← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 176

Sashe 96

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy ya rissina yace,"mu tafi gida Inna dare yayi sosai, ƙarfe uku har da rabi, alhamdulillah yarinyar ta samu sauƙi  dan Yusuf ma yace gida zasu wuce".
ta kallesa tace,"to su kuma waÉ—ancan da suka cunkushe waje É—aya tafiya zamu yi mu barsu bamu gama kallonsu ba?".
Daddy yace,"ai yanzu su ma zasu tafi".
tace,"kai Amadu bana son halin Aliyu a tare da kai, ni kawai kayi tafiyarka ku ƙyaleni anan idan an gama na biyo motar haya, haka kawai yaran can da basu sami zuwa ba su rasa me basu labarin irin aratabun faɗan da aka sha, kai kasan halin ƴarka Yusra da gulma bata ƙi ta zageni tass ba akan ban kai musu rahota ba, ta dinƙa ɗaga min murya tana me amfanin zuwana wajen, to gwara ka barni in samu na kai musu, ni ƙafar Aliyun ma banga ta yanda aka shanyeta ba, yanzu dai ɗau wayarka kawai kayi musu hoto me motsi sai akaiwa sauran ƴan gidan da basu ga tashin hankalin da akai ba".
Daddy yace,"wayata na barta can gida kinga a halin da aka taho ai".

tayi shiru dai bata ce masa komai ba, dai-dai da ƙarasowar Nuratu wajen tace,"Inna Wuro ashe matar da muka riƙe a wajenmu babar yarinyar da Aliyu ya buge ce, shekaru da yawa basu haɗu ba sai yau Allah ya haɗa fuskokinsu".
Inna Wuro ta daki ƙirji ta dafe, babu shiri ta miƙe da sauri tana cewa Daddy,"tarkata yanamu yanamu mu wuce Amadu, daga nan kai tsaye Kano zamu wuce wuce ko gida ba zamu koma ba, gwara muje wurin Malam Ahmad Sulaiman ya haɗo mana turaruka azo ake bankawa juna, ina dalili haka irin wannan ibtila'i na rainon Aljanu, to Allah yasa dai bata shiga jikin wannan ƴa Farha ba".

Daddy dai yay shiru, tashin hankalinsa ɗaya ta botsare tace sai anyi kano a tsakiyar daren nan, dan aka ƙi zuwa shi abin zai zamewa tashin hankali  ta dinga kuka kenan tana ita ya biyata nononta da yasha kawai sai ta san nayi.
Inna Wuro ta dinƙa bi tana cewa mutane ahalin Amadu Alfindiki kuna ina, mutane kuzo mu tafi gida ƙarfe uku ta dare tayi.
Ammi tace mata,"Inna kiyi musu sallama, ki ɗan ƙara basu haƙuri sai mu wuce".
ta daki cinya ta riƙe baki tace,"niiii, ba dani ba wallahi, akan me in bada haƙuri bani na kashe musu ƴa ba, ke dai da ya zamar miki dole da fitinannan ɗanki yaja miki masifa".

har sai da suka je bakin mota sannan aka kula da babu wanda ke riƙe da Farha, Nuratu tace,"Inna wa kika bawa ita?". Inna Wuro ta fashe da kuka tana faɗin,"na shiga ukuna, wallahi ban san wanda ya amsheta ba, a hannuna fa take ƴar nan ban san garin ya ta bar hannun nawa ba, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, to aini sai yanzu ma na kula babu abu a hannuna, to dama abu ka ɗauka kamar baka ɗauka ba, Amadu kira Malam Ahmad ya buga mana istikara ko aga hannun wanda ta faɗa".

tana yin shiru sai ga Yusuf nan ya fito ɗauke da Farha, ya wuce ta gabanta ko kallonta baiyi ba ya miƙawa Nuratu ita yace,"karki ƙara bawa tsohuwar can ƴata tunda ba'a kasuwa naje na siyota ba, ke ma kuma ba buɗe ido kika yi kika ga an ajiye miki ita kusa dake ba, sai da kika sha baƙar wuya kafin samunta". yay maganar ransa a ɓace.

