Sashe 44
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haka suka faɗa a sannan, kuma ba zai iya cewa ga wanda ya nuna masa hanyar laboratory ba, tsintar kansa kawai yayi a wurin, ba tare da kowa ya sa ni ba. abunda ya tsana a rayuwarsa shine ɓata lokaci da kuma dogon bayani, kuma abinda ya sani jininsa AB+ ne, to don me kuma sai an tsaya wani ɓata lokacin gwadawa?, dan haka dawowa kawai yayi ya kama hannun Zaytuna suka faɗa room ɗin da aka kwantar da Fillo.
_"ki saka mata jinina, ko leda nawa ake buƙata, ko da za'a kwashe shi duka"._ kayan aiki a ajiye suke to jiran me za tai?, dan haka kwanciya kawai yay akan gado tayi jone-jonen da zata yi, nan take jininsa ya fara shiga jikin Fillo. daga fara shigar jinin bai kuma sanin me ya faru ba, farkawa kawai yayi yaga wani yayi replacing nasa akan gadon, Dr Yusuf, likitan da shima yay kyautar nasa jinin wa yarinyar. sai daga baya Zaytuna ke masa bayanin ai ance shima yana buƙatar ya huta ne dalilin da yasa aka cire nasa kenan, dama leda 1 da rabi ake buƙata, Dr Yusuf ya bada rabin.
Turaki ya numfasa yay tattaki ya ƙarasa gaban Fillo dake tsaye har yanzu bata buɗe idonta ba, wataƙila tana jira ne taji ya fita daga kitchen ɗin sannan sai ta buɗe idon, ko kuma tana jira ne ya bata umarnin buɗewar, tunda ita bata da umarnin kanta sai na wani, ya lura da hakan tun farkon zuwanta.
sai dai yana zuwa dab da ita taji gabanta yay mugun faɗuwa, allon ƙirjinta ya girgiza, taji kamar ta arta a guje. so take tasa hannu ta toshe hancinta saboda ƙamshin turarensa da ke shiga hancinta, ba saboda rashin daɗinsa ba, idan tace ƙamshinsa babu daɗi tayi ƙarya, wannan ƙamshin yana ɗaya daga cikin ƙamshin da zata iya cewa da wuya a samu ƙamshi me daɗi irinsa. sai dai da ace tana da iko, da ace tana da iko da Turaki da ta haramta masa sanya wannan turaren, da tasa ya bar ƙasar nan yaje wata ƙasar sun wanke duk wani sauran ƙamshi na irin turaren nan dake jikinsa, ba ta son ƙamshin ta tsane shi, ba don komai ba sai don an haɗa asiri da shi, wannan asirin da yay sanadin zuwanta cikin dajin da ta kusa mutuwa.
ranar da Turaki ya tsareta da tambayar me ya kaita wancan wurin yana kama hannunta taji ƙamshin, ƙamshi ne da ba zata manta da shi ba, ta jima tana zuƙar ƙamshin a lokacin dan tabbatar daga inda yake fitowa, tunaninta ko asirinne ya kuma biyota, da ga baya ta ankara da cewa ba ƙamshin kowa ba ne sai nasa, that means ya tabbata kenan asirin nan nasan ne, kuma an haɗa asirin ne da turaren da yake sawa...saboda haka yanzu fatanta guda ɗaya ne, Allah ya bata wata dama da zata hana Turaki saka wannan turaren, ko kuma Allah ya ɓatar da turaren daga duniya gaba ɗaya.
jin takalmin Turaki gaba ɗaya akan kafaɗunta tai firgit ta buɗe ido ta sauke kallonta akan ƙafafunsa dake cikin takalmin shigowa kitchen. ta haɗiye wani busashshen yawu sannan ta iya buɗe baki tace,"kayi haƙuri ban san me kake cewa ba".
ya fito da hannayensa daga aljihu ya tamke fuska yace,"na miki kama da dodo?". da sauri ta girgiza kanta alamar a'a. yace,"to me yasa duk ranar da kika ganni kike rikicewa ki bi ki firgice, ko ina kama da aljaninki?". nanma ta girgiza kai cikin sauri tace,"a'a". yace,"to ina jinki tsoron na mene?".
a hankali tana shirin yin kuka tace,"bana so a ɗaga min murya ko kuma a min tsawa". yace,"ni kuma haka nake miki ko?". bata ce komai ba tayi shiru. sai taji yay ƙasa da muryarsa yace,"mene wancan abun da kike haɗawa?". ta ɗaga ido ta kalli robar da take dama kunun tace,"kunun shinkafa ne, Adda Samha tace na dama mata".
ya matsa daga gabanta ya ƙarasa wurin yana faɗin,"an gama?". tace,"a'a zan zuba madara ne". yace,"zo ki ƙarasa". sai tai ɗan jim bata motsa ba, ya juyo ya wurga mata wani kallo da niyyar ya doka mata tsawa sai kuma ya taushi zuciyarsa ya sauke murya ƙasa yace,"nace kizo ki ƙarasa ko". ta taho kamar me ciwon ƙafa, ta fasa madarar ta ɗaga gwangwanin tana zubawa hannunta nata rawa, madarar rabi ce ta shiga rabi duk ta zube a ƙasa, haka har ta juye gwangwani ɗaya sannan ta ƙara fasa wani, zata zuba sai taji ya kama hannunta ya karɓi madarar ya zuba da kansa ya jujjuya.
