← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 176

Sashe 59

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a duk sanda ya nemi abu a wurin Hajiya Madina take a wurin take yi masa ba tare da ɓata lokaci ba muddin bai fi ƙarfinta ba, amma a wannan roƙon da yay mata sai da ta ɗauki tsawon kwana biyu shi kansa bata shiga sabgarsa ba, wai sunan shawara take tayi da zuciyarta taga idan zata iya yafewa wanda ya ƙalawa ɗanta sharrin sata. daga baya kuma sai komai ya warware tunda suka ƙara tausarta shi da Khalil da Bello, daga nan kuma Hajiya Madina ta sauko ta ci gaba da bawa Fulani girmanta na matsayin da take da shi.

yana zaune cikin tunanin abubuwan da suka faru a baya Ilham ta dawo, sai da ta taɓasa tukunna ya buɗe idonsa ya sauke akanta. tayi kyau acikin shigar da ta sauya na sky blue ɗin code less me shegen tsada, ya miƙe yana ɗaukar key ɗinsa ya kalli Abbas yace,"babban Yarima zan wuce".
ba tare da Yarima Abbas ya É—ago daga operating laptop nasa ba yace,"ka gaida Maama da Zaytun".

fitowarsu daga sashin Yarima Abbas suka ci karo da Fulani Azima ta fito daga turakarta kuyangu uku na biye da ita. haka kawai Turaki yaji gabansa ya faɗi da ganinta, lokaci ɗaya kuma ƙwaƙwalwarsa ta shiga karanto wasu ayoyi na kariya dake cikin alƙur'ani, ba wai yana nufinta da mugun abu bane, a'a haka kawai tun a ranar da taje asibiti dubasa yaji zuciyarsa ta kasa kwanciya da ita, kuma yana ta ƙoƙarin yakice abinda zuciyarsa ke raya masa akanta amma hakan yaci tura, in yayi ƙoƙarin watsarwa sai maganar Fillo ta dinƙa dawowa cikin kansa na batun asirin da tace ta ɗauke akansa.

*ASIRI!* har yau kalmar nan tsaye take a cikin ransa. kenan inda Allah bai shigo da Fillo cikin rayuwarsa ba shikenan duk kalar asirin da yaji ta É—auke akansa sai ya kama shi?.

ya rufe ido ya buÉ—e yana kawar da wani tunani dake shiga sashen tunaninsa.
Fulani Azima ta tsaya da tafiya tana kallon Turaki da Ilham dake tafiya, wai Turaki ne tare da Æ´arta?. lokaci É—aya zuciyarta tayi wani mugun matsewa. taji kanta ya sara mata, lallai bata ga ta zama ba, sai ta sake sabon shiri, dole ne ma ta koma wurin boka, zata faÉ—a masa ya sauya tsarin aikinsa, sannan kuma yayi mata duba akan duk shegen dake lalata mata aiki.
a harzuƙe ta juya ta koma ta fasa zuwa inda ta nufa.

cikin motar Turaki dake tafiya akan titin zuwa PERKY FRAGRANCE STORE, wayarsa dake hannun Ilham tayi ringing a karo na huɗu, kuma a karo na huɗun ta ƙara ce masa,"Hamma ya kamata kayi picking call ɗin nan".

shima a karo na huɗun ya ƙara bata amsa da cewar,"picking ɗin ba ya da wani amfani".
a karo na biyar da kiran ya ƙara shigowa Ilham ta tsaya tana kallon lambar da babu suna ajiki. kasancewar kiran ba huruminta bane dalilin da yasa tun farko bata bi ta kan lambar ba, sai a yanzu da idanuwanta ke kallon lambar cikin kanta kuma na karanto mata lamabar ƙawarta Gimbiya Aisha.

