Sashe 32
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kamar bata gamsu da hakan ba a yacca ya gani a fuskarta, hakan yasa yayo tattaki zuwa gabanta, ya zagayeta sannan ya tsaya a bayanta.
"karki ji komai, babu wata matsala...wannan karan babu kuskure ina da yaƙinin hakan...wancan matsalar da aka samu yaran sun ce unexpected suka ji syring ɗin motar police, banda haka tuni sun gama da shi. kuma kinga muma bamu tsammaci hakan ba, ba ki karanta min da cewar hakan zai iya faruwa ba, da tunda wuri za'a aiwatar da komai...Hajiya Madina itace matsalarmu a komai shi yasa ya zama tilas dole mu fara ɗauketa daga kusa da shi".
ta sauke numfashi tace,"kasan mene?, a rayuwa raunin Turaki mutum biyu ne, Hajiya Madina da kuma Zaytuna, saboda haka tunanina ya sauya. zamu fara gamawa da Zaytuna kafin zuwan komai...Zaytuna tana da saurin yarda, tana da saurin sakin jiki musamman ga talaka, dan haka na san ta inda zan ɓullowa lamarin...kaima bance ka tsaya da naka aikin ba".
tana faɗar haka ta ɗauki wayarta da ke kan center table, ta nufi hanyar bedroom tana faɗar,"gobe zan bar ƙasar nan".
"nima haka". shima saurayin ya faÉ—a yana me É—aukar car key ya fice daga apartment É—in.
****
ƙafafun Turaki suka fito daga parlon, sanye yake da wata dakakkiyar shadda aqua colour da tayi bala'in yi masa kyau, ɗinkin boda ne da aikin sama. kansa babu hula sai dai sumar kan tasha gyara sai ƙyalli take yi. duk ya rame, ya fige, fuskarsa ta ɗanyi duhu, idonsa yayi jaa kuma ya faɗa ciki kamar mara lafiya, saboda kawai saka abu a ransa da yayi, yarinyar nan daya kaɗe wadda tsawon kwana uku sai jiya ta farfaɗo, tun ranar da accident ɗin ya faru baya iya cin abinci, rashin bacci da kuma rashin kwanciyar hankali duk sun dabaibaye shi.
ya kalli agogon wrist É—insa yaga goma harda minti biyu.
"Khalil". ya kira sunan Khalil wanda ke daga cikin parlo, ya amsa masa yana faɗin,"gani nan fa". Turaki ya ƙara magana da muryar ƙorafi,"kai indai za'a fita tare da kai sai ka ɓata lokaci".
a time ɗin ne kuma Khalil ya fito, suka jera tare zuwa part ɗin Baffa, bakinsu ɗauke da sallama suka shiga parlon, Baffa yana zaune da mijin ƙanwarsa Falmata SS Ƙasim Kurfi.
Khalil da Turaki suka zauna ƙasa suka gaishe su. Alhaji Ƙasim ya shiga tambayar Khalil wurin aikinsa. after few minutes Baffa ya dubi Turaki yace,"ya jikin yarinyar da ka bige?".
kansa na ƙasa yace,"ban sa ni Baffa, amma dai jiya da daddare likitan yace ta farka after mun baro hospital ɗin".
Baffa ya jinjina kai, kamar ba zai ce komai sai kuma yace,"amma dai you supposed to go and check on her, kai ne sanadin halin da take ciki, so alhakin kula da lafiyarta ya rataya a wuyanka na faÉ—a maka hakan tun ranar dana dawo, bai kamata a tambayeka jikinta ba kai tsaye kace baka sa ni ba...idan ni ne kai ko asibitin ba zan ke iya bari ba".