yana gama juyawa ya tura mata cup ɗin da ya ɗauko gabanta, bai magana ba amma ta fahimci me yake nufi. sai tace,"zan zuba siga". ta faɗa tana nufar drowern dake sama, ya bita da kallo yana tunanin ta inda wannan ƴar a bar dake iyakar cikinsa zata iya ɗauko abu a wancan drowern dake luluƙin sama. ya lissafa yaga ko da abu zata taka sai ta ɗora me tsayi tukunna tsayinta zai kai, lissafin nasa ya ƙare a kallon siraran ƙafafunta dake yawo a cikin zani, babu makawa ta taka wani abun ta faɗo sai ƙashinta yay breaking in to pieces.
ta ɗauko doguwan kujera zata taka ta hau sai ganinsa tayi ya ɗauko roban ya miƙo mata, tana so ta kalle shi amma tana tsoron idonsa, tasa hannu biyu ta karɓa ya wuce ya bar mata wajen.
zata zuba sugar É—in taji yace,"a little bit". sai ta dakata da zubawan. yana ganin hakan sai yace,"É—an kaÉ—an". kaÉ—an É—in ta zuba, kuma data zuba sai data É—ago ta kalle shi, ba tai magana ba amma kallon nata ya bayyana masa abinda take nufi, itama kuma shirun nasa ta gane cewar yayi.
ta zuba kunun a cup ɗin da ya ijje mata sannan ta ɗauko ƙaramin plate ta ɗora cup ɗin akai ta ɗora spoon, ta ɗauka zata fitar masa da shi taji yace,"give me". da sauri ta miƙa masa ya karɓa dan ta gane me yace, bata manta karatun ɗazu ba da teacher nasu ya faɗa musu ma'anar give me da hausa.
yana karɓa ya fice ya bar kitchen ɗin, da fitarsa ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya, ta ɗauki tea flask ta juye kunun aciki ta ɗauka ta fita da shi, tana fatan Allah yasa Turaki baya falon a lokacin.
samunsu tayi duk suna dining suna lunch, tace da Samha. "Adda Samha nan zan ajiye ko ɗakinki zan kai miki?". Samha bata kalleta ba tana wani shan ƙamshi tace,"ajiye anan". ta zagaya ta gefen da Nihal ke zaune ta aje, sannan tai tsaye ƙeƙam a wurin. tana jin idon Hajiya Madina akanta, duk sai take jin wani iri da kallon, ta ƙara yin ƙasa da kai.
"Idan kin kawo abu kike tafiya bayan kin ajiye ba sai kin jira an miki izinin tafiya ba, kinji ko?". tace,"tom Maama". Hajiya Madina tace,"da sauran abincin a kitchen ko zaku É—iba anan, ko kuma wani abun zaku dafa?". tace,"akwai saura Maama". tace mata,"to kije ku ci".
har zata tafi Zaytuna ta kalli cup É—in dake gaban Turaki, ya shanye rabin kunun ya bar saura. taga idan an barsa asararsa za'ai, kuma wannan na flask É—in yanda suke da son kunun shinkafa ba zasu bar ko kaÉ—an ba, kuma tasan Fillon da ta haÉ—a bata rage ko kaÉ—an da zata sha ba, tasan abinda zata iya aikatawa. dan haka tace mata,"zo ki É—auki wannan".
Fillo ta zagayo gefen da take, ta ɗau cup ta riƙe. "ki shanye shi karki zubar". ta wuce ta koma kitchen ɗin, ta tarar Ɗausiyya ta zuba musu abincinsu a wani ƙaton roba, da dukkan alama Ɗausiyyan na da shegen ci, kuma bata saba cin abinci a ƙaramin kwano ba. ta ɗauki wani cup ɗin separately ta juye kunun da Turaki ya rage, bayan ta wanke cup ɗin ta maida shi ma'ajiyarsa tabi bayan Ɗausiyya suka fita.
****
Boɗejo na zaune a tamfatsetsen falon na gidan Hakimi, wata maid nayi mata tausa. da sallama aka shigo falon, Boɗejo ta ɗauke kanta ga barin kallon tv ta koma kallon ƙofa. ganin masu shigowa ta buɗe baki cike da jin daɗi tace,"Ilham". ta faɗi sunan tana me cike da mamakin ganinta.
Ilham da ƙawarta suka ƙaraso ciki, ita ta ƙarasa inda Boɗejo take ƙawartata kuma ta zauna akan kujera. "bari in samu ladan nima".
Ilham ta faɗa sanda ta zauna a ƙasa tana cewa da maid ɗin ta tashi ta tafi zata ƙarasa ma Boɗejo tausar.
"rai kan ga rai, ashe da rabon ƴar nan zan ƙara ganinki kamin na mutu".
Ilham tace,"bar zancen mutuwa my Only Granny, yanzu ai zaki ke ganina akai-akai tunda dai Allah ya yarda an kammala karatun".
Boɗejo da har yanzu daɗi bai saketa ba tace,"ai ko dai naji daɗin kammala karatun nan, haka kawai Hashimu ya wani kwasheki ya kai ki wata uwa can duniya kiyi karatu ke ɗaya, ai ranar nan sai dana masa tatas nace idan baya ƙaunarki ne ya faɗa mana sai muje mu ɗauko ki mu dawo dake, wannan wane irin karatu ne ace shekara biyar anata faman yinsa babu ƙarewa".
Ilham tai murmushi tace,"to BoÉ—ejo ba gashi har mun kammala ba". "haka ne dama komai ai lokaci ne, yanzu ai ba tausa zaki ba Ilham jikina zaki taho".
Ilham ta bar matsa ƙafar da ta fara tayi jikinta suka rungume juna. duk su biyun suna masu jin daɗi. Ilham ƴar gidan Hashim ce mai martaba na yanzu ɗan Boɗejo, itace ƴarsa mace ta biyu wacce taci sunan Boɗejo Rumana, ta tafi america karatu inda ta karanci business administration, kuma tunda ta tafi bata dawo ba sai yanzu, shekara biyar cif.