← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 176

Sashe 40

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta ƙara rufe fuskar da hijab ɗinta, wani daɗi na ratsata. Yay ƴar dariya yana jin tana ƙara burge shi saboda wannan kunyartata.
yace,"duk da an hanani ganin fuskar hakan ba zai hana ni faÉ—in kinyi kyau sosai, matsalar guda É—aya ce dai da bana so".
ya ƙarasa maganar amon muryarsa na sauyawa, tai saurin buɗe fuskarta, so take ta kallesa amma ta kasa, ta sauke idanuwanta a ƙasa da rashin jin daɗi tana jan yatsunta tace,"wacce irin matsala ce?, mecece matsalar da baka so?, a shirye nake da gyara ko menene saboda kai?".

ya murmusa kuncinsa sannan yace,"Kunya! itace matsalar kuma itace bana so, amma a iyaka tsakaninmu banda wani daban, sai dai na san ba zaki iya dainawa ba balle ki rage, tunda ba tun yau ba nake roƙon alfarmar a rageta ko ya ya ne saboda tana ƙwarata, amma kamar ma ba'a jin me nake cewa...ni kuma tsakani da Allah ina so ake a bani damar ganin cikin idanuwan gimbiya, ina sonsu, so me yawa ba kaɗan ba".

Fillo na murnushi ta ƙara ƙoƙarin sake rufe fuskar sai taga ya haɗe hannayensa alamar roƙo yace,"dan Allah Fillo nah, ki tausayawa zuciyata, ki tausayawa idanuwana".
haka dole ta haƙura da rufe fuskar, ba zata iya saka ƙwayar idonta a cikin nasa ba, amma ba zata hanasa ganin fuskarta ba, dan haka ta ɗago kai yanda zai kalleta sosai, amma bata iya barin idonta a buɗe ba ta kullesu.

sai da Amir ya ɗauki kusan minti ɗaya yana kallon fuskarta ba tare da ita tai magana balle shi da ya shiga shauƙi. da yana da dama, da yana da yanda zaiyi da yau Fillo bata ƙara kwana a gidan nan ba, da yau Fillo a gidansa zata kwana, kusa da shi, kusanci sosai irin kusancin da zai ɗorata a saman ƙirjinsa ya dinƙa faɗa mata kalaman da zasu mantar da ita duk wani kalar ƙalubale da ta fuskanta a rayuwarta.

"ina sonki, ina miki so me tsanani, ƙaunar da nake miki ba mai fasaltuwa bace, bana fatan na rasaki Halimatu, bana fatan Allah ya kawo abinda zai rabani da ke, ke ɗaya ce tal a ƙurya da wajen zuciyata. please ki so ni ko da kwatankwacin yanda nake sonki ne, domin idan babu ke tare da ni Allah babu makawa sai na zama gawa".

tai saurin É—ago ido ta kalli raunanun idanunsa. "ina sonka ai kaima kasan da wannan, kuma ba zamu rabe ba insha'Allahu, matarka ce ni har a aljannah insha'Allahu". haka ta faÉ—a, kuma hakan ke maimaituwa a cikin ransa, maimaituwar kuma ke haifar da jin daÉ—i tare da shi.

da taga kamar yau bai da niyyar suyi karatun muryarta a sanyaye tace,"yau ina da aiki a cikin gida".
take annurin fuskarsa ya ɗauke, ya haɗe rai ɓacin rai na ziyartarsa. ya miƙe kawai ba tare da yace mata komai ba ya nufi inda suke zama suyi karatun, baya son wannan aikin nata ya tsane shi. ko wannan karatun da ya tsira yi mata, yayi hakanne dan ya daƙile mata zuwa aikin shi yasa ya saka da safe zasu ke yi, amma ashe na banzar yayi, kamar mayu sun liƙe ita zata ke musu aikin, yanda baya so tai aikin haka baya so Kaka tayi, to amma baida yanda zaiyi, shi ba me ƙarfi ba ne, idan ita ya nemi hanyar hanata bai isa ya hana Kaka tayi ba, to amma me yasa ba zasu nemi wata yarinyar da ta dinga yi musu ba?, su bar masa Fillonsa ta huta kamar a baya.

