Sashe 56
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
***
A ɓangaren Bello, Turaki da Khalil. zaune suke a parlo bayan sun kammala breakfast, kowanne da takardu a gabansa da kuma biro, suna tattaunawa akan batun sabon company da Baffa yace za'a ƙara buɗewa.
Khalil na kallon takardar dake gabansa yace,"anawa tunanin gaskiya gwara a buɗe na sarrafa kayan miya a maida su na gwangwani ko leda. tunda shine kamfanin mafi ƙaranci da muke da shi a nigeria, kuma ina ganin hakan za'a sami abinda ake so fiye da tsammani".
Bello yace,"view É—inka yayi kyau, sai dai yanzu mu fara kammalawa da wannan da Maama tace".
Turaki ya kalli Bello tace,"me Maaman tace?".
Bello ya duƙa yay rubutu jikin takardar gabansa tukunna yace,"Company ɗin dake Lagos da Baffa yace a siyar, tace ba za'a sayar da shi ba za'a maida shi na fulawa, Shine batun da nai muku jiya cewar zanje Hong Kong, saboda injinan da za'a siyo na yanda za'a sarrafa fulawan.
but ina ganin tafiyan ba ni É—aya zanje ba da kai zamu tafi Turaki, zanyi convincing Maama mu tafi tare. tunda tafiyan jirgi ne ba wai a mota ba, becouse kai ka fini sanin kaya masu kyau, idan ni É—aya ne za'a iya haÉ—ani da fake one".
Turaki ya ɗan ciji leɓensa kaɗan sannan yace,"why not su turo da kayan kawai ba sai anje ba".
Bello yace,"yanda ma fake one's É—in zasu fi zuwa kenan. Maama already ta riga taga hotunan su, dan ko launching nasu ba'ayi ba, shisa tace naje ayi a gabana, so ta re da kai dai zamu tafi".
Khalil yace,"shikenan Turaki Flour Mills ya tabbata kenan, dan nasan hakan za'a saka tunda Maama ce ta kawo idean".
Bello da sigar tsokana yace,"ah haba dai sai kace shi É—aya ne É—a, ai sai dai a haÉ—a sunan mu duka".
Turaki ya taɓe baki ya miƙe tsaye yana faɗin,"i don't think i will go with you, kayi tafiyanka kawai ko kuma kuje da Khalil. beside; Sameer ma na Hong Kong ɗin kana iya samunsa acan".
Bello yace,"aiko dole sai kaje, ka zama cikin shiri kawai Malam, coux daga nan ma tictiket É—inmu zanje amsa".
ba tare da Turaki ya ƙara cewa komai ba ya fice daga parlon. direct part ɗin Boɗejo ya nufa, acan ya tarar da sisters nasa duka a zaune sun saka Boɗejo a tsakiya sai hira suke, sai bayan ya zauna kan kujera ya fahimci lissafi suke tayi, lissafin aurensa.
Samha cikin zumuÉ—i da tsananin murna take faÉ—in,"ai BoÉ—ejo babu zancen wani 1week, biki zamu fara from day 1 to day 10, kuma kowacce rana sai mun zubar da naira, sai doller tayi kuka ita kanta sai ta san ana bikin first born a gidannan".
Nihal ta taso a kusa da Boɗejo ta dawo kusa da Turaki, ta kamo hannunsa tana cewa,"please Hammah ka sama mana Anty kaji, Allah mun ƙagu ayi bikinka, Allah duka burinmu na kan wannan ranar Hammah, I feel like your wedding day is the first wedding in the world".
shima ya riƙe hannun nata yana kallon innocent face ɗinta yace,"to kun zaɓa min matar ne?".
dai-dai nan Samha ta taso itama ta zauna gefensa,"ka yarda mu zaɓa maka Hammah?, akwai friends ena da friends Zaytuna da yawa da suke sonka, duk basa ƙasar nan, gasu kyawawa masu class, sai wacca muka ɗaukar maka".
tana kallon Zaytuna tace,"ina wannan balarabiyar ƙawar tawa da mukai vedio call ranar nan?, kin tuna ta?, basu dace da Hammah ba don Allah?".
bata jira cewan Zaytuna ba koma garesa tana ƙara cewa,"Hammah ka yarda muyi maka zaɓi?".
ya kalleta sai kuma ya kalla Zaytuna wadda ke ta kallonsa da tarin murmushi. kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace,"kuyi adu'a Allah ya kawo ta gari, aure ai lokaci ne".
