← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 176

Sashe 75

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baffa ya ƙara sauke numfashi sannan yace,"ki bar wannan tunanin Madina. kuma insha'Allah cikin daren nan zamu ganta, nayi report mawa police and zasu fara aikin nemanta yanzu".
sai ya ɗauko wayarsa yay dialling numbern Inspecter Sise, yana ɗagawa yace da shi,"ta farka, wanne irin bayani kuke buƙata daga wajenta?".

Inspecter Sise yace,"ka bata wayar muyi magana". Baffa ya kalla Hajiya Madina sannan yace da Inspecter,"tana da saurin ruÉ—ewa, please a san irin tambayar da za'ayi mata".
tambayar kayan dake jikin Fillo da kuma yanayin yarinyar da kamanninta da yanda akayi ta fito duk su Inspecter É—in yaywa Hajiya Madina, kuma duk ta ba shi amsa, sai dai daya tambayi hoto tace gaskiya bata tunanin yarinyar na da hoto ma.

daga nan kuma inspecter ɗin ya ƙara cewa da Baffa zasu yi arresting Ɗan Usaini domin shima zai iya zama suspect nasu.
motar police tazo asibitin cikin ƙanƙanen lokaci, aka sawa Ɗan Usaini handcuff aka wuce da shi, hankalinsa a tashe yana ta rantse-rantsen shi wallahi bai san komai ba akan ɓatanta, yaje kama ruwa lokacin, ai masa rai wallahi baida hannu.

To har wajen dai sha ɗaya na dare babu wani batu na ganin Fillo ko alamun ganinta, tun Baffa yana ganin ɓatan kamar da wasa har ya dawo ya ɗauke shi da gaske, a sannan kuma shima hankalinsa ya fara tashi. Hajiya Madina dai har lokacin banda kuka da ambaton Allah babu abinda takeyi, ƙememe kuma taƙi yarda aje gida a tambaya ko ta koma, sai Khalil kawai ta yarda Baffa ya kira ya gargarɗe shi akan kar ya bar kowa yaji zancen, kawai dai ya san yanda zai shiga wajen Kaka su gaisa ya gani ko yarinyar ta koma, shima kuma letter ya kira ya sanar musu bata nan.

a sanda waɗanda suka ɗauke Fillo suka fito daga cikin gari, lokacin ne kuma suka ƙara speed na motar, gudu na fitar hankali suka dinga shararawa akan titin da babu kowa, gudu na ganganci kamar basa son rayukansu. sai da suka yi tafiya a ƙalla ta awa guda sannan suka shigo cikin wata unguwa, daga nan kuma suka fara tafiya with normal speed gudun jan hankalin mutane zuwa gare su, har suka yi nisa sosai sannan suka sauka daga kan titi suka shiga wani layi, haka suka dinga wuce gidaje da shaguna, sai da suka zo kan wani incomplete building tukunna sukai parking motar, ɗaya daga cikin su ya fita ya buɗe gate suka shiga da motar ciki.

compound ɗin gidan ƙato ne, sai da suka je har entrance na shiga cikin gidan sannan sukai parking a wajen. na gaban motar shi ya fata fitowa yana cire face mask ɗin fuskarsa da ya dame shi, sannan wanda yay driving motar ya fito, sai ɗayan da ya rage a baya ya cicciɓo Fillo kamar wata jaririya, shima ya fito sannan suka nufi cikin gidan a tare da sauran. Babban parlo ne da ba'a gama ginasa ba but ansa tiles anyi filasta paint ne kawai ba'ayi ba sai ƙarashen wearing, suka wuce zuwa wani dogon corridor inda ananne zaka tarar da jerin ƙofafi na rooms, a ƙofa ta ukun ƙarshe suka tsaya, ogan nasu shi ya buɗe sannan wanda ke saɓe da Fillo a kafaɗa ya fara shiga, yana shiga ya kwantar da Fillo kan wani ƙaramin gado kamar gawa.
Madaidaicin bedroom ne da shi kaɗai akai completing gininsa acikin ɗakunan dake gidan kusan guda 7. ogansu ya ƙaraso gadon ya zauna daga gefe, yasa hannu ya mammari fuskar Fillo don tabbatar da nauyin sumanta, sannan ya ɗago kansa ya kalla ɗaya daga cikin yaransa yay masa alama da yazo.

