← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 176

Sashe 31

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta duƙa ta karɓa suna yi masa adu'a, sannan Yaya tayi musu adua suka tafi. fitarsu babu jimawa mai gidan Yayi sallama, sallamar da ta hassada faɗuwar gaba a zuciyarsu Hamid.
"Shema'u! Shema'u". kiran da me gidan keta ƙwalawa kenan, Yaya ta miƙe jiki a sanyaye ta fita tana cewa,"sannu da zuwa".

yay mata wani banzan kallo yana zuƙar tabar dake hannunsa sannan yace,"sai yanzu kika ji kiran nawa ko amsawar ce ba ki ga damar yi ba?".

bai jira cewarta ba ya ɗora da faɗin,"mutuniyar banza da wofi kawai, to ki gama rashin mutuncinki wallah idan banga dama ba aljannah dai ba za ki shigeta ba, tunda a ƙasan ƙafata aljannar taki take, kuma har saina ɗaga miki za ki shiga...kuma indai don ta ni ne na rantse sai da ki zama ƴar kallo, kina ganin mata na tururuwar shiga ke kina daga gefe can".

*Pls Vote, Comment and Share.*
[8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

*17*
Yaya dai tayi shiru bata tankawa maganarsa ba, idan ma tace zata basa haƙuri wani sabon cin mutuncinne zai biyo ba, to shirun shi yafi alkhairi, but down deep in to her heart zafi ta ke ji, wannan halin na mijinta bata so, ƙaddara dai ta riga fata, ta ɗauki aurenta da Hayyo matsayin wata jarabawa daga ubangiji, kuma tana roƙon Allah ya bata ikon cinyewa.

ta mayar da tarin ƙwallar da ta cika idanunta. ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ɗago ta kallesa tace,"a ɗauko maka abinci?".

Hayyo yayi mata wani kallon banza yace,"mayya kawai wadda kare ya cinye zuciyarta, indai haƙuri ne naga Halima ma, dan haka kema muna nan wannan kafirin haƙurin naki zai kaiki maƙurar da za ki bar gidan nan da ƙafafunki. yo guda nawa kuma akayi?, saki dai kike so saboda ki tafi da hujja to ni ba zan sakeki ba dan bana yinsa, musulmin ƙwarai ne ni sam bana son al'arashin ubangiji ya girgiza".

Yaya ta girgiza kai kawai tana me cike da takaici, ita kanta ta sa ni haƙuri yayi kaɗan ya barka ka zauna da Hayyo, sai dai darajar ƴaƴa, tun bayan aurenta da shi daya sami biyan buƙatar kansa ya fito mata da asalin halinsa wanda yake ɓoyewa a lokacin aure, ta kuma san asalin waye shi wanda yake ɓoyewa idan yaje neman aure.

tunda ta haihu ta bar zamansa ta koma zaman ƴaƴanta, ba zata iya tafiya ta bar ƴaƴanta a wurin uban da bai san darajar ƴaƴa ba sam, ba zata iya tafiya ta bar ƴaƴanta su gantale ba, gwara ko Hayyo zai kasheta ta zauna ta kula da su, ko da ace sai dinga gutsirar naman jikinta ne, zatai ta haƙuri tana jurewa har Allah ya raya mata yaranta ta aurar da su, daga lokacin sai ta tafi ta bar masa gidan, ta bar masa Yasir tunda shi namiji ne, kuma tasan zai sami kulawa a wurin Yayansa Abdulhamid.

Hayyo ya zuƙi sigarin hannunsa ya feso mata hayaƙin yace,"a fito min da tabarma". ta juya cikin parlon tana sa hannu ta goge hawayenta. Hamid na zaune ya kasa ƙarasa cin abincinsa saboda baƙin cikin da takaicin rashin kyan hali na mahaifinsa, ya kalli Yaya da tsananin tausayi, ya sauke ajiyar zuciya yana tuno da tasu mahaifiyar, itama haka tasha fama, dan zai iya cewa ma har yanzu Yaya bata ɗanɗani baƙar kuɗar da tasa mahaifiyar tasha ba a wurin Babansa.

adu'a yake kullum, kuma yasan adu'arsu ta karɓu, lokaci kawai zasu jira sai dai idan ba'a raye, but dole-dole za'a zo time ɗin da mahaifinsu most regret all his past, lokacin da Allah ya shirye shi kenan.
ya miƙe tsaye jiki a saɓule ya karɓi tabarmar da Yaya ta ɗauko, yana kallon yanda hawaye ke bin kuncinta zuciyarsa na tsinkewa. muryarsa can ƙasa gudun kar Hayyo ya jiyo shi yace da ita.

