Sashe 102
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a burkice yace,"hannunki?, me ya sami hannun naki?". bata iya ce masa komai ba sai rufe ido da tayi ta ɓingilar da kai a jikinsa.
sai ya kamo hannunta da ke jikinsa ya duba yaga babu komai, ya kai hannu zai kamo ɗaya kawai sai ƙwayar idonsa ta sauka akan yatsunta a jikin ƙofa ya ɓame da su, bai san lokacin da ya furta,"innalillahi wa'inna ilaihi waji'un". a matuƙar gigice ba ya saketa daga jikinsa.
da sauri ya buɗe murfin motar, daidai lokacin ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya ta wahala, gumi ya keto masa kamar yanda itama ta haɗa uwar zufa duk da ac ɗin cikin motar, ya kamo hannun yana duban yatsun, sunyi jazur jini ya tare a waje ɗaya, fatar da farcen sun haɗe sun laguɓe, siririn ƙashin wajen kamar ya karye, sai kawai ya rufe idanunsa yana kai yatsun ya saka su cikin bakinsa, ya cika bakin da iska ya hura musu iska, ɗumin iskar ya ratsa yatsun har ɓargon jikin Fillo.
tayi wani zullo a jikinsa saboda tsananin azaba, ta saki sabon kuka tana cewa,"da zafiii". ta faɗa da ƙyar cikin mawuyacin hali.
ya rugumeta sosai yana ɗora haɓarsa kan fuskarta yace,"am sorry Fulaniii, i didn't do it to you on purpose, please am very sorry".
yaji yacca tai wata iriyar shaƙuwa, irin shaƙuwar da ke fitowa ba saboda ƙishirwa ba sai dan tsananin azabar da mutum ke ji, ya rumtse idonsa sosai yana cije leɓensa na ƙasa, yana jin kamar duk duniya ya rasa jin daɗinsa har mutuwa.
wucewar sakanni 30 ya miƙa hannu ya ɗauko wayarsa ya kira Zaytuna, tana ɗagawa bai ko amsa sallamarta ba yace,"fito da sauri".
Tsantsar damuwar da ta tsinta a muryarsa ita ta shaida mata babu lafiya, kuma ita tasa ta fitowa da gudu bada sauri ba, tana zuwa bakin motar ta leƙo tana cewa,"Hammah lafiya?".
Ta tambaya da fargaba ganin tashin hankali shimfiÉ—e a fuskarsa.
bai amsa mata ba ya fito daga motar ya zaga ya É—auki Fillo ya shiga baya da ita, sannan ya iya cewa da Zaytuna,"mu wuce asibiti". ya faÉ—a muryarsa a sama kamar ita ke da laifin.
akan hanya tana tambayarsa me ya faru amma bai iya ko amsa mata ba, sai jijjiga Fillo yake a hankali kamar yanda ake lallashin jaririn da ake son yay bacci, kuma har suka isa asibitin yatsun Fillo na cikin bakinsa kamar yanda take rungume tsam ajikinsa tamkar zai sakata cikin ƙirjinsa.
ba asibitin su Dr Yusuf suka je ba, dan gani yake idonsa idon Dr Yusuf ba za'a kwashe ta daÉ—i ba, wani abokinsa ya kira Allah ya taimaka yana asibitin, allurar lidocane aka yi mata don kashe zafin wajen, aka haÉ—a mata da drugs na pain relive, duk tsoronta da allura amma ko kusa bata yi kuka ba saboda wahala ba zata barta yinsa ba, tana lafe jikin Turaki sai kallo da ido kawai, haka ma maganin da Zaytuna ta bata tasha sam bata iya musawa ba, ta zama kamar hoto sai kallon Turaki da duk ya hargitse take yi.
ya sauketa daga jikinsa ya zauna da ita kan kujera ya fita cikin sauri, in few minutes sai gashi ya dawo da malt da madara peak kamar wanda likita yace masa tana da buƙatar jini.