mutumin da duk cikinsu shine ƙato yazo ya hau kan gadon riƙe da shimfiɗeɗiyar igiya a hannunsa, ya jirkitar da Fillo gefe ya ɗaure mata hannayenta ta bayanta, ya kuma haɗa ƙafafuwanta wuri ɗaya suma duka ya ɗaure, sannan ɗaya daga cikinsu ya miƙo masa masking tape ya nannaɗe bakinta da shi.
Sai da suka tabbatar ko da ta farka babu ta yanda zata iya wani ƙwaƙwƙwaran motsi tukunna duk suka fice daga ɗakin suka barta ita ɗaya suka rufe da key.

Fillo dai bata farka ba sai da ana tada iƙama na sallar asuba, a hankali ta buɗe idonta da ƙyar ta shiga bin ɗakin da kallo, tana jin kanta yay mata wani irin nauyi, ga warin wani abu a ƙofofin hancinta, gaba ɗaya wani irin ciwo jikinta keyi mata tamkar wadda aka ɗau kwanaki ana duka, ta rufe idonta ta rumtse sose sannan ta buɗe tana jin eyelid nata yay mata nauyi sosai, sai a sannan kuma ta fara bin ɗakin da kallo har ta sauke ganinta akan roof na ɗakin, sose take kallonsa da mamaki sannan ta ƙara juyar da ƙwayar idonta ta sauke akan ƙofar ɗakin, daga roof ɗin har ƙofar basa cikin irin waɗanda ta sani, ba ƙuma sa cikin inda tasan tana kwana. daga paint na ɗakin har kan gadon da take duk bata san su ba, to aina take?.

tana ci gaba da bin ɗakin da kallo tana so ta tuna a inda take, da kuma yacca akayi tazo nan ɗin amma ta kasa, ƙwaƙwalwarta gaba ɗaya ta cunkushe taƙi yin tunanin abinda take so. sai tayi ƙoƙarin motsawa don ta tashi amma sai taji ta kasa, ta ƙara yunƙurawa taji babu ta yanda za'ai ko da hannunta ya motsa balle ƙafarta, wannan ya tabbatar mata da cewar a ɗaɗɗaure ta ke gaba ɗayanta.
sai sannan tayi ƙoƙarin buɗe bakinta tayi magana shima sai taji bakin a liƙe yake, ta hanci kawai ta ke numfashi banda baki. sai ta rufe idonta tana juyar da fuskarta ɗayan side ɗin sannan ta buɗe idon, nan ta ƙara tabbatar da bata san ina ne nan ɗin ba, take ta fara kokawa da numfashinta saboda tsoro, dai-dai lokacin kuma taji ana sallamewa daga sallah a masallaci, sallar da ta fahimci sallar asuba ce tunda raka'a biyu taji anyi, cikin kanta taji ƙwaƙwalwarta na biyo mata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, kuma a hankali cikin ikon ubangiji tunanin abinda ya faru da ita ya dawo mata.

sai ta rumtse idonta hoton komai na haska mata tarr tun daga ɗora wuƙa a maƙoshinta, da shigar da ita cikin mota, da kuma juyowa da akayi aka toshe mata hanci. take tayi ƙoƙarin ƙwalla razananniyar ƙara sai taji ashe fa bakinta a manne yake.
to Ina ne nan ɗin?, waɗanda suka ɗaukota su waye?, me yasa suka yi mata irin wannan ɗaukowar?, nan ɗin da suka kawota me zasu yi mata?, me yasa suka ɗaɗɗaureta haka har da toshe baki?. tarin tambayoyin da ta yiwa kanta kenan, kuma take ƙwaƙwalwarta ta bata amsa da,_"you have been kidnapped"._ take kuma zuciyarta ta ƙara maimaita mata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.

