← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 176

Sashe 3

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"lafiya?". Maijidda ta tambayeta.
"mu juya don Allah".
"saboda me?".
"ni wannan gaisuwar sarautar har ga Allah ba ƙaunarta nake ba. ko waye ma haka a ɓangarenmu oho".
ta ƙarasa faɗa da jan tsakin ƙorafi tana ƙoƙarin juyawa.

Maijidda ta fizge hannu tana cewa,"ai idan kinga na koma to tabbatarwa nayi ba wanda nake zato bane ya shigo wajen nan. haka kawai kiyi mana buƙulun ƴan silallan da zai bayar".

"banza mayyar kuɗi, wallah idan ba kiyi wasa ba da wannan shegen son kuɗin naki za'a cuceki". Fullo ta faɗa tana barin mata wajen ta fice da sauri gudunma kar Kaka ta hango inuwarta ta ƙwala mata kira.

tana fita ta nufi famfo ta wanke mangoro, ta dawo ta zauna kan wani É—an tudu tana sha. kusan tsawon minti biyar tana zaune a wurin, kuma zaman na dole, duk gudun kar tayi gaisuwar da bata da niyya.
a wajen Maijidda ta dawo ta sameta, ta zauna itama tana cewa,"kin gani, dubu biyu ce ya bawa kowa. kema ga naki na karɓo miki".

kallo ɗaya ta yiwa kuɗin ta ɗauke kai, kuma tana juyawa gefe idonta ya sauka akansa, yana tafiya cikin takun isa, taƙama da cikar izza. duk tsayin zamanta a gidan bata taɓa ganin me kalar halittarsa ba, hakan yasa ƙananun laɓɓanta taɓewa kan ta dawo da kallonta ga Maijidda tace da ita.

"waye wancan É—in? tunda naga ke babu wanda ba ki sa ni ba acikin gidan nan saboda shegen shishshigi...cikin masarauta ma idan aka je yanda kike faÉ—ar sunan jama'a kamar kece uwarsu".

"kanki ake ji. yanzu amsar tambayarki zan baki ko na jira ki gama neman maganar?". Maijiddan ke maganar tana ta shan mangwaronta.

"ki riƙe amsarki kar ki faɗa ai ba damuna yayi ba. dama naga ne ban taɓa ganin irin halittar bane acikin gidan nan tsawon zamana".

"to sunansa Turaki". jin sunan da Maijidda ta ambata ya ƙwala ƙarar sautin wani abu acikin kanta, babu shiri ta miƙe a zabure tana gyara ɗaurin zani.

"me kika ce?".
"ba ki ji me nace bane hala? to nace Turaki ko".

lokaci ɗaya idon Fullo ya manne a bayan Turaki da ke tafiya yana kusan kaiwa ga barin harabar ɓangaren masu aikin gaba ɗaya. a hankali kuma idonta ya rufe, cikin duhun idanunta na haska mata sunan Muhammad Turaki da ke jikin farar takardar nan da babu zanen komai ajikinta sai na sunansa.

"tashi muje Maijidda".
"zuwa ina?".
"ina wannan baƙar ledar da na baki ranar bikin gimbiya Safiyya?".
"tana É—akin Yami".
"je ki É—aukota da sauri. ki sameni a bayan tanki cikin lambu, ki taho da ashana dalon Allah".

_till we meet in the next page! Your Comment will make me to continue or stop._

*dont forget to vote, react and share to other groups please🙏*
[8/6, 18:33] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya

*3*
*Dare, 20:45pm.*

Ƙafafun Hajiya Madina suka shigo cikin ƙaton parlon, wanda ƙamshinsa ya haɗe da sanyin acn da ke hurawa ya haɗu ya bada wani sanyin ƙamshi me motsa zuciya.
Jikinta sanye da ash abaya wadda taji adon stones ajiki, ƙyallin stones ɗin sai wurgawa suke ta cikin hasken fitilun parlon. Ganin Ƴaƴanta ya saka ta sakin murmushin da bata shirya masa ba, tana ƙaunar yaran fiye da yanda take son kanta, kowa yasan da hakan, abu ne ma da kamar tayi tambarinsa a goshinta.

