← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 176

Sashe 78

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta sauke dogon numfashi tare da ɗaga gorar hollandia ɗin dake hannunta ta ƙara kurɓa, ta buɗe lumsassun idanuwanta a sanda take juyowa ta fuskanci kyakykyawan farin bafulatanin dake zaune kan kujera yana danna wayarsa, shima fuskarsa kaɗai ta isa ta shaida maka cewar zuciyarsa a ƙunci take.
Samha ta ɗauki tsawon daƙiƙu biyar tana kallon Sameer kafin ta buɗe baki tayi magana, muryarta ta fito acikin rauni da kuma damuwa.

"tsawon shekaru masu yawa, har kullum, har yanzu na kasa haƙuri da juriya akan yacca nake ganin mahaifiyata ta fifita wani daban akan ni da ta haifa, tafi son sa fiye da ni da ta haifa, tafi basa kulawa fiye da ni da ta haifa, tafi kyautata masa fiye da ni da ta haifa, tafi damuwa da damuwarsa fiye da ni da ta haifa, hankalinta yafi karkata 100% akan ƴaƴan da bana cikinta fiye da wanda ta haifa acikinta. ka faɗa min ta yanda za'ai nayi farin ciki duk da cewar ban taso a tagayyare ba, ban taso a cikin talauci ba, ban taso da rashin gata ba, ban taso na nemi abinda nake so na rasa ba, ban taso na rasa soyayyar mahaifi da ta mahaifiya ba, sai dai wannan soyayyar tasu ce tayi min kaɗan, ba kalar wannan soyayyar nake so daga wurin mahaifiyata ba, kalar waccan soyayyar da take nunawa Turaki da Zaytuna ita nake so, ita nake da buri ita nake da muradi, amma tsawon shekaru masu yawa na rasata, na kasa samunta duk ta yanda na so...shi yasa ya zama dole na kawo ƙarshen wannan bambanci da iyayenmu ke nunawa ko ta halin ƙaƙa, ko da ace asanadin hakan zan rasa raina".

ta ƙarashe maganar muryarta na bayyana wani irin baƙin ɗaci dake tasowa daga ƙasan zuciyarta.
shirun da tayi yasa Sameer ya É—ago da kai yana kallonta, tana tsaye hawaye na bin fuskarta, ba ta da alamar zata hana su zuba balle tasa hannu ta goge su.
ya rufe idonsa for few seconds ya buÉ—e yana sauke numfashi tare da ajiye wayarsa a gefensa.

"ke kaɗai ce dama kika rasa dukkan abinda kika lissafa?, ko kuma ke ɗaya ke cikin irin wannan ƙuncin?".
kanta na ƙasa tana kallon ƙafarta dake cikin black socks tace,"bani ɗaya bace, ko Hammah Khalil da Nihal na san basa jin daɗin haka, deep down there heart na san suna jin zafi, domin babu ɗan da zai so yaga iyayensa na nuna banbanci tsakaninsa da ƴan'uwansa...so amma abinda nake so ka fahimta Sameer inda ace hankalin mahaifiyamu na kan mutum guda acikinmu da ta haifa, to da atleast zamu sami sassaucin raɗaɗin zuci, ba wai take nunawa kamar ba ita tayi naƙudarmu ba".

cikin zafin nama tai wurgi da hollandia ɗin dake hannunta tasa ƙafa ta murje, tana huci take cewa,"wani sa'in zuciyata na faɗa min Turaki da Zaytuna asiri suka yiwa Maama, ba haka suka barta ba, don babu uwar dake cikin hayyacinta zata ke nuna irin son kai tsakanin ƴaƴanta da na kishiyarta, but what ever lokaci yayi, wallahi a wannan karan babu fashi da tsiya tsiya sai na aika da su lahira, zanbi ta irin waccan hanyar da suka bi, ko duk bokayen duniya zan bi saina sa an kawo min ƙarshen su Turaki".

