← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 176

Sashe 47

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a ɗaki ta sami Zaytuna tana waya, ta tsaya daga bakin ƙofa tana jiran ta kammala, Zaytuna tayi mata alama da hannu cewar ta shigo ciki ta zauna. ta bar ƙofar a buɗe ta shigo daga ciki ta zauna akan carpet.
Turaki yazo shiga ɗakin ganin Fillo sai ya fasa, ya tsaya yana kallon duk su biyun, babu wanda ya gansa kamar yanda basu ji alamar zuwansa wurin ba. yasa hannu ya janyo ƙofar a hankali yanda ba za tayi ƙara ba sannan ya wuce, duk dan kar suga giftawarsa.

sanda Zaytuna ta kammala wayar ta dubi Fillo tace,"me kike yi yanzu?".
Fillo tace,"babu komai, mun gama aiki, ina karatu ne dama kamin na tafi".

Zaytuna tace,"to kinga dama kayan wadrobe ɗin nan zaki gyara min, Hammah na min yankan farce ya yanke ni, na kasa taɓa komai".
Fillo tace,"sannu Addah". tace,"yauwa, na gode...idan kika gama ki ɗauki wancan ƙaraman trolly ɗin ki tafi da ita".
Fillo ta kalli trolly ɗin da take nuna mata, small size ce kamar waccan da ta bata, tace,"tom Adda, na gode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya ƙarawa Baffa da Maama lafiya".

Zaytuna tace,"amin...na dai faÉ—a miki tun ranar nan, duk wasu tsaffin kaya da kika san kina da su ki bayar". Fillo tace,"na bayar Adda, wanda muke iri É—aya da Maijidda kawai na bari".
Zaytuna tai shiru for few seconds kamin tace,"tom shikenan, goben kuzo ke da Maijiddan, ina son ganinta".

ta amsa,"insha'Allah Addah".
Zaytuna ta shiga toilet, ita kuma Fillo ta fara gyaran da ta sakata. lokacin da Zaytuna ta kammala shiryawa zata fita wayarta tayi ringing, ganin sunan Happiness a jiki tayi saurin picking tana faÉ—in,"Hammah nah".

daga inda yake ya amsa da,"na'am Zaytun". sai kuma tai shiru tana jin cewarsa. ta waigo ta kalli inda Fillo take kafin ta amsa masa da cewa,"to Hammah". ta ƙara yin shiru na few seconds sannan ta ƙara cewa,"to Hammah, nima zan fita ne yanzu sai na dawo". da haka wayar tasu ta katse.

tana sa wayar a jaka tace da Fillo,"idan kin gama kar ki tafi kinji, ki kunna system sai ki ƙarasa kallon da kike yi ran nan".

wani daɗi ya mamaye Fillo, tana masifar son film ɗin, tun wancan ranar da ta kawowa Zaytuna assignmnt ta tarar bata nan sai Turaki ne a ɗakin, ta juya da sauri zata koma taji ya kirata yace ta dawo, ta shigo ɗakin ta zauna tayi tsilli-tsilli kamar ɓeran da aka girgiza acikin ruwan buta.
tun zaman da tai a wurin gaba ɗaya sai ya manta da ita, kallonsa kawai yake acikin system. time to time sai yayi dariya ko kuma yay tsaki, Fillo dai na durƙushe a wurin kamar me neman gafara, kuma tun tana jin tsoro har tsoron ya barta, sai dai taita kallonsa ta wutsiyar ido, tana ƙara jin sabon haushinsa, idan taji yay dariya sai ta tambayi kanta dama yana dariya?.

tafi ƙarfin minti goma sha biyar duƙe a wajen, tun tana a takure har ta saki jiki itama ta shiga kallon da yake yi a system ɗin, sai da aka kirasa a waya sannan ya tashi ya fita, ya fita ya barta da ci gaba da kallon, daɗin kallo ya mantar da ita yammar da tai, ta miƙe ƙafafu har sai da cajin laptop ɗin ya ƙare, lokacin ana sallar magriba.

