Sashe 105
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*41*
with confusion Baffa ke kallon Turaki, kuma tashin hankali da damuwar da ke tattare da Mum da Maama sai suka juye zuwa tsantsar mamaki. Maama ta dinƙa kallonsa babu ko ƙifta ido, so take ta tabbatar da idan a hayyacinsa yay wannan maganar, kamar dai ba ɗanta ba an sauya mata wani, kuma kamar dai yasha wani abu da ya juyar da tunaninsa.
Mum ta jefar da kwalbar hannunta, ta mayar da ƙwayar idonta kan Bello wanda ganin zata kallesa ɗin yay saurin sauke idonsa ƙasa.
Baffa yay ajiyar zuciya wadda babu wanda bai jita ba, muryarsa ta fito da amon da babu wanda bai sha jinin jikinsa ba acikinsu, ya juya zai bar É—akin yace,"ku sameni a parlo".
wannan sautin muryar tasa da kuma yacca ya juya ya fice ɗin Turaki ya tabbatar da ya gama shiga uku, Bello ma ya ɗora hannu aka ya furzar da wata iska daga bakinsa, ya san Baffa ya san ya faɗansa idan ransa ya kai ƙololuwar ɓaci, yana da masifar son ƴaƴa shisa ma ba ya iya musu faɗa, but baya tolerating shits, ya san ba zai taɓa ɗaukar wannan kwaɓar da Turaki yajawa kansa ba, bayan wannan ɗan guntun jawabin da yay bai kuma san ta inda zai fara yin wani ba in aka tsaresu.
Mum tazo ta wuce ta kusa da shi fuuu kamar zata tashi sama, kallo ɗaya zaka mata ka san a fusace take. Turaki yabi bayanta da ido kafin ya maida kallonsa kan Maama ya buɗe baki zai yi magana, tayi saurin ɗaga masa hannu,"dakata, kar ɗan ƙwaya ya sake yace zai min bayanin da kaina ba zai ɗauke shi ba".
sai kuma ta miƙe tai bakin ƙofa tana ƙara faɗa masa,"kar in jini a cikin lamarinka". ta fice tana jin ita bama tasan actual tunanin da zatai akan maganar tasa ba, dan magana ce yay ba irin ta waɗanda ke cikin hankalinsu ba.
kowa ya fita a ɗakin aka bar Turaki da Fillo kawai, ya miƙe yana jin kansa na sara masa, Bello ya dawo yay tsaya jikin ƙofar yana kallon abokin nasa da tausayi yace,"ka taso muje tun wutar da sanyi sanyinta before ta balbala ta ƙona mu".
Turaki ya kallesa ya ɗauke ido, ya mayar da kallonsa kan Fillo da har yanzu take a wajen a duƙe kowa ma ya manta da ita, kukanta take tayi bata daina ba, ya tafi yana jin jikinsa kamar mara lafiya ya isa inda take, ya ɗagota tsaye yana faɗin,"please stop this crying its hurts me alot, from today ba zan ƙara saka ki hawaye ba, i promise".
ya faɗa yana ƙoƙarin ɗora kanta a ƙirjinsa, sai ta hana hakan tana ɗago da kanta ta kallesa tace,"me kace musu?".
Ya rufe ido ya buÉ—e yace,"ce musu nayi ke matata ce".
ta kasa ɗauke idonta akansa saboda itama a shock take, and gani take kamar ya sha ƙwaya ne shisa yake wannan maganar da hankali ba zai ɗauka ba.
"shi auren film ne dama?".
yana kallonta yace,"ba film ba ne, namu É—in ne dai ya zama kamar a film".
ya faɗa yana matso da ita ta ƙwace daga riƙon da yay mata ta tankaɗa shi baya, cikin sheƙar sabon kuka tace,"leave me alone, Allah i hate you, ji a matsalar da ka jefa ni alhalin ni babu wanda ya taɓa riƙe hannuna ma, shikenan yanzu zaka ja Ummina ta yanka ni".
tai maganar tana wani kukan sosai.
da damuwa sosai yace da ita,"muje". taƙi tafiya, ransa a ɓace ya doka mata tsawa,"nace muje ko".
jikinta ya fara kyarma ya kama hannunta suka fito, tafiya suke kamar marasa lafiya, ji yake kamar babu komai acikin kansa, kamar babu yawun da zai yi musu bayani, taƙaimaimai ma bai san ta ina zai fara ba.
