← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 176

Sashe 14

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sanyin tafiyarta ta wuce, kawai tsayawa tayi a bakin ƙofar dan bata san ta yanda zata buɗe ba, bata taɓa ganin irin wannan ƙofar ba, inda ma ace handle ne irin wanda ta saba gani sai ta murɗa wataƙila ta buɗe, amma wannan ma ai ba ƙofa bace glass ne kawai.
Kusan 2minutes tana tunanin ta yanda zata shiga, sai gani tayi an turo ƙofar daga ciki ta buɗe. ta kalli Sameer wanda ya fito bai lura da ita ba, ya saki ƙofan ta ƙarasa rufe kanta sannan ya fara taka steps zai sauka.

Fillo dai kokawa ta kama yi da ƙofar, ta tura ciki taƙi shiga, ta kuma yi ƙoƙarin kama handle ɗin ta janyota nan ma ƙarfinta ya kasa. kamar zata yi kuka ta juya taga saura steps 2 ya ragewa Sameer ya gama sauka.

Cikin saurin murya tace da shi. "don Allah kazo ka buÉ—e min".

Ko da ya juyo ya ganta kamar ba zai dawo ba sai kuma ya dawo É—in, ta wutsiyar ido ya ke kallonta.
Maama me Æ´an aiki, ko aina ta samo wannan kuma oho.
Yasa hannu ya janyo glass É—in da aka rubuta open daga jikin handle É—insa, yay É—an murmushi saboda yanda yaga Fillo ta kafe hannunsa da ido da alama tana so ta koyi yacce zata buÉ—e ne saboda gaba.

Ya bata hanyar shiga yana ce mata,"ki ke shiga ta back door, in ba haka ba ƙasusuwanki akan wannan ƙofar za su ɓalle".

Gyaɗa masa kai kawai tayi tukunna ta shige ciki, ai bama sai ya faɗa mata ba, dan ta gama ayyanawa daga yau ba zata ƙara dawowa ba. Yau ɗin ma saboda bata so Kaka taji babu daɗi ne shi yasa banda haka tuni ta juya, ƙofa sai kace dutsen duniya, ai da taci gaba da gwada ƙarfinta wajen buɗewa kaf ɗinta zata kakkarye.

Tana tsaye tana ƙarewa haɗuwar parlon kallo tare da saƙe-saƙe cikin ranta Samha ta fito daga wani room a cikin parlon, ganinta ƙatuwa yasa Fillo saurin durƙusawa tana gaisheta a tunaninta ita ce Hajiya Madina.
Murya can ƙasa Samha ta amsa gaisuwatata ba tare da ta ko kalli inda ta ke ba, ta wuce ta zauna kan kujera tana ɗaukan remote ta sauya channel.

Wani abu ya tuƙe a wuyan Fillo, kenan haka Hajiyan ke wulaƙanta mata Kaka?. tausayin Kakar ya kamata, cikin ranta tana adu'ar Allah ya horewa Amir dai suyi aurensu ko sa huta da wannan bautar a ƙasan wasu balle a dinga wulaƙanta su.

"gadin ƙofa aka saka ki ne?". Samha ta tambayeta bayan wucewar daƙiƙu biyar.

Fillo tace,"a'a Hajiya, ban san aikin da zanyi ba ne".

Samha ta ɗago ido tana ƙare mata kallo, garin kwashe-kwashen Maama yau kuma me ƙanjamau ta ɗebo musu, halitta babu kyan gani jiki sam babu tsokar arziƙi, kai da gani kasan ba'aci an ƙoshi ba.

baki ta taɓe sannan ta ƙara ce mata,"Maama bata karanta miki aikin da za ki ke yi ba?".

Sai a sannan Fillo ta É—ago ido tana kallonta, ashe É—azu kallon tsoro tayi mata, yarinya ce da girman jiki dalilin da yasa tayi zaton matar gidan ce.
A hankali tace,"ba'a nuna min ba".
ta faÉ—a tana tura baki gaba.

Da hannu Samha tayi mata nuni, ita kuma ta shige sum sum kamar munafuka ta nufi kitchen ɗin, sai faman takure ƙafafuwanta ta ke yi saboda sanyin AC da yay yawa a tiles ɗin, ga shi takalminta ta barsu a can waje.