Zaytuna dai sai kallonsa take yi tana murmushi tana kuma tausayinsa, ganin yacca duk yake ta abu kamar ba Hammansu da ta sani ba, ko su suka ji ciwo ko rashin lafiya ba ya wannan rawar jikin akansu, akwai dai kulawa kamar me amma ba irin wacca take gani a yanzu ba.
ta bisa da kallo har ya isa dispenser ya ciro cup ya haɗa malt ɗin da madara, ya durƙusa gaban Fillo ya kama hannunta ɗaya yana murzawa tare da kai cup ɗin bakinta, idonta ƙyam akansa da rashin makamar ma wanne irin tunani zata yi, ya kwantar da murya cikin sigar roƙo da lallashi yace,"please kisha kaɗan".
ta girgiza masa kai idonta na tara ruwa, yay saurin saka handky ya matse hawayen yana cewa,"kukan ya tsaya haka please bana so, ciwon zai warke yanzu, aima ya kusa daina zafin ko?".
sai kuma ya ƙara kai cup ɗin bakinta yana cewa,"please drink a little".
yacca face ɗinsa tayi turning zuwa na ban tausayi da kuma magiyar da yake yi mata yasa ta buɗe bakin ta sha kaɗan. yana ganin ta kau da kai ya miƙawa Zaytuna cup ɗin ya ɗora hannayensa saman ƙafarta yace,"am sorry please forgive me, ba da niyya nai ba ban san hakan zai faru ba".
ya miƙe ya fita ya dawo, lokacin Dr Anwar ya gama shafa mata wani magani a wajen, Turaki ya kasa tsayuwa waje ɗaya sai durƙusawa da ya ƙarayi agabanta yana riƙe hannun a hankali yace,"zafin yana raguwa?".
tana kallonsa kawai wasu sabbin hawayen suka sauko mata, wannan ya ƙara rikita shi ya miƙe yana ɗagata ya rungumeta a gaban mutane da ke ta wucewa.
"Fulanii bana sane, am sorry dan Allah".
yanda taga duk ya gigice ɗin nan ya ruɗe ta tabbatar da ba ya sane ɗin, dan haka kawai sai tai masa knodding kanta a saman ƙirjinsa, tausayin kanta take matuƙa amma ji take kamar tafi tausayinsa saboda ganin kamar ma kuka yake so yayi koma yayi bata sa ni ba, so take ta zame daga jikinsa amma ya hana hakan, har sai da Zaytuna ta dawo daga pharmacy tukunna ya saketa ya duƙa ya sunkuceta kamar wata ƴar baby, tana ta kai masa duka kan ita ya sauketa amma yaƙi har suka zo mota.
sai da suka shiga mota ta kallesa suka haÉ—a ido ta hararesa tana murguÉ—a masa baki tace,"ni nace maka bana son irin haka ba kyau".
tun ɗazu sai yanzu ya ɗan sami relief jin muryarta da yay, murmushi ya sauka a leɓensa ya kai hannu zai shafo fuskarta ta ture hannun tana cewa,"nace ma ba kyau".
a wannan karon kawai sai ya saki murmushi me gaba É—aya yace,"to naji".
cikin allurar da akayi mata dama har da ta bacci, so ko doguwan tafiya basu yi ba bacci ya É—auketa, ya kwantar da ita sanda yake nunawa Zaytuna wani suya spot yana cewa ta tsaya a wajen.
haka ya dinƙa tsayar da Zaytuna yana siyan kalolin nama a duk suya spot ɗin da ya gani, Fillo dai nata bacci bata san me ake ba, fruites ɗin ma da ya siya kamar me kafa tebur, a ƙarshe ya shiga wani store ya kwaso uban choculates kamar zai buɗe sabon kanti da su, gaban motar nan dai sai da ya cika maƙil da uban kaya kace mara lafiyan da ya shekara a asibiti za'a kaima.
akan cinyarsa taita baccinta har suka iso gida, yace da Zaytuna ta zagaya ta can bayan part ɗinsu tayi parking, lokacin yamma tayi ana gab da magriba garin yayi duhu, ya fito ɗauke da Fillo ya shiga ta ƙofar da babu me ganinsa ya shiga part ɗinsu, Bello ya tarar zaune a parlonsu ya ɗauke kansa kamar bai gansa ba yay bedroom ɗinsa, akan gadon ya kwantar da ita yaja blanket ya rufeta da shi yana yi mata peck a kumatu.
