Sashe 174
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tukunna suka yi mata sallama suka wuce, inda suka ɗauki hanyar gidan Me Martaba domin zuwa duba Fulani Azima, wacca har yanzu ta nan kwance rai a hannun Allah, gaba ɗaya halittarta ta sauya ta koma tamkar ta ƙadangare, sai ka rantse da Allah ba mutum ba ce tun asali, wasu gashi sun tsatstsafo mata a jiki, idanunta sun yo waje ƙwayar kamar zata faɗo ƙasa, bakin da hancin sun shafe a waje ɗaya, kai abun dai babu kyan gani da kwatance.
ga duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata ya zubar mata da hawaye idan bai san abun da ta shuka ba, wanda kuwa yasan me ta aikata muddin ya ganta sai jikinsa ya mutu gaba ɗaga, tsoron Allah ya ƙara shigarka, kaji gaba ɗaya duniyar ta fita a ranka, balle kuma kaji kana son sha'awa ko mallakar abun da ke cikinta.
Maama da ke kallon bakin titi tace da Turaki,"Abie don Allah zan bayar da sadaƙa".
Turaki yay parking a gefen hanya, ya zaro ɗari biyar a aljihunsa ya miƙa mata ta karɓa sannan ta buɗe mota ta fita. "na gode Abie".
ƴar tafiya kaɗan tayi daga inda motar tasu ta tsaya, ta tsuguna agaban almajirin ta saka masa kuɗin acikin robarsa tare da faɗin,"Baba kayi adu'a Allah ya kai ladan ƙabarin mahaifiyata".
tsohon ya shiga kwaranyo mata adu'a iya adu'a, daga mahaifiyartata har ita kanta da sauran ahalinta. ta ɗaga glass ɗinta tasa tissue ta goge hawayen da ya cika mata ido, kafin ta yunƙura ta miƙe jiki a sanyaye ta bar wajen nasa.
tana cikin tafiya tayi karo da mutum, ba wai don bata ganin gabanta ba, sai don hankalinta da ya bar jikinta a lokacin.
ta sunkuya ta lalubo gilashinta ta saka, sannan ta kalli mutumin da ta tsorata da ganin nasa, tayi saurin matsawa gefe tana ce masa,"kayi haƙuri don Allah".
muryartata ƴar ƙarama kuma ƴar siririya me zaƙi ta fito ta shiga kunnen Amir ta ratsa jikinsa, ya kasa ƙifta idonsa akanta, kallon mamaki kawai yake yiwa yarinyar gabansa, wacca gaba ɗaya yasan bata kai shekara sha bakwai ba.
abun da ya sani shi ne ya san wannan halittar, sai dai bai yi tsammanin zai sake ganinta a haka ba duba da tsawon shekarun da aka ɗauka, ya sani Fillo na da ƙaramin jikin da ba lallai shekarunta masu yawa su nuna a jikinta ba. to amma duk da haka abin da matuƙar mamaki ace ita ce a gabansa haka, babu wani alamar girma a tare da ita, after all shekaru goma sha bakwai ɗin da ya ɗauko bai ganta ba.
jikin Maama na rawa ta daÉ—a ce masa,"zan wuce".
Amir yay ajiyar zuciya bayan ƙare mata kallon tsab da yayi, tabbas wannan ba asalin Fillon da ya sani ba ce, wannan me kama da ita ce sak babu wani banbanci, sai dai in ace banbancin halayya, me hakan ke nufi kenan?, wata ce photocopy of her ko kuma ƴarta ce?.
lokaci ɗaga matacciyar zuciyarsa da babu tsoron Allah acikinta taji ta kwaɗaitu da yarinyar, yaji sha'awarta ta ratsa duk wani ɓargo na jikinsa, take kuma ya fara tunanin ta yacca za'ai ya shiga rayuwarta a irin matsayin da ya saba shiga rayuwar sauran ƴan mata?, ya shiga rayuwarta kamar dai yanda ya shiga rayuwar me kama da ita.
