Sashe 13
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yunƙurawa tayi ta tashi ta nufi jakar kayanta ta zuge zip ɗin, sai kawai ta zubawa kayan ido, bata san wanne zata saka ba dan yau Kaka ta manta bata ɗauko mata wanda zata saka ba. Kamar zata yi kuka ta shiga ɗebo kayan tana fito da su, kayan duk sun tsufa da yawa, kwana biyu Amir bai yi mata ɗinki ba kasancewar ba shi da kuɗi, kullum haƙuri yake bata.
Atamfar ta ɗaya ce me kyan gani ta sallah ƙarama da ya ɗinka mata, kuma da so take sai babbar sallah zata kuma sakata.
har tayi choosing wata atamfarta leda sai ta tuna da cewar Amir yace zai zo anjima shi da abokinsa. dan haka sai ta ajiyeta ta É—auko me sabuntar full cotton ta saka.
Ɗinkin riga da skirt ne, ya zauna ɗas ajikinta, rigar ta kwanta a shafaffen cikinta, breastcuff ɗinma yay dai-dai da breast ɗinta maidaidaita, ƙafar nan tata ƴar sirit acikin skirt ɗin.
kayan ta maida ta ɗauki ɗankwalin ta fita, wurin Maijidda zata je tayi mata ɗauri irin wanda ta taɓa yi mata Amir yay ta santinsa.
don ita ba iya É—aurin É—ankwali tayi ba, tafi gane ta saka hula akanta.
Tana fitowa su kai kiciɓis da Kaka ta dawo, da mamaki ta ke kallon Kakan, wadda kana gani kasan cikin ƙarfin hali take.
Saurin riƙeta tayi suka shigo ciki, Kaka ta zauna ta riƙe kanta da taji yana sara mata sosai.
"sannu Kaka, ni dama tun jiya nake cewa ba kya jin daÉ—i kika dage min ke lafiya kike".
Fillo tayi maganar kukan da ke bakinta na shirin fitowa.
Kaka tace,"ni ƙalau nake...ciwon kai ne kawai, kuma ina shan magani zai daina".
Cikin sauri Fillo ta miƙe ta shiga ɗaki ta ɗauko panadol da ruwan adu'a da take sha ta kawowa Kakan. Kaka ta karɓa tasha sannan ta kwanta ta rufe idonta kamar mai bacci.
Fillo dai kallonta kawai take yi, tsoro da fargaba fal ranta, idan mutuwa tayi mata haka ya zata yi?, ina zata kama?, wa zai zama gatanta?, shikenan sai ta dawo ainihin maraniya ta gaske.
Hannu tasa ta goge hawayen da ya sakko mata, ta kama hannun Kaka ta riƙe gam.
Kusan minti goma Kaka ta farka daga baccin da ya fara É—aukanta, ta kalli Fillo da ta rafka uban tagumi alamu na nuna hankalinta ma gaba É—aya baya jikinta.
Sau uku ta kira sunanta ba taji ba, sai da ta bubbugi kafaÉ—arta.
"tunanin ne kike?".
"kin farka?".
Tamyaryoyin suka fito daga baku nan su a tare, Kaka ce ta fara amsa mata da cewar,"ehh na tashi amma yanzu zan koma".
Ita kuma tace,"to ki koma dan Allah, ƙila isassan baccin da ba kya samu ne kwana biyu".
Kaka dai kallonta ta ke yi, tunanin da inda zata fara yi mata bayani take, kamar da wuya ta yarda taje tayi aikin nan, ba don komai ba ganin a halin da take ciki, sannan babbar damuwarta ma ta ya za'a sami jituwa tsakanin Fillo da su Nihal?.
Da ace Zaytuna ce kaÉ—ai to ba zata ji wani fargaban aikata ba.
"yau ba'a gama abinci da wuri ba, ko na tambayo miki Yami?".
