Sashe 132
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tana gama faɗa ta miƙe ta bar wajen, Maama ma ta fi ce, Zaytun ta haye Uptairs tabi bayan Mum, aka bar Fillo da Turaki kawai, ta ɗago kumburarrun idanuwanta ta kalle shi taga fuskarsa kamar baƙin hadari, hawaye na sakko mata ta ɗora ido akan takardar, sai taji fargabar yau tafi ta ko yaushe, bata san me yasa ba ko kaɗan bata ƙaunar adadin sakin da yay mata, sai dai kuma a sanda ta shiga karanta rubutun da ke ji sai taga saɓanin abin da zuciyarta ta faɗa mata tun ranar da ya bata takardar, idanuwanta suka karanta abin da yake daban da wanda take ta haskowa yana rubuce a jikin takardar.
wannan wani rubutu ne na daban, rubutun da ko kusa bai da alaƙa da abin da sakin da ta gama yankewa kanta anyi mata, rubutu ne take kallonsa da handwriting ɗin da ya burgeta, haka kuma taji kalaman da ke jiki na tafiya su na haɗewa da jinin jikinta, taji tana sha'awar da a karanta ma ta su a kunnenta.
ta karanta sau ɗaya ta kuma gane ma'anar but haka kawai sai taji tana ƙara buƙatar ta ƙara karantawa.
_my life depends only on you, i love you Fulani Nah, i love you up to the square of infinity, i promise you that i will take care of you morethan i will take care of my self, trust me when i say i can't do without you, Fulani Nah love me even just a bit._
ta rufe ido a sanda ta gama karantawa, taji bugun zuciyarta na sauyawa zuwa wani yanayi da bata taɓa riskar kanta a ciki ba a dai ga me da Turaki, ta sauke numfashi ta buɗe idon tana sauke akan Turaki.
tuni ya miƙe tsaye hannayensa na zube cikin aljihu, ta bi shi da kallo sanda ya wuce ta gabanta, sai da yaje bakin ƙofa sannan ya dakata ya juyo yana kallonta rai a haɗe murya a tamke ya ce,"kin taso ko kuwa".
ta ɗauke idonta da ga kansa ta mayar gefe, ya ƙara cewa,"ba za ki taso ba".
ta kumbura baki ta ce,"ai kace kar na koma maka gida".
Turaki ya saki baki yana kallonta, zai sake magana sai ga Mum nan ta sakko, tayi masa kallo É—aya ta É—auke kanta ta isa kujera ta É—auki wayarta, har ta juya sai kuma ta waigo ta kalli Fillo dake zaune ta ce,"tashi ki bi mijinki".
Fullo ta miƙe ta bi bayansa lokacin har ya kai bakin mota, ta buɗe baya ta shiga, ya kalleta ta mirrow ya ce,"do i look like your driver?".
ta hankaɗo laɓɓa gaba ta sunkuyar da kanta ƙasa tana shafa bandage ɗin hannunta, tsawar duniya ta dawo gaba tayi biris da shi kamar ba wannan Turakin da take tsoro ba, yay ƙwafa yaja motar suka bar gidan, sai da suka kusa zuwa gida sannan ya tsaya ya fito ya zagaya ya buɗe side ɗin take, yasa hannu ya yo waje da ita ya mayar da murfin ya rufe tukunna ya koma side ɗinsa ya figi motarsa ya barta a wajen.
tana kallo ya wuce gidansu da alama ba gidan ya nufa ba yanzu, ta juya ta kalla nisan da suka yo daga gidansu, sannan ta kalli kusancin da take da shi da na su gidan.
har ta juya zata koma can gidan sai taji yo haushin karnuka babu shiri ta tattare riga ta falla gida a guje, ta dinƙa buga gate babu ƙaƙƙautawa tsoro fal ranta, Baba me gadi kuwa na can toilet ya fito da sauri yazo ya buɗe yana cewa,"kai jama'a waye haka?".
yana buɗewa Fullo ta sunkuya ta ƙasan hannunsa ta shige da gudu, ya leƙo yana kallon waje bai ga komai ba, ya rufe ƙofar, yana juyowa yaga tuni har ta shige part ɗinta, ya buɗe hannu alamun ko lafiya?.
ƙarfe sha ɗaya Fillo taji ƙarar zuge gate, ta miƙe da sauri ta leƙa ta window taga Turaki ya fito a mota, ta ga sun tsaya da me gadi su na magana, idan ta fuskanta kamar Baban na labarta masa yanda ta shigo ɗazu ne, kuma da mamakinta sai taga ya wuce part ɗin Ilham as usual.
ta saki labulen windon ta koma kan gado ta kwanta da tunanin abubuwa kala-kala acikin ranta.
*Vote, share and comment.*
[9/6, 23:45] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*49*
washegari da la'asar Turaki na zaune a falonsa Bello ya shigo, kallo ɗaya Turaki ya yi masa ya mayar kan computer ɗin da yake dannawa, Bello ya ƙaraso gabansa ya ɗaga robar faro ɗin da yake hannunsa ya tuttule masa ruwan ciki akansa.
"Bello what kind of rubbish be this?".
"ɗan iska ma nan ya ganka ya ƙyale MT, yanzu na ƙara sarawa girman rainin hankalinka, kuma ban yafe ba zagin da ka ja min, akan kujera nake amma sai da na miƙe babu shiri tsabagen shigar zagin nan, har yau a jijjige nake da shi, sai kace kayi abu ni da banyi ba ni ke kwana aciki".
