Sashe 137
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
can yaji ta riƙo hannunsa, ya juyo yana kallonta, ta kifa goshinta akan hannun nasa, hawayen idonta ya sauka akan fatarsa, ɗumin hawayen ya wuce ta cikin jijiyoyinsa har zuwa ƙirjinsa, tausayinta ya wanzu a zuciyarsa, gaba ɗaya jikinsa sai yay sanyi, Allah ma ya sa ni yana tsananin tausayinta, basarwa kawai yake yi, ko shi da yake namiji ba ya jin zai iya ɗaukar 2days bai ji muryar Mum da Maama ba, balle har akai ga kwanaki tara, ai sai rashin lafiya ta kama shi.
but sai ya ƙara ɗauke kansa akanta, ya tamke murya ya doka mata tsawa yace ta fitar masa a ɗaki, ta miƙe jiki a sanyaye kamar wacca ƙwai ya fashewa a ciki ta fita, kai tsaye ƙasa ta koma wajen su Yami fuskarta duk caɓe caɓe da hawaye, sai da taje ta tarar su har sun wuce, sai ta dawo ta koma ɗaki ta rufo ƙofa, ta hau gado taci gaba da kukan gado.
sai bayan fitarta Turaki yaji gaba ɗaya bai kyauta da abin da yay mata ba, ko babu komai mahaifiyarta take ta roƙon ya kira mata, duk sai yaji ransa babu daɗi, kasa daurewa yayi ya ta shi ya bi bayanta, a dunƙule ya ganta a tsakiyar gado, ya girgiza kai ya ƙarasa ya hau kan gadon gaba ɗaya.
ya ɗagota zuwa jikinsa ya kewaye yana ɗora haɓarsa a saman kanta, yasa hannu yana goge mata hawayen fuskarta, ya shiga hura mata iska a kunne yana faɗin,"cry cry Baby what the cry for umm?".
cikin kukan ta ce,"ba kai ba ne".
ya ce,"OMG! laifin me nayi da har ya sa kike kuka?".
tana motsi a jikinsa kamar zata shige jikinsa gaba É—aya ta ce,"ba kai bane sai kake yi min tsawa bayan ka san bana so".
yaja dogon numfashi ya sauke sannan yace,"to ai kece Fulani nah ba kya ji, duk yanda na so nai controlling anger na akanki sai kinja na ɗaga miki murya, phone ɗina fa kika fasa min da abubuwa masu muhimmanci a cikinta, but shikenan daga yau insha'Allah ba zan ƙara ba in dai tsawa ce".
ya faɗa yana ɗago kanta daga ƙirjinsa ya ɗora goshinsa akan nata, ya hura iska a idonta suka lumshe yace,"shikenan?".
kamar jiran tambayar takeyi ta girgiza masa kai da sauri tana cewa,"a'a".
ya buɗe ido yana kallonta da shirin jin abin da yake tsammani, but sai yaji saɓanin haka. "ka bani haƙurin kukan da kake ta saka ni to, har ma da ciwon da kaji min".
ba shiri ya tsura mata ido yana kallonta, sai yau ya ƙara ganin yarinyartarta ta fito sosai, ya ƙara tabbatar da muguwar rigimammiya ce, bakinsa yaƙi rufuwa da murshin da yake me haɗe da mamakin halin rigimarta.
tana buɗe ido suka sarƙe a nasa, sai kawai ta tsuke fuska ta kai masa duka a ƙirji tana mayar da kanta ta kwantar, ya shafo gashinta yana cewa,"ni ne zan baki haƙuri ko da wani daban kike?".
"kai ne mana, ai kaine kaji min ciwo, kuma kake min tsawa, kuma kake sa ni kuka, kuma kake share ni".
ya ƙara ɗago kanta yana kallonta ya ce,"duk ni ɗaya!, to yanzu tsakani da Allah ba ki ji kunyar cewa in baki haƙuri?, ke fa kika fasa min waya me tsada, ni bance ki ban haƙuri ba sai ke".
ta zumɓura baki ta ce,"to ai kaine ka janyo na fasa ban sa ni ba".
"ni kuma?".
ta É—aga masa kai kawai.
"to da nayi mene na janyo?, sharri kika fara?".
sai kawai ta ƙura masa ido, kukan da ya tsaya ya dawo sabo, ya kwanto kanta jikinsa yana faɗin,"subhanallah!, ni kam naga ta kaina, Fulani wai me yasa kuka ba ya miki wahala?, wallahi Allah bana son hawayenki its hurts me alots amma kinƙi ganewa. kin ga ni dai yanzu mu bar ma zancen in dai kuka za kiyi, kin min laifi na miki laifi kowa ya rama anyi 1-1, yanzu dai mu shirya don ranar yau ba zata wuce ba sai anyi sulhu".
ta kamo gaban rigarsa ta riƙe har sai da maɓallin ya cire, a hankali tace,"ni ba zan shirya da kai ba sai ka bani haƙuri".
ya shafo wuyansa ya ce,"ya zanyi, bada haƙuri ai ba zai sa na ragu da komai ba, kiyi haƙuri".
ta ɗauke hannunsa daga bayanta ta ɗago tana kallonsa, a shagwaɓe ta ce,"ba'a haka ba".
sai ya lanƙwasar da kai yana kwaikwayon shagwaɓarta ya ce,"to a ya ya?".