Turaki na tsaye a bakin friedge, ya ɗauko maltina ya buɗe ya tsiyaya a cup, ta tsuguna tana gaishe shi, zaton ta ko me gidan ne, amma bai amsa mata ba kasancewar da earpod a kunnensa duka biyun, har ranta taji babu daɗi, a yau ta ƙara yarda da cewar talaka wulaƙantacce ne indai yana ƙasan me kuɗi.

Turaki kam bai ma san da shigowanta ba, ganin ya juyo daga inda yake facing tayi saurin matsawa daga bakin ƙofa ta ba shi hanya, yay ficewarsa still bai lura da ita ba dan hankalinsa ba wajen yake ba.
tafi ƙarfin minti biyar a tsaye daga gefe ɗaya, haɗuwa da tsaruwar kitchen ɗin kawai ta ke ƙarewa kallo, ita dai badan-badan ba sai ta rantse gidan ƴan yan kan kai ne nan, ko kuma tace ba'a duniyar take ba gaba ɗaya.

Fitowa tayi daga kitchen ɗin dan sanin abunyi, bai zai yiwu Kaka na can kwance ba lafiya ba tazo ta tsaya anan babu aikin fari balle na baƙi.
tana fitowa su kai kiciɓis da Hajiya Madina, tana kallonta ta shaida ita ne matar gidan, tayi saurin durƙusawa ƙasa ta gaisheta, Hajiya Madina ta amsa fuskarta da fara'a tana ce mata ta miƙe tsaye.

Fillo ta miƙe kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, Hajiya Madina tasa hannu ta ɗago fuskarta tana mata wani kallo, wani kwarjini yarinyar tayi mata, itama Fillon hakan ta ke a wurinta, shi yasa tun kallon farko bata bari sun ƙara haɗa ido ba.

Allah ma ya sa ni Hajiya Madina ta girgiza da ganin yarinyar nan wanda ta rasa dalilin hakan, tsintar kanta tayi da jin wanzuwar sabon yanayi, babu shakka yarinyar zata zamar mata jigon wani abu, ta san da wannan.

ta kawar da mamakin a gefe guda, Kafin ta buÉ—i baki tayi magana Fillo ta rigata.

"Kaka Rabi ce ta turo ni na ƙarasa aiki, bata jin daɗin ne yasa ta tafi".

Tayi maganar idanuwanta na kan tafin hannun Hajiya Madina da ke tallafe da haɓarta.

Hajiya Madina ta faÉ—aÉ—a fuskarta da murmushi tace,"masha'Allahu sannunki, ya sunanki?".

"sunana Halima".

"sannu Halima, Allah miki albarka...ke jikar Kaka Rabin ce?".

Ta É—aga kanta,"ehh jikarta ce, a wurinta nake da zama".

"to sannunki kinji, amma jikin nata ba tsanani yayi can ba ko?".

Ruwa ya kawo idon Fillo sanda tace,"ehh na dai baro ta zata yi bacci, tace kanta ke ciwo".

Hajiya Madina tace,"to Allah ya bata lafiya...kin ƙarasa aikin?".

ta girgiza kanta alamar a'a. "ai yanzu na shigo kuma ban san aikin da zanyi ba".

Hajiya Madina ta sauke hannunta daga haɓarta, bata san me yasa zuciyarta ke wani irin zillo ba. ta kalla kujerar da Turaki ke zaune, bai ci komai ba ta sani, kuma ba zai ci girkin kowa ba idan ba nata ba, ƙannensa ma sai an kai ruwa rana yake iya cin abincinsu balle na wata ƴar aiki, ita kuma tana so ta fita cikin gaggawa, su na da meeting na friends ɗinsu da suka saba duk ƙarshen wata.

"mu shiga kitchen É—in". ta faÉ—awa Fillo.

Tayi gaba ita kuma ta bita a baya. tayi mata nuni da wata drower tace,"buɗe ciki ki bani ƙwai guda 10".

cikin sauri Fillo ta ɗauko ta kawo mata, ita kuma ta ɓare ledar indomie super pack guda biyu ta jefa acikin ruwan zafi, sannan tasa Fillo ta yanka albasa ta kuma yi greating taruhu.