Bello ya faɗa yana zama kan kujera, Turaki ya dinƙa kallonsa da wani kallo kafin yay tsaki ya miƙe ya cire rigar jikinsa da ta jiƙe.
"tukunna ma ni ban gane maka ba har yanzu, ni ka rainawa hankali ko kuma su Mum É—in ka mayar marainan wayonka?, sarai dai da iliminka ka san yarinyar nan ba ta da iddah akanka amma ka barta tana zama acikin gidanka".
Turaki bai tanka masa ba ya ci gaba da aikinsa, sai can Bello ya fara masa ƴar murya,"haba Aminina kar muyi haka da kai mana, faɗa min gaskiya don Allah. gudun ɓacin ran su Maama yasa ka ƙaryata sakin da kace min kayi ko kuma ni ɗin dai ka mayar sauna?".
"munafiki kawai". Turaki ya ce da shi yana hararsa.
Bello yay dariya sosai ya ce,"naji ka kirani da koma menene, ka san Allah idan baka faÉ—a min gaskiya ba to zanje na faÉ—awa su Maama gaskiyar abin da na sa ni, dan ni dai kace min ka saketa".
ya faɗa yana miƙewa.
da sauri Turaki ya ce da shi,"kai wai mara hankalin ina ne, yanzu sai kaje ka faÉ—a musu hakan?".
Bello ya ɗaga kafaɗa,"ofcourse, zan zuba maka ido ka ci gaba da zaman haramun da yarinya saboda kana gudun ɓacin ran iyaye, ai gwara a faɗa musu kawai su san gaskiyar abin da ke faruwa, yarinya ta tafi gidansu ta sami wani mijin tayi aurenta, kai kuma ai maka duk hukuncin da ya dace da kai. ko nufinka ka mayar da ita ne baka faɗa min ba?".
Turaki na daɗa ɓata rai ya ce,"ni dama ban saketa ba, ko da nace maka na saketa to wallahi tallahi ban saketa ba".
dariya ta zo wa Bello ya ce,"yau har da su rantse min?".
"saboda ka ƙyale ni na huta, kamar yanda ka barni na huta da takurarka na 7days".
Bello ya jijjiga kai,"amma kai dai anyi mugun ɗan rainin hankali, da ma saboda na ƙyaleka na 2days yasa kace min haka saboda ka san zanyi fushi?".
Turaki yay masa banza, sai kuma Bello ya ƙara cewa,"to kuma na ga har yanzu baka bar nan part ɗin ba?, ko kewar ta nan ɗin kake yi tunda ita ka ɗanɗana ka ji?, ko kuma ita ma baka saketa ba hankalin mutane ka raina?".
Turaki ya dire abin da yake ya dafe kansa, wucewar wasu sakanni tukunna ya buɗe ido ya zuba akan Bello ya ce,"in kana ƙaunar Allah da Annabi ka ƙyale ni, saboda fa wannan shegen sa idon naka yasa na barka a yanda itama waccan yarinyar ta ɗauka".
Bello ya gimtse dariyarsa ya ce,"tun da kace Allah da Annabi an wuce wurin. mu koma kan aiki, É—a zu mun yi waya da financial sectary na IBTC company, ina wancan document É—in da ka haÉ—a?,".
"shi na ke haÉ—awa yanzu?".
"what! ba jiya ka ce ka yi completing nasa ba?, yau fa ya kamata ace mun yi printing an kaiwa Baffa".
"to ya zan yi, after na gama wayar ta lalace, kano ma na kai gyaran a jiya, na so na tsaya na taho da ita Khalil ya damen da kira akan in taho gida ya ga kamar ba lafiya, but mun yi da shi me gyaran za'a kawo yau, ni kuma ganin ba su kawo tun safe ba naga gwara in haÉ—a wani kawai".
"wai wayar da ka siya last week ne ta lalace ko wanne?".
"ita ce".
"kaii! da ma ba original ba ce cutarmu suka yi, but tawa fa normal take, me ya sami taka É—in da ma?"
Turaki ya É—an kalle shi sannan ya ce,"fasata ta yi, gaba É—aya ta tarwatsata ta koma fanko".
"ban gane ba, da ma ka haihu ne da har yara su ka fara yi maka babban ta'adi haka?".
"nop ban haihun ba dai tukunna, fitowa tayi da ga cikin ta fasa sai ta koma".
ya kalli Bello da kyau ya ce,"ka daina tambayar rainin hankali Bello, wataran sai ka haÉ—u da wanda zai rufeka da duka".
ya maida hankalinsa ga abin da yake yi, Bello dai sai cika shi da tambayoyin rainin wayo yake yi amma sam yaƙi responding nasa, da ya gaji kawai ya miƙe ya tattara komatsansa ya fice ya bar masa part ɗin gaba ɗaya.
part ɗin Fillo ya koma, lokacin tana kitchen su na aiki da yaran da aka aiko mata yau da safe, jiyo motsin shigowa parlon yasa tai saurin wanke hannu a sink ta fito, ganinsa ta yi zaune ya ɗora ƙafa ɗaya kan table ɗin, yatsansa ɗaya cikin baki ya kafawa laptop ɗin ido da alama nazarin wani abu yake yi, kafin ta ɗauke ido akansa taga ya miƙe da kayansa a hannu ya wuce upstairs, ta bi shi da kallo tana hararsa, sannan ta juyo ta mayar da idonta wurin da ya tashi tana faman ɓata fuska, haka kawai ya zo ya ɓata ma ta wuri, ya ɗauko table daga in da yake amma mayarwa ta gagara.