← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 176

Sashe 104

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da mamakinsa sai yaga ta saki kukan sosai, sai turesa daga jikinta take yi tana so ta tashi, shi kuma har ga Allah yau karo na farko kenan da yaji kukan nata na masa daɗi saɓanin da sai ya dinga jin kukan na haifar masa da jin zafi a zuciyarsa.
har tsawon minti uku bai daina kallon yanda take da bakin kukan ba kamar yarinyar ƴar 3years, yasa wayarsa yana ta mata vedio, dan kansa dai yaji kukan ya fara taɓasa tukunna ya tashi ya kamota ya miƙar da ita.
jikinsa ya janyota ya rungumeta yana lallashinta yana bata haƙuri, ita dai bata daina kukan ba kuma ba tai ƙoƙarin fita daga jikinsa ba.
a ranta kuwa rayawa take yau babu abinda zai hanata faÉ—awa Maama irin wannan abinda yake mata.

ya kai bakinsa saitin kunnenta ya kira sunanta, tana shagwaɓe murya tace,"ni Fullo sunana ba Fulani ba".
Yace,"ba haka naga damar faÉ—a ba".

Ya faɗa yana kai hannunsa saman sumar kanta. tasa ƙarfi tana ture shi tana faɗin,"dan darajan Allah ka ƙyaleni in fita, wallahi hakan da kake yi babu kyau, ni fa ba muharramarka bace, kuma idan wani ya shigo ɗakin fa?".

yace,"zan bar ki ki wuce yanzu i promise, but you answer me first me yasa kika dinƙa taimakona?".

ya faɗa yana janyeta daga jikinsa yana kallon cikin ƙwayar idonta, ta ƙanƙance ido tace,"taimako kuma?, wane irin taimako na maka ni kam?, ni ban taɓa maka taimakon komai ba, kaine ma ka taimaka min aka kulle Amir".

ya matse tsintsiyar hannunta yana cewa,"kar na ƙara jin kin ambaci sunansa ko ba'a gabana ba". ya faɗa da sautin ɓacin rai da kuma kashedi me kyau.

tace,"to ka sakeni in tafi".
yace,"fara ban amsata tukunna, asirikan da kika dinga ɗaukewa akaina me yasa kika ɗauke su?, me yasa baki bari sun same ni ba?, kuma me yasa baki taɓa faɗawa kowa ba?".

tai ƙasa da idonta tana so ta ƙaryata zancen nasa sai taji hannunsa a haɓarta ya ɗago fuskarta yana ɗagamata kai,"ehen am all ears, ba kuma na son ƙarya dan nasan komai".

tayi narai-narai da idanu tace,"ni fa duk ban san me kake cewa ba, ni waye yace maka na É—auke asiri akanka?".

yace,"bakinki".
ta waro ido waje tace,"da yaushe?".
Yace,"ranar da kike bawa ƙawarki labari a asibiti, accident ɗinki na farko da na kaɗeki".

tace,"da ma kaine ka kaÉ—e ni akace wani ne?".
Kan yay magana ta tari numfashinsa da faÉ—in,"shima kana sane ka kaÉ—eni?".

ya galla mata harara da cewar,"ehhh sai ki haÉ—a duka har marinki ki rama, yanzu amsa min tambayata".

ta tankaɗe shi daga gabanta ta bar wajen da sauri, tana zuwa bakin ƙofa ya isa ya fizgota ya haɗeta da bango yana faɗin,"Allah you are going no where sai kin amsa min tun yaushe kika sanni?, kuma me yasa kika min asiri?".

hakan yasa ta sakin kuka sosai, tana rantsuwar,"Allah ni ban taɓa saninka ba sai da na fara aiki a gidanku, sunanka kawai na sani ajikin takardar da akai maka asiri, amma wallahi bani nayi maka ba, banma san su waye ba jinsu nai kawai suna faɗa, kuma ma ai saboda idan na faɗa ba za'a yarda da ni ba shisa ban faɗawa kowa ba, ina tsoron kar ace ƙarya ne ni nayi maka, amma na rantse da zatin Allah bani ce nayi maka asiri ba".