"Yaya dan Allah ki bar kuka, komai lokaci ne kuma komai yana zama tarihi...kin san abinda zai kuma biyo baya idan yaga kina wannan kukan". ya faÉ—a tare da goge mata hawayen.

tace da shi,"na gode Hamid".

yace,"abincin nasa na kitchen ko?". ta É—aga masa kai,"ehh yana ciki, cikin wannan filas É—in daka siyo mana da azumi".
Abdulhamid ya fice hannunsa riƙe da tabarmar. Hayyo na jingine da jikin bango yana ta zuƙar tabarsa cikin ƙwarancewa da jin daɗi.

Hamid ya shimfiÉ—a masa tabar, Hayyo ya zauna har lokacin bai ko kalli Hamid ba.
"sannu da dawowa Abba".

kamar yanda ya tsammata dama babu amsa, dan shi zai iya cewa rabon da magana ta haɗasu da mahafin nasa tun azumi wata biyu kenan, haka ɗaya babu siɗi ba saɗaɗa, ko ya gaishe shi baya amsawa, hakana duk maganar da zai yi masa ba zai tanka masa ba. dan haka ya miƙe jiki a saɓule ya nufa soro inda ɗakinsa yake, ya ɗauko ƴar ƙaramar radio sabuwa ya dawo ya durƙusa gaban Hayyo.

ya kamo gidan radiyon daya san nan ne zaɓin Hayyo, ya ajiye a kusa da shi. lokacin kuwa ana labaran siyasa, cikin ran Hayyo yaji daɗi sosai, dan shi a rayuwarsa daka masa kyautar kuɗi ma gwara ka basa radiyo, tana saka shi nishaɗi musamman idan labaran siyasa ake. amma ba zai taɓa nunawa Hamid yaji daɗi ba balle ma har wata adua ko godiya ta shiga tsakaninsu.

jiya da shekaranjiya da bai saurara shirye-shiryen da yake ji ba duk jinsa yayi kamar mara lafiya, saboda tsohuwar radiyonsa taɓaci tun ranar da akayi wani mamakon ruwan sama, ta shige cikin ruwan daya cika ɗakinsa dalilin zubar da yayi. kuma babu kuɗi hannunsa dalilin ma da har ya ɗau wannan kwanakin babu ita.

kuma yasan Hamid ya siyo radiyon ne saboda shi, tunda akan ƴan ƙanan yaran ya sauke ɓacin ransa na lalacewar rediyon, dan duk sai daya bi ya zane yaran, ko yau da safe da zai fita yaga shatin wayar daya tsulawa Maimuna a fuska bai baje ba, amma bai ko bi ta kanta ba tunda ƴaƴa ne da basa gabansa, su rayu ko su mutu babu abinda yay masa zafi, haka suyi lafiya ko rashinta ko a gefen yatsansa.

ai yasha faɗawa ƴaƴansa da ku da shegu ɗaya na ɗauke ku, shi yasa bana wani ganinku da ƙima. zai fi muku ma ku nemi wani uban ko kwa ɗanji daɗi, amma a hakan dai Hamid yace masa a hakan kuma muke ƙaunarka Abba, muke alfahari da kai, duk tsanani ba zamu taɓa barinka ba, kuma zamu yi duk iyakar ƙoƙarinmu wajen ganin mun faranta maka, wajen ganin bamu saɓa maka ba. zamu maka biyayya, kuma zamu tsare mutuncinka.

acikin radiyon aka sako waƙar ɗan ƙwairo, Hayyo ya kama bin waƙar yana buɗe flask na abincin da Yaya ta aje masa. kamar wanda yaga kashi daya ga shinkafar, amma a haka ya cinyeta tas.

da yamma Yaran suka dawo daga makaranta, tunda sukai sallama suka ga Abban nasu a tsakargida suka kama raɓe-raɓe jikin bango. suna mugun tsoronsa, sunfi sakewa idan babu shi a gidan, idanma fita yayi sukan manta da shi. wataran Maimuna ta cewa Yaya ita gwara ma ace bata da Baba akan dai ta nuna Abba ace shine Babanta. a lokacin Yaya taita mata faɗa da cewar kata ƙara jin wannan zancen a bakinta, amma duk da haka Maimuna a makaranta bata amfani da sunansa, sai dai sunan Yayansu, Maimuna Abdulhamid haka ta ke using.

