← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 176

Sashe 118

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba ta ƙarasa ba Turaki ya dakatar da ita a fusace,"ya ishe ki Boɗejo, zan lamunci duk kalar rashin mutunci amma banda cin zarafin iyayena a gaban idona. haba don Allah don Annabi, duk kin bi kin hana kowa kwanciyar hankali akan wata banza yarinya can, idan tafi ƙarfin a wulaƙantata me yasa kika na ce aka aurawa wanda ba ya sonta ba kuma zai taɓa sonta ba".

bai san lokacin da ɓacin rai ya kaisa ɗaga ɗan yatsa ya na nuna ta da shi ba. "kina cin darajar kin kawo mahaifina duniya ne shiyasa nake ɗaga miki ƙafa akan irin cin kashin da kike yiwa Maama da Mum, darajarsa kike ci nake yi miki duk kalar wata biyayya da girmamawa, banda haka wallahi da comon inuwarsu aka ce ki yiwa kallon banza ba za kiyi ba, da tun na farko da kika yi ba za ki so ki ƙara na biyu ba. saboda haka yau ta zama rana ta ƙarshe da za ki ƙara ɗaga muryarki akansu in ba haka ba zanyi abunda ban taɓa yi ba".

kai da ganin yanda yake maganar ka san ya fusata, kamar ma zai kaiwa Boɗejo hannu, Hajiya Madina ta kallesa ta sauke idonta ƙasa leɓenta na talewa da murmushi, alamun taji daɗin abinda yayi.
Hajiya Ramla tayi saurin miƙewa tana sauke hannunsa da yake nuna Boɗejo da shi,"me haka Babana?, kar fushi yasa ka aikata ba daidai ba, yi haƙuri komai yay farko ai zai yi ƙarshe...".

yana kallon Bodejo da ta saki baki tana kallonsa da tsananin mamaki ta taho gare shi yace,"ai komai ɗin ma yazo ƙarshe, ba zan iya ci gaba da ɗauka ba".

ya faɗa yana barin kusa da Mum ya ƙarasa gaban Boɗejo kafin ta iso gare shi, ya miƙa mata farar takardar da ke hannunsa yana cewa,"na gaji, na gaji da masifarki da neman tashin hankalinki, gaba ɗaya kin hana kowa sakat, to ina buƙatar Mum da Maama da Baffa su sami nutsuwa hankalinsu ya kwanta su huta da fitinarki, nima kuma ina da buƙatar nawa hankalin ya kwanta, ba cikakkiyar lafiya gare ni ba so ba za ki kwantar da ni ba".

ya manna mata takardar ajikinta. "ga shi nan ki samawa kowa lafiya".

Boɗejo tayi mutuwar tsaye ta kasa ko motsi, bin sa kawai ta-ke da ido, taji ƙirjinta na bugawa kafin ta iya ɗaukar takardar tana duddubawa, tayi masa kallon tsab sannan tace,"wannan kuma na menene?".

bai ce da ita komai ba ya nemi kujera ya zauna yana dafe kansa, Khalil ya shigo a lokacin tayi saurin dakatar da shi daga hawa upstairs da yake shirin yi.

"zo, zo nan Khalil".

ya dawo ya tsaya gabanta, ta miƙa masa takardar hannu na rawa,"duba min mene aka rubuta a ciki".

ya warware takardar, kalmar NI da ya fara cin karo da ita tasa shi É—ago ido ya kalli Mum sannan ya kalli Maama sannan ya juya bayansa ya kalla Turaki.

BoÉ—ejo ta doke shi,"na ce ka karanto min abunda aka rubuta ba wai ka bi su da idanu ba, saninsu ne baka yi ba ko me".

ya sauke gwaron numfashi yana murza idonsa da kyau sannan ya shiga karanto ma ta abinda ke jiki tiryan tiryan.
BoÉ—ejo ta lailayo wata uwar ashar ta yarfa a sanda ya gama karantawa, ta fizgi takardar da ga hannunsa ta isa gaban Turaki ta wurga masa.

