← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 176

Sashe 71

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai dai fa duk wannan bidiri da akeyi Fillo bata ko ga tayar akwatin ba balle kayan da suke ciki, dan ƙememe tun ranar da Turaki ya tafi ta kasa zuwa ɓangarensu tsaboda bala'in tsoron da ke ranta, kayan sawarta ma sai Maijidda ce ta kawo mata tace musu wai jarabawa za'ai musu, kwana suke su na karatu ita da Ɗausiyya shisa.
farko dai a tsorace take da zuwan, to amma da aka kawo kayan sai tsoro ya haɗe da kunya shisa ta kasa ko da zuwa, idan taje bata san taya zata fara haɗa ido da mutane ba, tasan kuma halin Maijidda zata sata a gaba ne da aikin zolaya, dama tun washe gari ma tazo tana mata lissafin abubuwan da zasu yi da biki, ita dai har ta ƙaraci surutunta bata ce mata ƙala ba, Maijidda ma da haushi ya cikata ta karɓi wayar Yami da ta zo amsa tai wucewarta da cewar bata ƙara zuwa, ita zata je tayi nata shirin ita ɗaya.

tun ranar da aka kawo kayan Amir ke ta doka mata kira akan zai zo, tai masa godiyar kaya har yake tambayarta ko sunyi, tace masa sunyi tunda har Maijidda ta faɗa dan ita bata je ta gani ba. Amir dai juyin duniya yazo yaga Fillo sam taƙi, idan tayi kamar tace masa yazo sai taji inaa a dai yi auren tukunna, ai haka taji Turaki yace duk masu yin zance a gidan, shisa ga ƙannensa nan cikinsu babu wadda ke yin zance ashe dalilin kenan, Amir tun yana lallashi da roƙo da ƴar murya Fillo dai taƙi yarda da zuwansa, har yay fushi ma washe garin ranar gaba ɗaya bai kirata ba, kuma sai sauƙi yazo mata ranar Yami ta aiko Maijidda ta karɓar mata wayarta.

kuma da Hajiya Madina tayi mata batun me yasa bata zuwa wurin Kaka sai tai mata ƙaryar ai tayi tafiya ne, sai dai fa a wannan kwanaki biyun Fillo tayi muguwar rama, tun daga kan fuskarta har jikinta, na farko tsoro ya hanata sukuni, na biyu kuma kewar Kaka duk ta addabeta.
ɓangaren Amir dai da yaga ba zai iya da azabtuwar rashin ganin Fillo ba ya kwaso ƙafa yazo gidan, ya sanarwa me gadi cewar wurin Hajiya Madina yazo saboda ya sami damar shiga cikin gidan kai tsaye, ta yanda zai zaƙulo Fillo a duk inda take ya fito da ita, shi ba zai iya da rashin ganinta ba, yana ƙara kwana bai sata a idonsa ba tsab zai iya rasa ransa. Mai gadi ya sanar ma da Hajiya Madina, akayi masa iso zuwa parlon baƙi, taje ta same shi suka gaisa, zatonta ma ko masu buƙatar taimako ne amma sai taji yana mata bayanin wurin Halima yazo.

kusan minti guda Hajiya Madina ta ɗauka tana kallonsa cike da nazarinsa, tare da kuma mamaki matuƙa akan batun wurin wacca yazo, ashe yanda take tunanin Fillo ba haka take ba?. tashi tai tana ce masa ya jira yanzu zata zo, aka kawo masa ruwa da snacks da kuma juice na pineapple, kayan dai na aje kan table ɗin dake gabansa yana kallonsu amma ya kasa ko taɓa ruwan, bini bini sai ya duba agogon hannunsa, shiru shiru Fillo bata fito ba wucewar mintina goma da tafiyar Hajiya Madina, a ransa sai ya fara tunanin kamar ko ba zata zo ba ne, kuma kamar Hajiyar ce ba zata barta ba, sai yaji ransa yay mugun ɓaci.