Fillo ta ƙaraso jiki a sanyaye ta shimfiɗa masa dardumar, sannan ta shimfiɗa ɗankwalinta ita kuma ta zauna akai, har sanda ta zauna shi yana tsaye kamar ba zai zauna ba, ita dai bata ɗago ta iya kallonsa ba, saboda hawayen cikin idonta zasu sami nasarar zubowa, ko kaɗan bata son ganin ɓacin ransa, musamman ace itace sila.
sai da ya zauna sannan tace da shi,"kayi haƙuri, dole ce tasa ba dan muna so ba mu kanmu. aikin nan shine rufin asirinmu, kana gani Kaka daɗa tsufa takeyi jikinta na ƙara saki, ba zata iya ɗawainiyar da tayi a baya ba, ni kuma da ta riƙe ni bayan banda kowa dole na taimaka mata a yanzu dana kawo ƙarfi, tana buƙatar taimakona. kuma yanzu idan banyi aikin nan mun sami kuɗin ba da me kake so Kaka ta kaini gidanka Amir?".

ya tsayar da ƙwayar idonsa akanta yace,"ni ke nake so ba abinda za'a kai ki da shi ba". ta girgiza kai tace,"a'a Amir, duk da bamu da komai, kuma ni ɗin ba kowan kowa bace, amma ina so na wuce gori a ko ina ne. kuma baya nan ina so ko bayan ran Kaka na kalli wani abin da zan gani naji daɗi, na san nima an tafi an bar min gado".
yace,"shikenan, bismilillah". ya faÉ—a yana mata alamar ta fara karatun.

tasan maganarta bai masa daÉ—i ba amma dole ta faÉ—a, kuma gaskiyar kenan. ba'a san gawar fari ba, kuma ba fata take ba, amma idan Kaka ta mutu, shi kuma ta aure shi shima ya faÉ—i ya mutu rabo bai samu a tsakaninsu ba, wa take da shi kuma me zata kama?, gwara tai duk kalar wahalar aiki tayi su sami kuÉ—in da Kaka ke fatan su samu ta cika burinta na siya mata fili, da kuma jarin da zata samu sana'ar yi.

cikin zazzaƙar muryarta ta fara biyo masa haddar karatun da yake biya mata kullum, acikin ƙira'a me daɗin gaske, kuma tartilan tajwidan, kace wata balarabiya. haka tai ta biyawa har sai da ta kawo inda suka tsaya sannan tai shiru, ta buɗe ƙur'anin yay mata ƙari.
yau ko tajweed ɗin bai biya mata ba ya miƙe yana mata sallama, muryarta a raunane tace,"tun yanzu?, kuma ba zamu yi tajweed ɗin ba? kayi haƙuri dan girman Allah".

bai juyo ba daga tsayen da yake, hannayensa na aljihu idanuwansa a kulle. abinda ba tai zato ba abinda bata taɓa tsammata ba daga gare shi, magana ce ya faɗa guda ɗaya tal, amma magana ce me zafi, wadda take daidai da tsawon kalmomi fiye da dubu, zafinta ke dai-dai da sukar mashi a ƙahon zuci. bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba, ƙafafuwanta na rawa suna neman su gaza ɗaukarta, kallonsa take amma wani Amir ɗin na daban take gani ba Amir ɗinta da ta sani ba. tasan dai ɓacin rai kan iya saka mutum yay komai amma batai zaton ɓacin rai zai iya sa Amir ya huda ƙirjinta da kibiya ba.

