Sashe 115
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rauda ta fito daga cikin bedroom ɗin hannunta riƙe da biro da jotter, yayinda Fillo ke biye da ita a ba ya nata hannun riƙe da laptop. suka ƙaraso parlo Raudha na cewa,"yanzu to ya kika ga lissafin?, tunda dinner ce kawai ai hakan yayi ko? sai dai ban san ba ko after an kai ki akwai abinda za'ayi".
Fillo bata ce da ita komai ba ta zagaya ta side É—in da Dada take ta zauna kusa da ita, taci gaba da operating laptop É—in tana duba wata university acan Europe, dan tun bayan sati É—aya da rasuwan Abbanta ta zana private waec tare da su Raudha da Amatullahi sauran jikokin gidan, aka kuma ce kowanne ya nemo university É—in da yake so ya tafi, so ita taso ta zauna anan nigeria but due to haukar Asuu da ta sani yasa ta fasa cikewa ta-ke bincike akan Uni É—in da Raudha tace su tafi can kawai, yanzu lissafin karatunta kawai take yi ba lissafin wani aure ba kamar yanda taga an mayar da hankali akai tun bayan adu'ar arba'in.
Dada da ke shan tea ta É—ago kai ta kalla Fillo, ta girgiza kai tana yamutsa fuska kamar wacca taga kashi tace,"tirrrr, tirrr, tirrr da wannan mugun hali naki irin na Hayyo".
Fillo kamar zata yi kuka ta shiga dukan ƙafa a ƙasa tace,"kai dan Allah Dada, Abba nah fa ya mutu ki daina min irin haka, duk in kin ambaci sunansa fa sai ya tashi a ƙabarinsa".
Dada ta watsa mata wani kallo na ki shiga hankalinki da ni sannan tace,"an faɗa ko ba halin nasa ba ne, wani yace kar ya zama mutumin ƙwarai?, to in faɗa miki har duniya ta naɗe Hayyo dai bai da halin kirkin da za'a shaide shi da shi gwara ma ki daina nunawa duniya shi ubanki ne, ko kuma kike bari ana ambatarsa akai-akai ko ake masa adu'ar samun rahamar ubangiji.
banda iskanci ke kenan ba ki da aiki sai faman ɓata fuska ki yita turowa mutane laɓɓa gaba kamar ganda, to wallahi ki kiyayeni tun ban ɓata miki ba, ana tausaya miki saboda rashin mahaifi amma kina yiwa mutane iya shegen da kika ga dama, to ni ubanki zanci ba kowanne iskanci nake ɗauka ba".
ta gama faÉ—an tana harar Fillo kamar idanuwanta zasu zazzago, sannan ta juya kan Raudha tace,"ina jinki kin gama lissafin abin da na saka ki?, kuma kin duba shagon da yafi kowanne anan Jeddah É—in?, ba sanin kan shagunansu nayi ba inda dai Riyadh ne can nafi zama".
gaban Raudha ya faɗi, nan da nan ta shiga zare idanu kafin tace,"kiyi haƙuri Dada wallah na mance, amma zanyi yanzu".
da muryar faÉ—a Dada tace,"in saka ki aikin tun yammacin jiya kice min ba kiyi ba?, to uban me kike rubutawa yanzu?".
"Dada ai kin san can dangin mijin Fillo sun ce za'ai events kafin ta tare, shine dama nake lissafin abubuwan da zamu yi, ƙanwar mijin tana ta yo waya ta tambaya ko mun gama shirya abubuwan da muke so kuma duk banyi ba, ita kuma inata tambayarta taƙi ce min komai kiyi mata magana dan Allah".
ta faÉ—a duk a É—arÉ—arce saboda irin kallon da Dada ke bin ta da shi da makafin idanuwanta.
