← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 176

Sashe 147

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya faɗa yana shafa bayan Fillo, ita kuwa tun da idonta ya ƙara ƙyallawa ya sauka akan mirror ɗin ɗazu sai ta ƙara shigewa jikinsa tana sakin makirin nishin firgici.
Boɗejo kuwa zazzaga masifa da zagege da baƙaƙen maganganu kawai take yi, tana ta zagin kafatanin ahalin Fillo, da Hajiya Madina, ran Turaki ya ɓaci sosai yay ƙasa da kansa, ya kasa ko da motsi ƙwaƙwƙwara.

tun shigowar su Turaki parlon Ilham ita ma ta shigo ta ɗayar ƙofar, ganinsu yasa tayi turus a wajen, tayi tsaye ba tare da sun san tana wurin ba, ji take yi kamar ta juya, amma sai taji ta ka sa ɗaga ko da ƙaramin yatsanta, jan ƙafarta ma take so tayi but shi ma ta kasa, ji take yi kamar an daskarar da ita ne a wurin.

kuma a lokacin da Fillo ta faɗa jikin Turaki sai ji tayi kaman an kunna gobarar wuta a ƙirjinta. duk sai taji ta rasa me yake yi ma ta daɗi acikin ranta, tun da ta baro gidansa bata ƙara ganinsa ba sai a yau, yau ɗin da take ganin kamar an sauya shi, ya ƙara kyau ya ƙara kumari, annurin fuskarsa ya fita daban da asalin yanda ta san shi.

sai taji masifar son shi da kishinsa ya ƙara bin sassan jikinta, yau shi ne gabanta da wata mace da ba ita ba, macen da ta san ta fita asali, kyau, nasaba, ilimi kai komai na rayuwa ta san ta fi Fillo.
a gaban idonta yake ririta ƙwailar da ta san bata da uban komai bacin kyau irin na ƴaƴan aljanu, har yake rungumeta a jikinsa alhalin ya san a cikin gidan su yake.
duk sai taji duniyar ta ƙara yi mata zafi, taji kaman ta samu wuƙa taje ta ɓurmawa Fillo, gwara ta kasheta kawai ko ta samu ta sami sauƙin raɗaɗin ciwon son Turaki da kishinsa da ke neman hallaka ta.

tana ganin sun miƙe za su tafi zuciyarta ta yanke shawarar zuwa ta bangaje Fillo, ta hankaɗata daidai saitin in da idanuwanta ke hango ma ta garwashin wutar da aka ajiye wanda akewa Boɗejo gashin ƙafa da shi.
without second tought ta baro bakin ƙofar ta taho gadan gadan kamar wacca ake tunkuɗowa. idon Fillo ya ƙara sauka akanta ta cikin mudubin, kamar tasan abin da Ilham ɗin ke shirin yi, tana ganin ta kusa zuwa in da take, da gangan tai saurin wuntsilawa gefe zata faɗi aikuwa a kiɗime Turaki ya tarota yana faɗin Subhanallah.

"Fulani Nah yi a hankali, am sorry kinji, hankalina na kan wannan tsohuwar ne".
ta ɗage ƙafa tana cije fuska tace,"ka daina bani haƙuri ba kai ba ne".
sai ta dafa shoulders ɗinsa ta ɗago tana duban Ilham dake gefe ɗaya tana faman huci tace,"ina yini, ya mai jiki, Allah ya sawwaƙa ya tashi kafaɗunta. kiyi haƙuri ban san za ki wuce ba da ban tsaya a hanya ba".

Ilham taja dogon tsaki na baƙin ciki da takaici, ta bar wajen tana jin zuciyarta kamar zata ƙone.
Turaki ya bi bayanta da mugun kallo, ya dunƙule hannu yana ɗauke idonsa akanta.