In few minutes Hajiya Madina ta gama soya indomie da ƙwai ta zuba a plate, sannan ta dafa tea da ya ji kayan haɗin Sahaz Special Spices(08024976578) lokaci ɗaya kitchen ɗin ya kaure da ƙamshin spices, Fillo sai shaƙe ƙamshin ta ke yi.

Ita dai Fillo na tsaye a gefe tana kallon duk abinda ta ke yi, da kuma bin umarnin duk abinda ta sakata, tana yi mata bayanin abubuwan da zata yi, ba wani aiki ne me wuya ba, Kula da buƙatun Turaki ne kawai.

"miƙo min wancan tray ɗin na tsakiyan".

Hajiya Madina ta faÉ—a tana ma Fillo nuni da inda zata É—auko tray É—in. ta jere kayan break fast É—in akai ta bawa Fillo tace ta wuce da shi kan dining.

"Hajiya ina ne dining ɗin?". Allah ya taimaketa bata da ƙauyancin faɗin abu, Hajiya Madina tayi murmushi bata ce da ita komai ba.

Sai da ta gama wanke hannunta a sink tukunna tace da ita,"muje na nuna miki...in kin kai akwai ɗaki idan kika fita ƙofar kitchen daga baya, sai ki zauna in yana buƙatar wani abu za ki ga kira ya shigo ta wayar ɗakin, landline ce, ɗagawa kawai zaki yi ba sai kin danna wani wuri ba...please kar ki yi delay wajen amsa kiransa, becouse bai da lafiya isashshe".

Fillo ta biyota a baya suka fito, tayi mata nuni da dining area ta wuce taje ta aje akai.

"if ya gama sai ki kwashe kayan ki wanke...kar ki ce za ki É—ora abinci, ba ya cin abincin kowa sai nawa".

Tana faÉ—a mata hakan tace taje tace masa his breakfast is ready. da faÉ—in hakan ta haura upastairs cikin sauri.

Fillo dai bata gane guntun turancin da Hajiya Madina tayi mata ba, tayi shiru tana nazari da son gano abinda tace É—in amma ta kasa.
Ta ɗaga kai ta kalli inda Turaki ke zaune kan kujera ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya, cikin ranta tana mamakin isa da jin kai irin nasa, wato bama iyaka masu aiki yake walaƙantawa ba har da matarsa.

komai da take rayawa cikin ranta ya katse lokacin da Zaytuna ta shigo parlon, ƙananun kaya ne a jikinta sunyi mata kyau sose, kamar balarabiya ta watso gashinta ta baya, ta saka head band akan gashin.

Wurin Turaki ta wuce tana smiling É—in da ke fiddo da asalin kyan fuskarta, ta zauna kusa da shi kamar zata shige jikinsa, ta kamo hannunsa guda É—aya su kai shaking.

"Hamma nah yau ka tashi da wuri haka".

yasa yatsa ya lakuce mata hanci,"aka ce miki irinki ne ni, bacci babu sauƙi".

Dariya tayi tana kwantar da kanta a kafaÉ—arsa tace,"Hamma nah na fa rage, tunda ka dawo ai baka kalla na kai 10am ban tashi ba ko".

Idonsa na manne kan news É—in da ake a aljazeer ya É—aga mata kai kawai.

Conversation ɗin nasu shi ya warwarewa Fillo komai, kenan wannan shi ne Hammansu da Hajiya Madina ke ta faɗa mata ɗazu, ba me gidan ba kamar yanda ta zata. Kenan shine mara lafiyan da Kaka ke bata labari?, ta ƙara kallonsa da kyau tana jinjina wani lamari da ke cikin kanta.

tana jin Zaytuna na tambayarsa,"Maama bata sakko ba?".

"yes". Ya amsa mata before ya kalleta yace,"wa akai ma kwalliyan?".

Ya tambaya da salon zolaya. Ta maƙale hannunsa tana cewa,"kai Hammah nah ni kam wa zanma kwalliya banda kai".
Chapter 14 · 0% Book details