← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 176

Sashe 38

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shirunta ya haɗe ta kiran daya shigo a wayarsa, ya kalla sunan dake yawo akan screen ɗin, ganin sunan Inna Wuro ya kulle idonsa da yake jin yana masa zafi, zuciyarsa ta matse hankalinsa na ƙara tashi.
minti goma sha biyar suka ɗauka kamin su iso cikin unguwar gargajiyan, da ƙyar motarsa ta shiga cikin layin, daga bayan gidan yay parking motar.

yana kallon Ammi ta mirrow ta buɗe motar ta fita ba tare da tace masa ƙala ba, yaji kamar ya fashe da kuka. sai da ta kai ƙofar gidan tukunna ta sami yaro ta nuna masa mota tace yace da mai motar ya miƙo mata jakarta. a lokacin hannu kawai Yusuf ke jira ya ɗora akansa ya saki kuka, ya san da biyu ta manta jakar.

jakar kawai ya bata ya juya ya koma mota, Yusuf tun yana kallon wucewar sakanni har ya koma yana kallon adadin mintuna, minti 1 zuwa 5 suka wuce har aka tafi goma Ammi bata fito ba, lokacin ne kuma ya ɗauko wayarsa da niyyar kiranta sai yaji anyi knocking glass, yana ɗaga kai yaga Kawunsu wanda yake Yaya ne a wurin Ammi me suna Malam Mudi. cikin sauri ya buɗe motar ya fito ya duƙa yana gaida Kawun kansa a ƙasa.

"Yusuf gidan baƙonka ne daka ƙi shiga ka zauna a mota?".
Yusuf yasa hannu ya sosa ƙeyarsa yana neman abinda zai ce, kan yay magana Kawun ya ƙara cewa,"ai Zainab ɗin ke cewa kai ka kawota kana waje, shiru shiru baka shigo ba shine nace to bari nazo naji ko munyi maka wani laifinne".

Yusuf yace,"a'a wallahi Kawu babu komai, dama na É—an tsaya ne muna waya da abokin aikina, shiyasa ban shiga ba amma dama yanzu nake niyya".

tare suka jera suka nufa gidan, suna tafe suna tattaunawa akan wasu batutuwa har suka shiga gidan, da yake Malam Mudi mutum ne me sakin fuska. acikin gidan Umma Ladi taitawa Yusuf tsiya tana cewa ko dai sirikinta zai zama ne bata sani ba da ya maƙale a waje yaƙi shigowa, shi dai murmushi kawai yake har suka fito.

da suka koma gida shi ya kwashi siyayyar da Ammi tayi ya kai part nata, sannan ya fito ya wuce na Inna Wuro, yana tafe yana duba agogo, daga lokacin da ta kirasa zuwa yanzu awa biyu kenan.
hularsa ya É—aga ya sharce gumin daya haÉ—o masa duk da cewar ba zafi akeyi ba, amma halin da yake ciki na rashin sanin a wanne hali Nuratu ke ciki yasa shi haÉ—a zufa.

babu kowa a parlon lokacin da ya shiga, tsaye yayi kawai yana kallon trolly ɗin kayan Nuratu dake tsakiyar parlon a ajiye. mamakinsa ya tsaya akan Inna Wuro dake janyo ƙaramar trolley tana fitowa daga cikin ɗakinta tana maganganun ƙasa-ƙasa, har ta ƙaraso gabansa bai iya ɗauke idonsa daga kanta ba, amsar tambayar dake ransa kawai yake so ya samu tun kamin yayita.

bata lura da shi ba saboda sababin da take tayi har sai da ta zo gabansa, shima warin asibitin da taji ne yasa tasan da tsayuwarsa a wurin. ta É—ago tai masa kallo É—aya ta É—auke kai.
"ashe kazo, nai zaton ai ko ka zama tarihi da nake ta danna maka kira kana ƙin ɗauka. baka san ni ba wata tsiyar zance kayi min ba, idan ka manta na tuna maka ɗana me wannan ƙaton gidan ya tara abinda kai baka da shi, dan haka nafi ƙarfin roƙo a wurinka Yusuf".

tasa ƙafa ta tura masa duka trollys ɗin gabansa tana cewa,"gasu nan, dama niyya nake na fita da su na ajiye su daga bakin ƙofa sai kuma Allah ya kawoka ka rage min aiki".

