← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 176

Sashe 17

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"tashi kije kinji, ki zauna ɗakin baya inda abin buƙata za'a kiraki a waya". Zaytuna ta faɗa tana dubanta.
Fillo ta tashi cikin sanyin jiki ta wuce, Zaytuna ma ta fita daga part É—in zuwa nasu.

Bello yana kallon Turaki yace,"Beb É—in da ta tashi tana da hankali, itama Æ´ar'uwarku ce?".

Turaki yay masa wani kallo,"me yasa baka da hankali ne Bello?".

Bello yace,"tambaya fa nayi".

Turaki yaja dogon tsaki yace,"baka iya bambamce Æ´an aiki ne kai, ko kaga tayi kama da Baffa ne ko Maama".

ganin yanda yasha murr Bello yace,"sorry maida wuƙar, ban zaci maid bace saboda surarta na kalla ba kayan jikinta ba".

Turaki ya jefa masa wani banzan kallo,"kana nufin muma a rame muke kamarta?".

"thats is not what i mean, kuma itama ai ba rama bace da ita, halittar jikinta ce a haka".

ba tare da Turaki ya sake kallonsa ba yace,"wataran sai ka rasa idonka akan kallon mutane".

Bello yay dariya sosai, daga haka kuma suka ɗora hirarsu ta abokai tare da ƙara tattaunawa akan batun aikinsa da Maama har yanzu ta dage akan ba zai koma ba.

*Dubai, 12:00am.*
Nuratu ce a ɗakin zaune kan kujera, gefenta tarin drugus ne sai ɓallo su take yi tana zuba su a hannu. ta miƙe ta ƙarasa friedge ta buɗe ta ɗakko ruwa mara sanyi ta buɗe, sannan ta ƙarasa wurin gado ta zauna a gefe.

zuciyarta fal da tausayin matar da suka É—auko a asobiti suna kulawa da ita, ta kai hannu ta É—ago kan matar daga pillon da take kwance. sai a sannan matar ta buÉ—e nauyayyun idanuwanta ta zuba su kan Nuratu tare da sakar mata murmushi.

"sannu Mommi". Nuratu tace da ita tana sakar mata nata murmushin. kai kawai ta É—aga mata alamar yauwa.
matar da suke kira da Mommi ta buɗe baki Nuratu ta zuba mata maganin, sannan ta kurɓi ruwan da shima Nuratu ta bata, ta haɗa ta haɗiye maganin.

lokacin Yusuf ya shigo ɗakin, ya ƙaraso ya zauna akan bedside drower, cike da girmamawa haɗe da ladabi ya gaisheta, yana tambayarta sauƙin jikin. kasancewar bata magana sai da ta amsa musu da kai.

Yusuf yace,"Mommi yanzu ina ke miki ciwo?". ya tambaya da tsantsar kulawa, ta kalle shi ta sakar masa murmushi tare da girgiza kai alamar babu komai.

ya ɗan lumshe idonsa sannan yace,"masha'Allahu, Allah ya ƙara miki lafiya". ta jinjina kai alamar ta gode, sannan ta kamo hannunsa ta riƙe cikin nata, tana shaking nasu alamar nuna godiya a gare shi mara iyaka.
ya dubi Nuratu yace,"Mar'atussaliha ki shirya Mommi mu fita outing ta samu taga gari, zaman wuri É—ayan zai isheta haka".

Nurata tace da shi,"tom ur excellency". har ya miƙe tsaye zai fita kukan da Mommi ta saka ya dakatar da shi, wannan fashewar kukan nata ya haifar musu da tashin hankali. inda ya koma ya zauna shi da Nuratu suna aika mata tambayar me ya faru.
sai dai shiru bata ce komai ba illah hawayen dake daɗa sakko mata, kuka biyu takeyi, kukan baƙin ciki da farin ciki. abunda Yusuf da matarsa suke yi mata iyaka abunda Ƴaƴan cikinta zasu yi mata kenan.