har sanda kiran ya katse Ilham bata bar kallon lambar ba, haka ɗaya sai taji kamar an soketa da kibiya a ƙirjinta. kenan dama da gaske Aisha take yi mata.
conversation ɗin su na last haɗuwarsu ya shiga yawo acikin kanta. ranar buɗe company ɗin su Turaki, ranar da Turaki yay kwalliyar da babu macen da zata kalle shi bata kwaɗaitu da ya zama mallakinta ba. kuma a sannan Aisha ke bata labarin ta taɓa ganinsa a asibiti sanda taje duba wata cousin sister ɗinta, taso tayi masa wulaƙanci irin wanda kare ba zai shinshina ba amma sai ya juya ya tafi ya barta da zummar zaije ya dawo ya bata haƙuri, ashe juyawa yayi ya tafi da zuciyarta.

ya tafi da dukkan nutsuwarta da tunaninta, don haka a ranar buɗe company da ta ƙara ganinsa ba zata yi saken da zai suɓuce mata ba. a lokacin Ilham faɗa mata tayi kai tsaye cewar indai Hammah Turaki ne ba zai sota ba, hasalima ko kulata ba zai yi ba talkless of batun soyayya har ta kaisu ga aure. ta faɗa mata bai taɓa soyayya da wata mace ba.
sai dai buÉ—ar bakin Gimbiya Aisha ce mata tayi,"Ilham, ni kuma ki rubuta ki ajiye, zan sauke duk wani jin kai dake kansa, zai soni, zai nemi aurena, zai aure ni a sanda ya gama haukacewa akaina".

Ilham tace mata,"asirce min ɗan'uwa zaki yi?". Gimbiya Aisha na murmushi tace,"bana fatan watarana tazo da zan aikata saɓon ubangiji Ilham, amma ki sani, zan haukata ɗan'uwanki ne kawai da salon soyayyata me zafi, irin wacca zai hanaku sakat har sai kunzo kun ɗaukar masa ni kun kai masa gidansa. da gaske nake miki Ilham ina son Brothernki sosai wallahi, kuma ina adu'ar Allah yasa ya zama mallakina, nasan kuma zan samu tunda dai har sarauta ce ta haɗu da sarauta".

Ilham ta rumtse idonta sosai tana jin wani iri a ƙasan zuciyarta wanda ta rasa dalilin hakan. ta wutsiyar ido take kallon Turaki dake driving cikin ƙwarewa, yana bin karatun ƙur'anin da ya kunna. ta mayar da murfin idonta ta rufe tana jin a ranta kamar zata yi kuka.
Turaki ya kai sanyayyan hannunsa ya taɓa goshinta, lokacin ta buɗe ido tana miƙewa zaune.

yace da ita,"did anything happend?". ta girgiza masa kai,"ba komi Hammah". "kuma kika yi silent bayan na san wannan bakin baya rabo da labari".
tai murmushi tukunna tace,"to ai naga kana bin karatu ne". Turaki ya kai hannu ya kashe karatun sannan yace,"ina jinki, bani labari".
"wanne iri to?". yace,"irin fitinar da kika dinƙa yi da kina yarinya bayan na koma Europe wurin Granny".

tasa hannu ta rufe fuska tana cewa,"to ai kasan wannan time en, kaga babu batun a baka labari". ya ɗan waigo ya kalleta yana cewa,"give me my phone". ta miƙa masa yay dialling numba ɗin Zaytuna ya kira.

sai da kiran ya kusa katsewa sannan tai picking, bayan picking É—in shiru yay baice da ita komai ba. sai itace tayi murmushi daga inda take tana duban Fillo dake bacci hankali kwance akan gado tace,"bata tashi ba".
Turaki yace,"up to now?, lafiya kuwa?".

Zaytuna tace,"lafiya lau, rashin bacci ne da bata yi ba jiya". "why is that?".
tace,"naje wurin Kaka nace mata ko da zata ji shiru Fillo bata dawo ba zata kwana a wurina, saboda naga kaman bata jin daɗi tun ɗazu tana ta bacci...so Kakan sai take ce min ai jiya ma kwana tayi bata rumtsa ba tana ta kuka, kuma tayi tambayar meke damunta bata sanar mata ba, ta dai bar hakan a rigimarta kawai...dana dawo kuma naji jikinta da zafi, kukan da tayi ma zai iya sa mata zazzaɓi".