*VISION APARTMENTS, Zurich, Switzerland.*

a tsaye take a gaban windon parlon, windon dake É—auke da manya manya gilasai, kalarsa ta haÉ—e da yanayin yanda hasken garin yake a lokacin. lokacin yammaci ne, yanayin garin na nuna cewa ruwan sama bai jima da É—aukewa ba.
sanyin danshin ruwan na ratsowa ya shigowa cikin parlon, wanda ya gauraye da sanyin ac da kuma ƙamshin dake cikin parlon. hakan ya haɗu ya bada wani sanyayyan ƙamshi me daɗi, kalar komai na parlon ruwan toka ne.

sanye take da baƙin wando wanda ya ɗameta, hannayenta dake ɗauke da bangles acikin aljihun wandon, riga ce me ƙaramin hannu milk daga ciki sai ta ɗora rigar sanyi me kauri akai, irin rigar sanyin nan me gashi a hularta. hular ta rufe kusan rabin fuskarta. fara ce sosai, me kyan fuska, hancinta har baka, idanuwanta manya. jelar gashinta ta zagayo ta gefen wuyanta ta sauka akan kafaɗarta, hakan zai shaida maka kitso ne guda ɗaya tal a gashin nata.

kallon gilashin windon take tana ganin yacca sauran ruwan sama ke sauka akansa. sam ba haka taso ba, ba haka taso lamarin ya tafi ba, sai da ta rufe ido ta buÉ—e sannan tace.

"ba haka muka tsara ba, ba shirin da muka yi ba kenan. abunda muka tsara shine Turaki zai mutu a wannan ranar kuma a wannan lokacin cikin wannan dajin, lissafin da mukayi kenan, mun lissafa tarihinsa zai shuɗe ne cikin ƙanƙanan lokaci, zamu goge hotonsa da sunansa da duk wani abu daya dangance shi daga wannan zuciyoyin guda biyu...to amma me yasa komai ya rushe?, lissafin da mukai ya hargitse?".

da shi take magana, saurayin dake zaune akan kujera yana fuskantarta, fari ne shima, me kaurin jiki, me siririn saje. shekarunsa ba wasu masu yawa bane, ƙananun kaya ne jikinsa blue jeans and red t-shirt long slip, sai facing cap baƙa daya saka. tarin gashin girarsa ya kusa haɗewa, kallonta kawai yake tunda ta tsaya a gaban windon, har zuwa yanzu da take magana da shi.

"kina nufin laifina ne kenan?".
a zafafe ta juyo ta fuskance shi tana ɗage hular rigar sanyin ta koma baya ne. "ƙwarai laifinka ne, idan da ace ba lusaran mutane kaje ka samo ba me zai sa shirinmu ya ruguje?.". sai tayi shiru taja dogon tsaki sannan tace,"now what will happen next?".

har yanzu bai ɗauke ƙwayar idonsa a kanta ba, sai daya miƙe tsaye sannan yace,"shi zai kawo kansa garemu next ba sai mun wahalar da kanmu ba".
matashiyar budurwar tayi masa kallon baka da hankali sannan tace,"ta ya?". yay guntun murmushi yace,"rauninsa mana". tace,"like how?". ta faÉ—a fuskarta na nunawa da rashin fahimta.

"Mahaifiyarsa, Maama, Hajiya Madina. ita zamu ɗauke, ita ɗaya zamu ɓatar Turaki yazo garemu da kansa, da ƙafafuwansa ba'a mota ba, da wannan damar zamu yi amfani wajen ganin mun cimma burinmu akansa, burinmu kuma mafarkinmu na ganin baya raye".
Chapter 31 · 0% Book details