← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 176

Sashe 76

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana ƙoƙarin danne kukanta tace,"dan Allah zan fara yin sallah tukunna". mutumin ya sunkuyo da fuskarsa kusa da tata, a tsawace yace,"kaga nayi kama da wanda ke yin Sallah?, to nan wurin da kake gani ba'a sallah, ko adu'a muka ji kayi sai mun ɓula kanka da alburushi. adu'a ɗaya muka yarda kayi shine a biya kuɗin fansarka, daga wannan bamu yarda da kowanne kalan adu'a daga bakinka ba, do you hear me well?".

da sauri ta ɗaga kanta sai dai bata jin zata iya ta zama haka ba tare da sallah ba, don haka ta ƙara buɗe baki tace,"nayi muku alƙawarin wallahi ba zanyi wani motsi ba, ko adu'ar ficewata daga nan ma ba zanyi ba muddin ba zaku cutar da ni ba, amma don girman Allah ku barni nayi sallah, ko magriba da isha'i na jiya banyi ba".

tana rufe baki mutumin ya buga mata bindigar hannunsa a bakinta yace,"only when you are out of here shine zaka je kayi ta sallolinka, but not in this place, sallah acikin wurin nan is prohibited from you".
sai kawai ta fashe da kuka sose tare da faÉ—in,"to su waye ku?, Me nayi muku?, Me kuke so tare da ni?".

ƙaton mutumin ya bushe da dariya yace,"mu kidnappers ne, kuma ba zamu sakeka ba har sai an biya kuɗin fansarka naira miliyan biyar, idan kuma ba'a biya ba zamu yi gunduwa-gunduwa da namanka sannan muka aikawa da iyayenka".

cikin matsanancin kuka Fillo ta ambaci kalmar innalillahi a karo na babu adadi tun bayan farkawarta, suna batun miloyan biyar kafin a karɓeta. wa take da shi da zai biya waɗannan maƙudan kuɗin?, me Kaka zata ɗaga ta siyar a sami waɗannan kuɗin?, ta san babu me biyan waɗannan kuɗin a karɓeta kamar yanda babu abinda Kaka zata ɗaga ta siyar a sami wannan uban kuɗin.
saboda haka sai kawai ta rumtse ido tana jin tana sallamawa da duniyar, ita kuma haka kalar ƙaddarar take?, fatanta guda ɗaya ko da ace ba zata fita anan tana roƙon Allah yasa kar mutanen su cutar da ita su rabata da mutuncinta, a hankali yanda ba zasu ji me tace ba ta furta,"Ya Allah ka fitar da ni daga gurin nan cikin amincinka da salamarka".

Ƙaton mutumin ya ƙara sakar mata tsawa yana cewa,"buɗe abinci kaci". tana kuka cikin firgici da razanin da take ciki tace,"babu ta yanda zanci ai".
sai a sannan ya tuna da cewar a ƙulle take, ya daɗa kallon wanda ke tsaye kanta ya bashi umarnin kunceta.
cikin zafin nama tsamurmurin ya kunceta kamar zai wurgata ta faɗo ƙasa, sanda ya gama kunceta ɗin sai ta sauke ajiyar zuciya saboda relief da ta samu, ta kama hannun nata tana shafawa, jinin da ya daskare waje ɗaya na saki yana bin ko'ina, kamin a hankali taji dama-dama.

ba ta so ya ƙara yi mata tsawa don haka ta ɗauka pure water ɗin ta kuskuren bakinta ta zubar da ruwan a jikinta, sannan ta janyo kwanon abincin ta buɗe, taliya ce jallof babu kyan gani, lokaci ɗaya taji zuciyarta ta tashi, amma saboda babu yanda zata yi dole ta shiga cusawa a bakinta tana taunawa da ƙyar.
ganin ta fara cin abincin suka tashi suka nufi ƙofa zasu fita, tai ƙarfin halin cewa,"bani da kowa sai Kakata, ku taimaka min dan Allah".