Inna Wuro na jinsa tace,"nima halina yaja min na shegen shishshigi da ƙwala kai a faranti, in ban damu da ɗaukar ƴarka ba ai baka zagar min iyaye har haka ba Yusuhu, iyayen da sun jima a ƙasa, tunda suka mutu babu uban da ya taɓa buɗe ƙazamin bakinsa yay musu irin wannan ƙazamin zagin sai kai Yusuhu, kamar bani na haifi ubanka ba?, amma babu komai Allah yana ji kuma yana gani, ranar gobe ya bi min hakkina. ƴarka kuma ni da ɗaukarta har abada, kai kallonta ma ba zan ƙarayi ba indai na cika ƴar halas, shegen banza kawai da yayo kama da dangin uwassa duk munana".
tai gaba tana goge hawaye da gefen zani. "Amadu zo mu tafi kafin jinina ya hau".

tafiyarsu ba jimawa su Hajiya Madina ma suka fito, da su da su Kaka aka kwashesu duka a sienna har biyu. cikin dare ne amma kace tsakar rana saboda yanda suke ta hanyaniya a mota. dan lokacin har an kira Granny a waya vedio call, itama duk wannan fushin da take yi sai ta manta da shi, tana ganin Mum ta fashe da kukan farin ciki, tana faÉ—in gobe-gobe zata taho, yanzu Adil zai je ya yanko mata ticket.
taraddadin Hajiya Madina ɗaya ne su kuma Baffa ya lanƙwashe.
kuma suna gab da isa gida Baffa ya kira wayar Hajiya Madina yake shaida mata cewar,"Fulani Azima tayi mummunan accident, su wuce masarauta kawai ba sai sun koma gida ba".

*Vote, Comment and Share.*
[8/31, 01:22] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*38*
*Massachusetts General Hospital, Philippines.*
acikin silent ward ɗin babu abinda kake ji yana tashi sai sautin kuka me ban tausayi. wata tsohuwa baƙa na sanye cikin les me tsada milk colour, ta baro inda take tsaye ta dawo kusa da Ilham ta zauna. ta janyota zuwa jikinta cikin sigar lallashi da ban haƙuri tace da ita,"Ilham wannan kukan naki da kika shafe kusan awa guda kina yinsa ba shine zai bawa Mahaifiyarki lafiya ba, saboda haka ki sha re hawayenki ki mata adu'a dan ita tafi buƙata a halin yanzu".

maimakon Ilham ta daina kukan sai sabo ya ƙaru fiye da wanda take yi, kuma Kakar tata Hajiya Shema'u wacce take mahaifiya wurin Azima bata ƙara ce mata komai ba, sai bubbuga bayanta da take cike da matsanancin tausayin Ilham ɗin.
a lokacinne kuma Ahlan ya iso wajen, ƙani ne a wurin Azima daga ita sai shi. ya zauna akan kujerar kusa da mahaifiyarsa, shima da ka kalla fuskarsa zaka hangi damuwa acikinta.

yace da ita,"Umma me likitan ya ƙara cewa?".
ta sauke numfashi ruwa na kawowa cikin idonta tace,"tou Me Martaba dai ya tafi wajensa tun bayan da suka fito da ita daga theater room É—in, ban san yanzu kuma ya ake ciki ba".
Ahlan ya sauke numfashi sannan yace,"nima jiya muna tare da jami'an tsaron da suke ta bincike akan accident É—in nata, kuma har yanzu fa Umma babu labarin driver'n da suka fita tare. anje wurin iyalinsa su kansu sunce satin biyun nan cif ba su saka shi a idonsu ba nemansa suke, itama kuma jakadiyar tata fa har yau ba labarinta".