Sameer ya hura iska a bakinsa sannan yace,"bin boka is not the best solution dear tunda aikin asiri na karyewa, and ba zan bari ma mu aikata shirka ba. abu ɗaya kawai da yake nan waɗan nan mutanen su zamu ƙara bawa kwangilar...".
ai tun bai ƙarasa ba ta duki table ta katse shi da cewar,"kuɗina ba zai ƙara zuwa hannun gantalallun can ba".

sai kuma ta nemi kujera ta zauna ta dafe kai,"Sameer ni abinda ma yake ban mamaki, me yasa duk sanda mukai wani shiri sai kaga Turaki ya kuɓuta daga wannan shirin namu?, ka duba fa kaga last da muka sa aka datse burkin motarsa, tsakiyar dare fa muka bi, wa ya ganmu?, wa yaji plan ɗin mu?, amma sai ga shi da safe yana batun bai key na motarsa ba, kuma tun daga ranar har yau bai ƙara hawa wannan motar ba, anya Sameer?, ga shi ba wani muka sa akan aikin ba balle muce ya munafurce mu, da kanmu muka yi aikinmu, kai na kasa ganewa gaba ɗaya".

Sameer shima ya kwantar da kansa kan kujera yace,"ni kaina nayi mamaki sosai a wannan time ɗin, musamman da naga up to now baya hawan motar. amma mutumin da yake kwana yana sallah har sai gari ya waye sannan ya rumtsa, mutumin da yake driving yana sauraron karatun alƙur'ani yana bi, mutumin da baya rabo da ambaton Allah a bakinsa, mutumin da common magana ɗaya yayi sai ya ambaci Allah, to ki faɗa min ta ya ba zai kuɓuta daga haɗarinmu ba?, taya ba zai kuɓuta daga sharrinmu ba?, ai muma wasa muke, iyakar kuɗin da muka ɓarnatar ya kamata zuwa yanzu ace mun haƙura kawai, mu fahimci cewar Turaki yafi ƙarfinmu dan yana tare da kulawar ubangijinsa".

Samha tace,"idan kai ka haƙura ni dai ba zan haƙura ba, dole ne ma sai na ƙwaci soyayyar mahaifiyata, dole ne ma sai na ƙwatarma kaina hakki. ka duba kaga banda mota guda ɗaya da kuma fili guda ɗaya me Baffa ya taɓa mallaka mana?. amma Zaytuna motarta biyu, bayan fili har gida tana da shi, Turaki kuwa an handame duk wata kadara an basa, komai Baffa yay yunƙurin yi mana sai Maama tace shi ya kamata a bawa saboda shine Babba, ko kuma tace ai su basu da uwa sai kace mune muka sa uwar tasu ta gudu".

Shiru ya ratsa kafin Sameer yace,"to yanzu what next kike ganin zamu yi?".
tace,"akwai wani dodo anan ƙasar, na faɗa masa zan basa kwangilar kisan mutum biyu, yace min zan ba shi 20ML, nace masa 10ML zan ba shi, da ƙyar dai muka ƙarƙare a 15ML, dan haka zan sayar da motata ɗaya da kuma sabon filin da Maama ta bani, sai muga abin yi".

Sameer yace,"hakan yayi".
daga haka ta wuce ciki ta barshi anan parlo.

*Gombe.*
a cikin parlon na Kaka, tana zaune ta zabga tagumi tana jan carbi, sai Yami ma a gefe ta zabga nata uban tagumin, sai Maijidda dake kwance akan ledar É—akin, ba bacci take yi ba idonta ne kawai a rufe.
dukkansu kallo ɗaya zaka yiwa fuskokinsu ka shaida bala'in tashin hankalin da suke ciki, duk sun rame sosai. tun a daren jiya Amir ya ƙara kai kuɗin da kidnappers suka nema amma shiru har safiyar yau babu wani labari na dawowar Fillo, tun kiran da suka yi na cewar sun ɗauki kuɗin zasu yi abinda ya dace to basu ƙara kira ba, haka su Kaka suka yi kwanan zaune kamar yanda Amir yay daga can gidansu, amma shiru-shiru babu wani bayani.