_(hmm Allah ya kyauta, ya kuma kiyashe mu daga sharrin zuciya, dama haka abun yake, ance wasu ko zasu je lahira su dawo halinsu ba zai taɓa canjawa ba, sai dai muyi adu'ar Allah ya tsare daga sharrin mugwayen mutane.)_
sai ya sauke idonsa akansa yana kallon jikinsa, wannan sam ba wancan Amir ɗin ba ne me ji da tashen ado da ƙwalisa a zamanin baya, wannan wani Amir ɗin ne na daban, wanda halittarsa ta sauya tun yana cikin prison, ya dafe ya zama mugun baƙi, yay wata muguwar rama kamar me cutar S, ya haɗa uwar ƙasumba a fuska kamar dodo, haka kansa ma ya tara uban gashi kamar mahaukaci, duk yayi duƙunduƙun kayan jikinsa duk a yayyage, ga uban ɗoyi da ke tashi a jikinsa kana ji kasan kwanan bola yake yi.
warin jikin nasa ya doki hancin Maama, take ta duƙa a ƙasa saboda aman da ya taho mata, ta shiga kyalaya amai kamar hanjin cikinta zasu fito.
Amir ya duƙa a gaban nata shi ma, zuciyarsa na harbawa kaɗan kaɗan, abu ɗaya yake tunani wanda yake jin har in ya rasa zai iya shiga wani hali, halin da yafi wanda yake ciki muni, muddin bai samu ya kusantu da yarinyar ba zai iya rasa lafiyar jikinsa.
don haka zuciyarsa na ingiza shi ya kai hannu zai taɓa Maama tayi saurin miƙewa tana ja da baya.
"mene haka?, na fa baka haƙuri".
ya miƙe yana lashe leɓe, a hankali yace,"Ki tsaya na taɓa jikinki don Allah ko ya ya ne, idan na taɓa zan haƙura na barki ki tafi".
Maama ta shiga girgiza masa kai tana ja da baya, yanzu kam ya gama tabbatarwa ba Fillon da ya sani bace, kuma ko da ace ita ɗin ce ma ba zata taɓa gane shi ba, don kwatakwata ya fita a Amir ɗin da mutane suka sansa, shiyasa har yanzu ma Ƴan sanda suka kasa kama shi bayan wani laifin da ya ƙara aikatawa lokacin da ya fito a prison.
"sau ɗaya yarinya, sau ɗaya kawai za ki barni in taɓa ƙirjinki, ki tausaya min wallahi a bola nake kwana".
yayi maganar da kana ji kasan ƙwaƙwalwarsa ta fara taɓuwa, lokaci kaɗan ya rage ya fara hauka tuburan.
san da Maama ta kai ƙarshe ajikin wani ƙarfe, lokacin Ayan da Turaki suka iso waje, tana ganinsu ta ƙwala kiran Abie, Ayan yasa hannu ya juyo da Amir, da yake irin tsayin mahaifinsa yayo sai ya zamana tsayinsa yay daidai da na Amir ɗin.
cikin zafin nama Ayan yasa hannu ya wanke fuskar Amir da zazzafan mari, ya damƙi ƙwalarsa yana jijjiga shi har sai da ya kai Amir jikin ƙarfen da ke bayansu ya buga kansa a jiki.
"kai ba mahaukaci ba ne zuciyata ta faɗa min hakan, ubangiji yayi min baiwar gane mutane a kowanne hali suke ciki. sai na kasheka tun da ka yi yunƙurin taɓa min ƙanwata".
ya faɗa yana ta buga kan Amir ajikin ƙarfen, Turaki kuwa na gefe rungume da ƴarsa a jiki zuciyarsa sai zafi take yi masa, idan har yace zai kai hannu ya taɓa Amir to bai san me zai ya faruwa ba, don wataƙila kafin ƴan sanda su iso wajen ya kashe shi.