Kaka tace,"a'a naci zuwa anjima...yanzu tashi za kiyi kije kici gaba da aikin dana baro".
Fillo ta buÉ—e baki tana duban Kaka da irin kallon mamaki. murya a kumbure tace,"ba ki da lafiyar ma ba za su yi miki uzuri ba Kaka, ni babu inda zanje na barki ke É—aya a haka babu lafiya, suyi aikin da kansu ko kuma su nemi wata".
Kaka ta kwantar da murya tace,"a'a Halima ba haka za'ai ba, kinga aikin nan ma fa ba wata wuya ne da shi ba, daɗewar ma da kika ga ina yi saboda mara lafiyar gidan ne, hatsari yayi me muni yana buƙatar kulawa, zama kawai za kiyi idan yana da buƙatar wani abu kiyi masa, idan dare yayi Hajiyar ta sami zama shikenan sai ki taso kiyi tahowarki...kina gani fa kula da shi kawai aka ƙara yawan albashina ya koma har dubu ɗari".
Fillo ta daɗa ɓata fuska babu alamar zata amince da zuwan tace,"yau ya kula da kansa, gobe naje in Allah ya kaimu".
Ta faɗa tana miƙewa ta fita ta wuce ɗakin Yami, babu kowa a falon su, tana ta sallama ba'a amsa ba. ba tayi mamakin jin shirun Yami ba, wataƙila tana can wurin aiki tana lura da masu yi, tun da ita da Kaka ne manya.
Maijidda kuwa ta san ba zai wuce ta kaɗa yawonta ba, ta ɗaga labulen zata fito sai ga Yami ta dawo. kular abincin dake hannun Yami ta karɓo ta shigo ma ta da ita, gaisawa suka yi ta ke faɗa mata Kaka bata da lafiya.
jin hakan Yami ko zama ba tai ba ta suka fito suka wuce, idanun Kaka na bisa ƙofa suka sameta.
Yami tai mata sannu Fillo kuwa ta shige ɗaki dan ma kar Kaka ta ƙara tada maganar zuwanta cikin gida, tayi shiru a ɗakin tana tunanin dake sakata zubar da hawaye, kiran Yami yasa ta fito.
Yami ce ta lallamata ta yarda da zuwan, kafin ta wuce sai da ta ƙara komawa ɓangaren Yami tace da Maijidda dan Allah ta kula da Kaka bata lafiya, yanzu zata dawo ba jimawa zata yi ba.
A compound ta tsaya ta rasa entrance ɗin da zata nufa, ƙofofi ne suke kallonta na part har guda guɗu, ita bata san ina Kakan ke zuwa ba, ita bama ta taɓa shigowa nan ba, kuma bata ga kowa da zata tambaya ba, kuma ba zata iya zuwa wurin me gadi ta tambaye shi ba.
Ta nan tsaye Khalil yazo ya wuceta, fitarsa kenan ya dawo saboda mantuwar da yayi. yafi minti biyar kafin ya kuma fitowa, ya ƙara wuceta. sai da zai shiga mota sannan hankalinsa ya ba shi kamar fa mutum ya gani tsaye har 2 times.
[8/9, 19:25] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*©ï¸Halima h.z*
*9*
Khalil ya kalli me gadi daya buÉ—e masa gate,"waccan fa?". ya tambaye shi yana Indicavit masa Fillo.
Me gadin yace,"ehh tou Yallaɓai nima dai bayan fitowata daga banɗaki nan na ganta tsaye, ina ce ma cikin masu aiki".