Yusuf dai kallonta kawai yake yi, sai da tai shiru sannan yace,"kiran da kika min na mene?".

jin yanda yay maganar ta ɗago ido ta kallesa ta taɓe baki sannan tace,"naga duk ka firgice kamar wanda ya tsarewa zaki. to ni dana kiraka ce ka ke me ya faru?, kasan dai haihuwa ba yanzu ba. gani nai nayi na Allah nayi na Annabi, to na gaji da rainon cikin da ba ni nayi ba, shi yasa na doka maka kira kazo kai awon gaba da ƙazamiyar matarka, ba zan iya da tofe-tofen yawu da amai ba, duk ta lalata min wuri da ƙarni. kai baka ji ba daka shigo?, ko da yake yanzu yarinyar can me aikin babarka tasa omo da turaren ƙamshi ta goge min ko'ina, wallahi da ba zaka iya shigowa ba daga bakin ƙofa zaka tsaya, amma matarka ai bata haɗu ba yasin, ciki sai kace akanki aka fara, sakan ɗaya biyu sai a tofar da yawu, can kuma sai dai kaji ana kyalayo amai".
ta rufe ido ta dafe goshi tace,"wuwuwu abin dai ba kyan gani da kwatance".

ran Yusuf idan yayi dubu ya ɓaci, idan da tasan muhimmancin aikin da tasa ya baro da bata masa haka ba. yaji kamar ya bige ta dan takaici, ya matsar da trolly ɗin gefe ya shige ɗakinta, yana shiga ya fito yana tambayarta ina Nuratun?.

"yo ni ina nasan ma inda take, wannan dai fitsararriyar ƙanwar taka ita tazo ta ɗauketa bayan ta gama karta min rashin kunya...yo tsakani da Allah ina gani zan cutu kuma sai naƙi yin magana?, ƙarnin yawu da amai ne fa ke neman halaka ni. banda ma dai halin butulci irin na ɗan adam ina wani zai kallen ya gurza min baƙar magana, to akan Nuratu dai idan ba'a gode min ba ba za'a tsine min ba sai dai idan kuma son zuciya, wane zai iya ɗawainiyar da nai da ita, ce nake ita kanta ƙanwar Uwartata da aka kawowa ita guduwa tai ta barta ta wani fake da ta tafi umarah. haka nake hana idona bacci saboda yarinyar nan, tana bacci ina gefenta ina tofa mata duk kalar adu'ar da ta zo bakina gudun kar a haifi ɗa mara ƙafa, tunda naga alamar tana da mutanen ɓoye, Allah na tuba mene jinnu basa iya aikatawa sai dai Allah yay mana katangar ƙarfe da su kawai...ita dai waccen ƙanwar taka in kaje ka faɗa mata ɗibar albarkar da tai min taje dan kanta ni ba ramawa zanyi ba, kuma ba zanyi Allah ya isa ba tunda dai ina da hankali".

Yusuf ya É—auke idonsa daga kanta yaja trollys É—in zai fice daga parlon kukan Inna Wuro ya dakatar da shi.

