tsakiyan tsakar gidan sannan ta tsaya tana kallon mai yi mata hidima wadda ke biye da ita a baya tun fitowarta, hannunta riƙe da ƙwaryar fura babba, ita ɗaya ta rage acikin matan Alhaji Aminu Barkinɗo, cikin su uku da ya aura ita ɗaya tayi tsawo rai haka.
cikin yaren fulatanci tace da Hadimar,"ki nemo Gaji ki basa furan ya kaiwa Dottijo, tun ɗazu ya aiko Manga kuma ba'a samu an kai masa ba, kuma ƙila zai sha tare da baƙi ne, yi maza du Allah".
Hadimar ta wuce da sauri tabi dogon soron da zai kai ka wani babban fili kafin ka fita zuwa waje.
Dada ta waiga tana kallon masu fitowa daga ɓangaren Hakimi, ta ƙwala kiran,"Munyoɗo".
sai da ta kira sau biyu tukunna wata farar dattijuwa ta fito da sauri tana amsawa, tazo gabanta ta rissina tana faɗin,"Dada gani, lafiya kika fito ke ɗaya?, kuma kin tsaya ai a rana, me kike da buƙata?, ina Petel din?".
tayi maganar tana kamata ta matsar da ita daga cikin ranar.
ta kalleta ta cikin glass É—inta tace,"ina wannan shike, amnn mata na wurin Hayyo?".
MunyoÉ—o tace,"wacce daga ciki Dada?".
Dada ta ɗan ɓata fuska da muryar ƙorafi tace,"wannan yaro dai Allah ya jiƙan shi kawai, du yaje ya haɗo mata da yawa in ka tashi neman ɗaya sai kayi ta faman kwatance".
tayi tsaki sai kuma tace,"wasu sun ƙara zuwa ne?".
MunyoÉ—o tace,"ai Dada jiya duk sun gama zuwa, su bakwai ne yanzu sauran huÉ—un ance sun rasu, suna babban parlo yanzu haka".
Dada ta girgiza kai alamar Allah ya kyauta sannan tace,"to wannan Balarabiyar za ki kirawo min".
MunyoÉ—o tace,"tom Dada bari na duba".
ta faɗa tana juyawa ta nufi ɓangaren da yake nanne na mahaifiyar Hayyo, ta shiga babban parlon da ya tara ƴan zaman makoki, ta dinƙa wuce su har ta ƙetara inda Ammi da Ummi suke zaune tace da Ummi,"Dada tana kiranki".
Ummi ta amsa da to tana yunƙurawa ta miƙe, Ammi ma ta miƙe tana faɗin,"kin san Allah na sha'afa gaba ɗaya Dada tana nemana".
tare suka fito gaba ɗaya, suka tadda har an ajiyewa Dada kujera ta zauna akai, suna zuwa ta ɗaga sandar hannunta ta bugawa Ammi, Ammi ta kauce tana faɗin,"kiyi haƙuri baƙi ne suka tsayar da ni".
Dada ta harareta ta cikin glass bata ce mata komai ba, ta mayar da dubanta ga Ummi da ke tsugune a gabanta tace mata,"kije ki sako mayafinki mu wuce asibiti, ance tun shekaranjiya baki koma wurin yarinyar nan ba, ban sani ba ko isashshen hankali ne baki da shi".
Ummi ta miƙe cikin sanyi jiki ta wuce, Dada ta kalla Ammi tace,"kije ɓangaren Giɗaɗo kice da matarsa ta bayar da ferfesun kaji da nace ayi, na santa da ɗan banzan cin yajin jaraba, idan ta san yayi yaji da yawa to ta zubar da shi ba mayu ne zasu sha ba, ta ɗora sabo na mara lafiya ne".
har Ammi ta wuce sai kuma ta ƙara tsayar da ita,"kice da Belɗo ya fito da mota zai kai ni asibiti, yace da Safara'u taje ta haɗa min kayana a kawo min yau can ina kwana".
tana tafiya sai ga wata hadima daga bangaren Modibbo ta fito, tayo wurin Dada da sauri tana zubewa tare da cewa,"Allah juttin balɗe ma, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana Dada, da akwai abunda kike buƙata ne ayi miki cikin gaggawa?".
Dada ta dubeta tace,"a'a bana buƙatar komai".
Hadimar bata tashi ba ta cire takalmanta ta zauna akai ta shiga matsa ƙafafun Dada. lokacin maƙwabtansu suka shigo, da girmamawa matar ta tsuguna tana gaida Dada tare da ƙara yi mata ta'aziyya, Dadan ta amsa tana yi mata godiya sosai. matar tace mata tare da mijinta suke, Dada tace taje ta shigo da shi,ba jimawa sai gasu tare, suka gaisa da Dada wadda ke ta sanya masa albarka.