Tana tsaye daga bayansu tana ƙare musu kallo cike da so da ƙauna, su kuma hankalinsu ya tattara kan tab ɗin da ke kan cinyar Sameer su na kallon pixx ɗin da su kai ɗazu na birthday ɗin Turaki. Gyaran muryar da tayi ne ya ankarar da su zuwanta, suka ɗago a tare su na kallonta fuskokinsu na washewa da murmushi.

Ta zauna a kujerar da ke fuskantarsu tana faɗin,"shi ne aka kasa jira nazo, wannan cin amanar har ina?". Tayi maganar da sigar wasa kamar wadda ke tare da ƙawayenta.

Samha ta É—auko tab É—in ta nufo wurinta tana faÉ—in,"Maama kinga wanda aka maku ke da Hammah duk yafi kyau wallahi".
ta zauna kusa da ita tana nuna mata hoton da aka É—auka a sanda Turaki ke saka mata cake a baki.

Allah ɗaya yasan me taji cikin zuciyarta a wannan lokacin, dan shi kansa murmushin da ya suɓuce a leɓenta bata san da zuwansa ba. Ta kai hannu ta shafa hoton, ƙwayar idanuwanta na haskawa da ƙyallin wata ƙauna da ke tsakanin Uwa da Ɗa wanda Ubangiji kaɗai ya san girmanta.

"gaskiya munyi kyau, kamar ban haifi Hammah ba, kalle ni wata Æ´ar suwet a kusa da shi. Wannan idan sirikata ta gani ai sai tayi jealous idan bata san wacece ni ba".
Ta faɗi hakan cike da raha, haƙoran makkan da ke bakinta guda biyu su na bayyana duka a waje.

Taci gaba da scrolling har tazo kan wanda su kai gaba ɗayansu,"kai amma wannan ma yay kyau. 1 Family na Baffa kenan". San da tazo kan wanda Turaki yake shi kaɗai ta ƙara cewa,"wannan kam shima enlargement ɗinsa zan bada a ƙara min, Hammah yayi kyau sosai kamar wani magidanci".

Sameer yace,"Maama wai duk sai kin cika bangon É—akinki da parlonki da hoton Hammah ne?".

"ƙila hakan ce zata kasance, dan sai dai idan bai yi sabon hoto shi ɗaya ba".
Sai da suka zo ƙarshe a kallon hotunan sannan ta ƙara cewa,"gaskiya Hammah ya dawo ya fito min da matar aure, dan na ƙagu naga sirikata".

nan dukansu suka haÉ—a baki wurin faÉ—in,"aiko dai Maama ya kamata ace Hammah yayi aure, sai tsofewa yake yi".
Kallon da tayi musu ne yasa babu shiri suka gimtse bakinsu, saboda kalmar tsufa da suka jinginata da Turaki.

"Hajjah nyamdu mae henyi". (Hajiya abinci ya kammala). Mai aikin da ta ƙaraso wurin a yanzu ta faɗa sanda take tsugunawa a gefen hannun kujerar da Hajiya Madina ke zaune.

Ba tare da ta juyo ta dubeta tace,"usema be habdugo". (sunnu da ƙoƙari)

"aha Hajiya Miyetti". (yauwa Hajiya na gode)
Daga haka ta miƙe ta bar wajen cikin azama dan barin musu wajen. Hajiya Madina ta ɗauke tab ɗin daga kan cinyarta tana ajeta kusa da ita, sannan ta kalla ƴaƴan nata tace da su,"my bloved ones dinner is ready".

Tare suka miƙa kaf ɗinsu suka nufa dining area, warm coolers na abinci ne zafafa masu kuɗin gaske, an jere akan dining table ɗin wajen kala shidda, kowanne cooler da kalan abinci da ke ɗauke acikinta, ta yanda kowa idan zai ci abincin zai ci favorite nasa ne.

Zaytuna ta buɗe flask ɗin da ke ɗauke da Mandi rice ta zuba a plate ta miƙa shi gaban Hajiya Madina, sannan kowa ya shiga zuba nasa abincin. Tunda suka fara ci babu wanda yay magana sai ƙarar cokula da kake ji har su ka kammala, wanda Hajiya Madina ce ta fara gamawa, ta yagi tissue ta goge bakinta.

"albishirinku". Ta faÉ—a tana jefa tissue É—in cikin durstbin.