Turaki took a deep breath with out saying anything, hakan yasa Zaytuna kwantar da murya tace,"i will prescribe some drugs sai ka taho da su saboda ciwon yatsanta. like da fever ma a jikinta".
yace,"oak send it to me right now via message".

sai kuma yace,"Bello fa?". Zaytuna tai dariyar da ya bayyana haƙoranta tace,"he left since, da ƙyar na taushe shi wai sai yaje wurin Maama anyi wacca za'ai".
tsakin Turaki ya fita da ƙarfi yana cewa,"mahaukaci ne ai...don't pick up his calls again".
Zaytuna na murmushi tace,"na hannun daman naka Hammah?". yace,"ehh shi". ya faÉ—a yana katse wayan.

ya kashe kiran yana parking a ƙofar store ɗin da suka zo. suka fito a tare da Ilham wacce ya zagaya yana tambayarta dalilin sauyawan mood ɗinta alhalin ba a haka suka fito ba.

****
a hankali Fillo ta buɗe idonta daga ɓaccin da ta tashi, ta sauke ƙwayar idonta akan gadon da ta san ba katifarsu bace ita da Kaka.
tayi wani mugun zabura ta tashi zaune tai saurin durowa daga kan gadon, cikin ranta tana faÉ—ar kalmar innalillahi.

ta rasa ma da wanne irin tunani zata yi amfani wajen tuna komai. bakin ƙofar da ta san ta riƙe handle tana kuka kawai take bi da kallo, da yaushe tayi baccin?, kuma ya akayi tazo kan wannan gadon?. kawai sai ta duƙe a wurin ta kifa kai da gwiwa tana fashewa da kuka, lokacin kuma taji kiran sallah ya shiga cikin kunnenta wanda ko ba'a faɗa ba tabbata na magriba ne.

ta miƙe da sauri ta wuce ƙofa zata buɗe taji ƙofar a rufe, ta dawo a hargitse ta shiga duba keys acikin drowers bata gani ba, taji zuciyarta ta ƙuntata. shin Turaki wanne irin mutum ne shi mara uzuri da yafiya a rayuwarsa, akan kawai ta fasa turare zai kulleta a ɗakinsa ita ɗaya?. kawai sai maganarsa ta dawo mata sanda yace idan ta fita a ɗakin nan to biyansa turarensa tayi.

kulle idanuwanta tayi tana jin hawaye na biyo kuncinto da tsananin jin haushi da takaicin kanta. me ma ya kaita?, har sai yaushe ne zata daina shiga hurumin da bai shafeta ba bai shafi wani nata ba?, dan ana so a cutar da Turaki doesn't mean ana so acutar da Hammah Hamid ne. ina ruwanta da Turarensa ma da har zata fasa kawai saboda bata so?. bata taɓa jin taji haushin kanta a wani abu da ta aikata ba sai a yau.

ta san turaren me tsada ne kamar yanda ya faɗa, to yanzu da wanne kuɗin zata biyasa?, shekaranjiya Kaka ta kwashe ƴan kuɗaɗenta ta bayar an siya tumakin da suke kiwo. kawai sai ta ƙara durƙushewa a gaban mudubi tana kuma sakin kuka, ko na misƙala zarratan Turaki baya da tausayi kuma baya da imani, sam baiyi gadon mahaifinsa ba, kuma bai yi gadon mahaifiyarsa ba kamar yanda taji labarinta a bakin Maama ɗazu.

tana cikin wannan kukan ne taji an buɗe ƙofar, ko bata ta ɗago ba tasan shine, hakan yasa taƙi motsawa, saboda so take yi ta taushi zuciyarta gudun aikata abinda zata zo tana dana sani, dan tasa a ranta sai Turaki yasan ya kulleta a ɗaki.
yau zata masa abinda zai sa ya koyi haƙuri da yafiya, in ba haka ba kuma ta barsa da sharrin waɗanda suke neman rayuwarsa, wannan ma kaɗai ya isa ya shiga hankalinsa.
Chapter 59 · 0% Book details