"Dada wajen kuma da zafin rana da kin koma daga ciki".
tace da shi,"zanje dubo yaron Hayyo ne, zafin mutuwar uban ya taɓata shi yana can asibiti kwance rai hannun Allah, Belɗo nake jira yanzu zai fito".
daga nan suka yi mata sallama suka wuce.
a ƙofar gida sanda su Ummi suka fito zasu tafi motar su Hajiya Ramla tayi parking, tun ranar ɗaya da suka zo suka koma sai yau suka dawo, Ummi ta ƙarasa wajensu tana yi musu barka da zuwa, su kuma suna ƙara yi mata ta'aziyya, Ummi tayi musu godiya sosai da sosai akan irin kyatatawarsu gare su.
Hajiya Madina da damuwa a tare da ita tace da Ummi,"to ya jikin Fillon?". Ummi tace,"Alhamdulillahi da sauƙi, yanzu ma can zamu je, wataƙila ma dai zuwa dare su sallamota".
Hajiya Madina ta kalla Hajiya Ramla tace,"to ko ni na bisu ne?".
Hajiya Ramla tace,"ah ki dai bari mu shiga muyi gaisuwan, idan muka fito tafiya sai mu biya ta can É—in ko".
Hajiya Madina tace,"to shikenan". sai kuma tace da Ummi,"Me Babban suna yana nan É—in ko yana can asibitin?".
Ummi tace mata,"acan asibitin yake kwana ai, ya hana kansa natsuwa kwata-kwata, jiya ma nayi ta fama da shi kan ya dawo gida ya huta yace min to, sai bayan su LamiÉ—o sun dawo suke ce min yana can É—in dai bai tafi ba, dan Allah Hajiya ku wuce da shi yau É—in ya samu yaje ya huta shima".
Hajiya Madina tayi É—an jimm kamin tace,"to bari dai muga yanda za'ai, sai kun dawo".
Ummi ta kira wani cikin jikokin gidan tace yaywa su Hajiya Ramla iso zuwa wajen Dadda wadda itace matar Maudo babban yayan su Hayyo hakimin yanzu kenan.
direct Taraba State Specialist Hospital motar su Dada ta nufa, a reception su Ummi suka tadda Kaka ita da ƙannan Hayyo da suke uba ɗaya su biyar, tare suka wuce ward ɗin da aka kwantar da Fullo, suna tafe Dada nata ƙorafin asibitin basu iya aikin komai ba, ace mutum kwanansa biyu yau amma shiru jiki babu sauƙin arziƙi, to ita dai idan jikarta bata sami lafiya yau ba to gobe ƙasar waje za'a fitar da ita ƙwararrun likita su dubata.
Belɗo dai sai bata haƙuri yake yana tayi shiru kar likitocin suji, in suka ji ba zasu ji daɗi ba, tayi masa banza bata saurare shi ba har suka iso room ɗin da Fullo ke kwance.
Ummi ta dakata daga ƙofar room ɗin bata shiga ba saboda nauyin sirikinta da take ji, tunda taga su Kaka a reception ta san shine zaune a wurinta.
Turaki ya miƙe cikin sauri daga gefen gadon a sanda su Dada suka shiga room ɗin, ba shi yake cutar ba amma kallo ɗaya zaka masa ka hango bala'in ramar da yayi, ga damuwa kamar a lakuta a fuskarsa, ya matsa daga gefen gadon yana yi musu sannu da zuwa.
Dada ta kallesa ta girgiza kai saboda tausayinsa tace,"sannu namijin ƙwarai, Allah ya baka ladan kulawa da matarka, ka kwantar da hankalinka zata sami lafiya insha'Allahu".
ya kalli Fullo da ke ta bacci sannan yay ƙasa da kansa kamar zai yi kuka yace,"Allah ya amince".
Kaka na kallonsa tace,"Me Babban suna ko zaka je gida kai wanka ka samu ka É—an huta, rabonka da abinci ma tunda jiya da rana, dan Allah kaje kaci tunda likitan yace gobe da safe zasu sallame mu".
da damuwa tsantsa a muryarsa yace,"Kaka ina so naga ta farka ne tukunna".
Kaka ta gyaɗa kanta tace,"to Allah ya farkar da ita cikin ƙoshin lafiya".
Dada ta zauna kan kujera tana fuskantar Fullo cike da jin tausayin yarinyar, sai adu'a take tayi mata a sanda ta kama hannunta ta riƙe, ta zaro wani diamond ring daga yatsanta ta saka ma Fullo, kuma sai ya zama kamar dama na Fillon ne, yay cif a yatsan nata.
kamar zata yi kuka ta dubi Kaka tace,"se yaushe ne zai farka ni kam?".
Kaka ta kalli Turaki shi kuma ya kalli agogon hannunsa sannan yace,"nan da awa É—aya insha'Allahu".
Dada ta dubi Hadimar da ke ta shigo da kayan abinci tana ajiyewa tace,"Uwar wannan yarinya shina waje ko?".
Hadimar tace,"ehh ranki ya daÉ—e".