← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 176

Sashe 114

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya kama hannunta ya maidota kan kujerar ta zauna, kawai sai ta ƙara fashe masa da kuka ita lallai ya saketa yanzu ba sai anje gida ba, ya dinƙa bata haƙuri da lallashi amma kamar yana tunzurata, ransa ya kai ƙololuwar ɓaci ya sakar mata uwar tsawa da tasa babu shiri ta faɗo jikinsa tana ƙanƙame shi, jikinta banda kyarma babu abinda yake yi.
"ban san irin illar da zan yi miki indai kika ƙara ambatar min kalmar saki".

sai kuma ya kwantar da murya gwanin ban tausayi yace,"wannan Kukan naki ba komai bane illa damuwa, muyi avoiding duk kalar wani abu da zai saka ki a damuwa muddin muna sonki da rai, haka Dr yace, bana so na rasaki Fulani nah ina so na rayu da ke, ki taimaka min, wannan kukan naki na faÉ—a miki baida amfani, in har za'a bawa Abba damar magana da yayi yace ki bar yi masa wannan kukan kiyi masa adu'a, so please ba kuka ba just pray for him".

tayi ɗif tare da lafewa a jikinsa kamar ba ita ba, shashsheƙar kukan ma a hankali take yi yanda ba zai ji ba, ya kai bakinsa saitin kunnenta a hankali yace,"za ki bi ni mu tafi tare?".

ta girgiza kanta da sauri alamar a'a, sai kawai ya rufe idanunsa tare da miƙewa ya kama hannunta itama ta miƙe.

tana taka ƙafarta tace da shi,"zafi ƙafata".

yace,"to in É—auke ki?". ta girgiza kanta da sauri.

ya riƙe hannunta suka koma office ɗin Dr, sai da Dr ya tabbatar masa ciwon ƙafartata babu damuwa ya kuma gamsu sannan ya kamo hannunta suka fito.

su Kaka har sun tafi lokacin, tana wurga idanu a compound É—in tace masa,"ina su Kaka?".

yace,"sun wuce". ya faɗa yana nufar inda motarsa take, ita dai binsa kawai ta-ke yana riƙe da hannunta har lokacin, sai kallon baƙon asibitin ta-ke yi tunda ba nan aka saba kaita ba, suna zuwa bakin motar sai ga wani mutumi nan ya ƙaraso wurin da gudu-gudunsa.
ya rissina yana cewa da Turaki,"ance in zo in tafi da ku ne".

Turaki na kallonsa yace,"a'a ga motata ai, kaje kawai".

mutumin ya ƙara rissinawa yana cewa,"umarnin Dada ne yallaɓai, Dottijo ma ya ƙara da nasa akai".

Turaki ya kalla Fillo da ke ta kallon mutumin da rashin sanin sunayen da yake ambata. yace da shi,"kaje kawai babu damuwa".

"tom shikenan ranka shi daÉ—e, A iso lafiya".
ya juya ya bar wajen. Turaki ya buɗe front seat Fillo ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ɓangarensa, ya tada motar suka bar asibitin yana driving kamar baya so, ya maƙale hannunta a nasa kamar wanda za'a ƙwaceta ko wadda zata gudu.

ita dai kanta na jingine da jikin kujerar, tana ta kallonsa ta gefen ido tana ganin yanda yake cije fuska yana matse goshinsa tare da dafe kai, har stearing ya kusa ƙwace masa, hakan yasa ya gangara gefe yay parking, ya kifa goshinsa akan stearing, Fillo dai sai kallonsa ta-ke yi, bayan wucewar daƙiƙa biyu tace da shi,"baka da lafiya?".

yay shiru bai ce mata komai ba, har sai da ya ɗauki minti biyar a haka yaji ya ɗan sami relief tukunna ya ɗago, ɗagowar tasa tayi dai-dai da shigowar kiran Maama, yay picking yana magana da ƙyar.

tace da shi,"me Babban suna na rasa yanda zanyi da Baffanku, kayi haƙuri kawai mu koma tare tunda Fullon taji sauƙi kaji, kasan dai yanda lamarin Boɗejo yake sai haƙuri".

