← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 176

Sashe 39

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ki daina kukan nan please". ta ƙara narkewa a jikinsa tace,"ka kira min Umma". ya ɗauko wayarsa a aljihu ya kira Umman ta vedio call, idon Nuratu na kan wayar tana jiran ɗagawarta.
daga can ɓangaren Umma na kitchen lokacin ta ɗaga kiran, kallo ɗaya taima Nuratu ta hangi tarin kukan da idonta yasha ayau.

da tsananin tausayinta tace,"what's wrong Nuratu?". "Umma ki dawo dan Allah, ki dawo ki kaini a cire min wannan cikin bana sonsa, na haƙura da samun Bilal ɗin".

Umma ta sauke numfashi tace,"a'a Nuratu ba'a faÉ—ar haka, babbar ni'ima ce fa Allah yay miki da ya azurtaki da samun cikin nan, wasu na nan basu samu ba suna cikin damuwa. adu'a kawai za ki Allah ya yaye miki wahalar laulayi ya kuma sa ki haihu lafiya. kar na kuma jin kince ba kya son cikin nan kinji ko".
Nuratu ta É—aga mata kai alamar taji, tana kwance a jikin Yusuf har lokacin, ko kunyar Umman basa ji.

Umma ta kalla Yusuf wanda hankalinsa baya wajen, ta ƙara cewa. "am coming back next tomorrow insha'Allah, zuwa yamma in Allah ya yarda na dawo gida, ki daina kukan ya isa haka...irin wannan wahalar Mamanki tasha fama da ita lokacin da tana da cikinki, kamar ba zata rai ba, me ciki dama sai tai haƙuri ta jure".

sun jima suna wayar Umma na lallashinta da kwantar mata da hankali kafin su yi sallama. sai magriba Yusuf ya fito daga ɗakin su Yusra shi da matarsa, har lokacin Ammi bata san cewar suna ɓangarenta ba.
yasa Yusra ta kai kayan Nuratu motarsa, ba zai iya barinta a gidan ba tunda Umma bata nan, Inna Wuro kuma ta gaji, Ammi kuma ba sauraronta zatai ba, sisters nasa kuma kowacce na busy da study nata ba zai yiwu ya takura musu ba.

so is better ya tafi da ita can hotel É—in da yake kwana su kwana for 2days É—in da ya rage masa ya koma aiki kano, in yaso sai yasa wata nurse din ta ke lura da ita.
hannunsa riƙe da nata sukai parlon Daddy, sai da zasu shiga ya saketa, shi ya fara shiga sannan itama ta shiga. Daddy na zaune akan carpet lokacin, Ammi na kan kujera suna hira da shi, Daddy ne ya amsa sallamar tasu Ammi kam har ta buɗi baki zata amsa ganin Nuratu yasa tai shiru ta amsa a ciki.

daga baya suka tsuguna dukansu, bayan Yusuf ya gaida iyayen nasa Nuratu ma ta gaishe su, Daddy ne kawai ya amsa mata, jikinta taji yay sanyi tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo mata a lokaci ɗaya, har ga Allah bata son wannan ƙiyayyar ta uwar mijinta, kuma duk duniyarta idan aka cire mahaifiyarta aka cire Umma babu macen da take so irin Ammi, ko da ace ba ɗanta take aure ba tana son Ammi saboda tana ɗaya daga cikin mata da suke burgeta.

Daddy ya kalle su yana smiling yace,"my daughter i hope there is no worries?". kan Nuratu a ƙasa a ladabce tace,"babu Daddy". yace,"to Allah yayi muku albarka, ya ƙara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya kuma rabaki da cikin jikinki lafiya". ita ta amsa a hankali Yusuf ya amsa da ƙarfi. Ammi dai tun amsa sallamarsu bata ce komai ba.

Daddy ya ƙara cewa,"ina mara lafiyar da kace kuna ruƙo a wajenku?". Yusuf yace,"tana can gida muka barota, There was a widow's nurse who took care of her zuwa mu koma gida".

