← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 176

Sashe 69

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya maida ƙofan ya rufe ya dawo ciki ya wuce kan kujera ya zauna.
har sha É—aya na dare yana kan computer, kuma a lokacin suka yi waya da Bello yake faÉ—a masa flight É—in 8 zasu bi gobe in Allah ya kaimu.

a wannan lokacin Turaki bai iya amsawa ba har Bello ya gaji da hello hello ya kashe wayar. zuciyarsa kawai yake ji tana bugawa, kamar yanda gabansa ya tsananta faɗuwa, me ke shirin faru da shi?, tunda yake bai taɓa jin irin haka a tare da shi ba.

doguwar ajiyar zuciya ya sauke tare da kwanciya akan kujeran, ya rufe idonsa da zummar yin bacci amma sai ya kasa, wannan faɗuwar gaban nasa ya tsananta har ya kai stage ɗin da ba ya jin zai iya yin bacci sai dai in ɓarawon bacci ya ɗaukesa.
tashi yay ya shiga toilet yayo alwala yay nafila raka'a huÉ—u, ya É—an jima yana ta adu'a kamin ya tashi ya buÉ—e closet ya É—auko pijams nasa ya saka.

gaba ɗaya ya manta da wata Fillo a ɗakin sai yanzu da zai hau kan gado, yasa hannu ya dafe goshinsa, me ya sa me shi ne?, agogo ya kalla yaga har 12 tayi babu damar ya tasheta yace zai rakata. ƙaramin tsaki yay ya hau gadon ya kwata ta gefe, ita kuma tana daga tsakiya ta dunƙule rufe da blanket sai baccinta take, baccin da bata san lokacin da ya ɗauketa ba.

wasa-wasa dai har ƙarfe ɗaya Turaki na kwance idonsa a lumshe ya kasa bacci, ya miƙe zaune yana kunna deemlight. ya matsa tare da ɗago Fillo dan gyara mata kwanciyarta, amma sai yaji cewar ba hakan ya kamata yay ba, ya rufe ido yana cije fuska sannan ya ɗagota gaba ɗaya ya kwantar da ita a jikinsa. dai-dai nan ya ƙara hasken light yana ƙarewa innocent face ɗinta kallo, hawaye duk ya bushe akan fuskar, ta tsuke fuskan kaman me shirin dambe, ga zufa da ta ke haɗawa kaman an watsa mata ruwa.

shi jikinsa ba me son sanyi bane dalilin da yasa bai fiya zama da Ac ba kenan, amma haka dole ya sauka yaje ya kunna Ac sannan ya dawo again ya É—agota zuwa jikinsa ya kwantar, da hannunsa ya dinga goge mata zufar kan fuskarta yana jin zuciyarsa na matsewa da zafi zafi.

sai yay hugging ɗinta tightly a jikinsa kanta na mannewa a chest ɗinsa, wani irin baƙon al'amari yake ji tare da shi, gefen fuskarsa ya haɗe da tata fuskar, ya kamo hannunta a hankali ya riƙe cikin nasa.
ya bayar da sadakinta amma yau sai yake jin like he can't believe cewa wannan jaririyar mallakinsa ce, halalinsa, his wife, his only wife da ya gama tsarin rayuwarsa cewar da mace ɗaya zai rayu, ba tare da sanin cewar itan bace, ba kuma tare da ya taɓa lissafin cewa zai rayu da irinta ba ma, is he dreaming?.

sai yaji wani abu me kama da farin ciki a tare da shi, ya É—ago da fuskarsa akan tata yasa hannu ya shafi gefen fuskarta, yana jin kwantaccen sajenta na burge shi, É—aya hannun kuma na cikin nata hannun yana murzawa.