"ita ta bige ki?". Fullo ta kalle shi tayi narai-narai da idanu kamar zata yi kuka ta ce,"don't bother your self, mu tafi kawai kaga ran Boɗejo a ɓace yake".

sai ya tallafota jikinsa ya juya ya fuskaci Boɗejo, muryarsa na shaida zallar ɓacin rai yace,"wurinki muka zo ba wajenta ba, a da nake da hurumi da ita amma a yanzu ban da wata alaƙa da ita, ki ja mata kunne karta ƙara gigin illata min Mata ko da kuwa bisa kuskure ne, dan ba zan ɗauka a hakan ba. ina da sauƙin kai but akan wannan jaririyar da ke jikina ina iya rufe ido na manta duk girman alaƙar dake tsakanina da ko wanene in ci zarafinsa, wannan jaririyar tafi min duk wani mutum a duniyar nan bayan mutum uku, domin ta sadaukar da ranta da lafiyarta akaina tun kafin ta san waye ni, ta cusa kanta a haɗarin da ko wanda yake sona ba zai iya ba, saboda haka nake mutuntata, nake martabata, nake darajtata fiye da ƙima, fiye da lissafi duk wani me tunani. zan ɓata da ko waye matuƙar ya nemi ya cutar min da jaririyata, if not zan manta da alaƙa in nuna the bad side of me, hakan kuma babu wanda zai yiwa daɗi".

a hasale Boɗejo tace,"to ai ka rufe mu da duka ni da ita shi ne kawai,  mene wani gargaɗinka, gargaɗin banza da zai bi ta iska, ai rama ma ta kawai zaka yi, wato ga Ramla an taɓa ko Zaytuna dole ka nuna baka da mutumci".

ya rufe ido yana ƙara dunƙule hannunsa, Fullo ta riƙe shi ganin kamar yana ƙoƙarin aikata abin da ba zaiwa kowa daɗi ba.

ya buɗe ido yana kallon Boɗejo yana ta huci yace,"kamar yanda Baffa ba zai iya haɗaki da Mum ba, haka ma ni, amma ki sa ni, gwara a taɓa Zaytun akan a taɓa wannan, saboda haka me kiyayewa ya kiyaye, wanda ba zai iya kiyayewa ba kuma ya shiga sata gonar Muhammad Turaki".

yana gama faɗar hakan ya duƙa ya ɗauki Fillo suka fice, tana ta cewa ya sauketa amma yaƙi, hadimai da dakaran gidan sai kallonsu suke yi har suka shiga mota.
ɓangaren Ilham kuwa su na fita ta kalli Boɗejo tana nuna kanta ta ce,"ni yarinyar nan zata haɗawa sharri, ko fa taɓata fa banyi ba Boɗejo, amma ki ga irin maganganun da Hammah yake faɗa, to wallahi ko ban da niyyar komawa gidansa sai na koma, zata gane tayi da ni".

ta miƙe tana barin falon haɗe da yin ƙwafa me girma wacca ita ɗaya ta san ma'anarta.
a hanya Turaki ya tsaya ya sayi kaza da takeaway na mandi rice. tun da suka taho daga shi har Fillo babu wanda yay magana a motar har suka koma gida.

yana yin parking Fillo ta buɗe ƙofa ta fice tai tafiyarta, shi ma kuma ko da ya shiga part ɗin bai bi ta kanta ba ɗakinsa ya wuce, ya sakar ma kansa shower sannan ya kwanta akan gado ya runtse idonsa, tunaninsa guda ɗaya ne, Anya zai dawo da Ilham cikin gidan nan?.

ya daɗe kwance yana lissafi acikin kansa, kafin ya buɗe ido ya sauko akan gadon ya fita, ɗakin Fillo ya shiga, zaune ya ganta akan gado tayi shiru kanta jingina da gadon, ya tsaya yana kallonta kafin ya ƙarasa bakin gadon, yana zuwa ya ɗaukota ya fito da ita zuwa ɗakinsa.
[9/7, 01:16] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*54*
akan kujera ya zaunar da ita, idanuwan Fillo suka manne akan hannun Turaki da suke cikin plate É—in abincin da yayo takeaway, abincin da ta san ya siya ne saboda ita, ba don shi yaci ba.

ya ɗebo ya kai bakinta, har yanzu ɓacin ran da ke saman fuskarsa bai gushe ba, idanuwansu ya sarƙe ana juna, ta kaudar da hannun nasa da ke nufar bakinta.

