← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 176

Sashe 155

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tai saurin barin jikinsa ta ajiye wayarta ta dunƙule a waje ɗaya.
"ni a'a, har yanzu ina jin zafi".

Daga wannan ranar, sabuwar rayuwa ta *MH*(Muhammad & Halima) ta fara,  sabuwar shaƙuwa, sabuwar soyayya, tarairayar juna da kulawa.

zuwansu ƙasar Ausburg ba ƙaramin daɗi yayi mu su ba, Fillo an waye an kile, mo re soyayya kawai suke yanda su ke so, kullum su na kan hanyar yawon shaƙatawa, a fita tun safe a yini a bakin beech.

wata irin soyayya Turaki yake nuna mata me ban sha'awa, yayin da ita ma anata ɓangaren bata ƙyale ba, don tuni Nuratu ta ɗorata a layin manya, ƙoƙari take yi sosai wurin ganin ta faranta ran Turaki, wajen ganin ta mantar shi kowacce mace a rayuwarsa, wajen ganin ta zama ita ɗaya a duniyarsa, gaba ɗaya rayuwar Fillo ta sauya acikin irin kulawar mijinta da tarairayarsa, this week su ne a wannan ƙasar another week su ne a wata ƙasar, acikin wata guda sun manta ma da nigeria gaba ɗaya.

su ci abinci tare, su yi wanka tare, su yi bacci tare, shi kansa aikin gida tare su ke yi, su shiga kitchen tare su yi girkin su a tare, don ba sa tsayawa wani bin order, goggling girki take da irin kayan abincin ƙasar su sarrafa abinsu, kuma in suka dafa kamar ma sun fi ƴan ƙasar iyawa.

a kullum idan suna tare sai su ke ganin tamkar lokaci a tsaye yake cak, tamkar babu kowa a duniyar nan sai su biyu kacal, rayuwa su ke yi acikin kwanciyar hankali da natsuwa.

wajen ƙarfe bakwai na safiya a ƙasar Australia, Fillo na tsaye ne gaban mirror tana tattare jelar gashinta ta tufke acikin ribom, tana sanye ne da ƙaramar riga armless milk  colour da tayi matching da skin ɗinta, sai short skirt da ash color da ko gwiwarta bai kai ba.

kayan sawarta kenan a kullum tun da su ka baro nigeria, don su ne choice ɗin Turaki, ba ya son wata atamfa da danginsu, shiyasa ko da za su taho ko ɗankwali bai bari ta ɗauko ba banda kayan dake jikinta, sai da su ka sauka a ƙasar tukunna yaje ya rakito ma ta uban ƙanan kaya kamar wanda zai buɗe store.

tasa hannu a bayanta ta barƙala yay ƴar ƙara, a gajiye take gaba ɗaya, daren jiya su ka dawo daga saudia, bata taɓa jin rashin jin daɗin zaman jirgin ba sai a jiya.
madubin ya haska ma ta fuskar Turaki da ke tsaye a bayanta, wanda yasa hannu ya zare ribon É—inta gashinta, ya baje a kafaÉ—arta.

"na fi son ganin gashinki a haka".
ya faÉ—a yana rungumeta ta bayan tare da É—ora fuskarsa akan gashin yana goga hancinsa akai.
"kullum ƙara kyau kike yi, tell me the secret".

ya faÉ—a yana kama hannunta, ya shiga tracing jan lallen da akayi mata da suka je india.
"hannun ya ƙara kyau da ya fara ƙiba yanzu".

sai ya ƙara cewa,"na ga twins ɗina suna ƙara cika". ya faɗa yana zura hannunsa cikin rigarsa ya shiga shafa breast ɗinta.
ta lumshe ido kawai kamar me jin bacci, jinta take yi kamar bata da lafiya.

ganin yanda tayi wani collapse ya juyo da ita yana cewa,"what happened to my Angel?".

da narkakkiyar shagwaɓa tace,"yaushe zamu koma gida, na gaji da zaman nan ɗin, yawon ma na gaji da shi, i want to see Mum, Maama, Ummi, Kaka, Dada, Adda Zaytun, Hammah Hamid, and Boɗejo, i am missing them alot".

ya rufe ido kafin yace,"not now".
ta riƙo hannunsa kamar zata yi kuka ta ce,"haba my soul, mu tafi gobe please, Allah na gaji da cin abincin ƙasarar nan, duk komai na ci babu daɗi, ina so inje in ci tuwon Kaka".