tai maganar idanuwanta a rufe, dalilin ba zai iya jin kukan ba ya kwantar da ita a ƙirjinsa yana shafa bayanta yace,"na yarda daina kukan cry cry Baby, kanki zai ciwo za ki zazzaɓi".

tana fizgar numfashi da ƙarfi tace,"wallahi Allah bani bace kuma ban san su waye ba".

ya ƙara yin ƙasa da murya very calmly yace,"ohh nace na yarda, na yarda ba ke kika min ba shikenan daina kukan haka, ko ba kya so na barki ki tafi?".

da sauri ta girgiza kanta,"ina so".
yace,"to inji kinyi shiru sai in barki ki tafi".

É—iff ta É—auke wuta kamar ba ita ta cika É—akin da kuka ba yanzu, ta lafe a chest É—insa tana jin yanda heart É—insa ke bugawa ba irin yanda ta san ainihin bugun zuciya ba, shima fuskarsa kwance akan gashinta ya lumshe ido, wayarsa na ta uban ringing bai ma san anai ba.
har aka turo ƙofar ɗakin aka shigo daga shi har ita ba wanda yaji motsin buɗe ƙofar balle kuma motsin mutum.

Hajiya Ramla tayi mutuwar tsaye daga inda take tana neman bango ta dafe, kafin dai tayi ƙarfin halin ɗaga ƙafarta da take jin kamar ta mutu ta dawo saitin inda zata ga fuskar wacce yake rungume da ita haka, bata san ba ko matar tasa ta dawo basu sani ba, sai dai tana zuwa ganin fuskar Fullo wacce idanuwanta ke lumshe yasa tayi saurin ja da baya tana dafe bango da furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.

wannan dogon salatin da taja cikin razani shi ya dawo da Turaki cikin duniyarsa, ya buɗe ido a tsoroce jin muryar Mum akansa, ya kalleta ya juya ya kalla ƙofa sannan ya juyo ya kuma kallonta, sai kawai ya saki Fillo yana ja da baya, lokaci ɗaya sai ya dawo kamar wanda ya kashe ɗan sarki aka gurfanar da shi a gaban sarki.
Mum ta bi ɗakin nasa da kallo sannan ta tsayar da kallonta akansa, ta tattaro yawun bakinta da ƙyar tace,"Babana, me nake gani haka?, kai ne da kanka tare da wadda ba matarka ba?".

sai kawai ta ɗaga hannu ta wanke shi da marin da ya kai fuskarsa ƙasa, da kanta ta ɗago da shi ta ƙara wanke shi da wani sabon marin da ya kaisa ƙasa gaba ɗaya gwiyoyinsa suka zube a gabanta.

Zaytuna tasa hannu ta rufe bakinta tana fashewa da kuka, tun ɗazu take kiransa a waya bai ɗaga ba, abinda take ta so ta faɗa masa kenan ga Mum nan. Fullo dai tuni ta durƙushe a wajen tana kuka sosai kamar ranta zai fita, cikin ƙunar rai da zafin zuciya ta rarumi lamp zata buga masa Zaytuna tayi saurin riƙe hannunta tana faɗin,"Mum ki tsaya kiji".

tayi wancakali da ita gefe tai kansa tana kai masa ƙafa ta ko'ina. "mutumcin gidan namu zaka zubar mana?, dama abin da na haifarwa kaina kenan?, sheɗani na haifa dama ban sani ba?".

yay saurin ɗagowa yana kallonta idonsa na hawaye yace,"Mum". bata barsa ya faɗi abin da zai faɗa ba tasa ƙafa ta daki gefen cikinsa.
"kaico, kaico da haihuwar irinka, nayi dana sanin haihuwarka, me ma yasa na saka maka sunan da ba zan iya kiranka da shi kai tsaye ba na zazzageka, me yasa nake jin ba zan iya tsine maka ba kai tsaye, wallahi na tsani ganinka, kai ba É—ana bane, yau sai dai ko ni ko kai a gidan nan".

ta ƙarashe maganar dai-dai lokacin da Hajiya Madina ke shigowa a rikice, tayi fatali da kwalbar da taga Mum ta ɗauka zata rotsa masa, ta riƙeta da kyau tana cewa,"me idanunki suka gane miki your excellency da har ba za ki iya excusing ɗinsa ba".