"kai ka isa, ka isa ka saki Ilham, to bilahillazi samun kwanciyar hankalinka da na iyayenka shi ne ka mayar da auren nan".

Maama ta miƙe zata bar wajen tayi saurin dakatar da ita cikin hargowa,"tsaya baƙar munafuka, gidan uwar wa za ki je da kika miƙe sim sim za ki tafi?, ai na san ba kowa yasa yayi sakin nan ba sai ke algunguma, wallahi ban san Dukko annoba ya kawo cikin gidansa ba sai yanzu, Madina!, baƙin kaidin ki har ya kai haka Madina?, to kuwa tunda kika sa ya saki Ilham, sai kin sa ya saki ɗayar ko kuma ke ma in sa a sake ki".

Hajiya Madina taji wani abu ya taso mata, tayi saurin haÉ—iye shi da ambaton Allah.
Boɗejo ta miƙo mata takardar tana faɗin,"yanda kika sa ya saketa haka za ki sa ya mayar da ita, ungo nan ba shi".

Maama na kallonta tace,"na san ina da babban matsayin da zan iya sawa ya saketa, amma ban yi hakan ba tun farko, ki daina alƙanta sakin jikarki da ni, ba ni na saka shi ba, wadda take ganin ta isa da shi kaf duniya itace ta ba shi wannan umarnin ba ni ba, kuma saboda gujewa fushin ubangijinsa da kuma taɓewar duniya yasa ya bi wannan umarnin".

Boɗejo ta bi Mum da kallo kafin tayi ƙarfin halin ce ma ta,"Ramla kika sa ya saki Ilham?".

Mum ta kawar da kanta gefe tana jan yatsunta tace,"kiyi haƙuri, amma abin da nake ganin ya dace shi na sa shi ya aiwatar, hakan shi kaɗai zai sa hankalin kowa ya kwanta, da ga mu har ke har kuma ita yarinyar".

mayafin BoÉ—ejo ya zame ya faÉ—i.

"haka kike Ramla?". ta tambaya da tsananin mamakin Mum ɗin, wanda take tantamar da ƙyar idan ita ce tasa Turaki yayi wannan sakin.

Mum ta fuskanceta tace,"ba zance haka nake ba ko ba haka nake ba, amma idan hakan bai yi miki daɗi ba Allah ya huci zuciyarki. naga masalaha ake ta nema tuntuni, wanda kuma ta hakanne kaɗai za'a samar da ita. kiyi haƙuri da abinda zan faɗa, ina son farin cikin ɗana, ina so ya sami kwanciyar hankali da nutsuwar da ya rasa tun daga ranar da ya auri Ilham...".

"dakata! me kike so ki faɗa min?, so kike kice an aura masa annoba da har kike faɗar ya rasa kwanciyar hankali. to cikin ku biyun kar wadda ta ƙara ambatar min kalmar tashin hankali anan, tashin hankali na can wurin shegiyar yarinyar da yaje ya aura a titi, kuma tunda kika sa ya saki Ilham, to ya zama dole kisa shi ya saki waccan yarinyar da ban yarda da asalinta ba, ba zan taɓa yarda a kawo mana gurɓatacce cikin zuria'armu ba ku san da wannan, dan haka ba shi umarni ya saketa".

Mum ta rufe ido ta buɗe sannan tace,"ina son rayuwar ɗana, ban shirya rasa shi a yanzu ba, kamar yanda nake tsananin son farin cikinsa, hakan yasa ba zan taɓa raba shi da abunda yake farin cikinsa ba. idan kika ce lallai sai ya saketa hakan zai zama barazana ga rayuwarsa, domin kuwa uwar gidansa itace rayuwarsa, rabuwa da ita dai-dai yake da rasa ransa, saboda haka ni ba zan sa ya saketa ba, dan Allah kiyi haƙuri a bar min yaro ya huta haka, kamar yanda ɗanki yake so ya rabu da ke lafiya haka shima yake so ya rabu da ni lafiya, sam ba zai iya ƙetare umarnina ba".

