← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 176

Sashe 2

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"au kana ma tambayana ne me ya faru ko?, Allah dai ya dawo daku lafiya zaka min bayani daki-daki. lawyer nake, kasan abunda zan aikata da wanda ba zan aikata ba".

*No 3. Shongo Housing Estate, Gombe State.*
*17:00 pm.*

gidaje guda 5 ne a duk girman estate ɗin, kuma a kallo ɗaya zaka yiwa gida me lamba na uku ka gane ba ɗaya yake da sauran gidajen ba, tun daga girmansa zuwa tsaruwar ginin da yanda aka fitar da fasalinsa. anyi tsarin ginin gidan da ado da kwalliya irin na gidan sarauta, idan har ba sani kayi ba zaka tsammaci wata babbar masarauta ce. duk jikin bango da zaka kalla birjik yake da ado na ƙawa cikin nau'i iri-iri don burge idon me kallo.

daga cikin gidan, second part da ke kallonka a yayinda shigowa cikin haraban gidan, a cikin tamfatsetsen parlon na alfarma wanda yake shaƙe da kayan alatu na more rayuwa, me ɗauke da royal italian cushion.
sautin waƙa ne ke tashi acikin wata mp3 da ke manne ajikin wani glass kamar drower.

_Happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday happy birthday, happy birthday to you._

waƙar na fitowa ne a cikin sautin kiɗa, yayin da ƴan mata da yaran da ke kewaye da shi ke tafi da hannayensu cikin murna da annashuwa, suma su na bin sautin waƙar fararan haƙoransu duk a waje.
yana tsaye ne a gaban ƙaton cake ɗin da akai masa kwalliya da tsari me kyau an saka +1 ajiki, ga candle guda ɗaya a kunne a saman cake ɗin.

irin yanda fuskarsa ke washewa da murmushi ba zaka taɓa ganewa hakan ba a kallo 1 zuwa biyu da zaka yi masa. lokacin da sisters ɗin nasa suka gama bin waƙar sai ya sunkuyo da kansa yayi blowing wutan candle ɗin sannan ya ɗago yayin da idanuwansa ke a lumshe yana yiwa kansa adu'a acikin ransa, for few seconds ya buɗe yana sauke ganinsa akan ɗaya daga cikin sisters ɗinsa wadda duk ta fi sauran matan haske da kuma dogon hanci.

kyakykyawan murmushi suka sakarma junansu lokaci ɗaya. da ido yay mata alama ba tare da yay magana da baki ba, hakan yasa ta matso kusa ta riƙe hannunsa ya yanka cake ɗin, laɓɓansa na talewa da murmushi mai faɗi. ya yanko cake ɗin yana juyowa ga hannun damansa inda wata farar dattijuwa kyakykyawa ke tsaye sai murmushi ta ke, haƙoranta sunƙi rufuwa saboda irin farin cikin da take ciki, jikinta sanye da tsadadden less brown and black colour, tasha ɗauri kace budurwa me ji da tashen ƴan matanci.

bakinta ya nufa da cake ɗin da ya yanko ya saka mata, ta karɓa tana faɗin. "Happy birthday Son. wish you long life and prosperity".

"Use miyyete Maama, midon nana beldum joddaki emada eder duniyaru am". (Amin na gode Maama, ina alfahari da kasancewarki cikin rayuwata).

ya faɗa yana yanko wani cake ɗin, sai da ya kalla duka sisters ɗin nasa su huɗu sannan ya sauke kallon ƙarshen nasa akan Zaituna, kallon da yay mata ne kawai ya fahimtar da ita mai yake nufi, dan haka ta matso kusa da Maama, ta buɗe baki itama ya saka mata cake ɗin a baki, ta karɓa tana faɗin.