da damuwa sosai Hajiya Shema'u tace,"to Allah masanin abinda ya faru, kuma ni gani nake idan lamari ne na Æ´an garkuwa ai ita zasu É—auke ba drivern ko Jakadiyar ba, kuma idan kidnappers É—inne da tuni sun kira waya, amma koma mene dai mun barwa Allah, fatanmu Allah ya tashi kafaÉ—unta".
sai kuma ta fashe da kuka sosai tana cewa,"da banyi niyyar faɗa muku ba saboda kar hankalinku ya tashi, sai dai faɗar ya zama dole ko don a tayata da adu'a. likita yace ta kamu da paralyse, ɓarin damanta ya mutu ya gama aiki Ahlan, idonta guda ɗaya ma shima ya mutu wai ruwan ciki ya tsiyaye gaba ɗaya, ƙafar hagun ma yanzu suna bayanin yanketa za'ai, Azima dai na cikin wani hali Ahlan, wannan yarinya sai dai Allah yay mata sakayya da wanda ya zama silar shigarta wannan hali".
sosai take kuka sanda take maganar, wanda hakan ya ƙara tsawaita kukan Ilham.

Ahlan a razane yace,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, paralyse Umma?, yanke ƙafa?, rasa ido ɗaya?, kai rayuwa kenan kowanne bawa da kalar ƙaddararsa, ita kuma Yaya ga ta yanda tata tazo mata. hasbunallahu wani'imal wakil".
shima bai san lokacin da hawaye ya sakko masa ba, tausayin ƴar'uwar tasa yay matuƙar kama shi.
Mai Martaba ya ƙaraso wajen jikinsa a mace, yana zuwa Ilham ta taso a jikin Hajiya Shema'u ta tafi ta faɗa jikinsa. ya rumtse idonsa sosai saboda tsananin tausayinta, ya kalli su Hajiya yace,"Dr yace kuna iya shiga wajenta". da sauri kuwa suka miƙe suka nufi wani dogon corridor hanyar da zai sadaka da room ɗin da aka kwantar da Fulani Azima.

Mai Martaba ya zauna akan kujerar da suka tashi, ya kwantar da kan Ilham a cinyarsa, yay dauriya da dakiyar maganar da yake jin kamar da kuka a cikinta. yace,"kina so Maminki ta sami lafiya?".
tai saurin ɗaga masa kai, yace,"to adu'a za ki mata ba kuka ba, indai kina kuka ba zata sami lafiya ba, kinga dai a halin da take ciki, halin da ko maƙiyinka ba zaka yi masa fatan ya shiga ba".
ta É—ago daga cinyar tasa, yasa hannu yana goge mata hawaye, wani na kuma bin wanda yake gogewar.

duk cikinsa ƴaƴa mata yafi son Ilham saboda sunan mahaifiyarsa da taci, ƙari da kuma da kyan halinta, dan duk cikin yaransa mata tafi kowa haƙuri da biyayya da nuna ita ɗin ba ƴar kowa bace.
yana riƙe da hannunta ya nunfasa yace,"ya kamata ki koma gida haka Ilham, ba zai yiwu ki baro mijinki kizo ki tare anan ba, karki damu ko every weekend ne sai kizo kike ganinta kina komawa".
tai saurin cewa,"Dad ni ba zan koma ba sai Mami taji sauƙi".
yace,"a'a Ilham".
cikin kuka sosai tace,"to Dad ai shima yayi min uzuri tunda yasan wacce bata da lafiya, ni dai ba zan koma ba, Allah Dad ba zan iya zama a ko'ina ba yanzu in ba kusa da Mami ba".

Mai Martaba yay shiru bai ce komai ba, wucewar daƙiƙa ɗaya ya ɗauko waya ya kira Turaki, yana ɗagawa daga ɓangaren Turaki cike da girmamawa da tsantsar ladabi ya gaida shi. bayan sun gama gaisawa Mai Martaba yace da shi,"Muhammad babu damuwa dai ko idan Ilham ta zauna nan?".
Turaki yace,"ba damuwa Dad".
"ka tabbata Muhammad?, karka ce zaka yi kara ko kuma alkunya".
yace,"ko É—aya Dad, ai abinda ya zama dole shi ake dubawa".
Mai Martaba yace,"to shikenan, Allah yayi muku albarka".
Chapter 96 · 0% Book details