← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 176

Sashe 21

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Samha ta ɗaga landline en dake gefensu ta kira wayar ɗakin ma'aikata. bugun da bai wuce 2 ba Fillo dake can ta ɗaga. "ke kizo mun kammala". abinda tace da Fillo kenan ta kashe wayar. wanda a ɓangarenta azamar tashin ta ke yi saboda tana lissafe ne da lokaci, su kan ɗauki 10-15minutes a dining, kuma buƙatarsu da zarar sun kammala da shi ai clearing wurin.

tana shigowa parlon Hajiya Madina na shirin hawa upstairs, ta kalleta tace mata.
"idan kin gama ki sameni a É—aki". Fillo ta amsa da,"tou". sannan ta shiga gyara wajen.
komai nata cikin sanyin jiki ta ke yinsa amma kuma nan da nan ta ke gama abu, tana gama wanke-wanke bata tsaya É—ora lunch ba tunda tasan basa nan kuma bai wuce suyo takeaway na dinner ba idan sun tashi dawowa.

zata wuce É—akin Hajiya Madina Khalil dake parlon a zaune shi É—aya ya tsayar da ita.
"sojan rana zo nan".
ta tsaya daga hawa saman ta juyo da murmushi fuskarta, abunda ke burge shi da ita fara'arta da tsabtarta, bata da wannan cunkus É—in irin na sauran Æ´an aikin da suka yi a baya.

har ta ƙaraso ta tsuguna a gefen kujerar da yake zaune bai bar kallonta ba, kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace,"Hamma Khalil gani". ta faɗi sunan nasa kamar yanda taji ƙannensa na faɗa masa.
yace,"ai nai zaton ko kina ciwon baki ne". ya faÉ—a da salon zolaya.

ta murmusa da cewan,"ciwon baki kuma?".
yace,"ehh mana, da na kiraki ai ba ki amsa ba tahowa kawai kika yi".
ta saki murmushi me faÉ—i da cewar,"Hamma Khalil to ai kaine kake faÉ—in sunan da ba nawa ba, shisa sai nayi zaton ko bada ni kake ba".

shima murmusawar yay kafin yace,"yanzu ke tsakani da Allah duk wanda ya ganki ranar nan da kika yi ƙeƙam a tsakiyar rana me zai yi zato?, kinga kam dan na kiraki da sojan rana ai ba laifi ba ne".
murmushi kawai tayi bata ce komai ba.

"anyway, wanne class kike before ki taho aikatau?".
furucin da yay yasa ta ɗagowa ta kalle shi kaɗan sannan ta mayar da kanta ƙasa.
"bana zuwa makaranta ai".
da mamaki ya kalleta,"gaba ɗaya ba ki taɓa zuwa makarantar boko ba?".
ta É—aga masa kai tabbacin hakan.

ya girgiza kansa,"to islamiya fa?".
ruwan hawaye ya cika idonta kafin tace,"nayi islamiya kamin Ummi ta rasu, kuma itama tana yi min a gida".
yace,"wace Ummi?".
sai da tasa hannu ta goge hawaye tukunna tace,"mahaifiyata".

lokaci ɗaya tausayinta ya kama shi. "Allah ya jiƙanta". ta amsa da,"amin na gode, Allah yaja da ransu Baffa". shima ya amsa da,"amin na gode. amma kuma idan baki je makarantar boko ba taya akai ranar nan kika karanta saƙon da Maama ta bar miki?".

taja yatsanta na tsakiya bata ce komai ba. ya katse shirun,"tambayarki nake". murya a hankali tace,"wanda zan aura ne ya fara koya min yanda zanyi karatu, kuma daga baya sai muka daina saboda ayyuka da suka yi masa yawa".

kalmar wanda zan aura ta ba shi mamaki. to amma sai dai aure wa ƙaramar yarinya kamar wannan a wajen ƴan ƙauye ba wani abu bane, wataƙila da ace ba anan suke zaune ba yanzu haka tana da ƴaƴa. ya sauke numfashi yace,"yayi ƙoƙari shi wanda za ki aura ɗin...yanzu yaushe ne bikin?".