"goro Maama". Suka faÉ—a bakunansu a haÉ—e.

"this time Baffa yayi suprising namu, mo don dow lawol vartugo". (yana kan hanyarsa ta dawowa).

"na jam kam?". (amma dai Lafiya ko?)

"jam saliiman, mo vii mo yenwi Muhammad mako tan". (Lafiya lau. Kawai yace yana kewar ganin Muhammad É—insa ne)

"daÉ—in biyu kenan, to Baba ma yiidama to Dada ma kam yiidima". (Idan Babanka baya sonka to Mamarka na sonka).

Muryar Khalil da ke shigowa cikin parlon a yanzu ta amsa lokacin da shima yake jan kujerar dining zai zauna.

Idon Hajiya Madina ya maƙale akansa tana cewa,"dume a tammi". (me kake nufi?)

Khalil yay murmushi kamin yace,"banda nuna launiyar warin fata kawai Baffa sai ya dawo gida saboda mutum guda, hala mu dama ya manta ya haifemu?". Maganar yake cike da zolaya.

Hajiya Madina tayi murmushi kaÉ—an tace,"me yasa baka yi zuciya kazo a na farkon ba?".

Shima yana murmushin yace,"to yanzu dai ba sai ya dawo ba ya tarar Hamman baya nan. Dole dai ni zai gani ai".

"Jealosy". Ta faÉ—a tana binsa da wani kallo. A rayuwar Hajiya Madina babu abin da take so irin ta ganta cikin Æ´aÆ´anta, kuma kowanne cikin farin ciki da jin daÉ—i ba a cikin damuwa ba.

Suna cikin tattaunawa akan batun gobarar da ta kama ɗazu wajen ɓangaren Lambun gidan, take basu labarin aima har an sallami me gadin wajen, saboda sakaki da yake akan aikinsa. Inda dukansu suka ce hakan yayi daidai, duba da ko lokacin da aka zo wajen bama ya cikin gida gaba ɗaya, baima san da kamawar wutar ba, balle yasan abin da ya haddasa kamawarta.

Wata matashiyar budurwa baƙa ta faɗo parlon cikin sauri me kama da sassarfa, kayan jikinta kawai zaka kalla ka shaidi itama ƴar aikin gidan ce. Wayar hannunta na ringing a karo na uku da kiran wayar ya ƙara shigowa. Ta ƙaraso gaban kujerar Hajiya Madina da sauri ta durƙusa tana miƙa mata bakinta na faɗin.

"kiyi haƙuri Hajiya, na ɗan matsa ne har kira na farko ya shigo ya yanke". Hajiya Madina ta bita da wani irin kallo, ƙwayar idonta na haskawa da ƙyallin ɓacin rai, ta karɓi wayar tana karawa a kunnenta. Kana iya jiyo sautin maganar da ke tashi ta ciki, sai dai baka iya jiyo abin da ake cewa, tsawon wucewar 120second ta miƙe daga kan kujerar da ta ke, Zaytuna taja mata kujerar baya sannan ta fito ta nufi ƙofa.

Ba tayi magana ba har sai da ta sanyo ƙafarta waje, kan step na farko da zai shigo da kai cikin parlon, sannan muryarta ta fito da wani irin amon sauti.

"Suite Eo5, 6th Floor Plot 1010 1st Avenue, By Shehu Shagari Way, Central Business District, Abuja".

Abunda ta faɗa kenan ta kashe wayar, kuma tana kan hanyar kaiwa ga ɓangaren Baffa sai jiyo horn tayi a baya, tana juyowa taga motarsa ce ke shigowa. Hakan yasa ta dawo da baya domin tarbar mijinta, inda wani farin ciki da annuri ya mamayeta.

*Dare, 20:45pm.*

"wai ha jonta a nyamae nyamdu mae na?". (wai har yanzu ba ki ci abincin bane?)

"mihari Kaka". (na ƙoshi Kaka)
"nde nyamuda dume?". (da kika ci me?)

"Kaka nabfa ƙoshi ne kawai".
"bimi daga fajira wala ko metuda wukkugo nder reduma". (ce nake tun safe babu abinda kika ƙara sawa a cikinki).
Chapter 3 · 0% Book details