Boɗejo ta nemi kujera ta zauna tana salati, ta dafe kai tana girgiza shi,"yau naga abinda ban taɓa gani da ji ba a tarihin rayuwata, ni yau ake bijirewa umarnina, ni yau ake ja-inja da ni. Ramla da Madina me ku ka taka?, me Azima tayi muku da ku ka tsani ƴarta haka?, zumuncin da ubangiji yace a yi shi ku ke so ku rushe yau?...babu komai bari Dukkon ya shigo".

ta miƙa hannu ta ɗauko jakarta da ta tangarar a ƙasa ta ɗauko wayarta, da ƙyar ta iya lalubo lambar Baffa dan ta san duk wanda tasa ya nemo mata ayanzu ba zai nemo ba.
ringing biyu ya É—aga, ta amsa sallamar tana cewa da shi,"kana ina?".

"ina gida".
"kana cikin gidan naka ka barni da matanka suke min rashin mutunci suna gaggaya min maganganun da suka ga dama?, Dukko kana so ka gama da duniya lafiya kuwa?, to ka bar duk wani abu da kake kazo ɓangaren Mandina yanzu dan babu lafiya".

tana faÉ—ar hakan ta kashe wayarta, idonta akan Turaki da har yanzu yake dafe da kansa, danasanin aurensa duka biyun fal cikin ransa.
mintunan da basu wuce biyar ba Baffa ya shiga parlon Hajiya Madina, tun daga baƙin ƙofa yake kallon Hajiya Madina da Kuma Hajiya Ramla waɗanda ke tsaye sun kasa zama, ya ƙaraso ciki da sauri wajen mahaifiyarsa ya zauna a ƙasa yana cewa,"ranki ya daɗe gani, lafiya dai?".

"ina kuwa lafiya Dukko". ta faÉ—a tana É—auke ido daga kansa ta mayar kansu Hajiya Madina tace,"waÉ—annan marasa mutuncin matan naka sun sa yaron nan ya saki Ilham".

with shock Baffa ya É—ago yana kallon Maama, BoÉ—ejo tai saurin cewa da shi,"a'a ai ba ita ce tasa yay sakin ba, gata nan ita ta saka shi ya saki matarsa saboda bata tsoron Allah bata gudun girgizar al'arshin ubangiji".

ran Baffa a ɓace ya miƙe yana kallon Hajiya Ramla. "kika sa ya saki Ilham?, a bisa wanne dalili Ramla?, wace ke?".

Mum tayi murmushin takaici tace,"wace ni kake tambaya Dukko?, har ka manta shekaru 33 ba ya da na tsuguna na haifa maka yaron cikin tsananin wahala?, tunda ka manta bari na tuna maka, ni ce wannan matar da ta ɗauki cikinsa tsawon wata tara, na raini cikin da wuya bata daɗi ba, na kuma haife shi acikin mawuyacin halin da kai kanka kake tunanin ba lallai na rayu ba, na shayar da shi tsawon shekaru biyu, na ci kashinsa na sha fitsarinsa, ka tuna wacece ni ko kuma dai still na tuna maka?, to ni ce mahaifiyarsa, ni ce wannan uwar da ubangiji ya faɗeta sau uku kafin ya faɗi uba sau ɗaya tal. ka san kuwa da cewar ni ɗin bata wasa ba ce, ina da ikon sawa ina kuma da ikon hanawa ko ana so ko ba'a so muddin ana so a gama da duniya lafiya, so banga dalilin da zai sa abi a takura rayuwar yarona ba, yayi biyayyar amma hakan duk bai yi muku ba, ya kuke so yayi da ransa?, so kuke sai ya faɗi ya mutu tukunna?, tunda har yay biyayya ya auri zaɓinku ku barsa ya auri zaɓinsa mana, amma son rai duk ya hanaku kuyi masa adalci, to ni nasa ya saki amaryarsa zai kuma tare da uwar gidansa kamar yanda zuciyarsa take so, kamar yanda hakanne zai zama farin cikinsa da kwanciyar hankalinsa".
Chapter 118 · 0% Book details