_su waye su?, aina suka tsintota?, ina ne nan wurin da ta ke sabuwar rayuwa?._ tambayoyin da suke yawo cikin kanta kenan tun daga ranar data farka a asibiti zuwa ranar da suka É—aukota suka dawo da ita gidansu. so ta ke tasan amsar waÉ—annan tambayoyin sai dai ba ta da bakin da zata yi magana, haka kuma bata san ta yanda zata gwada musu ba har su fahimceta.

tunawa da wani lokaci yasa ta É—ora hannu a kunnuwanta ta toshe. domin tana jin faruwar abunne kamar a yanzu da ta ke zaune.
[8/12, 07:57] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

*2*
"Maijidda na kasa gane wajen".
Fullo ta faɗa a sanda ta ke ƙarewa babban filin wurin kallo. Dukkan tunaninta da hasashenta ta ɗora shi a wurin na fiye da daƙiƙa biyar amma sam ta kasa ta fahimci inda akai haƙan ramin.

Maijidda na tsaye itama ta ƙarasa bakin kujerun wajen(resting chairs) ta zauna. Ta ajiye digar da ke hannunta sannan itama tabi wajen da kallo cike da nazari da kuma son tunanowa.

"wallah Fillo nima na kasa tunawa kin san an kwan biyu...amma wai ajiyar me ki kayi ne a wurin nan?".

Fullo bata ce da ita komai ba, sai baki da ta zumɓura mata ta harareta kaɗan. ta zauna bakin tudun da ke wajen tare da naɗe ƙafafunta, kamar wadda ta shiga ajin makarantar allo. Yatsanta manuniya akan leɓanta na ƙasa tana ƙarewa faɗin wajen kallo, da kuma tsirran ciyayin da suka firfito a ƙasar wajen.
Cikin zuciyarta tana ayyana ya za'ai ta manta wajen nan, bayan tasan tsawon watanni biyar da aka É—auko bata ko zo wurin ba, hoton gun na haska mata acikin idonta a duk san da ta tuno, abu ne da bai shafeta ba bai shafi wani nata ba amma ta kasa mantawa da shi a cikin ranta.

Ita dai ta san ta kuɗuri aniyar tarwatsa alƙadarin waɗanda su kai aikin dama wanda ya saka su. Abunda ta ke son sani a yanzu shi ne waima waye Muhammad Turaki?, mene alaƙarsa da waɗanda suke neman ganin bayansa?, wanene shi a cikin gidan nan?, me yasa tsawon shekaru takwas da ta ɗauka tana rayuwa a cikin gidan nan bata taɓa ganin ko da gimlawar inuwarsa ce ba sai yau?, me yasa bata taɓa jin zancensa ba a inda ya dace a dinga ambatonsa?, me ya yiwa masu son kassara rayuwarsa?.

Bata da dukkan amsar waÉ—annan tambayoyin, sai kawai ta lumshe ido tare da hura iska a bakinta kamin ta furzar sannan ta sauke ajiyar zuciya. Bata manta da abunda ya faru ba a wajen, tsawon watanni biyar da suka wuce. Komai yana nan daki-daki a cikin kanta, fuskokin mutanen da su kai aikin ne kawai ba zata iya shaidawa ba, dan a lokacin bayansu da kayan jikinsu kawai ta gani kamar yanda taga Muhammad Turaki a yau, amma ko muryarsu taji a yanzu zata nuna su ta rantse da Allah cewar su ne.

MUHAMMAD TURAKI, harufan sunan da manyan baƙi suka ƙara haskawa cikin idonta, sunan da yake a jikin wannan farar takardar da babu zanen komai acikinta sai na sunansa da jan fenti. Sunan da ta kasa karantawa a randa tayi arangama da layar, kuma haka tayi ta ajiyar takardar har sanda Amir ya shigo cikin rayuwarta, ya fara koya mata karatu har tazo ta iya haɗa harufan a wata takarda ta daban ta maimaita rubutun sunan, sannan ta iya karantawa.

