Sashe 122
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ita da ta gansa ma sai da tayi mugun tsorata saboda kumburar da ya yi kamar an hura shi, a yacca yake ma zaka ce gawa ce, har yanzu ta kasa kwatanta abin da taji a lokacin da ta gansa da kuma abin da take ji zuwa yanzu.
kawai sai ta rufe idonta tana hasko lokacin da ta gyara masa zaman hannunsa akan gadon a sanda ya buƙaci hakan, lokacin da taji ta kasa rabuwa da hannun nasa ta riƙe tayi masa irin riƙon da bata taɓa yiwa hannun wani mahaluƙi ba, har yanzu tana jin sautin muryarta a kunnuwanta da suka dinƙa fita da amo na tsananin tausayi suna jera masa kalmar sannu tamkar yawun bakinta zai ƙare, kuma a sanda take ji a jikinta kamar yana buƙatar wani abu daga gareta sai taji ya riƙo ɗaya hannunta ya zura ma ta farar takarda, wannan farar takardar da ke ɗauke da baƙin rubutu me ɗacin ɗanɗano, rubutun da take ji gwara a soketa da mashi akan abata karatunsa kuma a alaƙantata da shi, rubutun da taji ya tsayar da wani dunƙule abu a maƙoshinta ya hana ko da yawu wucewa, ita dai ta san ko kaɗan bata son Turaki, daidai da bugawar sakan na agogo ba ta taɓa jin wani abu me kama da sonsa a cikin zuciyarta ba, tausayinsa kawai take ji wanda shi ma daga Allah ne, amma ta rasa dalilin da yasa ta damu da sakin da ya yi mata, ta rasa reason ɗin da yasa take jin kamar ta mutu akan wannan sakin.
ƙwayar idonta ta ƙara haska mata san da ta ɗauki tsayin daƙiƙu uku tana kallon takardar kafin ta iya ɗauke idonta daga kai ta sauke su akansa da yake kallonta da wani rauni da zata iya cewa ta gani acikin ƙwayar idonsa, ta san lokacin da idonta ya manne acikin ƙwayar idonsa, amma ba zata ce ga sanda hawaye masu azababben zafi suka shiga sauko ma ta ba, ta san dai ta ɗau tsayin lokaci tana kallonsa har sai da shi ya ɗauke nasa idon akanta ya kauda fuskarsa gefe, kauda fuskar da yasa taji kamar an tsikareta, tayi saurin miƙewa tana sakin hannunsa da ta riƙe ta fita da ga room ɗin tana danne kukan da yake cinta, kukan da har yau kowa ya rasa na menene har da ita kuwa, kuma kukan da har yau yaƙi tsagaita ma ta.
hawaye su ka sauka akan foundation ɗin da me makeup ke blending ma ta, me kwalliyar taja tsakin ƙorafi tana matsawa da baya da cewar,"haba ke kuwa don Allah, haka fa jiya ma kika yi mana ki kasa akai ta westing time. idan ba za ki iya daina kukan ba kice a fasa yi miki mana ki daina wahalar da ni, ni wallah ban taɓa ganin amarya me masifaffan kuka ma irinki ba".
tai maganar da muryar ɓacin rai.
kowa sai ya hayayyaƙowa Fullo akan kukan da take yi sam bai dace ba, ran kowa ya ɓaci aka fara fita daga ɗakin ana barinta, Maijidda da tsananin tausayinta ta kamata suka shiga toilet ta wanke ma ta fuskar sannan suka dawo, me kwalliyar taƙi tasowa, duk da kuɗi za'a biyata masu yawa bata jin za tayi ta yin aikin wahala haka, har sai da Ammi ta shigo tayi magana tukunna ta miƙe tana jaddadawa Fillo akan kar ta ƙara ɓata ma ta aiki.
sharp sharp akayi kwalliyar da tayi bala'in haska Fillo, ta dawo tamkar ba ita ba, aka fito da ita cikin shigar fulani kamar ka saceta ka gudu, Maijidda ta dinga roƙonta akan ta daure tayi murmushi ta kore damuwar fuskarta kar tayi musu irin ta jiya, duk ta yanda ta so ta yi hakan ta kasa, har sai da suka shiga parlon Maudo taji Dada na ba da labarin.
"ehh mana, ai ni ban taɓa ganin ƴar banza mata ba irin wannan tsohuwar, ke ni da naje asibitin ma ban san sanda na tofar da yawu ba da na ganta, kin ganta kuwa a fige kamar figaggiyar kazar da bata kama abinci ba, naji haushin kaina ma da na zauna waje ɗaya ina ta masifa banje munyi ido huɗu da ita ba tun farko ta raina kanta, muna haɗa ido na zabga ma ta harar da ta fi tata, tana ta maganganunta ni dai na kirawo likita nace masa ga sabuwar mara lafiya nan".
ba ta san lokacin da siririyar dariya ta suɓuce ma ta ba, kuma cikin sa'a Nuratu ta ɗauketa hoto a lokacin, hasken camerar yasa ta ɗago ido karaf camera woman ma ta ƙyasta ma ta, sai kawai taji abun ya burgeta hakan ya bayyanar da dukka kyawawan fararen haƙoranta, suka fito cikin wani salo na burgewa da ɗaukar hankali, idanuwanta su ka yi wa ta lumshewa suka buɗe ta kalli me hoton da irin kallon da ke tsuma zuciyar duk wani lafiyayyan namiji.
tafin da aka fara ana waƙa irin ta su ta fulani sai taji a lokaci ɗaya yana tafiya da damuwar da take ciki, yana tafiya da wannan tarin hawayen da ke cikin ƙwayar idonta yana musanya shi da murmushi me faɗi.