to haka yau ɗinma tun 11 na rana Hajiya Madina tayo musu aiken abinci amma sun kasa ci. dan a inda Ɗausiyya ta ajiye flask ɗin tun ɗazu yana nan a inda yake babu wanda ya taɓa shi.
Yami ce tace,"Ƙawata ki ɗanci abincin nan ko loma biyu ce dan Allah".
Kaka ma tace,"ke ya kamata kici tunda kina da matsalar ulcer".

Kaka ta dubi Maijidda tace,"tashi ki zuba abincin nan kici".
bata buÉ—e idonta ba hawayen daya taru aciki ya sauko tace,"ba zan iya ci ba Kaka".

dai-dai nan suka ga an ɗaga laben ɗakin, da sauri suka waiga kusan a tare suna kallon ƙofar, da fatansu ace Fillo zasu gani, but sai saɓanin hakan, sai suka tsaya suna kallonsa sun kasa ɗauke idonsu akansa. kamar yadda shima ɗin bin su yake da kallo ɗaya bayan ɗaya.
kallon su yake yana so ya hango maganar da Khalil ya faÉ—a masa a fuskokinsu, babu wanda yasan da dawowarsa hatta kuwa Maama, dan ko driver bai kira yaje É—aukansa ba, daga airpot napep kawai ya nema ya hau ya taho.
ta gate É—in ma'aikatan gidan aka sauke shi, kuma yana shigowa straight É—akin Kaka yayo bai ko bi ta kan ma'aikatan dake gaishe shi ba, dan wata magana ma da yaji suna yi ta Allah ya sanya alkhairi duk bai fahimta ba.

Kaka ta ɗauke idonta akansa tana cewa,"bismillah me Babban suna". baya jin zai iya ɗaga ƙafafunsa daga wurin da yake ya shigar da ita cikin ɗakin, dan ya riga ya gama samun amsar tambayarsa a fuskarsu, ta tabbata matarsa ta ɓata, har tsayin lokaci ba'a ganta ba.
kuma sai ka lura sosai zaka hango uban hakin da yake yi tamkar wanda ya taho a guje tun daga El-Salvador.

Yami ta yunƙura ta miƙe ta ɗauko darduman sallah ta shimfiɗa tana cewa,"bismillah ga wuri". Turaki ya ziro daguwar ƙafarsa ciki yana takawa tamkar wanda bai da jini a jikinsa.
ya zauna hoton Fillo na haska masa acikin idonsa, tunaninsa ya katse sanda Kaka tace,"ina yini, an sauka lafiya?".
Yami ma ta gaishe shi sannan ya buÉ—e baki yana jin kamar ba zai iya maganar ba yace,"lafiya lau". sai kuma duk sauran maganar tasa ta katse ya kasa faÉ—in komai.

sai da Yami tace,"muna godiya da kulawarku, Allah ya bada lada". shirunta ya haÉ—e da fashewar kukan Kaka. Turaki ya juyar da idonsa kanta yana ta kallonta kamar yaune ya fara ganinta. kuka sosai Kaka take kamin tace,"ni da gawarta ne ma na gani hankalina zai fi kwanciya, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".

furucin nata na ƙarshe ya haɗe da rufewar idanun Turaki yana dukan ƙirjinsa, for few seconds yana jin kukan Kaka acikin kansa da kuma hasashen halin da take ciki.
ya buɗe idon ya sauke a ƙasa murya a sarƙe yace,"ki daina faɗar gawa Kaka, ganin gawarta ba yanzu ba insha'Allah, za'a ganta very soon aci gaba da adu'a Allah ya bayyanata". yanda yake yin maganar sai yaji kamar me koyon magana dan bai ma san ta yanda ya haɗa kalmomin ba ya faɗa.
Chapter 78 · 0% Book details