Turaki yace,"dama can zan tafi yanzun". Baffa yace,"tou yayi, kuma idan kaje ka zauna da doctor É—in nata kaji game da lafiyarta".
ya amsa da,"to Baffa". suka tashi zasu tafi Baffa ya tsayar da su, yace da Khalil ya ƙarasa ya buɗe drower dake can wajen tv ya ɗauko masa envlope. few seconds ya ɗauko ya kawo, Baffa ya buɗe ya ciro sabbin dollers ya bawa Khalil, ya karɓa yana jiran cewar Baffan.
already Turaki ya kai ƙofa, kiran sunansa da Baffa yayi ya dakata ya juyo, Baffan yace da shi,"kuyi changing nata before ku ƙarasa asibitin sai ka bawa Kakar Yarinya".
Turaki yace,"to Baffa Allah ya ƙara wadata".
da haka suka fice. bayan sun shiga ɓangaren Boɗejo sun gaisheta sannan suka wuce wajen Maama, a bedroom nata suka sameta, sun ɗan jima wurinta kafin su fito, itama ta bada nata saƙon dubiyar akaiwa Kaka.
motar Khalil suka shiga, Turaki ne ke driving, yayin da Khalil ke kujerar gefensa yana karanta jarida, news update ɗin da aka saki akan ASUU strike, tsaki yake taja saboda takaici, yanata ƙorafi akan strike ɗin, gami da tausayawa ɗan talaka da baida yanda zai yi.
ko jiya yana zaune Maama ta É—auki nauyin karatun wasu yara su biyar zuwa turkey, maza uku mata biyu. tunda yake ta complain É—insa dai Turaki bai ce komai ba, hasalima tun shigowarsu motar bai yi magana ba, seems like hankalinsa ma baya cikin motar.
Khalil ya ɗaga wayarsa da call ya shigo, yayi taking 3minutes yana wayar before ya gama. kuma sanda ya gama ɗin Turaki ya juyo ya kalle shi a lokacin da yake ƙoƙarin yin U-turn.
"ina sketch É—in ne?, jiya kace zaka nuna min muka manta gaba É—aya".
Khalil ya juya baya ya É—auko takardar, yana nunawa Turaki yanda akayi zanen sabon company nasu da Baffa zai buÉ—e. yana kallon sketch din yana kuma driving a hakan. yanda akayi sketching É—in bai yi masa ba sam, hakan yasa shi cewa.
"wanne Arch É—in ne yay wannan zanen?".
Khalil yace,"Yahya Ƙosa".
yace masa,"why zaka bawa daƙiƙi irin Ƙosa zanen abin arziƙi?, me Ƙosa ya iya?, kai baka ga irin haukan daya zuba ba ne a gidan Hakimi, har kwanan gobe Hakimi complain yake da wannan gidan".
Khalil yace,"ni fa Hammah is not my fault, Baffa da kansa ya basa, nawa karɓa ne kawai. Baffa ma so yayi ana kawowa a bawa engineer na faɗawa Maama ai baka gani ba tukunna".
Turaki yace,"ka yaga shi kawai dan ba za'ai amfani da shi ba, ji wani shirmen banza fa wai office na accounter a compound na Company...kuma a hakan degree holder yake ko?".
Khalil yay dariya yace,"kafa san komai Hammah".
tsaki Turaki yayi yace,"ka kira Lawan Shehu kai masa bayanin komai, shine zai yi mana aiki me kyau".
sai da suka tsaya a banka sukai changing doller tukunna suka É—auki hanyar Miyetti Hospital.Â
Khalil ne ya fara wucewa ward ɗin yayin daya bar Turaki a mota yana waya da Bello Ƙaraye, zai biyosa daga baya.
kiran sallar da akeyi a masallaci ya fito da Turaki daga motar, yana waya da Zaytuna a lokacin bayan sun gama da Bello. cikin sauri yake tafiyar yana so ya fara zuwa ward É—in da Fillo take sannan ya wuce masallaci dan baya son rasa jam'i.
yana tafiya yana wayar bai gani ba yayi karo da mutum, wayarsa ta faÉ—i ita kuma jakar hannunta ta faÉ—i kayan ciki suka zube kasancewar jakar ba me zip bace. Turaki ya kalla wayarsa daya tabbata ta fashe, tukunna yabi tarkacen jakar da suka zube da kallo, kayan makeup ne duka, sannan ya É—ago ido yana kallon wadda suka yi karon.