kuma sanda ta miƙe zata fita daga ɗakin sai ga shi ya dawo, ya kalleta ya kalla room ɗin, ta dabarbarce tana sarƙe yatsunta, ƙirjinta yana ta bugawa.
daga sama taji muryarsa yana tambayarta,"ina Zaytun?". kanta a ƙasa tace,"bata dawo ba". sai yay mata kallon tsab yace,"ke kuma me kike yi anan?". ta ɗago kai tai masa duban mamaki tana saurin ɗauke ido daga cikin nasa da ya kafeta da su, bata bar jan yatsunta ba tace,"kaine ai ka tsayar da ni, kace nazo kuma aka kiraka ka tafi".

yay shiru bai ce komai ba, ya juya zai tafi muryata na ɗan rawa cike da tsoro tace,"na tafi?". yace,"a'a kiyi ta zama". daga haka ya wuce ya barta a wurin. ta bar ɗakin da kewar film ɗin da bata ƙarasa gani ba, kuma da ta koma ranar raba dare suka yi tana bawa Maijidda labarin film ɗin, bata ma san ya akai Zaytuna tasan ta kalli film ɗin ba.

kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta tace da Zaytuna,"Adda ban iya kunna laptop ɗin ba". Zaytuna tace,"kina buɗewa zata kama, Turaki is the password". tace,"tom". sai ta ƙara ce mata,"zaki iya ɗin ko na kunna miki?". tace,"zan iya Adda, Adda Nihal ta taɓa gwada min".
Zaytuna tayi murmushi tace,"ranar da kika sa ta dinƙa mana mitar ƙauyancin da kika mata?". kunya tasa Fillo rufe fuska.

bayan fitar Zaytuna babu jimawa ta kammala gyaran wadrobe ɗin, ta ɗauki ƙaramar trolly ɗin ta buɗe taga sabbin kaya ne kamar wancan time ɗin da ta bata. abaya guda huɗu sai riga da skirt na material guda biyu da na atamfa guda ɗaya. duka kayan kamar sai da akayi measurement ɗinta, dan babu alamar ma kayan ragesu akayi. cike da farin ciki ta mayar ta zuge zip ɗin, wannan ma rabawa zasu yi ita da Maijidda kamar yanda suka raba wancan.

maimakon taja trolly ɗin sai ta ɗauka ta ɗora akanta, ta fito ta rufe ɗakin farin ciki duk yaƙi barinta. zata sauka a stairs sai taji kamar mutum na sauke wahaltaccen numfashi a cikin ɗakin da yake gaba dana Zaytuna. sai taji ta kasa tafiya, ta tsinci kanta da komawa da baya har ta iso ƙofar ɗakin, ta tsaya tana ƙara tabbatar da abunda kunnuwanta ke jiyowa.

bata manta da wani lokaci ba da suka zo gyara ita da ÆŠausiyya, Nihal ta ke ce musu su gyara kowanne room dake upstairs banda wannan da yake da coffee door, shi ba'a buÉ—e shi totally. for sure daga room É—in take jiyo sautin, to anya kuwa daidai ta ke ji acikin kunnuwanta?,
ai ranar har suka gama zaryarsu anan basu ji wani abu makamancin haka ba, ta tsaya tana Contemplating ta buɗe ko ta tafi, abunda kunnenta ke jiyowa dai ba na wasa ba ne, ba irin abunda mutum zaiji bane ya ƙyale ya tafi.

sai kawai zuciyarta ta tsaya akan ta buɗe ɗin, ta sauke trolly daga kanta. tasa hannu ta murɗa handle na ƙofar room ɗin, door ɗin ya buɗe yana bada wani sautin ƙara.

tsabar mamaki da tsorata Fillo sai taji kamar ƙafafunta ba zasu ƙara ɗagawa ba, tabi wurin da Turaki yake a yashe a ƙasan tiles dafe da ƙirjinsa, numfashinsa na fita da ƙyar. ruwan hawaye na sauka ta gefen idonsa, kawai sai taji kanta yayi wani irin nauyi, hawayen nasa ya ɗimautata, kamar wannan ace yana hawaye?, me ke damunsa?.