"ka kama kunnenka sai ka sakko ƙasa ka tsuguna".
ganin bai da niyyar yi yasa ta juya masa baya tana faÉ—in,"to kayi tafiyanka kawai". ta faÉ—a tana sakin kuka kaÉ—an.
wannan kukan ya sa shi saukowa ƙasa ya durƙusa, ya kama kunnensa da hannu ɗaya sannan ya kamo ɗayan hannunta ya ce,"to look at me mana".
ko da ta juyo ta gan shi sai ya kusa bata dariya ganinsa ya koma kamar É—an yaro.
ya sarƙe yatsunsu wuri ɗaya wanda hakan yasa ta jin wani abu ya tsarga ma ta, shi kuma ya lumshe ido ya buɗe sannan ya ce,"we should ask for forgiveness if we make a mistake, I made a mistake and i am asking for your forgiveness, and i know you will forgive me, please am sorry for all my wrong deed, am so sorry Fulani Nah, promise you not to repeat such a mistakes insha'llah".
kamar ya ƙara tunzurata sai hawaye sha, ya dafe kansa yana faɗin,"ya Allah! what again Fulani nah?, Is there anything else you want me to do after this?, ko kalar ba da haƙurin ne bai yi miki ba na sauya?".
ya faɗa duk a ruɗe dan Allah shaidarsa ko kaɗan ba ya son irin wannan kukan nata, yana taɓa zuciyarsa, kawai dai dan babu yacca zai yi ne ma yake dakewa ya nuna kamar bai damu da ita da lamarinta ba, amma can ƙasan zuciyarsa shi ɗaya ya san me yake ji.
cikin kuka sosai kamar zata shiɗe ta ce,"don Allah...". sai kuma tayi shiru ta kasa ƙarasawa. yay saurin komawa kan gadon ya riƙe hannayenta duka biyu cikin nasa ya ce,"don Allah what?, say it please, i am ready to do whatever you want".
sai ta faÉ—a jikinsa tayi masa tight hug ta ce,"don Allah kar ka auro Aisha, bana sonta kar ka aureta don Allah, kace baka sonta, i will do whatever you say, but for Godsake don't marry her".
he took a deep breath closing his eyes ya ce,"wacece Aisha?".
"wadda kace zaka faÉ—awa Baffa zaka aureta".
"when did i say that?".
"ranar da ka ji min ciwo, kana faÉ—awa abokinka zaka aureta wai kana sonta, har na fasa maka waya bana sane, kuma ni bana sonta don Allah karka aureta".
ya cika bakinsa da iska ya fesar, ashe plan É—insa yayi, ya shiga shafa gadon bayanta da gashin kanta in a romantic way ya ce,"the crying is enough, kinga ba ki da lafiya".
tana sassauta kukan ta ce,"to ka fasa auren nata?".
ya ce,"ba zan iya fasa aurenta ba".
"saboda me?". ta faÉ—a tare da fashewa da sabon kuka tana zamewa daga jikinsa.
"saboda tana so na, ni kuma ina so na auri wacca take so na, kuma tunda tana so na idan na aureta zanji daɗi, zata ke yi min duk abin da nake so, zata kiyaye ɓacin raina, ba zata barni da yunwa ba, zata ke yi min soyayya me daɗi.
to kuma kinga yanzu ke É—aya ce matata, ke kuma ba kya so na balle duk kiyi min wancan abubuwan...".
bai ƙarasa ba ta katse shi,"who told you i don't love you?".
"ke fa kika faÉ—a a gaban su Baffa ranar da nace na aureki, kuma ma fa har kika dage sai na sakeki, to ni bana so in takura miki shiyasa zan aureta saboda ina so in zauna da wacca take so na".
sai kawai ta ƙara faɗawa jikinsa ta ƙanƙame shi tana faɗin,"Allah ina sonka, kuma zan ke yi maka koma menene, but don Allah kar ka auro ta".
ya janyeta ajikinsa yana faɗin,"ba zan iya ba fa, Aisha tana so na sosai, ba zan iya butulce mata ba, kiyi haƙuri".
lokaci ɗaya tari ya sarƙe Fillo, ta dafe ƙirjinta da take jin yana yi mata mugun zafi kamar ana hura wuta, ta damƙe hannunsa ƙam jikinta sai shaking yake yi, hawaye tamkar an buɗe famfo, abu kamar wasa kan gadon sai ya ɗauki rawa kamar yanda jikinta yake yi, sai juyi take yi da kanta tana sosa ƙirjinta da yake yi ma ta wani mugun zafi.
Turaki ya ruɗe ya kamota, yanda yaga tana yi da ƙirji da yacca numfashinta ke neman yankewa sai ya tuna da maganar doctor na heart failure ɗin ta, hankalinsa ya tashi ya shiga ambaton innalillahi yana kiran sunanta, ya kasa janyota jikinsa saboda yacca ta sarƙafe, ta riƙe hannayensa sosai ta tsayar da ƙwayar idonta akansa, hoton yacca za su dinƙa shairing ɗinsa su uku ne kawai take hangowa cikin idon nasa, kamar ba zata iya jurar ganin faruwar hakan ba, kamar gwara ta mutu, kamar gwara ya rabu da ita kawai.
"Fulani nah, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".
maganar yake yi a kiɗime, ya sauko akan gadon ya bar ɗakin, ɗakinsa ya nufa cikin hanzari ya ɗauka drugs ɗinta da ya siya ya ajiye su safe gudun ɓacin rana, ya ɓallo ya buɗe bakinta ya zuba ma ta, sannan ya shiga tayata shafa ƙirjinta da take ta cewa zafi.
a hankali taji ta fara samun relief, sai ta kai hannunta gefen fuskarsa ta kama tana faÉ—in,"Allah ina sonka, i am saying this from the bottom of my heart".
ya shiga É—aga ma ta kai yana faÉ—in,"yes i know, na fasa auren Aisha, ba zan aureta ba na yarda kina so na, kuma za ki min ko me nake so".
ta sa babban yatsanta a gefen bakinsa ta ce,"i love you much, but ai kai baka so na, ka daina so na, kana sa ni kuka da yawa".