tace,"ba'a tsayar ba tukunna amma dai da an kusa wani dalili yasa aka É—aga". ta faÉ—i hakan idonta na kawo ruwa sosai, kuka ta ke sonyi a lokacin amma saboda Khalil É—in ta hana kukan samun Æ´ancin fita daga bakinta, domin bata so ya gano wani ciwo da rayuwarta ke É—auke da shi.

ya ɗaga kafaɗarsa ya ajiye wayarsa sannan ya fuskantota gaba ɗaya. "to kin san menene?, mu a gidan nan idan mutum zai yi aiki dole sai yana karatu, kije ki tambayi duk wanda ya taɓa aiki anan, haka tsarin Baffa yake...and dalilin daya sa ma inaga Maama bata yi miki zancen ba kwana biyu aiki ya sha kanta ne, amma yanzu idan kinje ki tuna mata, akwai Malamin da yake zuwa yana yi muku karatu".

ta ɗago ido tana kallonsa, kamar bata fahimci me yake son cewa ba. ya ɗaga mata gira,"ehh idan kinje ki cewa Maama ke ba ki yi karatu ba". ta gyaɗa kai kawai sannan ta miƙe zata wuce. Turaki ya shigo parlon a lokacin yana waya. ta gabansa ta wuce tana ji yana cewa,"me zan yi da yarinyar da bata waye ba, ka bar wannan batun she is not my type...infact ni babu aure ma a lissafin rayuwata".

hannuwan Fillo suka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta buɗe, tayi sallama amma ba'a amsa ba. hakan yasa tasa kai zuwa ciki ƙafafuwanta na luntsumewa cikin tattausan carpet ɗin dake malale a duka ɗakin tun daga bakin ƙofa, kai kace cikin auduga kake sanya ƙafa saboda tsabagen taushi.

tayi tsaye daga nan bakin ƙofar bayan ta maida ƙofar ta rufe, jikinta take takurewa saboda yanda sanyin ac ke ratsata. ta kusan minti uku tsaye sannan Hajiya Madina ta fito daga wata ƙofa da idan ba sani kai ba ba zaka ce ƙofa bace. da sauri ta durƙusa a ƙasa tana kama gefen zanenta ta riƙe. dalilin wani abu da yayi duka acikin kanta sanadin furucin da taji Hajiya Madina tayi acikin wayar da ta ɗauka yanzu da aka kira.

"asiri fa kika ce Lubna, wa ya faÉ—a miki?". abinda Hajiya Madinan ta fara kenan cikin muryar razani, amma ita a wannan lokacin kalmar asirin ce ke ta maimaituwa acikin kwanyar kanta, lokaci guda kuma hankalinta ya gushe daga cikin É—akin ta lula wani wurin can daban da tunanin abinda ya danganci asirin.

"to shikenan Allah dai ya kyauta...ni ma kinga zamu je gidan Alhaji Babba ne akan lamarin Hammansu, sam yaƙi aure kuma ko zancen auren baya so ayi masa, mun rasa kuma dalilinsa dan ko jiya sun fi awa shi da Baffansa kan ya sanar masa da dalilinsa yace shi babu komai haka ɗaya, sannan babbar matsalar duk wannan nacin ibadar tasa yanzu ba yayi, sai kiga ko sallah ake yana zaune...to shine Boɗejo ke ganin abun kamar ba lafiya ba".
Hajiya Madina ta faɗawa ƙawarta Lubna da suke wayar.

daga ɓangaren Lubna ɗin tace,"subhanallah, gaskiya kam dai wannan labari ba lafiya ba a tashi a nemi magani, namiji har namiji kamar Turaki ace baya son aure, ai lamarin akwai duba...Allah dai ya kawo komai da sauƙi".