ɓangaren Amir kuwa abu guda ɗaya ya sani, ba zai taɓa iya ƙwatar kansa ba a hannun Ayan, bai da wannan ƙarfin ko kaɗan, hatta ruƙon da yaron yay masa ji yake kamar an jona masa electricity.
zuwan police wajen suka ƙwace Ayan da ga kan Amir wanda yake ƙoƙarin kaiwa ƙasa. banda haki babu abin da Ayan ke yi, idonsa yay jawur kamar bana ƙaramin yaro ba, police suka kama hannun Amir suka saka masa ankwa, sai a yanzu idonsa ya kai kan Turaki, yaji gabansa yay mugun faɗuwa, ya wurga ido ya ƙara kallon Ayan, jini ba banza ba, don lokaci guda ya tuna da mugun dukan da ya sha lokacin da suka yi kidnapping Fillo.
don haka tsananin tsoro ya kama shi, ya tabbatar yanzu idan Turaki ya gane waye shi to sai dai waninsa, dan haka gwara yabi Æ´an sandan, duk runtsi zai fito ya sani.
police su ka kama Amir suka saka shi a mota suka tafi. bayan su Turaki sun dawo daga dubiyar Fulani Azima, direct gidan ya wuce da yaransa, in da anan suke cin abincin dare duk friday.
ana jin tsayuwar motarsu BoÉ—ejo tace,"to ga kajin nan sun iso".
Mum na zaune kan kujera, da jaririyar Nihal a hannunta ta gama yi mata wankan yamma, tayi murmushi da jin furucin BoÉ—ejon.
Turaki ya shigo tare da yaransa, waɗanda sai da suka fara zuwa ɓangaren Baffa suka gaida shi.
jikokin gidan duk suka yi wajensa su na yi masa sannu da zuwa, ya É—auki Æ´ar gidan Zaytuna me suna Aisha.
Maama tayi jikin BoÉ—ejo tana cewa,"nayi kewar tsohuwa".
BoÉ—ejo tace,"kinga ni kuwa yau ba wanda nayi kewa a cikinku, ko babu komai bakina da na Kakarku luff babu rabon faÉ—a".
"ai kuwa tun da kika faÉ—i haka ba zan ba ki abin da na taho da shi ba".
Boɗejo da a yanzu ta ƙara zama tsohuwa tukuff ta janyo Maama jikinta tana faɗin,"haba ƙawata ƴar mutunci yi haƙuri, ai yanda bana iya fita inci ni ɗaya ban rage miki ba haka kema na sa ni".
Maama ta dubi Turaki da ya zauna akan kujera su na gaisawa da Mum, tace,"Abie ka É—auko min leda ta?".
ya kalli gefensa yay mata nuni da ledar, sannan ta miƙe taje ta ɗauko, tazo ta zauna ta buɗe ta ɗauko dublan ɗin ciki tana bawa Boɗejo, wacca ke tambayar aina suka siyo shi, ita kuma tana bata labarin yacca ta kwaso shi a ɗakin Inna Wuro.
da daddare bayan sun gama cin abincin dare, suka fara haramar tafiya gida.
Mum ta juye musu sauran teba da miyar gandar da akayi a flask tace su tafarwa da Ilham.
ko da suka koma gida Turaki ajiye su yay ya ƙara fita, ya tafi siyo magungunan da likita ya rubutawa Ilham, wacca likitoci suka yi iyaka bincikensu akan rashin haihuwarta, suka tabbatar da cewa da wuya idan ta haihu sai in kuma wani iko na ubangiji.
tana zaune a parlo tana kallo su Ayan suka shiga, tayi musu kallo É—aya ta É—auke kanta taci gaba da kallon film É—in da ake yi a mbc action.
ganin bata kula su ba Ayan yace,"Anty daga wurin Maminki mu ke".
furucin nata yasa ta mayar da hankalinta gare shi tana jin cewarsa.
"ya ku ka ƙara samun yanayin jikin nata?".
Ayan yace,"ba sauƙi, sai tsanani da ya ƙara. yau da muka je jini yana ta zuba ta duburarta, sai botiki aka tara mata ma a wajen, ta ƙara motsewa babu kyan gani".
Ilham ta saka kuka sosai tana kifa kanta akan ƙafafunta, tsawon minti biyar tana kuka kafin ta ɗago tare da ɗaukar wayarta ta shiga kiran lambar Turaki, sau kusan sau biyar kiran yaƙi shiga, ana ta faɗa mata not recherble.