Dada ta gyaÉ—a kai ta juyo ta fuskanci Fillo tace,"ke É—auko min sanda ta".
sanin hali yasa Fillo miƙewa babu shiri ta wuce ɗakin Dada, in few seconds sai gata ta dawo tana miƙawa Dada sandar daga baya-baya. Dada ta karɓa ta saita kafaɗar Raudha ta muƙa mata, tuni zafin dukan ya ratsa Raudha idonta ya ciko da ruwa.
Dada ta fara mata masifa,"uwaki da ubaki ke da lissafin bikin, wato har wani shirin bikinta kuke yi saboda ba kwa ƙaunarta ko?, saboda ubanta ya mutu shikenan sai ace bata da me tsaya mata?, to tana da ni Kakarta, ni ce nan gatanta, dan haka banga wanda zai ɗaukar min jika ya kaita inda ba'a ƙaunarta ba. ko za kice baki da labarin Kakar yaron bata sonta?, har tana faɗin wai ya sakar min jika, to dama ko bata sa shi ya saketa ba ai mu zamu buƙaci ya saketa tunda dama jikar tamu ba sonsa take yi ba, ni inama na taɓa jin anyi gantalallen aure irin wannan Allah dai ya gafartawa Hayyo, to in har ba so ake rai ya dinƙa ɓaci ba kar in ƙara ji an tada maganar auren nan".
taja dogon tsakin da duk su Fillo sai da suka toshe kunne, ta doka sandarta akan table ɗin dake gabanta, fuskarta na bayyana tsurar ɓacin rai ta hau ruwan bala'i kamar zata haɗiye gidan.
"wace ita da zata ce jikanta yafi ƙarfin jikata ba zai zauna da ita matsayin matarsa ba?, to me take ji da shi, kuɗi ko mulki ko kuwa sarauta?, idan tana ɗagowar cewa suna da Gombe a hannunsu to muma haka muke da Taraba a tafin hannunmu tun daga sama har ƙasa. ita wai ƴar wofi har wani kashedi take turo min kar in sake jikata ta tare a gidan jikanta saboda yana aurar ƴar sarki, to idan ban sa an ƙwace sarautar tasu ba Allah ya tsine, babu ƙulla ƙullar da ba zan iya yi ba akan a tsigesu a kujerar sarautar nasu sai inga ta tsiya, yo banda ma dai ƙaddara ina jikata ina jikanta?, ai wallah sam babu haɗi, jikata tafi ƙarfin wannan mummunan jikan nata, wani dogon banza ma da shi kamar basamude, ai Fillo matar larabawa ce ba matar mutumin da zuwansa saudia ma bai fi ƙirgen yatsu ba, yaron ma da bai ma san darajar mace ba, tun sadakar uku bai ƙara waiwayanta ba shi ga shi ɗan iska, iya haka ma ai ya shaida maka wannan yaro baida ilimin addini sam, mu kam kaf zuri'ar Barkinɗo babu wanda yake jahili babu kuma wanda ke auran jahili, babu ta inda aka barmu daga addinin har bokon, saboda haka can ta kwaɗa jikan nata ta cinye itace a yunwa ce, mtswww daga jin ma yanda take hayagaga akan sarautar tasu kasan ci akai aka rage musu".
tai shiru tana faman huci sai girgiza ƙafa ɗaya akan ɗaya take yi, ta kuma jan tsaki ta kurɓi tea sai kuma ta zubar da shi acikin wata ƙatunwan silver me kama da sink.
ta kama haɓa tana jijjiga kai na irin takaicin nan ya isheta, ta ɗora manyan idanuwanta akan Fillo tana faɗin,"to ni dai ban yafewa ubanki ba da yasa aka raina mu haka, banda yaja mana raini har ina wannan figaggiyar tsohuwar ta samu zarrar yo min aiken in raba jikata da jikanta dan yafi ƙarfinta, jikarta ƴar sarki ce tafi ƙarfin ta haɗa kishi da jikata ƴar aiki a gidan Alƙali yake ko uban me oho?, har ƙara faɗa take yi mu kuka da kanmu in har muka bari akayi tariyar auren nan".