zata jure komai ba, amma ba zata juri maganar ba, cin fuska baya ɗaya daga cikin abinda zata ɗauka, dole zata mayar masa, dole itama ta saka masa ɗacin da ya saka a tata zuciyar, ya kamata ace shima yasan wacece asalin Fillo, wannan Fillon da bata ɗaukar wulaƙanci daga ko waye, duk kuɗinka, mulkinka, matsayinka, muƙaminka, basu zasu hana ta rama abinda akai mata ba. ta tattaro sauran courage ɗin da take da shi, laɓɓanta suka tale da niyyar yin magana daidai lokacin shi kuma ya juyo ya fuskance ta.
taja dogon nunfashi ta sauke, ta haɗiye wani abu da bata san menene shi ba, ta dunƙule hannunta da zuciyarta ke ingizata akan aikata abinda dole zai saka tayi da na sani.

Amir kallonta kawai yake yana ganin yanda take haɗa zufa duk da iskar dake kaɗawa a wurin, ɓacin ran dake fuskarta na haɗewa da jin zafin abinda ya faɗa mata acikin zuciyarsa, yana jin tamkar wuta ce ke ruruwa a tare da shi, me zai ce yanzu?, ta ina zai fara?, me zai faɗa mata da zai goge tabon da dasa mata yanzu?.

_"akwai abinda bai sani ba, tabbas akwai abinda bai sani ba a tare dake, ki faɗa masa hakan Fillo"._ abinda zuciyarta ke faɗa mata kenan, sai dai at the moment da ta ɗago kai suka haɗa ido sai komai nata ya ruguje, dukkan plan ɗinta na cin zarafinsa ya rushe, ta sauke idonta ƙasa tana jin ba zata iya komai ba, ba zata iya yiwa wannan mutumin komai ba, wannan mutumin dake gabanta ba ɗaya yake da kowa ba a duniyarta.
ta duƙa ta ɗauƙi qur'anin da dardumar ta juya zata tafi, sai taji muryarsa a sanyaye ɗauke da sautin nadama da danasi yana cewa,"dan darajan Allah kiyi haƙuri ki yafe min, ba laifina ba ne, na kasa controlling zuciyata ne".

Fillo taji wani dunƙulen abu ya tsaya a maƙoshinta ya hana yawu wucewa, halaccin da Amir yay mata ba zata manta da shi ba, amma bata jin ko me Amir zai faɗa mata ayanzu zata iya ci gaba da tsayuwa a wurin nan, bata jin akwai wani mahaluƙi a wannan duniyar da ya isa ya hana ƙafafuwanta takawa ta bar wajen nan, ba zata saurare shi ba, ba zata taɓa sauraronsa ba, kuma ba zata ƙara zuwa wurin nan ta tsaya ba wai saboda Amir, ko da ace kuwa gawar Amir ce.

tana ɗaga ƙafarta taji yace,"ki tsaya ki fahimceni dan Allah". a ranta ta maimaita ta tsaya?, yana nufin ta tsaya su fuskanci juna ya bata haƙuri ta haƙura?, ai ba zata taɓa tsayawa ba balle ƙwayar idonsa ta karya alwashin data ɗauka. cikin ƙunar rai ta bar wajen, tana ji yana ƙwala kiran sunanta yana roƙonta, kuma wannan kiran sunan nata da roƙon da yake mata na dawo mata da rayuwar ta a baya, yana tuna mata wani lokacin a can baya, lokacin da ta haura katangar gidansu ta dire, cikin duhun dare ba da rana ba.
har ta isa ga ƙofar shiga ɓangaren nasu Amir bai daina kiran sunanta ba, kuma duk da irin tazarar dake tsakaninsu bata bar jin kiran sunan nata ba a bakinsa, kiran sunan da take jinsa ba daga muryar Amir ba, daga wata murya ta daban, muryar Yayanta abin ƙaunarta Hamid, Hammah Hamid. ayanzu Kaka kawai take lissafawa wadda ta rage mata a cikin rayuwarta, amma duk ranar da Kaka ta faɗi ta mutu to tasan tana da Hamid, shi kaɗai take da shi ko da ace kuwa har lokacin Hayyo na raye.
Chapter 40 · 0% Book details