maganganun da ta faɗa masa a mota ɗazu suka haska acikin kansa,_"ni me nayi maka a rayuwa ka tsane ni, ban taɓa cutarka ba haka ban taɓa munafurtarka ba, amma kai kullum burinka ka ƙuntata min, akan me?, saboda ina ƴar talakawa?, ina yi maka biyayya iyakar iyawana matsayinka na wanda nake a aiki a ƙarƙashin iyayensa, mahaifiyarka bata taɓa min kallon banza ba balle har ta nuna min tsana, amma kai ko da yaushe ka ganni burinka bai wuci kasa na zubar da hawaye ba, a wanne dalili?, idan har nayi maka wani laifi ne bisa kuskure da ban sani ba sai ka faɗa min na baka haƙuri, ba wai ka dinga muzguna min ba duk sanda ka ganni. yanzu ka karya min ƙashin hannu ka fasa min leɓe duk saboda me fisabilillah?"._

ya ɗora goshinsa kan nata yake cewa,"ban taɓa jin na tsani wani mutum ba balle kuma ke da kika taimake ni, kuma ta ya zan karya siririn hannun da nake kallo yana burgeni?, wannan bakin kuma ban san zai fashe ba Allah, but am so sorry, shikenan?".
maganganun yake yi kamar tana jinsa.

and for the very first time he felt her all over his blood, he felt as if his life depended on her, ajikinsa yake jin kamar she needed him at this time, kamar ya fasa yin tafiyar just becouse of her, duk wannan faɗuwar gaban da yake ji akan zai yi nisa da ita ne, abin da bai taɓa ji ba tsayin rayuwarsa ko da akan Maama da Zaytuna da ba ya so yay nesa da su.

A hankali ya kai fuskarsa daidai tata yana daɗa ƙarewa ramammar fuskarta kallo, fuskar rigima, fuskar kasada, sai yay murmushi yana kai babban finger nasa kan lips ɗinta yana shafawa.
Fillo dai kamar matacciya, baccinta kawai take yi. Turaki still holding her hands da ɗayan hannun kuma yana shafa lips ɗinta yake ta kallon lumsassun idanunta, zai iya rantsewa bai san time ɗin da wani fitinannan murmushi ya ƙwace masa a fuska ba, ya lumshe idanu tare da ƙoƙarin kai lips ɗinsa saman nata trying to kiss her sai kawai yaji zuciyarsa na faɗa masa,"not now, not today, but one day, in that special night, the night that will come not once, but for your entire life".

ya rumtse idonsa sosai tare da jan wani wawiyan ajiyar zuciya ya sauke, ya ɗago kansa yana kwantar kansa a pillow, ita kuma ya daɗa gyara mata kwaciyarta ajikinsa tare da jan blanket ya rufesu, sai shafa gashin kanta yake yi, duk shafa ɗaya sai yaji zuciyarsa ta buga, haka har ɓarawon bacci ya ɗauke shi.

sai gab da asuba Turaki ya farka, yana tashi yay alwala yay raka'atanil fajr sannan ya wuce masallaci saboda ya makara, ko da ya dawo masallaci side É—in Maama ya wuce, ya shiga bedroom nata ya sameta ta idar da sallah tana lazimi, anan ya zauna har ta idar suka shafa aduan tare, lokacin 6 har tayi.

gabanta ya zauna ta ɗora hannunta saman kansa, ta dinƙa jero adu'oi tana tofa masa tana hawaye, har sanda ta ɗauki kusan minti 7 a haka sannan ta ƙarashe da faɗin,"Allah ya kai mun ku lafiya ya dawo da ku lafiya, Allah ya tsare min kai, dan Allah ka riƙe ibadarka, kar kayi wasa da azkar da adu'a. Bello yace ƙilan zaku iya kaiwa har 7days, but bana jin hakan zai yiwu, in ya wuce 4days ɗin ko ka taho ko na biyoku, Allah ya tsareku".

Turaki ya amsa da amin yana me É—ago da kansa, ganinta tana hawaye hankalinsa yay mugun tashi.
"Maama lafiya?, menene?, in ba kya so naje na haƙura kawai, Bello zai iya komai shi ɗaya and beside zai sami Sameer acan".

ta girgiza masa kai da cewar,"a'a ku tafi tare, Sameer ai ya dawo jiya, yace yaje room É—inka time kayi bacci".