suka mata shiru suka fice suna rufe ƙofar, sai kuma taji an ƙara buɗewa ƙaton mutumin ya leƙo yana faɗa mata,"if you dare try to make any sound, i swear I will fill your brain with this". ya faɗa yana mata nuni da bindigar hannunsa, kuma ta tabbata he means it.

taji alamun an saka key a jikin ƙofar which means sun ƙulleta kenan, sai ta ture kwanon abincin dake gabanta, tabi ƙafarta da kallo tana noticing yanda ta kumbura sosai, ta jawo ƙafar da ƙyar tana shafata sannan tayi ƙokarin zuro ƙofar ta sauko daga kan gadon tana tsayawa akanta.
da ƙyar taja ƙafarta bayan ta ɗauko pure water ɗin ta isa bakin wata ƙofa da ta gani acikin ɗakin, daban da wacce suka shkigo. ta kama handle ta buɗe ƙofar a hankali sai taga banɗaki ne, tai saurin faɗawa ciki tai tsarki sannan tayi alwala ta fito.

ɗankwalinta tasa ta tattare ƙasan wajen, bata san ina ne gabas ba, kuma lokaci ɗaya maganar Amir ta haska mata sanda yake cewa shi addini ɗan sauƙi ne, idan ka tsinci kanka a garin da ba naka ba, kuma babu mutane a wajen da zaka yi sallah balle ka tambaya, to kana iya fuskantar ko'ina ne ka tada sallarka, don haka ta fuskanci inda take jin yafi kwanta mata ta tada sallarta da babban mayafin dake jikinta, sai da ta rama sallolin jiya dake kanta tukunna tayi asuba ta kuma yi sallar wadha ɗin da bata wuceta.
Bayan ta idar bata yi saurin tashi a wurin ba sai da tayi dogayen adduoi sannan tai saurin miƙewa ta koma kan gadon gudun kar su dawo ɗakin su sameta.

ta zauna da yaƙinin duk sanda suka kawo mata abinci zata yi amfani da ruwan wajen yin ibadarta. kuma zamanta kenan cikinta ya murɗa, tasan ba komai bane face yunwa, kuma take sai amai saboda tuntuni take jin zuciyarta na tashi saboda wannan farar taliyar da ta ci mara ɗanɗano.
har yanzu tunaninta guda É—aya ne, ta ina zasu fara neman wanda suke saka ran zasu biya kuÉ—in fansarta?, alhalin a wannan duniyar babu wanda ya san da su banda Allahn da ya halicce su.

a can ɓangaren kuwa tunda gari ya waye ƴan sanda suka ƙara tsananta bincikensu, har sannan kuma ba'a sallami Hajiya Madina ba don ita tace gwara a barta a asibitin har sanda za'a ga Fillo sannan ta koma gida ta iya haɗa ido da Kaka, amma banda cikin critical situation ɗin nan da suke ciki.
sai dai tunda ta farka ta tashi da zullumin ko zasu ji labarin cewar an ganta, amma police É—in na daÉ—a faÉ—a musu shiru babu labarin yarinyar, sai dai sun sanar da Baffa cewa za su cigaba da bincike insha'Allah, kuma ganin har rana tayi still babu wani labari ya saka dole aka sanar da Kaka halin da ake ciki.

ba Kaka kaɗai ba, hatta ƴaƴan Hajiya Madina sai a sannan suka san abinda ya faru banda Khalil da ya san komai tun a jiya. dan Baffa ce musu yayi sun ɗauki hanyar abuja a lokacin Maama na da seminar a gobe ƙarfe 8.
Kaka dai mutuwar zaune tayi daga inda take, tabi Hajiya Madina da Baffa da Khalil da kallo, kamar dai bata fahimci zancen da suke mata ba, kamar ba dai-dai taji ba, kamar suna so suce Fillo ta ɓata tun daren jiya kuma har zuwa yammacin yau ba'a ganta ba, wannan mummunan labari ne, kuma bata tunanin waɗannan salihan bayin zasu iya zuwar mata da shi.