Zaytuna kuma ta dinƙa shigo da uban kayan da ya siya tana ajiyewa, ta tsaya tana kallonsa yanda ya zube a gaban gadon gwiwoyinsa duk a ƙasa ya riƙo hannunta yana kallon fuskarta kamar zai haɗiyeta, ko me neman gafara ko wanda akace in ya tashi za'a saceta, ta sauke numfashi tana tunanin ta yanda za'a faɗi wannan aure dai, da kuma yacca za'a karɓe shi, sannan ta ankarar da shi cewa an fara kiran sallah a masallaci.
kansa kawai ya gyaÉ—a mata alamar yaji, ita kuma tasa kai ta fita daga É—akin haka kawai tana jin faÉ—uwar gaba da kuma tausayinsa.
da ƙyar ya iya miƙewa yaje yayi alwala ya fito shap shap, ya ƙara zubewa a gaban gadon yana shafa fuskarta, ji yake kamar ya bari kawai yay sallarsa a gida ba sai yaje masallaci ba. ya kamo hannunta me ciwon wanda hakan yasa ta ɗan motsa amma bata tashi ba, sai ya dakata da motsin da yake yi, ya dinƙa kallon yatsun yanda suka koma, ta ƙara basa tausayi sosai yana jin kamar ya ciro zafin ya dawo da shi jikinsa, yana jiyo sautin ƙarar da ta ƙwala tana kiran sunan Ummi.
jin ƙarar buɗe ƙofa yasa shi waigawa, ganin Bello yasa ya miƙe da sauri yana haɗe rai tare da ɗaukan key room yace da shi,"lafiya?".
Bello ya kalli Fillo sannan ya kallesa yace,"uban me ka yiwa Æ´ar mutane?".
Turaki yace da shi,"ina ruwan munafuki da abinda ya shafeni ni da matata".
Bello yay dariya yace,"you find the solution right?".
yace,"you don't have any access to worry about that, that's my personal issue, so get out".
ya faɗa yana nuna masa ƙofa.
Bello na kallonsa ido waje yace,"in fita daga ina?".
Turaki ya kuma É—aure fuska yace,"i don't want to waste my time masallaci zanje, dan Allah fita". ya faÉ—a yana tura Bello.
a ƙufule Bello yace,"dilla Malami alwala zanyi ko baka ji ana kiran sallah ba ne".
yace,"ba anan kaÉ—ai ne akwai famfo ba, in ba zaka iya shiga other toilets ba sai ka bari kayi a masallacin, ko in kaje gidanku kayi".
Bello na ƙunshe dariyarsa yace,"ban key ɗin zan rufe idan na gama".
Turaki yay masa wani wawan kallo yace,"ka rufe ina in ka gama?".
yace,"to ai naga kamar saurin da kake yi ne yasa ba zaka iya jirana nai alwalar ba".
Turaki ya juya ya kalla Fillo na baccinta peacefully, yay Æ™asa da muryarsa yana cewa da Bello,"kayi a hankali mana karta tashi, dan Allah dan Annabi kayi haÆ™uri kaje toilet É—in Khaleel ko na Sameer kayi".Â
da rainin hankali Bello yace,"to ni anan naga damar yi dan haka ba inda zanje, mene za'a ɓoyen da za'a hanani alwala, shigowarka ai bai isa har ka aikata wani abu ba".
Turaki ya rumtse ido yana jin kamar ya saka masa ƙafa yace,"kaiwa Allah ka bar ɗakin nan Bello, baka san zafin da nake ji a zuciyata ba kana kalle min matata kwance akan gadona, kai baka san haramun bane hakan?, Allah banda bana so ta tashi tuni nasa maka ƙarfi ka fita".