Daddy yace,"but kana following situation É—in da take ciki ko?". yace,"ehh Daddy, ko É—azu ma munyi vedio call da ita, magana ce dai har yanzu bata yi amma she is getting better".
Daddy yace,"masha'Allah, Allah ya bata lafiya, amma har yanzu baka sa cigiyar Æ´an'uwanta ba ne?".

Yusuf yay É—an jim kamin yace,"ehh Daddy banyi hakan ba tukunna, saboda kaga ba mu san ma daga inda take ba, and if mukai mata zancen da ya shafi Æ´an'uwanta da kuma inda ta fito, her mood was changing a lokaci É—aya sai ta shiga state of frenzy, so thats the reason yasa muka daina mata maganar gaba É—aya".

Daddy yace,"Allah ya kyauta, Allah masanin gaibu, but there must be something about her gaskiya, kuma ko menene lokaci zaizo da zata biɗi komawa inda ta fito, kace da dukkan alama tana da ƴaƴa?, kaga kuwa ba zata ƙare rayuwarta haka bata nemi ta koma garesu ba, ku dai kuci gaba da bata kulawa da taimaka mata, Allah ya baku lada".

a tare suka amsa da,"amin ya Allah Daddy". shiru ya gifta a parlon, Yusuf na taraddadin yanda zaima Ammi maganar tafiyarsu. da Daddy yaga shirun yay yawa ya katse abinda zuciyar kowa ke saƙawa yace,"or do you need anything?".

Yusuf yace,"a'a Daddy, dama zamu tafi ne". yace,"ok ba anan zaka barta ba?". ya ɗan sosa ƙeyarsa da kunya yace,"ehhh Daddy". Daddy ya kaɗa kai yace,"alright to ku tashi haka dare nayi, amma dai ita da ka barna nan cikin ƴan uwanta ai yafi ka tafi da ita wani hotel".
Yusuf yace,"da yake zamu je asibiti ne da safe". Daddy yace,"to yayi, Allah bada lafiya. ku tashi haka".

Yusuf na kallon Ammi wadda ke zaune tana jinsu amma kamar ma hankalinta baya garesu, ta haɗe girar sama da ƙasa ta ɓata rai.
yace,"Ammi zamu tafi". yana faɗar hakan Nuratu ta ɗago ido ta kalleta, yanda taga Ammi ta taɓe baki taji kamar an soka mata kibiya a ƙirji. Yusuf ya miƙe tsaye ita kuma ta rissinar da kai tana cewa,"mun gode Ammi da Daddy, Allah ya ƙara muku lafiya da nisan kwana me amfani".

daga haka suka fice daga parlon zuciyar kowannensu babu daÉ—i.

****
"kin tabbata ba kya jin ciwon komai?". Yusuf dake tsaye a gaban gadon Fillo ya faɗa, yayinda wata nurse dake kusa da shi ke riƙe da file.

Fillo tace,"bana jin ciwon komai Dr". ya jinjina kansa, ya karɓi file ɗin hannun nurse ɗin yay rubuce rubucensa.
ya ƙara cewa,"gobe da safe insha'Allahu zamu sallameki, Allah ya ƙara lafiya".

Fillo ta amsa da amin sannan ta ɗago ido ta kallesa, ƙwayar idonsu ta sarƙe ana juna, Yusuf yaji zuciyarsa ta girgiza, yasan akwai kamanni, amma bai taɓa zaton cewar akwai tsananin kamannin da suka kai irin haka ba bayan na wanda suke identical 2wins, a tare da wa zaisa kamannin yarinyar nan?, idon, fuskar, yanayin komai iri ɗaya ne, sai dai ya rasa iri ɗaya da na waye, tunaninsa da hasashensa ya gaza basa.

yayinda a wannan lokacin zuciyar Fillo ke ƙara faɗa mata tabbas tasan wannan fuskar ta Yusuf, sai dai ta kasa tuna aina ne, aina ta taɓa ganinta?.