"Mi seyake be yaltugo nyandere danyeki ma Hamma am. Allah ɓeddane njamu be jutal balde barkante jo". (Barka da zagayowar ranar haihuwarka Yayana. Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana masu albarka.)

fuskarsa ta ƙara washewa da annuri, ƙwayar idonsa na haskawa da wani ƙyalli na farin ciki da son ahalinsa. sai ya dangwalo icing cake ɗin ya lakuta mata a hancinta da gefen kumatunta kamar ita ce birthday girl ɗin, yana faɗin. "Special thanks to you Sweetest".

daga nan kuma ya dinga yankar cake ɗin yana sakawa sauran sisters ɗin nasa a baki, suma duk su na binsa da wishing. haka ya gama basu sannan suma kowacce ta yanko ta nufo bakinsa da shi, sai dai bai karɓi na kowa ba sai da ya fara amsar na Maama da Zaitoon tukunna.

su na haka Kalil ya shigo aka ɗora da shi, gaba ɗaya shi sai ya koma ma kamar shi ne me birthday ɗin, dan gaban cake ɗin ya zauna yana ta ci. kuma zuwansa wurin sai ya sauya ƙaramin birthday partyn da Maama ta haɗa zuwa babba. cike da murna gami da so da qauna for one another suke ta abinsu, kowa jikinsa ya ɓaci da cream na jikin cake.

*Ɓangaren Masu Aikin Gidan.*
*17:40 pm.*

"Fillo kar ki zauna don Allah". wata ƴar tsohuwa fara ƙal da ke zaune a gefen katifa tana cura fura ta faɗa. "Kaka am debbo ba zan jima fa yanzu zan dawo". ta faɗa tana zura hijab kalar c-green wanda ya ɗauki farar fuskarta matuƙa.

ta zura siririyar ƙafarta cikin takalmi sannan ta nufi ƙofa tana faɗin,"sai na dawo Kaka". Can bayan gidan ta nufa, kasancewar yamma tayi hayaniya ta ɗan ɗauke ba kamar da safe ko rana ba, mafi akasari a irin wannan lokaci masu hidimar gidan sun tafi don hutawa kasantuwar ayyukan da suke sha tun sanyin safiya.

da yake gate ɗin gidan biyu ne, kuma gate ɗin baya ta nan ma'aikatan gida ke shige da ficensu, shi kuwa main gate na masu gidan ne. a bakin bishiyar da Amir ya saba tsayuwa duk sanda yazo anan ta same shi yanzuma, ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa ya jingina da jikin bishiyan yana jiran isowarta. tun daga nesa da ya hangota ya kafeta da ido, kuma kamar kullum sai Fullo ta tsaya da tafiya tana ɗan turo baki gaba.

ganin hakan yasa Amir ɗauke idonsa daga gareta yana fitar da siririyar dariya a fuskarsa. sannan yasa tafukan hannunsa ya rufe fuskar. bai san da ƙarasowarta wajen ba sai jin maganarta yay acikin kunnensa tace.

"ja66ama". (barka da zuwa) tayi maganar a hankali.

sai a yanzu ya buɗe fuskar ya juyo da fuskarsa zuwa gefen damansa inda ta ke a tsaye, bai ce mata komai ba sai wani sanyayyan murmushi da ya ɓalle masa a saman fuska. irin kallon da yake mata yasa taji nauyi ta rufe fuskarta tana ƙara faɗin.

"awari jam?". (anzo lafiya?) nan ma shiru yay bai amsa mata ba, ita ma kuma bata jira ƙara cewarsa ba ta kuma ɗorawa da faɗin. "noi him6e sare?". (ya mutanen gidan?)

Amir ya sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya tare da jan leɓensa na ƙasa zuwa cikin bakinsa ya tsotsa kaɗan. a shagwaɓe tace,"wai yau ba za'a min magana bane?". har yanzu murmushin da ke kan fuskarsa bai ɗauke ba yace,"mi tawi on jam?" (na sameki lafiya?)

"lafiya lau". ta faɗi hakan tana ƙara yin ƙasa da fuskarta da alamar dai macece ita mai kunya sose.