tai shiru tana cizon yatsa kafin ta shiga nuna kanta,"har ni ake yowa wannan baƙin aiken rashin mutumcin ban ɗau matakin komai ba?, ni ƴar sarkin taraba, uwar gwamnan taraba, uwar hakimin wurkum, Kakar soja, uwar macen da tafi kowacce mace kuɗi a nahiyar africa, yo ni kam yaushe nayi wannan saken?, dama har haka tsufan ya lalatar da ni?, ko da yake duk Hayyo ne yaja min ba kowa ba kuma yaje shi da Allah".
cikin ɓacin rai ta ƙara buga sandarta akan table har saida glass ɗin ya tsage.
"to billahillazi idan ban sa jikan nata yayi fatali da gimbiyar waje ba ya zauna da Fillo kaɗai ba shegiya nake, Hassana sunana na fita fitina da rigima wallahi, taje ta binciki tarihi taji ba'a taɓan ƴaƴa da jikoki a zauna lafiya".
tahi ƙwafa tare da miƙewa,"na rantse Allah ne ya rufawa Hayyo asiri bamu ƙara gamuwa ba da wallahi tallahi babu abin da zai hanani kai ƙararsa gaban alƙali, haka kawai yaja anai mana kallon ƙanan mutane har ana ci mana mutuncin da kare ba zai shinshina ba, akan jikarmu zata tare a gidan aurenta a kira waya ana mana gargaɗi, kashhh, amma babu komai idona idonta sai ta san tayi min aiken baƙaƙen maganganu, sai ta san tasa shegiyar matar tasa ta kira jikata ta zazzageta, zan nuna mata na fita ɗanyen kai, kowa ai shegen kansa ne, jikan nata da ta-ke ta haƙilo akansa zan nuna mata mune rayuwarsa, ba dai ance yana matuƙar ƙaunar Fillon ba, to aradu sai ya sakar min jika sai dai ya mutu, in ya mutu ita ke da asara bamu ba".
zata bar wajen ta kalla Fillo taga tana kuka, ai ko ta ɗaga sandarta ta dinƙa bugun Fillo da ita tana faɗin,"saboda nace sai ya sake ki shine kike kuka, ke ko ace ma Kakar tasa bata kira taci mutuncinmu ba kya yarda ki koma wurinsa ne yanda yay fatali dake ɗin nan ya manta da aurenki da ke kansa, to kuwa sai dai ki bi ubanki amma wannan aure sai ya mutu a yau-yau ɗin nan, dan ba zan yarda kije inda za ake miki kallon raini da ƙasƙanci ba duk da cewar ubanki yaja miki, kiyi kukan jini ba na ruwa ba, indai jikan wannan figaggiyar tsohuwar ne na rabaku bake ba shi, ya sakar min ke ki samu mijin aure anan kafin mu koma, babu abinda za kiyi da ɗansu, in ma saboda taimakon da suka yi miki ne gantalallar uwarki ta kasa cewa komai to ai kema kin masa taimakon da yafi nasu, ni na gode Allah ma da bai mayar da ke saura ba".
tayi hanyar ɗakinta sai jaraba take yi, ta buɗe ƙofa zata shiga ta waigo ta kalla Raudha tace,"ɗau waya ki kira min Jagarɗo".
sai kuma ta fasa shiga ɗakin ta dawo ta zauna, ranta ɓace take ta kallon Fillo da take kuka, banda tana tausayin karta ɓaɓɓallata da sai ta ƙara mummuƙa mata sandar ko ta shiga hankalinta.
Raudha ta miƙo mata wayar tana cewa,"ga shi Dada".
ta karɓa ta kara a kunne tare da saka glass ɗinta kamar ganinsa zata yi, bayan sun gaisa tace da shi,"kana jina?".
daga ɓangaren Jagarɗo yace,"ina ji Dada".