Khalil ya maida kallonsa ga Fillo, ba fuskarta yake kallo ba, side view É—inta kawai yake iya gani, tsinin hancin nan ya fita ta gefe kamar allura. to ai kaf cikin masu aikin babu fara kamar wannan, infact bama sa gari dukansu, banda tsohuwar da ya gani jiya su Samha suka ce masa ita ke aiki yanzu kamin a sami wasu.
to ko dai ba mutum bace?, banda haka ya za'ai bawa yazo cikin rana ya tsaya sama da minti biyar, kuma bai ganta da jakar kaya ba balle yace baƙuwa ce ta shigo, to wannan ƴar ƙauyen ma baƙuwar wa zai ce?, yana da tabbacin ba tasu bace, and cikin yaran gidan babu me yin ƙawance da wannan villager ɗin.
ba tare da ya dubi me gadin ba yace,"baka ga lokacin da ta shigo ba ne?".
"a'a ranka ya daÉ—e, bata nan ta shigo ba gaskiya, dan ko second É—aya banyi da shiga É—aki na É—akko radio ba na fito, can kuma ina É—aga kai na hangeta tsaye a wurin".
mamaki ya kama Khalil, ya bar motar a buÉ—e ya nufi inda ta ke, me gadin ya mara masa baya.
taji zuwan mutum wurin, taga kuma inuwarsu a ƙasa inda idonta yake kallo, amma sai tayi kamar bata san da zuwan kowa ba. ai yana kallonta ɗazu yazo ya wuceta yay shigewarsa ciki, ya ƙara fitowa ya wuceta ko sannu kamar bai san darajar ɗan adam ba.
To yanzu da ya dawo ya tsaya gabanta me ya dawo da shi ko kuma me zai mata?, tukunna ma shirun da yay bai yi magana ba yana jiran cewarta ne?, ashe kuwa wannan ranar zata ƙare akansu.
Shi kam Khalil tsayawa yayi yana ƙare mata kallo da yanda ta ke wasa da yatsun hannunta, yatsunta sirara dogwaye gwanin sha'awa, farcenta fari ƙal da shi.
abunda zuciyarsa ta raya masa shine yarinyar kurma ce ko kuma makauniya, tunda ga shi dai ko yanzu da ya tabbatar tasan da tsayuwarsu a gabanta ko motsi bata yi ba, tana nan kamar wadda aka sassaƙa. yanayinta ne kaɗai zai nuna maka ba'a waye ta ke ba, amma kyawun surarta ba zaka taɓa cewa hakan ba.
"lafiya dai?". Ya tambaya idonsa tarr akanta.
Ta ɗago kyawawan idanuwanta farare ƙal da babu ko kwalli ta ɗan kalle shi, tukunna ta mayar da idonta ƙasa tace,"aiki nazo yi?".
Da mamaki yace,"Wanne irin aiki?".
Har yanzu idonta na ƙasa ta ba shi amsa da cewa,"ni dai haka aka ce nazo nayi aiki, Kakata ce ke yi, ita kuma yau bata lafiya".
Khalil ya gyara tsayuwa tare da cewa,"kuma sai tace miki idan tazo aikin cikin rana ta ke nema ta tsaya?".
ta girgiza kai tace,"a'a, ban san inda zan shiga nayi aikin ba ne".
yana daɗa ma ta duban tsanaki, a cikin ƴan ƙauyen ma wannan lamba ɗaya ce.
yay wani guntun tsaki yace,"shi kuma bakinki wari yake yi da ba za ki iya buÉ—e shi kiyi tambaya ba?".
muryarta tayi sanyi yayin faÉ—in,"ai banga mutane ba ne".
Yay mata wani kallon up and down na ban haushi sannan yace,"shi me gadin da kika gani dodo ne ko?".
Fillo na ƙifta idanuwa ta ɗago zata dube shi taga har ya bar wajen, tabi bayan nasa da kallo, saurin tafiya yake amma ba zaka gane hakan ba a lokaci ɗaya.
Tana jan yatsunta hannunta tace da me gadin,"Baba ina zan shiga?, ginin ne na gansa da yawa".
"ko dan gaba in kika je wuri ki dinga tambaya, ai matambayi baya ɓata".
Me gadin ya faÉ—a yana yi mata nuni da part É—in Hajiya Madina.