Bello dake daga gefensu yace da Fillo,"ki ɗaga ƙafa dan Allah, acikin matsala fa muke".
suka haÉ—a ido da Turaki yace masa,"kaita innalillahi ni inata yin hasbunallahu".
sai da Bello yay adu'a sosai tukunna ya iya saka ƙafarsa cikin parlon, ƙafafun Fillo suka fara shiga sannan na Turaki, idon Maama ya sauka akan hannunsa dake riƙe da nata wanda da alama forcing nata yay ta ƙasa ƙwacewa, lallai me babban suna ya riƙa da yawa.
bai yi gigin nufar inda Mum da Maama suke ba, still hannunsa na riƙe dana Fillo ya wuce ta bayan kujerar da suke suka zagayo ta ɗaya side ɗin, Fillo tayi-tayi ta ƙwace hannunta ya hana hakan har suka zo tsakiya ya zauna sannan itama ta zauna, duk akan idon Baffa dake jinjina ƙarfin hali irin nasa, sai da suka zauna ya saki hannun nata tayi saurin matsawa ta bar kusa da shi.
Baffa ya ajiye wayar dake hannunsa yana girgiza ƙafa, sai da yaywa Turaki kallon tsab ya tabbatar ba ƙwaya ce ke aiki a jikinsa ba sannan yace da shi,"maimaita abinda kace ɗazu".
Turaki yace,"Baffa...". ganin zai masa dogon jawabi ya dakatar da shi wajen É—aga masa hannu. "ce nayi ka maimaita abinda kace ba dogon turanci nace ka min ba".
Turaki ya sauke numfashi ya sunkuyar da kansa yace,"na aureta tun 5months da suka wuce".
yana yin shiru Baffa ya maida kallonsa kan Bello yace,"ehen?".
yay saurin É—aga masa kansa,"ehh Baffa da gaske ne ya aureta". Baffa ya sake cewa,"kai ka zama waliyin right?".
da sauri ya girgiza kansa ganin irin kallon da Baffa ke watsa masa yace,"a'a wallahi Baffa, ban ma san yay auren ba sai after yake faÉ—a min, wallahi ban san yanda auren...".
tsawar da Baffa ya sakar masa ta dakatar da shi,"shutup, waye marainin wayonka anan da zaka faÉ—a masa ba da kai akayi komai ba, marasa mutunci banza Æ´an iska marasa hankali, waÉ—anda baku É—auka iyayenku a bakin komai ba, wato har kuna da bakin ma da kuke maimaita min ko?, gaku kun balaga bari kuyi gaban kanku, to tunda ka aureta sai ka saketa yanzu dan ni ba zan yarda da wannan auren iskar ba, ba'a gidana ba, ba'a zuri'armu ba, ka saketa yanzu nace sannan ka min bayanin uban da yasa kayi gaban kanka".
furucin Baffan na ƙarshe ya doka wata tsayawa acikin kan Turaki, bai san lokacin da ya ɗago yana kallon Baffa da wani bala'in tsoro ba, muryarsa na breaking yace,"saki kuma Baffa, dan Allah kar ka yanke min wannan tsatstsauran hukuncin ba zan iya ba".
Baffa dai ya riƙe haɓa couldn't stop looking at him, dama saboda ya ƙara tabbatar da abinda yace shisa yace ya saketa ɗin, kenan da gaske yake ya aureta ɗin tunda ga tashin hankali nan ɓaro-ɓaro akan fuskarsa saboda yace ya saketa, ya dinga kallonsa da wani expression da shi kansa ya kasa fahimta, yayi aure kuma har 5months duk ba wanda ya sa ni, to waye ya ɗaura masa auren?, kuma when hakan ta kasance?.