"ban ji daÉ—in yanda ka yiwa BoÉ—ejo ba".
ya rufe idonsa bai ce komai ba.
"don Allah kar ka ƙara, ko babu komai ita ce fa ta haifi Baffa, tana da girman da bai kamaci ai faɗa ma ta kowacce irin magana ba saboda ɓacin rai".

still idonsa na rufe ya ce,"ba don hukuncin ubangiji ba, sannan ba don ke da taimakonki ba, da yanzu bana raye, ko kuma da ban kawo yanzu da lafiyar da zan yi tafiya ba, da yanzu wataƙila ina kwance marabata da matacce numfashi kawai, kuma wataƙila da har yanzu ban ga mahaifiyata ba. saboda haka girmanki da nake gani yafi gaban tunani, kina da girman da ba zan iya ganin an ci mutunciki na ƙyale ba".

ta buɗe baki zata yi magana ya ɗora yatsansa a leɓenta,"shhhh bana son magana, ki ci abinci".
ta kalli abincin ta ce,"bana ci".
"saboda me?".
"saboda kaima ba zaka ci ba, me yasa zaka tsaya siyan abinci bayan na iya dafawa, and beside da ka siyo bafa ci zaka yi ba, so kake ka kwana da yunwa?, ban iya rashin adalci ba kuma ba zan fara ba daga yau, Ummi ta jaddada min sau babu adadi cewar kar na taɓa barinka da yunwa".
kafin yay magana ta miƙe, ta kamo nasa hannun shi ma ya miƙe.

"muje kitchen na dafa mana abin da zamu ci".
ya dakatar da ita,"kin gaji ba za ki iya girki ba, kuma kinga akwai ciwo a ƙafarki".
"ni ban gaji ba". ta faɗa tana saƙalo hannunta guda a wuyansa sannan ta ƙara cewa,"idan ƙafan na ciwo ai sai ka ɗauke ni".

murmushi yay tare da ɗaukarta su ka fita a ɗakin,  su na saukowa downstairs kitchen ya nufa, sai da suka shiga ya ajiyeta, ya kama ƙugu yana cewa,"zan ga yanda ake aiki da gurguwar ƙafa".
tayi murmushi me sauti tare da jan gemunsa ta ce,"to ai da ka É—auko ni na warke".

ya buɗe ido yana kallonta,"ƙatoto da ni kika yiwa wayo?".
ita ma ta kama nata ƙugun ta ɗaga kai sama ta juya idanu, sannan ta ce,"me zamu ci?".
"duk abin da aka girka da waÉ—annan siraran hannun zan ci".
ta dafa kafaɗarsa ta ce,"ummm Maama ta taɓa cewa kana son soyayyan indomie, so yau zan ci abin da kake so ni kuma bana sonsa, but na san daga yau zan fara so, in dafa ko?".

ya É—aga ma ta gira yana jin wani daÉ—i a zuciyarsa, ta wuce ta É—ora tukunya a gas, ya bi ta yana faÉ—in zai tayata, ta dakatar da shi,"no ba yanzu ba, zaka fara girki but not today not now, but one day. for now just sit and watch".

kujeran dining ɗin dake kitchen ya ɗauko ya zauna gefe daga in da cooker gas yake, kafin ta gama yankan albasa idonsa duk ya cika da ruwan hawaye saboda yajin albasar, tuni kuma suka zubo, sai ƙyafta idanu yake, Fillo duk na kallonsa tana ƴar dariya, tace,"me aka maka kake kuka?".
ta tambaya tana dariya ƙasa-ƙasa.

"ni kike yiwa dariya?".
ya miƙe zai bar kitchen ɗin ta maido shi ya zauna tana faɗin,"sorry, idan ka fita ina jin tsoro".
Chapter 147 · 0% Book details