Hajiya Madina tace,"amin ya Allah...shikenan sai mun ƙara yin waya, dan Allah karki manta da saƙon nan ki bayar akai musu".

daga ɓangaren Lubna ta sake cewa wani abu sannan Hajiya Madina tace,"ina ta ƙoƙarin yin hakan. sai dai ina tsoro Lubna, ban san mutanen dake bibiyar rayuwarsa ba, haka ban san wanne irin shiri suke yi akansa ba, dalilin da yasa na dage akan cewar ya haƙura da kowanne irin aiki zamansa a gida shine kwanciyar hankalinmu, haka kuma shima a nasa ɓangaren wannan ne kaɗai tsaron da zai samu...wallahi ba ki ga munin last accident ɗin da yay ba, Lubna sai dana gama cire rai da shi tukunna ya farfaɗo...amma akan maganar wannan company ɗin da Baffa ke cewa zai buɗe musu wataƙila na yarda ya zama jagoran ciki amma in har bai ɗara daga state ɗin nan ba, amma muddin wani gari ko wata ƙasa ce can daban hakan ba zai yiwu ba".

haka suka ci gama da tattaunawa tsawon mintuna kafin suyi sallama. ta ajiye wayar tana mai cewa da Fillo,"buÉ—e wancan closet É—in ki É—auko min wasu takardu daga sama".
Fillo ta miƙe dan cika umarninta, tana ɗauko takardun tana mamakin irin jama'ar da Allah ya bawa Hajiya Madina, ko da yaushe acikin yin waya ta ke, inda take gani da itace gaskiya ba zata iya ba, domin idan kunnenta bai ciwo ba to bakinta zai yi. yanzu fa ta gama waya ko minti biyu ba'a ƙara ba amma har an kuma kiranta.

"zan bar su a gida, akwai yarinya idan kazo zata baka". abinda ta ke cewa dana wayar kenan, kuma lokacin da Fillon ta ƙaraso ta durƙusa ta bata takardun.
"alright sai ka zo".

daga haka wayar tasu ta yanke, ta dubi Fillo tace da ita,"gobe za ki fara É—aukar karatu a gidan nan, ba ke É—aya bace akwai wata sabuwar Æ´ar aiki da za'a kawo anjima za kuci gaba da aiki tare. bana son fitina Halima, bana son kuskure, ki kula da hakan. karatun boko da arabiya zai ke yi muku. ki tsaya ki maida hankali, domin akwai aikin da nake so kiyi min, aiki ne na masu ilimin boko, idan kin mayar da hankali, idan har kinyi nasarar samunsa Halima za ki sha mamakin yarda zan mayar da ke, duniyarki zata sauya, za ki zama abar kwantance, bayanki zai zama tarihi, idan kuma akasin hakan, tabbas ina mai tausaya miki da asara mafi girma da za kiyi a rayuwarki".

Fillo so ta ke ta ɗago ta kalleta amma ta kasa, jan yatsunta kawai ta ke. "ungo wannan". sai a sannan ta ɗago tasa hannu biyu ta karɓi takardun.
"ki adana su, zuwa ƙarfe biyar na yamma akwai wani zaizo ya karɓa, baƙi ne dogo yana da ƙasumba...ba shi kawai nace kiyi, kije masa da fuskar mutumcinki Halima...nasan kin gane lissafina".
Kan Fillo a ƙasa tace,"tom Hajiya".
"bani lafayata fara".

Fillo ta miƙe ta ɗauko ta kawo mata. ta cikin mudubi Hajiya Madina ke ta kallonta, zuciyarta na me jin so da tausayin yarinyar.
bata bar kallonta ta cikin madubin ba tace,"zo ki saka min wannam fil ɗin". Fillo ta matso zuwa bayanta ta karɓi fil ɗin a hannunta sannan ta saka mata kamar yanda taga Zaytuna nayi mata a duk sanda ta saka lafaya.

ita ta ɗaukar mata jakarta suka fito a ɗakin, suna saukowa ta ke faɗa mata,"akwai key ɗin ɗayan bedroom na Hammansu acikin drower na mirrow, idan mun fita kije ki gyara masa. dan Allah ki gyara me kyau, ki kaɗe duk wata ƙura".
Chapter 21 · 0% Book details