ƙirjinta ya dinga bugawa hawaye nabin kuncinta, tashin hankalinta ɗaya shin wanne hali Kaka ta ke ciki yanzu?, Wanne hali Amir yake ciki?, wanne hali Maijidda da Yami suke ciki?, ya Hajiya Madina zata kasance idan ta dawo taga babu ita?.
idan har kidnappers ne suka ɗauketa shin sunyi contacting da wani nata?, wa suka tuntuɓa?, adadin nawa suka nema kuɗin fansarta?, wa zai biya maƙudan da suka ambata?, sai brain ɗinta ta ƙara biyo mata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Hasbunallahu wani'imal wakil.

ta buÉ—e idanunta ruwayen hawayen ciki na samun damar gangarowa, kuma a sannan ta fahimci hasken dake ta wajen window da take gani gari ya fara wayewa kenan?.
take kuma ta tuna da cewar fa bata yi sallar magriba da isha'i ba, ga asuba ma a kunnenta akayi amma bata yi ba.

taja ƙafafuwanta da suka sandare tana so ta lanƙwasa su sai taji kamar zasu karye idan tayi hakan, saboda azabar ciwon da suke yi mata. babu ta yanda zata iya miƙewa ta tashi ko da zaune ne, balle kuma ta iya sauka daga kan gadon, dan haka kawai sai ta fashe da kuka sosai, can bayan wasu awanni taji muryar mutane  ƙasa-ƙasa a bakin ƙofar ɗakin.

Ta juyo da fuskarta tana kallon ƙofar, tana kallo aka turo ƙofar mutane uku suka shigo, Ƙaton cikinsu shi ya fara shigowa tukunna wasu sirara suka biyo bayansa bayan ɗayan cikinsu ya maida ƙofa ya rufe. tana kallo su suka ƙaraso bakin gadon, Ƙaton ya jawo wata kujera ya zauna yana facing ɗinta, tana kallo yaywa ɗaya daga cikinsu alama wanda shine duk yafi siranta a cikinsu, ya zagayo daga bayansa ya hau kan gadon ya ɗagata ya zaunar da ita, sai a sannan ta sami damar ƙarewa inda take kallo da kyau da kuma mutanen dake tare da ita fuskokinsu duka a rufe.

ƙatoton ya auna Fillo da bakin bindigar da take hannunsa yace,"zamu buɗe maka bakinka, idan har muka buɗe kayi wani yunƙuri na yin magana ko kuma ihu sai na fasa kanka da alburushi". Ya faɗa muryarsa da ƙarfi har tana amsawa a ɗakin, sai dai kana jin hausar tasa kasan riƙaƙƙen inyamuri ne.

hawayen Fillo ya ƙaru akan fuskarta, tana jijjiga masa kai alamar taji me yace cike da tsanin tsoro gami da tashin hankali.
Ƙaton ya kalli tsamurmurin dake kan Fillo tsaye yay masa alama da bakin bindigarsa. take tsamurmurin yasa hannu ya ɗaye masking tape dake manne da bakin Fillo, tsananin azaba yasa ta rumtse ido don ji tayi kamar ya haɗo da fatar bakin nata ne ta cire.
so ta ke tasa hannu ta shafa wurin ko ta sosa amma babu dama, tunda basu kunce mata hannu ba, saboda haka sai ta rumtse idonta sosai tana jinginar da kanta da bango har sai da taji zafin ya lafa tukunna ta buÉ—e.

ta buɗe ido ta sauke kan ƙaton mutumin dake latsa waya, rabin fuskarsa rufe take da hanky, tana kallo ya ɗaga hannunsa, ɗayan mutumin dake tsaye tun ɗazu a bayansa ya zagayo ya dire kwanon abinci a gabanta da pure water guda ɗaya. sai tabi kwanon abincin da kallo sannan ta ɗago ta kalli ƙaton dake saita da ita da bindiga, ya zare mata manyan idanuwansa yace,"buɗe kaci".
Chapter 75 · 0% Book details