ya juya yana kallonta da mamaki, kuka takeyi sosai tana faɗin,"wallahi karka daɗa karka raga ni ko zagin matarka banyi ba, kawai na gaji da ƙazantar ne na tofe-tofen yawu da amai shi yasa nace ta bar min wuri, kuma inda ace ta ban haƙuri ai zan haƙura, amma da yake butulu ce sai dai ta kalleni ta fashe da kuka duk dan wani ya ganta taja min masifa, nace to ta fita ta zauna daga bakin ƙofa idan kazo ba sai ka shigo min ciki ba tafiya kawai zaku yi, ashe taji haushi sai ta faki idona ta dannawa ƴar dabar gidan nan waya, ko minti ba'a ƙara ba sai gata kamar kububuwa ta faɗo parlon nan tana ta huci, da ace ban matsa baya ba da yanzu akan gawata kake tsaye, baka ga irin ɗiban albarkar da Yusra tai min ba, karka ji irin zagin da ta dinƙa surfa min Yusuf, harda kalar zagin da ban taɓa ji ba tunda uwata ta haifeni, wai akan matar Yayanta ba abinda ba zata iya ba, da zasu fita fa sai da ta bangaje ni, nai galantoyi zan kife a ƙasa bangon nan ya riƙeni, yo ka faɗa min ina zan manta da wannan cin mutuncin?, har da cewa fa idan an haifi yaron nan ba zan ɗauke shi ba sai dai kallo daga nesa, to dama ita ta haife shi?, matsalar ban iya haɗa husuma ba ne dana kai ƙararta gaban Amadu wallahi, amma duk da haka ka sanar mata inuwarta na ƙara gani a ɓangarena sai na buga mata duk abinda na raruma".

Yusuf bai ce mata komai ba ya fice ya barta tana kukanta. sai da ƙyar Aliyu da ya shigo ya iya lallashinta tai shiru, amma har sannan bata bar maimaita maganar ba.

Nuratu na kwance akan gado Yusra ta shigo ɗakin nasu, ta ajiye bowl ɗin dake hannunta akan dressing mirrow sannan ta isa gadon ta miƙar da Nuratu wadda duk jikinta yay weak, pillow ta saka mata ta jingina da shi, tukunna ta koma ta ɗauko bowl ɗin dake ɗauke da fruite salad da ta haɗa mata.

"Anty please ki daure ki shanye wannan duka, kinga dai cikinki babu komai".
Yusrah ta faÉ—a tana me cike da tausayinta.

Nuratu ta karɓa tasa spoon ta fara sha, sai da ta kusa shanyewa tukunna ta ajiye, tunda ta tashi yau babu abinda ta iya ci, duk abinda tasa a baki baya zuwa cikinta yake dawowa, tayi amai yafi sau biyar, shi yasa Inna Wuro tace yau ba zata iya ba.

Yusrah na waya da saurayinta da ta kalla ta ajiye bowl É—in ta taso. "ina zuwa i will call you letter". ta faÉ—a tana aje wayar a gefen gadon.

"Anty Nuratu ai babu abinda kika sha, gaskiya ni dai ki daure ki ƙarasa shanyewa". Nuratu kamar za tai kuka tace,"na ƙoshi Yusra".
haka dai har sai da Yusra tasa ta ƙarasa shanyewa, a lokacinne Yusuf ya shigo, tana ganinsa kuma tasa kukan shagwaɓa, kamar wanda aka zarewa laka ya ƙaraso ya zauna a bakin gadon.

Yusra ta gaida shi ya amsa murya a ƙasa, ya janyo Nuratu jikinsa yana shafa kanta yana lallashinta.
ba tare da ya kalli Yusra ba wace,"what did she eat?". Yusra tace,"yanzu ta gama shan fruite salad". ya sake cewa,"ki gasa kaza ki kawon yanzu". "tom Yaya". ta faÉ—a tana fita daga É—akin.

Nuratu kuka ta ƙara sawa tana faɗa masa,"Excellency ni na gaji da wannan cikin, plss remove it for me".

bai iya cewa komai ba ya rufe idonsa ya ɗora haɓarsa akan gashinta, hannunsa na kan cikinta yake bata haƙuri. ji yake da damar da zai mayar da cikin jikinsa da ya maida, tunda ta sami cikin nan bata huta ba, kullum a cikin wahalar laulayi take, ga shi yanzu aka fara ba'aje ko'ina ba, cikin ko 4 months bai kai ba.
Chapter 38 · 0% Book details