Turaki ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya rungumo Maama shima hawayen na sakko masa, ya tsani tafiyar nan da zai yi sam baya son yaje, dan ba shi da yanda zai yi tunda Maama tace yaje ɗin, amma ji yake kamar in yafi wani abun zai faru, kamar tafiyar tasa zai sa ya rasa ɓarin jikinsa.

Fullo dai da asuban bayan fitar Turaki masallaci ba daɗewa ta tashi, taga ita kaɗai ce a ɗakin, cikin ranta ta ƙara yabon kyan hali irin na Turaki, watakam bai ma iya kwana the same room da ita ba, ta sauko a gadon tana tafiya a hankali saɗaf saɗaf saboda har sannan tsoron daren jiya bai barta ba, abinda ta fara tunawa ma kenan da ta buɗe idonta, maciji a compound da kuma bakin gate, yo ita kuwa me zai sake tsayar da ita a wannan wurin, ai har mutuwa.

a rufe taji ƙofan sanda taje buɗewa, ta ɓata fuska ta dawo ciki ta shiga toilet tayi alwala ta fito, tana idar da sallah ana ɗauke wuta, hakan yasa a sukwane ta koma kan gadon ta kwanta tana ƙudundunewa tana adu'a a fili, har bacci ya ɗauketa.

Turaki ya turo ƙofan ɗakin ya shigo, darduman sallah kawai ya kalla ya shaida tayi sallah ta koma ta kwanta, a yanayin kwanciyar kuma yasan tsoron jiya dai har yanzu bai barta ba.
kayansa ya cire ya shiga yay wanka, komai a hankali yake yinsa gudun kar ya tasheta, 7:30am ya gama shiryawa cikin ƙananun kaya da bai cika sasu ba, ya ɗauka brief case daidai nan Zaytuna ta shigo ɗakin.

duk da ita tasan Fullo matar Turaki ce hakan bai hanata jin kunya ba da ta shigo ta tarar da shi yana kissing forehead ɗinta. sai ta tsaya ɗaga bakin ƙofan tace,"B Ƙaraye yazo". ta faɗa tana murmushi.

ya ƙaraso gabanta ya kama kumatunta yace,"ki zage ki dinƙa faɗar sunansa Bello, dan shi gatsal yake faɗar Zaytun a gabana".
tasa hannu ta rufe fuska tace,"ai ni ba ya faÉ—a a gabana".

Turaki yay murmushi yay mata side hug yace,"ki kula min da kanku, mussaman waccen fitinanniyar, dan Allah kisa ido akanta sosai kin riga dai kin san bata ji, sanya kai a hatsari shi yafi komai sauƙi a wurinta. ki faɗawa Kaka zata dawo wajenki da zama for some days dan na riga na tsoratata ba lallai ne take iya zaryan zuwa side ɗinsu da nan ba. ki sa ido akan fitarta, bata son cin abinci, bata son shan magani, na baki amanarta na baki amanar Maama na kuma baki amanar kanki, just 4days zanyi in dawo".
ya ƙarasa faɗa Zaytuna ta rungume shi.

cikin kukan da take yi tace masa,"jiya nayi mafarki Mum ta dawo, ta dawo hannunta da ƙafarta duk ciwo". ya kwantar da kanta a ƙirjinsa yana shafa bayanta yace,"ta kusa dawowa da izinin Allah, ina dawowa zamu nemota ni da Fulani".

a sanyaye tace,"Hammah bana tunanin Mum na raye".
yace,"yaro ma na riga babba mutuwa, so shekaru ba sune mutuwar mutum ba, gamu da Maama har yanzu a raye, kisa a ranki Mum ta kusa dawowa garemu da ranta da lafiyarta, zan faÉ—awa Fulani issue É—in da zarar na dawo".
Chapter 69 · 0% Book details