bata san lokacin da ƙafafunta suka kaita gabansa ba gwiwoyinta suka durƙushe a saitin da kansa yake, ta kallesa taga kamar ma a sume yake, gabanta ya faɗi saboda yacca idonsa ya tsaya a wuri ɗaya cak baya ko motsi. ta kai hannu ƙasan hancinsa taji yana numfashi, sannan ta sauke wata nauyyar ajiyar zuciya.
tausayinsa yay bala'in kamata, taya zata iya barinsa taje ta sanar da halin da yake ciki?, idan ta tafi me zai iya faruwa before ta dawo?, me zata yi don taimaka masa a wannan lokacin?, a yanzu kamin wani yazo?, sai taji cikin kanta kamar babu komai, dukkan wata dabara tata ta yanke mata, bata san me zata yi ba.

acikin wani yanayin dake da wuyar fassaruwa tasa tafin hannunta me taushi ta shafa fuskarsa, sannan ta duƙo da kanta saitin kunnensa muryarta da rauni tace masa,"baka da lafiya? sannu, ka daina hawayen, bari naje na kirawo Maama".

ta faɗi hakan tana ƙoƙarin miƙewa, ta yunƙura zata miƙe sai taji ya ruƙo hannunta ya dawo da ita. ƙwayar idonta ta faɗa cikin nasa a sanda hawayen ciki suka sami nasarar gangarowa kan kumatunta.

a sanyaye tace,"zanje na kira maka Maama ne". sai taga ya girgiza kansa a hankali cikin ƙarfin hali. ta sake cewa,"to kana da magani a kusa na ɗauko maka?, aina zan ɗauko?". nan ma kansa ya girgiza mata a hankali. cikin dauriyar abinda yake ji acikin zuciyarsa.

sai ta samu kanta da ce masa,"to me zanyi maka? me kake so?". sai taji ya ƙara damƙe hannunta sosai, ya sauke kallonsa daga kanta ya tsayar ajikin bangon dake facing nasu. ta tsaya kawai tana kallon gefen fuskarsa, tana jin yanda ruwan hawayensa ke ɗiga a saman skirt ɗin jikinta, tana jin yana ɗauke kansa daga ƙasa yana ɗorawa a saman cinyarta, tana ji yana ƙara damƙe hannunta, tana jin yanda wani abu ke fita daga tafin hannunsa yana shiga cikin nata, tana jin wannan zafin da ta tabbatar yana ji a zuciyarsa yana taɓa tata zuciyar.

ta rumtse ido for few seconds sannan ta buɗe, ta buɗe tana bin inda yake kallo har sanda ta sauke kallonta gaba ɗaya akan ƙaton enlargement ɗin dake manne a bango. tayi mugun zabura da hoton da ta gani, ta tsayar da ƙwayar idanuwanta cak akan hoton tana ƙarewa dattijuwar matar dake jikin hoton kallo, ba sai an faɗa ba matar balarabiya ce, kallon matar take tana hango tsananin kamanni na Turaki dana Zaytuna a tare da ita, tun daga murmushinta har dimple ɗinta daya lotsa ciki sosai babu abinda ya banbanta daga na Turaki dana Zaytuna. _but who is she?_, tambayar da taiwa kanta kenan, kuma kafin zuciyarta ta raya mata wata amsa sai ganin Turaki tai ya miƙe tsaye yana toshe duka kunnuwansa biyu yana doka goshinsa a jikin glass da ƙarfi.

tayi azamar miƙewa tana ruƙo shi tana faɗin,"ka daina, zaka ji ma kanka ciwo". ta faɗa cikin tashin hankalin da ta rasa na menene, kuma rufe bakinta kenan jinin dake fita a goshinsa ya zuba akan ƙirjinta.

ta kalla jinin dake ƙirjinta, ta kalla jinin dake fitowa a goshinsa, idonta a waje tace,"ka bari". ta faɗa da wani mugun ƙarfi tana sa hannu da iya ɗan ƙarfin da take da shi ta fizgo shi daga bakin glass ɗin da yake tsaye, sai gasa a gabanta, taja hannunsa ta zauna da shi a ƙasa tana kunce ɗankwalinta ta ɗaure masa goshin.
Chapter 47 · 0% Book details