"haba Hottie we just spend only 3months fa, ai bamu gama honeymoon ɗin ba, ki bari mu cika 5months ɗin da Bello ya ban takardar hutu da ƙyar".
tayi shiru bata ce komai ba.

zai É—auketa ta hana shi tana faman yamutsa fuska, ya waro ido yana cewa,"why?, wani abu na damunki ne yau?, duk naga kin yi wani iri kamar mara lafiya, tell me ina ne yake miki ciwo?".

ta wuce ta barshi bayan tace,"idan ka É—auke ni zan iya yin amai".
ya bi bayanta da kallo, har sanda ta kwanta kan gado kamar wata mage, duk sai yaji tausayinta ya kama shi, may be har yanzu stress É—in jiya bai rabu da ita ba.

ta buÉ—e lumsassun idanuwanta ta kalle shi kaÉ—an tace,"i want to sleep".
ta faÉ—a tana mayar da idonta ta rufe.

ya cire bluetooth ɗin dake maƙale a kunnensa ya ajiye akan mirror, tun da tace she want sleep tana nufin yazo ta kwanta a jikinsa, dan in dai ba dole ba bata taɓa iya bacci in ba ajikinsa.
ya hau gadon tare da kwantar da ita a jikinsa, a hankali yake shafa bayanta.

_tauraruwa ɗawisu, a Mata ni banga kamarki ba Fulani Nah. ke ce gaba domin kin ba su rata, tauraruwa ke ce me haska Mata, ko ince autar Mata don kina da gata, ba mai taɓaki in bar shi, me sonki dole in so shi...ehh ki yi ta farin ciki wurina kenan, in ga kina ta dariya shikenan, komai kike so zana zam yi miki sannan, abin da ba ki so in daina wannan, sannu sha yabo kece abar yabawa, Allah ya tsareki Mata ta kirki, Fulanin Turaki._

cikin golden voice ɗinsa yake rera mata waƙar a kunnenta, waƙar da a lokaci ɗaya ta kore baccin da take ji ɗin, wannan waƙar ta M Sharif da zata ce ita ɗaya ya iya a waƙar hausa, ita ma ɗin ya iya ne just becouse of her.

a kullum bai rera mata ita ba yay sama da sau biyar, su na aiki yana rerawa, in tafiya suke a mota, balle kuma ta lafe a jikinsa.
hatta bishiyar da su ke zama a ƙasanta in sun je beech za ta iya cewa ta haddace baitin.

Turaki yay ta ƙoƙarin da zai hanata baccin, don so yake yi ta tashi su yi excercise, ba ya so ta koyi lalaci tun da wuri haka, and ya fara ganin alamu 3days ɗin da suka wuce.

tana kuka kaÉ—an tace,"don Allah Jannaty ka barni in huta, shiru nake so ko da banyi baccin ba".

"idan kuma kika yi baccin fa?".
"zan so hakan, domin shi kaɗai ne abin da nake buƙata a yanzu".

"ki bari sai da daddare, yanzu kina kwanciya za ki cika É—akin nan da minshari sai kace rago na kuka, duk ki cika min kunne ina tsorata".

babu shiri ta miƙe a jikinsa, ta sauka akan gadon tare da ɗaukar pillow, sai da taje bakin ƙofa sannan ta tsaya ta saita kansa ta jefa masa pillown.