Mum na huci sosai kuka na zuwar mata tace,"kin san i spent morethan 5minutes a bakin ƙofar nan ina jiyo kukan yarinyar nan tana roƙonsa akan ya rabu da ita, amma ɗan banzan yaron nan yaƙi barinta ƙarshe da na buɗe ɗakin ajikinsa na ganta rungume da ita tana sauke numfashin wahala, bai ma san na shigo ba tsabar ya riƙa a iskanci, ki barni kawai na kashe shi Madina ba zamu zauna da gurɓatacce ba wallahi".

Hajiya Madina taja da baya tana neman faÉ—uwa, tayi saurin dafe bango saboda daina gani da ta fara yi, ta shiga tashin hankali na farat É—aya da take jin kamar zuciyarta na neman bugawa, batun hawan jini kuwa tasan tuni ya hau, tabi Fillo da ke kuka sosai da ido, sannan ta dawo da kallonta kan Turaki bata san lokacin da ta zube ba a gabansa, nan da nan hawaye ya shiga sauko mata.

tana magana da ƙyar tace,"this is not the background i gave you, ba foundation ɗina bane wannan, dan Allah na roƙeka ka ƙaryata abin da idanuwa da kunnuwa suka ji, me babban suna me ya sameka?, me kaje ka sha da har ka nemi ka aikata abin da baka taɓa aikatawa ba tsawon shekaru talatin da biyar?, ina kaje aka baka wani abu kasha?, me yasa ɗazu baka ce min in barka kaje wurin matarka ba kana buƙatarta?, me ƙaramar yarinya kamila kamar Fillo tayi maka da zaka lalata mata rayuwa?, me babban suna me nai maka da zaka saka min da hakan?, so kake ka kashemu ko so kake kace mu mutu mu bar maka duniyar?, ashe da rabon kaine silar yanke farin cikin rayuwata?, ban yafe maka ba me babban suna, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".

ta faɗa tana fashewa da kuka sosai, da ƙarin cewa,"ba tarbiyyata bace wannan me babban suna, ba haka na raineka ba, wannan sabon halin me muni daga ina?".

Mum tace,"ki matsa daga gabansa kar na fallatso miki jini, ki matsa nace miki".

ganin abin da take ƙoƙarin aikatawa Samha tai saurin doka tsalle ta dire a bayanta tana rirriƙeta.

Zaytuna ta duƙe a wajen tana cewa,"Maama duk fa ba yanda kuke zato ba ne, dan Allah ku barsa yay muku bayani".

a fusace Maama ta dunƙule hannu ta kai mata naushi ta baya tai mata wani mugun duka a hanci, tsananin zafi yasa tai shiru tana dafe hancin da take jin kamar ya cire.
Turaki ya dinga kallon Maama dake ta kuka a gabansa, kuma irin mugun kallon da take masa in har ya bari ta miƙe akansa sai ta kaisa har lahira, ya ɗaga kai ya kalli Mum dake faman kokawa da Samha da Khaleel tana so ta ƙwace daga riƙon da sukai mata ta rotsa masa kwalbar hannunsa.

ya rumtse ido sosai ya daki kansa da bango sannan ya buɗe baki yace,"Maama she is my wife, na bayar da sadakinta 5months da suka wuce, na damƙa sadakinta a hannun mahaifinta".

"what?!!!". abin da Maama da Mum da Baffa da ke shigowa yanzu suka faÉ—a tare. Bello ma da ke zuwa yace,"ehh Maama ya aureta tun da daÉ—ewa".

*Vote, Comment and Share.*
[9/3, 07:45] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*
Chapter 104 · 0% Book details