ɓangaren Fullo kuwa su na can su na aikin suyar wainar shinkafa Baffa zai yi baƙi, suna faɗansu ita da Ɗausiyya kan ita Ɗausiyya na cika mai a suyar, ita kuma Fillo na zuba kaɗan, faɗan dai ya tashi akan kowacce ta sakawa ƴar uwarta ido, Zaytuna da Nihal kuma na gefe suna haɗa miyar agusi da ganda, suna jinsu suna yi musu dariya.
Nihal ta waigo É—auke da dariya a fuskarta tana kallon ÆŠausiyya tace,"ke fa kece aikinki baya kyau, mai idan yay yawa a abinci baya daÉ—i ÆŠausiyya kuma kin san dai akwai masu ulcer".
Fillo na kallon Ɗausiyya tai dariya tace,"ah tou kin dai ji, in kuma man kike so ai sai ki bari in tazo ƙarshe ki soya taki da duka galand ɗin, lafiyarki ai ba lafiyar wani ba".

Ɗausiyya ta galla mata harara ta ɗauki waina guda ɗaya acikin wacca Fillon ta soya ta wuce wurin Nihal tana faɗin,"Adda Nihal kalla fa ki gani, abu ƙamas ai sai taja mana magana ace muna da maƙon mai alhalin akwai wadatarsa". ta buɗe cikin wainar tana ƙara faɗin,"ji fa aba a bushe kamar ba'a saka komai ba, yanzu dan Allah cikin abokan Baffa wani ya kai bakinsa ai direta zai yi dan wannan dai ba zata ciyu ba Allah".

Nihal na taɓa wainar tace,"gaskiya kuma fa haka ne, mutane da basa rasa abin faɗa sai su tafi suna cewa Baffa baya wadata gidansa da isassan man abinci".
Ɗausiyya ta kalla yanda Fillo ta cika tai fam tace,"ah tou, dan haka ki zuba mai isashshe kiyi suya Malama, in yaso kyayi tsumulmularsa a gidanki babu ruwan koya, ƙarƙari kijawa mijinki magana wurin abokai da dangina a tafi ana yi da ke biki iya girki ba".

tai ƙarashen maganar tana dariya. Fillo tace,"ko ba komai dai mijina yace ina da tattali, ke kuwa kullum sai kinsha masifa akan haukar almubazzaranci da kike masa".
Zaytuna tai dariya sosai. Nihal da bata fiya shigowa kitchen É—in ba tace,"haka kuke aikin dama kamar kaji?".
har sannan dariya bai É—auke akan fuskar Zaytuna ba tace,"kika biye su ba abinda zai hana bakinki yagewa, dan kamin barinki kitchen É—inn sai kin ji wani complain É—in na daban".

dai-dai nan Hajiya Madina ta shigo, duk suka yi shiru, ta dubi Zaytuna da Nihal tace,"sannunku da aiki". suka amsa da yauwa, tace da su,"where is Samha?". Nihal tace,"na ga ƙawarta tazo ɗazu sun fita".
Maama bata tace komai ba ta maida kallonta ga Fillo tace,"meet me in my room". ta faÉ—i hakan tana juyawa ta fita.

Fillo ta miƙe tana wanke hannu a sink, taiwa Ɗausiyya gwalo tace,"kuma ai aiki me kyau in ba haka ba ran mutum ya ɓaci". ta faɗa tana mata gwalo sannan ta fice daga room ɗin.
tun da ta shiga room ɗin Hajiya Madina taga yanayin fuskarta sai jikinta yay sanyi, ta ƙarasa shigowa ta zauna a ƙasa tana fuskantarta, duk lokacin da taga fuskar Maama ahaka tasan to da matsala,so farkon abinda yazo cikin kanta shine Turaki, 4days dama taji Zaytuna na faɗin zai yi, ga shi yau har kwana 5, lafiya?, meke faruwa?, ko kuma yana kan hanya?.

rashin sanin amsa yasa ta É—ago kai da sauri ta kalli Hajiya Madina da ke ta kallonta ta kasa cewa komai. murya a hankali tace,"Maama lafiya?, Hamman har yau bai dawo ba".
Hajiya Madina ta sauke numfashi tace,"zasu taho jiya sai Baffa ya tura su El-Salvador zasu yi signing wani contract da wani kamfanin fulawa acan, jibi insha'Allahu zasu sauka".