Ita dai bata san asiri ba, bata san ya ake yinsa ba, kuma bata san ya yake ba. amma zata iya rantsewa cewar aikin da waɗannan mutanen su kai asiri ne duk da bata ji sun ambaci wani abu da zai haska mata hakan ba, kuma babu tantanma asirin yana da alaƙa da sunan da ke rubuce ajikin wannan farar takardar da aka maida ita laya.

Abu guda kawai ta san da shi, shine idan har ta manta wurin da akai haƙan aka binne, to ba zata manta maganganun mutanen ba a lokacin da suke aikinsu. Aikin da suka gudanar a sanda ƙafafu suka ɗauke a cikin wannan babban gidan da ba ya rabo da shiga da fice ako da yaushe, ranar da akai naɗin Yarima Abbas zuwa wani matsayi da bata san wane matsayi bane, taji dai labarin irin rikicin da aka sha akan naɗin a wajen Kaka da Yami.

kuma zata iya cewa Allah ya nufeta da zuwa wajen ne saboda ta zama wata hanya ta tarwatsa mugun ƙudurin da ake shirinyi akan wani bawan Allah, tunda tsawon shekarun da ta ɗauka tana rayuwa cikin gidan bata taɓa zuwa wurin ba sai a ranar, lokacin kowa ya watse ana can masarauta ita kuma ta dawo dan ɗaukar ƙwaryar furar da ta dama zata bawa Amir.

A lokacin bata san ta ya ma akai ta kai kanta wajen ba. Ita dai kawai ta ganta ne ta ɓullo ta cikin lambu, ta durƙusa ta ƙasan bishiyan ayaban ta fito, kuma tana fitowa ne taci karo da wasu mutane su uku su na kalle kalle dan tabbatar da babu kowa a wurin da alama basu da gaskiya.

Bata kawo komai a ranta ba ta É—au hanyar zata fito ta bar wajen sai kawai taji namijin cikinsu na cewa.

_"nan wajen ne, tace daidai inda tafukan ƙafarsa za su taka kamin ya kai ga shiga cikin lambun"._
_maganar ta fito ne daga bakin bafaden da ke tare da wasu mata su biyu._

_"andai ƙi aji shawarata, amma ni gani nake yafi ace an binne acikin lambun gaban kujerar hutawan da yake zama...amma anan wurin zai iya ma tsallakewa ya wuce"._
_ÆŠaya daga cikin matan ta faÉ—a._

_ÆŠayar muryar ta amshe da faÉ—in,"ni sai da muka zo gudanar da aikinma sannan nake jin zuciyata ta cika da fargabar abin da zai biyo baya, sai nake ganin kamar ba zamu yi nasara ba asirinmu zai tonu"._

_Ɗayar matar da ke tsaye kusa da ita ta wurga mata harara tana faɗin,"to kuwa mugun tunaninki ya ƙare akanki ke ɗaya...wannan ma ai baƙin ciki kike mana, kina jin irin uban kuɗin da Shugaba tayi mana alƙawari amma shi ne kike wannan mugun fatan...mtswww gaskiya ba ki haɗu ba, to ni kam dai akan wannan ɗaruruwan kuɗin da naji babu kasadar da ba zanyi ba"._

_"zafa ki iya samun kuÉ—in kuma ki kasa jin daÉ—insu. Tunda idan aka kama mu bamu da wani mataimaki sai Allah dan ko ita shugaba sanin kanku ba zata waiwayemu ba gudun kar nata asirin ya tonu...ni kam ina tsoro sosai wallahi jikina na bani wani abun zai faru, dan ba lallai muyi nasara ba sai da mu faÉ—i"._

_A ƙufele ɗayar ta kuma cewa,"to zabiya uwar zancen ai sai kije ki faɗawa Jakadiya ke ba za ki iya wannan aikin ba saboda ga abunda kike gudu...kinga sai ta musanya ki da wadda take ganin za tayi mata aikinta ba tare da ta ji wani ɗar ba...mutum da shegen son kuɗi amma sai uban tsoro"._
Chapter 17 · 0% Book details