BoÉ—ejo tace,"a'a lokacinka fa yayi kai harma ya wuce tuni, dan dai kawai Uwarka da Ubanka sun zuba maka ido ne, sai abinda kake so za'ai, yo wannan gata ai ba gata bane. kai in baka san mutumcin mutum aure ba ai su sun sani, to ni dai ina gajiya sai na haÉ—aka da duk wadda naga dama, Allah na tuba Æ´an mata gasu nan birjik a danki...kuma dai ma ni in faÉ—a maka yar gida muke so jinin sarauta ba bare ba, ah tou karma lokacin da hankalinka zai dawo jikinka kace zaka É—auko wata can daban, ina ga Madina ce kawai ta shigo zuri'armu a bare".
shi dai bai ce komai ba ya jinginar da kansa jikin kujerar. Nihal ta daɗa riƙe hannunsa sosai tana faɗin,"can't wai to see your wedding day Hammah, wayyo Allah wa ya ganni da Sister inlaw". ta faɗa cikin wani irin expression tana faɗawa jikinsa.
ranar a part É—in BoÉ—ejo suka yi lunching, shi Turakin ma bai iya cin komai ba, yanayinsa kamar dai wanda bai cikin natsuwarsa.
after la'asar ma da ya dawo daga masallaci part É—in BoÉ—ejo ya koma, lokacin da ya shiga bedroom nata tana waya da Inna Falmata. ganin shigowar tasa yasa tace,"to sai anjima Falmata, a dai ci gaba da aiki me kyau don Allah, kinga acikin sati huÉ—u yau munci kwana biyar, to shi haka lokaci yake sai dai idan ba'a saka shi ba, nan dai nan sai kiga yazo".
daga haka ta kashe wayar ta ajiye a kusa da ita, ta kalli kan gadonta da Turaki ya kwanta, he don't know why yake jin jikinsa yayi sanyi, tunda Bello yace masa zasu yi tafiya tare yake jin wani feeling mara daɗi a tare da shi, and for the first time da yake jin kamar zai rasa rabin jikinsa, Boɗejo ta kai hannu ta taɓa ƙafarsa taji zafi like zazzaɓi ne ke shirin kamasa.
tai salati tana faÉ—in,"baka da lafiya ne Turaki?".
ba tare da ya buÉ—e idanuwansa ba yace,"lafiyata lau, kawai ina jin ba daÉ—in yanayina ne".
Boɗejo tayi saurin tashi tsaye,"a'a baka jin daɗi ai yana nufin baka da lafiya, tun ɗazu dama na lura da yanayinka, to da yake kai ɗin me ƙauran baki ne ba zaka fito kace baka da lafiya ba sai dai ciwo yay ta cinka".
dai-dai nan Ɗausiyya ta shigo ɗakin riƙe da ƙwaryar fura a hannunta. ta shigo da sallama ta nemi wuri ta ajiye, zata juya Boɗejo tace,"kinga garzaya da gudu ki kira min Zaytuna a, kice tazo da sauri Turaki babu lafiya. bance ki bari Uwassa taji ba balle tazo ta ɗaga min hankali da bala'ƴaƴƴan kukanta anan".
in few minutes Zaytuna ta shigo É—akin hankalinta a tashe, kai tsaye inda yake kwance ta wuce.
kamar zata yi kuka ta taɓa jikinsa da yay zafi rau. "Hammah wake up mu tafi asibiti". ya buɗe idonsa da sukai jajir ya kalleta. ahankali yace,"ɗauko drugs ena".
yana faɗa ta miƙe cikin sauri ta fita, bata jima ba ta dawo ɗakin jikinta sai rawa yake yi, tuni kuma hawayen dake cikin idonta ya sami nasarar gangarowa, bata ƙaunar wannan ciwon nasa na kidney ya tashi, idan ya tashi sai sun gama fidda rai da shi tukunna lafiya take samuwa.