*Gombe.*
"ka yi wankan?".
Bello ƙaraye ya tambayi Turaki lokacin da ya sakko daga upstairs.
Turaki bai ce da shi komai ba ya wuce dining, da ga yacca yake tafiya zaka san bai gama warwarewa ba, har yanzu jikin nasa da saura, duk ya bi ya rame, Bello ya taso shi ma ya isa dining É—in yaja kujera ya zauna.
"me za ka ci na zuba maka?".
ba tare da Turaki ya kalle shi ba yace,"mene aciki?".
Bello yana nuna masa flask na abincin guda biyu yace,"nan fried suppagetti ce, nan kuma tuwan shinkafa miyan agusi".
Turaki ya sauke numfashi yana kwantar da kansa jikin kujerar dining É—in ya ce,"couscous na ke so da miyan hanta".
Bello yay ta kallonsa before yace,"akwai data a wayarka?".
Turaki yay masa wani kallo, kallon da ya shaidawa Bello abin da yake nufi, hakan yasa shi cewa,"to ni dai duk da ba'a ji da ni a gidanmu irin yanda ake ji da kai, na rantse da Allah ban taɓa shiga kitchen da sunan girki ba sai dai in shiga in kwasa, to tsakani da Allah ta ina zan san yanda ake dafa wani couscous balle miyar hanta, yunwar dare dai ta taɓa sawa na dafa ƙonanniyar taliya, idan kuma za ka ci irinta yanzu in shiga kitchen ɗin".
Turaki ya harare shi tare da jan tsaki. Bello yace,"to ai shiyasa nace ka ban wayarka sai in yi dowloading vedio, ina ce ai kuna da komai ko?".
jin Turakin bai tanka masa ba yace,"yanzu dai tun da babu wanda kake so ɗin ka daure kaci tuwon shi ma ai ɗan uwan miyar hantar ne, kafin a kira Maama a faɗa mata, kaga tun safe baka ƙara cin komai ba kuma Dr ya hanaka zama da yunwa".
Turaki ya ture plate ɗin da ya ajiye masa a gabansa, Bello ya ɗaure fuska yana cewa,"ban da ma dai girma irin na rashin lafiya me zai sa in zauna ina biyewa ƙaton gardi irinka ina yin nan nan da kai kawai saboda baka da lafiya, ehh tou sai kuma girma irin ta ƴan'uwantaka, kuma itama gaskiya na ga zaka cutar da ni sai a koma abota irin ta haɗuwar gate rabuwar bakin gate".
yay tsaki,"haka kawai mutum Allah yay masa gata ya ba shi mace ya ta shi ya korata gidan iyayensu, Allah ma ya rufa maka asiri da wata billahi da ka ɗanɗana kuɗarka, ka bar ganin ina tare da kai ba komai zan iya yi maka ba kamar yanda matarka zata yi maka, banda ma rashin tunani da rashin shawara irin naka, da ka san Baffa yayi maka gate da gidansa ai da ka dawo sai kace ka mayar da ita, da tuni yanzu kana gaban Maama ana tarairayarka kamar ƙwai, abincin ma a baki ake baka ni kuwa duk abinka wallahi sai dai kaci da kanka ko kuma mu koma asibiti aci gaba da zaman jinya".
Turaki ya kalle shi da takaici ya ce,"Bello when za ka zama me cikakken hankali?".
Bello yana kai lomar tuwa ya ce,"ka siyo min kawai maganin jiran lokaci".
Turaki zai yi magana akayi sallama a parlon, Bello ya kai idonsa kan Hamid, yay masa bismilla da ya ƙaraso, ya iso wajen nasu suna ta cewa ya zauna yana ce musu a'a.
yana kallon Turaki ya ce,"akwai room guda É—aya da babu key É—in sa".
Turaki ya rufe ido ya shafo wuyansa, kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce,"wanne room ne?".
Hamid yace,"wanda ke downstairs".
Turaki ya sosa girarsa sannan ya ce,"bari na dubo maka".
ya ta shi ya shiga bedroom ɗin Ilham da ke nan ƙasa, ya buɗe drowern madubi ya ɗauko makullayen da suke ciki duka, ya dafe kansa da yaji yana mugun sara masa, kafin ya fito ya bawa Hamid ya ce su gwada dan bai san wanne ba ne aciki.
Hamid ya fita bayan yay musu sallama, Bello ya kalli Turaki da damuwa ke fito masa ɓaro ɓaro me haɗe da tsoro ya ce,"Dr ya kawo maka result ɗin ne?".
Turaki ya ce,"bai kawo ba, ya dawo ranar kuma sai ya tarar mun tafi hospital, but ya kira ni É—azu ya ce she is not pregnant, ni dama na san zance ne irin na BoÉ—ejo kawai, da na kusanceta ai ban bari sperm ya zuba a ciki ba".
Bello ya tallafe haɓa yana dubansa ya ce,"ɗan ƙara min haske mana MT, kaga ni ma na kusa shiga da ga ciki and bana so na fara tara ƴaƴa da yawa, anyway before kace min ɗan iska, ni dai tsakani da Allah ban ga abin ƙi ba a tare da yarinyar nan Ilham ba da har ka yi kuskuren sakinta MT, Mace irin cikakkun matan da ake so da suka haɗa komai, waccan kam ta zo sai kama sha wahalar raino kamin jikinta ya ginu".
Turaki ya cika bakinsa da iska sannan ya ce,"a wurina sakinta da nayi ba shi ne kuskure ba, babban kuskure a wajena shi ne da bana iya sirrinta abuna dole sai na faÉ—a maka".