_Comment ɗinku shine ƙwarin gwiwata, rashinsa shi yake sawa na hutar da kaina._

*dont forget to share, comment and vote.*
[8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

*20*
bayan sati ɗaya jikin Fillo ya ƙara yin sauƙi sosai, yarinyar har wani fresh tayi hasken fatarta ya ƙara fitowa saboda kwanciyar da tayi a asibiti me kyau, da kuma irin cimar da take ci me rai da lafiya. na musamman Hajiya Madina ke yin lafiyayyan girki a kai mata, girkin da zai ji ganyayyaki masu ƙara lafiyar jiki da kuma hanta acikinsa, tunda aka kwantar da ita duk wani abinci da zata kai baki da hanta take yin lomarsa, fruite salad kam da bata taɓa shansa ba sai da ya ginsheta. kuma tunda suka dawo bata ci gaba da zuwa aiki ba sai Kaka ce ke yi, Hajiya Madina tace ta ƙara samun hutawa na sati ɗaya sannan sai taci gaba, har wannan lokacin kuma bata san Turaki ne ya kaɗeta ba, duk zuwan da yake yi akai akai zatonta halin karamci ne kawai irin nasu.

sa fiya ce yanzu dan ko takwas da rabi bata yi ba, Kaka na daga falo tana sauraren Shaik Ibrahim Daurawa a radio, Fillo kuma na É—aki tana shiryawa.

Kaka tace,"wai ba zaki fito ki wuce ba ne?, kullum sai kin ɓatawa bawan Allah lokaci Fillo, Allah raina yana ɓaci da wannan abin naki".
daga inda Fillo take ta ɗan gwame fuska tace,"Kaka fuskar hijab ɗin ce fa ta yage shine nake ɗinkewa". Kaka tace,"uhm haka dai kike kullum da uzurin da zaki bayar, to ki bar ganin saurayinki ne Allah sai nace ya fara yi miki bulalar makara, wataƙila ki fi maida hankali akan karatun".

dariya kawai Fillo tai bata ce komai ba, amma har hangowa take wai Amir zai daketa, tana sonsa dan haka ba zata ƙi tsayawa ba amma shi ɗin tasan ba zai taɓa iyawa ba, ko wani me gangancin yaga zai gwada sai iyakar inda ƙarfinsa ya ƙare.

ta fito daga ɗakin sanye da hijab ruwan toka, hannunta kuma tana riƙe ne da qur'ani izu sittin ta rungume shi a ƙirjinta haɗe da dardumar sallah.
"na tafi Kaka". Kaka ta ɗago ta kalleta tace,"Allah ya bada sa'a, amma ku gama da wuri kinga Hajiya Madina tace ki koma aikinki yau, kya gaida Amir ɗin kice ina daɗa masa godiya Allah ya jiƙan mahaifa". tace,"tom Kaka". da haka ta fice.

daga can bakin gate wurin da ya saba zama ta gansa, a durƙushe a ƙasa da alama ya gaji da tsayuwa ne. bakinsa na motsi yana latsa counter dake saƙale a yatsansa, baƙin yadi ne a jikinsa mai taushi mara tsada wanda ya karɓi jikinsa sosai. ya kuma fito da kyawunsa na usulin bafulatani, sumar nan tasa kwantacciya ta fulani tai luff sai ƙyalli takeyi, da takalminsa da agogonsa dai-dai na me rufin asirin ubangiji.
tunda ya ɗaga ido yaga Fillo na tahowa zuwa gare shi kyakkyawan murmushi ya ɓalle a saman fuskarsa, zuciyarsa na ƙara cika da tausayi da soyayyar Halimatunsa, ruhinsa na ƙara buƙatuwa da ƙwaɗaituwar ta zama mallakinsa.

a lokacin da ta iso wurin ta sakar masa nata sanyayyan murmushi da yake motsa zuciyarsa. ta durƙusa a gabansa ta gaishesa.
Ya amsa yana kasa ɗauke ido daga dogayen yatsunta da ta rufe fuskarta da su, murmushinsa na ƙara faɗaɗuwa. sai da yay gajeriyar ajiyar zuciya sannan yace,"Barka da fitowa gimbiyar Amir, sarauniyar da ta kafa fadarta acikin zuciyar Amir, kazalika uwar ƴaƴan Amir".
Chapter 39 · 0% Book details