"Inna vi mi hofnuma". (Inna tana gaisheki)
"mi ja6i". (ina amsawa)

"shine kika barni na daÉ—e a tsaye haka ko?".

ta ɗan cije leɓenta kaɗan tana kallonsa sannan tace,"kayi haƙuri. na tsaya ƙarasa aiki ne, kasan me Martaba baya gari, to kuma duk san da zai dawo Kaka ake bawa aikin fura, shi ne yau bamu gama da wuri ba sai yanzu. yanzu haka ma na taho na barta tana ƙarasa curawa ita ɗaya. da ta gama zamu tafi can masarautar mu kai".

"Allah sarki Kaka...Allah dai ya kawo min arziƙin da zan zo na ɗauke ku nan bada jimawa ba".

ta haɗe girarta alamun son ƙarin bayani akan abinda yace.
sai ya É—aga tasa girar yana cewa,"ehh mana, ai idan na aureki ba ke É—aya zan É—auka ba. har da Kaka zamu tafi...Halimatu indai na aureki to lokacin hutun Kaka ne yayi".

wannan furucin na Amir zuciyarta taji ya ƙara burgeta, ta kuma ƙara yin amanna da shi. muryarta mai sanyin nan ta fito a hankali da cewa,"Allah ya buɗa ya bada arziƙi mai yalwa da albarka. ya kaimu lokacin".
"ameen Æ´ar aljannah". ya faÉ—i hakan san da yake sunkuyowa daidai fuskarta.

"yanzu bari na barki kije kici gaba da taya Kaka aiki, nasan yana da yawa. gobe in Allah ya kaimu na dawo".

"tom shikenan Allah ya kaimu. ka gaida min da Inna idan ka koma".

ya sunkuya ya ɗauko wata ƙaramar baƙar leda da ya aje a ƙasa ya miƙo mata. "ga wannan mangoro ne da bai nuna ba irin wanda kike so".

tasa hannu biyu ta amsa cike da jin daÉ—i. "amma kam na gode. dama ranar nan Maijidda ke ce min ta ganshi a kasuwa da suka je, ina ta kwaÉ—ayinsa tun ranar ashe da rabon zan sha".

"nima na fito zan taho wajenki naga ni a bakin hanya, nace to ba zan zo haka ba hannu na dukan cinya ba, sai na siyawa farin cikina wani abun".

yatsun hannunta na naɗe acikin ledar tayi murmushi da ƙara yi masa godiya. sai da ta juya ta nufa cikin gida sannan shima ya juya ya tafi.

"Fullo! Fullo!!". muryar Maijidda da ke fitowa daga nasu ɓangaren ke ƙwala kiran sunan, sunan da kusan kowa ke kiran Halima da shi a cikin gidan idan ka ɗauke Kaka wadda ba ko da yaushe ta cika faɗa mata hakan ba, tafi kiranta da Halimatu. jin kiran ya sata dakatawa daga tafiyar da take tana yatsina fuska har lokacin da Maijidda ta ƙaraso wajenta.

"na rasa me ya shiga kunnenki ya toshe miki ji akan cewar bana son irin wannan kiran sunan na mafarauta".
Fullo ta faÉ—a tana É—an hararta.

"ke kuma gaki kullum a cikin ƙorafi". "nayi ɗin". ta faɗa tana sake ɓata rai.

Maijidda ta taɓe baki tana cewa,"ke dai kika sani. daga ina kike? mene wannan?". ta jera mata tambayoyin tana ƙoƙarin amsar ledar hannunta.

"daga inda kika aike ni Kaka".

Maijidda tayi gajeriyar dariya bata ce komai ba. wanda tuni har ta buÉ—e ledar ta É—auko mangwaron ta fara gatsa. hakan kuma yasa Fullo jan tsaki tayi gaba abinta, dan idan da abinda ta tsana a halin Maijidda shi ne cin abu ba tare da ta wanke ba, ita dai da ta ga abunda bakinta yake so ba ruwanta da tunanin wankewa zata afashi cikin baki.

sun shigo tsakar gidansu suka ci karo da Masu aiki nata zubewa ƙasa su na aika gaisuwa da kirari.
Fullo ta ɓata rai sosai ta kama hannun Maijidda ta dakatar da ita daga tafiyar da suke.
Chapter 2 · 0% Book details