Fillo tace,"Allah ya kaimu ya dawo da su lafiya".
ta faɗa kanta na ƙasa. Hajiya Madina na studying nata tace,"kunyi da wani zai zo wurinki ne?".
tambayar taji ta a wani iri, hakan yasa tai saurin É—ago kai tana kallon Maaman, kan tai magana Hajiya Madina ta jefa mata tambayar,"Amir yazo wajena yace min yana son ganinki. waye shi?, aina ku ka haÉ—u?, dama can ya sanki ne?, da yaushe kika fita har ya ganki ya biyo sawunki?".

Fillo ta sadda kanta ƙasa tana wasa da fingers dinta tace,"wanda zan aura ne, amma wallahi ba muyi da shi cewar zai zo ba yau".
with Astonishment Maama tace,"wanda za ki aura Fillo, asin how?".
Fillo ta kwashe duk bayanin komai har kayan sa ranar da aka kawo ta faɗawa Hajiya Madina. ita dai kallonta kawai take tana ganin kamar yarinyar ƙarya take yi, ƙarama da ita haka age of 17 going to 18 ace za'ai mata aure?, tasan cewar su ƴan ƙauye ne da basu fiya bawa rayuwar ƴa mace muhimmanci akan yanda zamanin yanzu ke tafiya ba, amma bata taɓa tsammanin za'a iya aurar da yarinyar nan kusa ba kasancewarta me ƙaramin jiki sosai, in ba sani ma kayi ba zaka iya rantsewa ba 18 zata shiga ba.

dalilin da yasa tun a ranar da yarinyar ta kwanta mata a rai ba tayi hanzarin shigar da tata buƙatar garesu ba kenan, kiwon Fillo da take yi tanadi ne take taiwa ɗanta Muhammad Turaki, ashe har wasu sun mata shigar sauri, wani ya riga ɗanta, wani daban zai mallaki kamilar yarinya me natsuwa da hankalin da irinta ke da wuyar samu, ba ɗanta Muhammad Turaki ba, wani daban can. yanzu wa zata ƙara kama masa?, har cikin ranta bata ji daɗin wannan batun ba sam, to amma ya zata yi, shirinta da lissafinta daban ne, hakama yanda ubangiji ya shirya lamarinsa daban, kuma na ubangiji shine dai-dai, kuma dama ita kullum adu'arta alkhairi take nema.

dan haka yanzu adu'a ta rage mata akan Allah yaywa Turaki da Khalil zaɓin mace mafi alkhairi a gare su. ta sauke numfashi tana daɗa kallon Fillo tace,"amma Fillo me yasa baki faɗan ansa ranar aurenki ba na fara shiri?, ko haka kike so na kaiki?, ko kin manta nace ke ƴata ce?". ta faɗa cike da zolaya, Fillo kanta na ƙasa bata iya cewa komai ba saboda kunyar da ta kamata.

Hajiya Madina ta miƙe ta isa wadrobe ta buɗe ta ɗauko wasu sabbin kaya irin na ƴan turkey, kayan da Baffa ya tahowa da Nihal ne tsaraba, ta ciro set biyu aciki ta bawa Fillo tace,"ungo kiyi maza kije ki shirya yana parlon baƙi yana jiranki tun ɗazu".
Fillo ta kalla kayan sannan tace,"Maama zanje da waÉ—annan ma". ta girgiza mata kai tace,"daga wurin suyar waina fa kika taso, haka zaki je wajensa kina tsami?, salon ya raina min Æ´ar tawa tun yanzu...a'a je ki gyara jikinki shaf shaf kije ki samesa dan ya jima kusan 15minutes, in kin dawo kizo ki min list na abinda kike so na siya miki".
Chapter 71 · 0% Book details