Boɗejo ta fito daga toilet a lokacin, tana kallon Zaytuna tace,"ciwon ne ko? ai tun jiya nake lure da shi tunda naga ƙwayar idonsa da kuma yacca ya ɗan kumbura ɗin nan, to kin sansa da ƙarfin halin jaraba, bai san cutar kansa yake ba".
Zaytuna na hawaye tace,"inje in kira Maama?". da sauri BoÉ—ejo ta girgiza kai,"a'a sam bakinki alaikum, da yardar ubangiji yana shan magani zai sami lafiya. ko kin manta itama bata da lafiya ne?, jiya likita da ya aunata yace jininta yayi mugun hawa sama, so kike tazo ta mace mana lokacinta bai yi ba, a'a bari tukunna dai a É—aura aurensa ta gani tana raye".
ta zauna kan kujera tana faɗar,"dan Allah kinga kwaɗa kira ɓangaren masu aikin nan wannan yarinyar Fulani tazo ta matsa min ƙafata, naga ta iya matsa ƙafa, kwanaki da tayi min kyace tausar inji irin wacca Hashim ke biyan uban kuɗaɗe ai min, ni tunda nazo ma ban ganta ba sai wannan baƙar nake ta gani tana suntiri, yanzu ma ita ta kawo min fura kuma ba zan iya sha ba gaskiya, da ganinta ba bafulatana bace irinmu. ni Allah yasa ma ba korar Fulani ɗin kuka yi ba, ni ƴa su aka koreta kuwa ba'a kyauta ba, yarinyar ga natsuwa ga hankali ga kyau da tarbiya, in kuwa an koreta to zama a dawo da ita gaskiya, dan ina son tausarta tayi masifar iyawa".
Zaytuna tace,"tana nan ba'a koreta ba. bata jin daɗi ne". Boɗejo tace,"Allah sarki ashe shisa, ni wannan ƴa ma da ƙyar in ba sikila bace, Allah dai ya bata lafiya, anjima sai ki rakani wajensu na dubota, wannan yarinya ai tayi, idan nazo biki ga ladabin da take min ba wallahi, ba irin sauran ƴan aikin ba da sunzo sun waye sai su koma maka kallon ɗan banza, yanzu dai ban ruwa a kofi inyi masa tofi sai ki basa maganin ya sha, wannan ciwon nasa ba ƙaunarsa nake ba".
Zaytuna ta ƙurawa Turaki ido sosai, wannan gajeran numfashin ke ɗaga hankalinta, fatanta ɗaya kar akai stage ɗin da kowa zaiji jiki ata dalilin ciwon. ta sauke numfashi sannan ta miƙe ta fita ta ɗauko faro ta dawo, a cup ta zuba ta miƙawa Boɗejo. zata ƙara fita Boɗejo tace,"tsaya ki basa ya sha, kin san ba sanin kan magungunan nayi ba". tace,"ya sami bacci ne, zanje na dawo".
Boɗejo tace,"to alhamdulillah indai yay bacci ciwon ma ai da sauƙi".
kusan awa ɗaya da rabi Boɗejo na tare da Turaki, yana ta bacci har zuwa lokacin, ita kuma tana gefensa cike da tausayinsa sosai. tana tayi masa adu'a iri iri, lokacin har ƙarfe shida da rabi na yamma tayi.
lokacin Fillo ta tura ƙofar ɗakin ta shiga da sallama, Boɗejo ta amsa tana yi mata maraba.
ta shigo ta tsuguna tana gaidata, idon Boɗejo akanta tace,"sannu, aiko ga shi nan duk kin ƙara zaftarewa, kina cin abinci kuwa ƴar nan?".