"kayi aure Muhammad?, wa yay maka auren?".
Turaki ya ƙara yin ƙasa da kansa yace,"Baffa ni ɗaya naje, dama ina da niyyar zan faɗa muku".
ran Baffa ya ƙara ɓaci yana jijjiga kansa yace,"kana da niyyar faɗa mana bayan kayi gaban kanka?, ka ɗaurama kanka aure ba tare da saninmu ba Muhammad?, kayi aure babu ni ubanka da nake raye, babu ƴan uwana, ka shiryama kanka aure kai ɗaya, yaushe ka zama ɗan iska har haka?, yaushe ka mayar da ni mutumin banza ban sani ba?".
sai kuma yay shiru ya mayar da kallonsa kan Hajiya Madina yace,"dama har haka ku ka mayar da ni mutumin banza da wofi?".
kan ya ƙara magana ta tari nunfashinsa,"ya dai mayar da mu ƴan banza da wofi, ko idan da haɗin bakina akayi kaga na bari anyi wannan zaman?, to ni wiwin ma da ya fara sha ban sani ba balle sanda yaje ya ɗaura ma kansa aure, saboda haka kayi jan idonka akansa shi ɗaya, inma ɗauresa zaka yi duk kayi ba damuwata ba ce".
sai kuma ta kalli Fillo tace,"kema ashe tantiriya ce ban sa ni ba...".
kuma bata ƙarasa ba Turaki yay saurin katseta da cewa,"Maama bata san komai ba itama".
da mamakin da yafi na da Maama ta saki baki tana kallonsa, sai ya juya yay facing Baffa yay kneeling murya a hankali yace "Kayi haƙuri Baffa, na san nayi kuskure amma ka yafe min dan Allah, wallahi ba zan ƙara maimaita makamancin haka ba, ba zan ƙara aiwatar da abu ba da saninku ba, dan darajan Allah kayi haƙuri ka bani damar da zan maka bayanin da zaka fahimce ni".
Baffa yace da shi,"ai na kawo ƙarshen komai, sakinta kawai zaka yi dan wannan gantalallan auren ba'a zuri'armu ba".
Turaki ya rumtse idonsa yana jin kamar ya kurma ihu, ya dinga roƙon Baffa akan yayi haƙuri ba zai iya sakinta ba,"dan Allah Baffa kuyi min duk abinda zaku yi min amma karku ce in saketa ba zan iya ba, dan Allah ku bani damar da zan muku bayani ku fahimta".
Baffa ya jinjina kai yace,"zo nan Muhammad".
bai iya miƙewa ba ya dinga jan gwiwoyinsa har ya kai gaban Baffan, Baffa ya miƙa masa waya yace,"ka kirasa kayi masa bayani, ƙila shi ya fahimceka, dan ni ban da ta cewa dan lamarinka yafi ƙarfin tunanina".
Turaki ya karɓi wayar hannunsa na rawa, tun bai kai ƙwayar idonsa kan screen ɗin ba ya san wa Baffa yake nufi da ya kira, yana kallo kuma yaga sunan Hakimi ne akai calling kawai zai yi, sai yaji kamar ya fashe da kuka sanin cewa in har Hakimi ya san wannan maganar tasa kuma ƙare, ina shi ina kiran wannan azababben mutumin ya faɗa masa laifin da yayi da bakinsa, he can't even imagine yanda Hakimin ma zai yi fata-fata da shi, abu mafi sauƙi ne a wurinsa yasa a ɗaure shi bayan ya raba auren, saboda haka sai yay switching wayar off ya riƙeta a hannunsa, ko giyar wake ya sha babu abinda zai sa yay ma Hakimi bayani da kansa, ba ma ya fatan maganar taje kunnensa, inma zata je gwara ace taje masa a sabon aure zai yi, ƙaramin laifi ma yana ɗaure mutum na tsawon shekaru balle wannan da shi kansa ya san bai kyauta ba, dan lamarin aure ba abinda wasa ba ne.