Hajiya Madina ta fashe da kuka ganin yanda Kaka ta daskare, tana cewa,"ki yafe min Kaka, wallahi ban san hakan zata faru ba da ban fita da ita ba".
Yami dake tsaye itama ta kasa motsi take kallon Maama da tausayawa tace,"ki daina kuka Hajiya, tsautsayi ne, kuma cikinmu babu wanda bai san ƙaddara ba me kyau ko mara kyau".

sai sannan hawaye ya sauko a fuskar Kaka, dai-dai take ji da gaske faɗa mata suke jikarta ta ɓata, tayi inda ba'a san ta nufa ba, kuma yini guda babu ita babu labarinta.
cikin muryar kuka tace,""Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ya Rahimu ka bayyana mana yarinyar nan a duk inda take, ka dawo da ita garemu cikin amincinka".
ta faɗa tana mayar da idonta kan Hajiya Madina tace,"ki daina kuka Hajiya, ba ki da laifi ko ɗaya, dama ubangiji tuni ya shirya faruwar hakan, ko ace bata dalilin fitarku ba, ni musulma ce nayi imani da ƙaddara, saboda haka ki daina ɗorawa kanki laifi, ki share hawayenki don Allah, adu'a kawai ya kamata muyi Allah ya tsareta a duk inda take ya kuma dawo da ita garemu cikin amincinsa".

sannan Kaka ta ƙara maida dubanta ga Maijidda dake ta uban kuka, tace da ita,"ki kira Amir a waya ki sanar masa".
Yami tace,"a sanar masa kuwa?".
Kaka tace,"to ɓoyuwar ai babu amfani, gwara a faɗa masa ɗin sai su shigar da adu'a kafin tashin ɗalibai a makaranta".
Yami tace,"haka ne kuma, tunda su gidan malamai ne ko saukar ƙur'ani a iya yi cikin ƙaramin lokaci".

Maijidda ce ta kira Amir, kuma tun kamin ta sanar masa yasan babu lafiya tunda yaji muryarta tana kuka. kuma zata iya rantsewa da ta faÉ—a masa faÉ—uwa yayi a inda yake saboda yanda taji ya saki salati a gigice.
ƙarar salatin da kowa sai da ya jiyo daga cikin wayar, wannan yasa Kaka ta ƙara ruɗewa hankalinta yayi ƙololuwar tashi.

kowa dai a wajen yayi shiru, zuciyar kowa da abinda take saƙawa, daga ƙarshe dai Baffa yace su Zaytuna su kwaso kayan Kaka a taho da ita ɓangarensu, hakan kuma akayi suka ɗaukar mata abinda zata buƙata suka taho da ita wajensu ita da Maijidda da har yanzu ita ɗaya ce bata bar kukan fili ba.
kuma ita kowa yafi jin tausayi bayan Kaka, tsabar kuka idonta sunyi luhu-luhu.

ɓangaren Ameer kuwa har drip aka saka masa, dan lokacin da aka faɗa masa akan machine yake bai san ma sanda ya saki kan machine ba ya faɗa wani rami shi da machine ɗin, duk ya kurkurje yay rauni a duk jikinsa, ƙarshe sai wasu bayin Allah ne suka kaishi asibiti, a asibitin ya bayar da lambar Mahaifinsa aka kira nan da nan kuwa sai ga asibiti ya cika da mutane, abinka da me tarin ƴan'uwa.
Innarsa na zuwa ya faɗa mata abinda ya faru, kuma take ta ƙaryata tace sai dai in ko yaranne a ƙuruciyarsu suke so su gwada shi da irin son da yakewa Fillo, sai dai itama ko da ta kira abinda Yami ta faɗa mata kenan, Amir dai nata kallonta with his all hope ace ƙaryar suke yi masa, gwada shi suke so suyi, kuma in har gwajin ne yasan yayi nasara, sai dai zai faɗa musu kar su ƙara yi masa irin wannan wasan gudun rasa rai wataran.
Chapter 76 · 0% Book details