yace,"tom Maama".
tace,"ba ku taho a asibitin bane?, su Kaka sun dawo tun ɗazu anata tambayar ko lafiya ku baku taho ba, ka san akwai ƴan uwan Babanta daba ƙasar nan suke ba suna so su ganta kafin su koma".

yace,"ina kan hanya Maama".
tace,"bana son damuwa Me Babban suna, karka zo min da ita ka jefar da ita tun a hanya kaji".

ya amsa da,"as you wish".

yaci gaba da driving ɗin, Fillo dai tsoro ya cikata duba da kamar ba'a hayyacinsa yake tuƙin ba, can yaji muryarta cikin ƙarfin hali ta ƙara tambayar,"baka da lafiya?".

yay mata wani kallo yace,"kina da damuwa da lafiyar tawa ne?".

idanuwanta suka yi narai-narai, ta kauda fuska gefe tana kallon titi tana jin zuciyarta nayi mata zafi, ita bata taɓa sonsa ba a rayuwarta, kuma bata taɓa jin zata so shi, abin da tayi masa taimakonsa kawai tayi, so how comes za'a ce shine mijinta?, me yasa ƙaddara zata yi mata haka?, ta ina zata fara zama da shi irin wannan zaman da taji su Ummi na faɗa wai zama na har abada?, taji ƙwalla ta cika idonta, wani dunƙulallan abu ya tsaya a maƙoshinta, in ace shima yana sonta wataƙila ta iya haƙurin zama da shi ɗin, but shima ba sonta yake ba, ya aureta ne saboda ya taimaketa da kuma tausayinta, sannan kuma ya aureta alhalin ya san ba zai iya zama da ita kaɗai ba?, shin ta ina zata fara zama da shi da bata sonsa da kuma kishiyar da bata ƙauna.

ta rumtse idonta sosai cikin ranta tana adu'ar Allah ya É—auki ranta kafin zuwan lokacin da za'ace an kaita gidansa.
lokaci ɗaya hawaye ya shiga zubo mata, wataƙila da Abbanta yana raye da ya tsaya mata har sai an raba auren tunda bata so, ta kulle idonta tana jin wani bala'in zafi da ɗaci a ƙasan ranta, kishiya! ita Fillo da kishiya!, kuma kishiyar ma ƴar sarki yacce zata ji daɗin taka ta!, zata iya ɗaukar bull shits ɗinta kuwa?.
kawai sai ta cije leɓenta na ƙasa, for some seconds ta buɗe ido a sanda motar ke ƙoƙarin dukan bishiya, da ƙarfi tace da shi,"kayi a hankali zaka ka bugi bishiya".

yay saurin juya kan motar yana kaucewa bishiyar da ya kusa daka ba tare da ya sani ba, duk sai yaji dama ya bar wancan mutumin ya tafi da su, dan shi kansa ya san ba'a hayyacinsa yake ba, banda bala'in ciwo da kansa yake masa yana jin ƙirjinsa ma kamar zai bar jikinsa, ga idonsa ma ba sosai yake gani ba saboda azababben baccin dake cikinsu, ya ɗauka wayarsa zai kira Hamid yazo ya tafi da su sai kuma ya fasa, yaci gaba da lallaɓawa yana jan motar a hankali.

sanda suka sauka akan titi ya shiga street É—in da zai kai su gidan BarkinÉ—o, daga saman kansa yaji tana tambayar,"wai ina zaka kaini?, dan Allah ka kaini gida, ni ba wurin Maama zanje ba".

bai ko waiga ya kalli inda take ba balle ya amsa mata. ta ɗauke idonta daga kansa taci gaba da kallon hanyar da bata sa ni ba, da irin ginin gidajen da zata ce in ba a tv ba bata taɓa gani ba, hanyar sam bata yi mata kama hanyar da ta taɓa bi ba, tunaninta ɗaya ne ta yanda zata buɗe murfin motar ta faɗa waje.

sunyi tafiya me nisa a street É—in sannan ya samu wuri yay parking, idonsa na manne da gabansa yace,"fita".