"kai ne kake minshari ba ni ba, É—akin nan ma shaida ne. ka sha zamanka kai É—aya, bye".

yana dariya ya taso, ganin hakan tayi saurin jan ƙofar ta rufe tasa key, bata ko cire key ɗin a jiki ba gudun kar ma ya buɗe da spare, ta nufi ɗayan bedroom ɗin, don tana so ta huta ne sosai a yanzu, duk jikinta take jin ba ƙwari balle daɗi, ga zuciyarta da ke ta tashi, burinta tayi amai kawai ko ta huta, amma aman yaƙi zuwa.

*BAYAN WATA ÆŠAYA.*
*Nigeria.*
[9/7, 02:02] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*57*
*ƙarfe tara na safe.*

tun daga ƙofar gidan zaka shaida ana wani babban taro a gidan, taro irin na bikin aure.
motoci ne iri-iri daban danƙare daga wajen gidan, a yayin da gate ɗin gidan yake a wangale gaba ɗayansa, wasu mutanen na shiga ciki wasu kuma na fita.

Khaleel ne tsaye a bakin gate, wanda yake ango a yanzu, waya ce kare a kunnensa yana faÉ—a akan abin da ban san menene ba.
Sameer ya iso wajen a lokacin yana cewa da shi,"Hammah yace kaje gida ka same shi".

sai a yanzu na fahimci da wanda yake faɗan a wayar, amaryarsa ce suke rigima akan irin ɗan ƙaramin lamarin nan da ba'a rasa shi tsakanin kowanne ango da amaryarsa.
"to ba zan bayar ba, in za ki haƙura ki haƙura".

daga cikin wayar ɓangaren Rashida ta ce,"haka kace?, to zaka san kayi da ƴar halak, wallahi sai in ce ma ba za'a kawo ni gidan naka ba".
ita ma tayi maganar a fusace kamar yanda shi ma yayi.

"hakan zai sa ki burge ni".
ya faɗa yana kashe wayar ya jefa cikin aljihu, ransa a ɓace ya nufi mota ya shiga.

daga cikin gidan, idan ka shigo compound, zaka kutsa ne ta cikin tarin jama'ar da ke ta hayaniya su na kaiwa da komowa wajen aikace-aikace, wasu na wucewa da manyan kuloli na abinci, yayin da wasu ke tsaye akan babban kaskon da ake suyar nama a cikinsa.
idan ka lura da part huɗun da ke jere, za ka fahimci a ɓangare na uku daga ɓangaren dama, wanda shi ne ɓangaren Hajiya Ramla, anan ne taron mutanen yafi yawa, don ga takalman jama'a nan birjik daga wajen ƙofar parlon.

a yayin da ka shiga cikin parlon, zaka tarar da manyan mata masu ji da kansu, waɗanda suka sha ilimin boko, boko ta ratsa su ta ko'ina, waɗanda mafiya yawan su ma'aikata ne a ƙarƙashin federal government.
wasu na zaune akan kujera yayin da wasu ke zaune a ƙasan carpet ɗin da aka malale duka parlon da shi, kowa na hira da abokin zamansa, hayaniyar dai tayi yawa wacca ta kai ga har ba'a iya jiyo sautin muryar wata dattijuwa da ta shigo ciki tana kiran sunan Hajiya Ramla.

a lokacin ne kuma Hajiya Ramla ke sakkowa daga saman bene tare da É—aya daga cikin amaren da ake aurarwa wato Samha.
magana suke yi yayin sakkowar ta su inda Samha ke ta ƙorafin hayaniyar.

"na nemi Nihal na rasa, ki lalubo min ita acikin taron jama'ar nan don Allah, ta zo driver ya kaita su karɓo mana ɗinkin mu. kina kallo ma Fillo bata sami saka ankon ɗaurin auren nan ba, haka Babana ya zo ya sakani a gaba yana ta kumbure-kumbure, ni ban san ya akai ku ka kaiwa ɗan shiriritar tela ba".
Chapter 155 · 0% Book details