haƙuri yake niyyar bata, amma ganin yacca take faman cika tana batsewa sai ya ɗauke kansa ya fasa, laifinsa ne amma haƙuri dai ba zai bada shi ba.
ganin baida niyyar bata haƙuri kuma baida niyyar tsugunawa ya kwashe mata kaya yasa a gadarance tace da shi,"are you blind da kake tafiya baka kallon gabanka?, kuma hala baka gaji arziƙi ba shi yasa baka san yanda ake bada haƙuri ba. to ka duƙa ka kwashe min kayana ka miƙon jakata".
da wani irin ɗacin rai Turaki yake kallonta, imagine wadda yayi ƙanwa ta uku da ita take faɗa masa haka. yarinyar kyakkyawa ce, me hasken fata kamar madara, mai kyakkyawan jiki irin wanda yaji komai da ake buƙata a jikin ƴa mace. kallon farko ba sai ka ƙara na biyu ba zaka san macece da ta samu hutu, gata, da tarin ilimin boko. Kuma ba sai an faɗa maka ba, a maganarta da yanayinta zaka gane ƴar sarauta ce da mulki ya gama ratsa gaɓoɓin jikinta.
Turaki ya ɗauƙe idonsa akanta yana me fesar da iska daga bakinsa, matsawar yaci gaba da tsayuwa anan komai zai iya faruwa, saboda haka ya taka da niyyar barin wajen ba tare daya tsaya ya ɗauki wayar ba, baida buƙatarta domin ba zai rasa komai ba tunda yana ajiya a goggle, welcome back na line nasa kawai zai yi. sai dai yana niyyar barin wajen kawai yaga fadawa sun kewaye shi ta ko'ina, one by one ya kalle su, sannan ya ƙara kallon yarinyar, bai san lokacin da wani murmushi ya suɓuce masa ba har sautinsa ya fito. yasa yatsansa ya sosa girarsa, kafin ya shafo wuyansa still da smiling akan leɓensa.
a lokacin ne ɗaya daga cikin fadawan ke ce masa,"ka bawa gimbiya haƙuri sannan ka nemi yafiyarta, idan ba haka ba fushin Mai Martaba zai tabbata akanka, kuma zaka fuskanci hukunci daga masarautar kano".
shirun bafaden ya haɗe da tayar da iƙama a masallaci, muryar Turaki ta fito da wani amo mai taushi zuwa ga Gimbiya Aisha yace,"zanje nayi sallah, ki jira na dawo zan duƙawa izzarki kamar yanda kike so, zanta baki haƙuri har sai kin ƙoshi". yana faɗin hakan ya wuce ya ɗauki hanyar masallacin cikin sauri, tafiyar da ba zaka ce sauri yake ba saboda nutsuwar da ta shimfiɗu acikinta.
Gimbiya Aisha tabi bayansa da kallo tana jin wani malolon abu na tsaya mata a rai, _ta jira shi ya dawo._, haka ya faɗa mata fa, waye shi?, me yake ji da shi?, aina ya samo wannan isar?, ina ya sami ƙwarin gwiwar saka idonsa cikin nata bayan yaji wacece ita?. ta rufe ido tare da haɗiye wani busashshen yawu na takaici, for few minutes ta kalla fadawan dake yin kamar zasu yi mata sujjada ta basu umarnin tafiya.
Fillo na kwance kan gado drip na shiga jikinta, drip na kusan huÉ—u kenan da aka saka mata a yau, daga safiya zuwa yamma.
saman room É—in kawai take kallo, dan su Kaka duk sun tayar da sallah, Maijidda kuma ta tafi raka Amir. hankalinta yana cikin É—akin amma tunaninta yana waccan ranar da komai ya faru, komai É—in da har yay sanadin kwanciyarta a asibiti.
tunda akayi admiting nata sai jiya ta farka a kwana na uku, mutumin da idanuwanta suka fara gani a lokacin da ta farka likitan da yake dubata. kallo É—aya tayi masa ta mayar da murfin idonta ta rufe.