Fillo ta ɗauke idonta daga kan symbol ɗin da take karantawa ta juyo tana kallonsa, kamar ba shine taji yayi maganar ba kuma sai taji ya cire mata tantama da ƙara maimaitawa. "fita".

tace,"ai ban san ina ne nan É—in ba, ba zan iya gane hanya ba".

shirunta yayi daidai da doka mata tsawa yana ƙara cewa,"i said get out of my car".
babu shiri ta buɗe motar jikinta na kyarma, ta fita ta tsaya tana riƙe da murfin motar, "dan Allah kayi haƙuri idan ka saukeni anan wallah ba zan iya zuwa gida ba, ban san ta nan hanyar ba".

yana jinta dai bai tanka mata ba, ya É—auko wayarsa ya danna kira a lambar Hamid, yana É—agawa yace da shi,"kaine ka shiga mota yanzu?".

Hamid yace,"ehh".
yace da shi,"ƙaraso ka ɗauki wannan yarinyar, tana wajen symbol ɗin da akai addressing da sunan Hakimi".

Abdulhamid yace,"ok tom gani nan".
sai da ya hango motar Hamid ta taho tukunna ya figi tasa ya bar wajen, Fillo tayi saurin sa hannu ta kare idonta gudun kar ƙurar da ya baɗeta da ita ta afka mata a ido.

Hamid yazo ya ɗauketa kuma har suka ƙarasa gidan bata iya ce masa komai ba, sai magana yake yi mata tayi shiru bata amsa masa ba, tambayoyi ne fal a bakinta amma jin bakin nata take yayi mata nauyi.
tunda ta fito a mota kuma sai ta zama Æ´ar kallo, idonta kamar zai faÉ—o waje saboda kallon gidan da ake nufa da ita da kuma mutanen dake ta tururuwa akanta, suka shiga gidan tana jin muryoyi da dama na faÉ—in,"ga Æ´ar gidan Hayyon, masha'Allahu ta sami lafiya".

sai kuma taji wata dattijuwa na cewa,"É—auko ruwan tofin nan a bata Malam yace tana shigowa ta fara shansa".

idanuwanta suka sauka akan Ummi da ke tsaye a bakin ƙofar ɗakin Hajjah mahaifiyar Hayyo, ta ƙwace daga hannun mutanen da ke riƙe da ita ta tafi wurinta ta faɗa jikinta, Ummin ta kama hannunta suka wuce ɗakin Dada, kuma zuwan nasu ne ta samu duk amsar tarin tambayoyin dake cikin kanta tun kafin tayi tambayar a bata amsarsu.

mutuwar iyaye bata daɗi, kuma ba'a farin ciki da mutuwarsu duk lalacewarsu, but a ɓangaren Fillo abu ɗaya da zata iya buɗar baki tace shine mutuwar mahaifinta tayi mata rana, domin ta dalilin mutuwarsa yau gasu cikin jin daɗin da basu taɓa hangar cewar zasu ji shi ba har su mutu, gatan da basu san suna da shi ba yau gasu acikinsa.
sai nan da nan ake da ita da Hamid da sauran sisters ɗinta kamar wasu gwala-gwalai, tarairaya kace ƴaƴan wasu shegen ƙusan, motsi kaɗan a tambayesu me suke so.

cikin satin mutuwar kafin ayi adu'ar bakwai haka aka dinƙa ɗaukarsu ana zagawa da su cikin dangi, babu inda ba'a kai su ba adai familyn mahaifinta da suke nan cikin taraba state, waɗanda basa ƙasar ne kawai ba'a kaisu wajensu ba amma suma sunyi vedio call da su.
a hankali ta dinƙa jin damuwar mutuwar na tafiya tana barinta, sai in sun zauna ita da Hamid ne sai suyi ta tambayar junansu wai me yasa Abba ya tsiyatar da kansa haka har yayi irin wannan rayuwar ƙasƙancin bayan yana da gatansa, amsar da basu da ita har kullum kenan.

*After 55days.*
*Saudiyya, Jeddah, Sanabile, House no 08.*
*13:00pm.*
Chapter 114 · 0% Book details