Sashe 172
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a lokacin da aka isa maƙabartar, Hamid da su Yusuf da Baffa su ne suka fito da gawar daga cikin makara, Bello ya kama hannun Turaki ya kama kan gawar sannan aka sata a cikin ramin ƙabarinta, yana kallo ana fuskantar da fuskarta zuwa ɓarin gabas, yana kallo aka ɗauko fasassun tukwane aka jejjera a saman gawar, kafin daga bisani yaga ana zuba ƙasa ana toshe ko'ina, yana jin muryoyin da ba zai iya tantacewa ba na faɗin a toshe kowacce ƙofa, yana kallo bayan an gama rufe gawar ruf da ƙasa aka yayyafa ruwa a samanta, sannan aka ɗauko allon shaida aka dasa a wajen kan, allon da yake iya karantawa, komai yana faruwa kamar dai sati biyu da suka wuce.
sunan da ke jikin Allon ɓaro ɓaro, sunan matarsa, sunan abar ƙaunarsa, wannan Fulanin tasa, wannan Fulanin da yake jin ba zai iya rayuwa ba a duk san da babu ita a tare da shi, yau shi ne a gaban ƙabarinta, da shi aka kawota, yana kallo aka sakata cikin rami bai iya hanawa ba, bai iya buɗar baki yace a'a ba, bai iya motsawa ba balle ya riƙe gawar.
*Marigayiya Halima Muhammad Barkinɗo(Fulani), Allah ya jiƙanki da rahamarsa, 03/10/2022.*
kamar hakan allon ke ɗauke da rubutun cikin manyan baƙi, ji yake kamar ya fincike allon ya jefar.
a hankali ya dawo da tunaninsa ɓangaren da yaji ana doguwar adu'a, sai ya fara kallon kowa ɗaya bayan ɗaya, kowa a tsugune yake ya ɗaga hannunsa, sannan Dr Yusuf da Hakim da Khaleel idanuwan suna hawaye, sai Baffa da Daddy(Baban su Dr Yusuf) fuskarsu fayau, sai ya mayar da kallonsa kan ƙabarin, shi ma ya ɗaga nasa hannun, ya shigo jero tarin adu'a wa ruhin matarsa, yi yake yi yana maimaitawa, har zuwa lokacin da yaji takun tafiya alamu na ƙafafu sun fara barin wajen.
yana ji mutanen da ke kusa da shi suna tashi, kuma kafin kowa ya tafi sai an zo an dafa kafaɗarsa ance masa,"Allah ya jiƙanta, Allah ya bada haƙuri".
da haka da haka sai da ya tsinci babu kowa a kusa da shi, sai shi kaɗai da yake zaune yana kallon ƙabarin ya kasa sauke hannunsa, har sai da Bello ya zo ya dafa shi yace,"kayi haƙuri ka tashi mu tafi".
sai yaji Khaleel ma na ce masa,"Hammah kayi haƙuri".
kawai sai ya saki kuka me ƙarfin sauti, ya kai hannunsa ya ɗora akan ƙabarin, a hankali yace,"insha'Allahu zan yi duk abin da kika ce, zan kula da yaranmu, zan ba su tarbiyya, zan saka su a makarantar da kika faɗa, ba zan bari su yi kuka ba, ba zan sa suyi kuka ba, ba zan bari su shiga cikin ƙunci ba, ba zan bar su suyi maraici ba, zan riƙe amanar da kika bar min, nayi miki alƙawari, zan kuma cika miki shi tabbas. don Allah ki yafe min da duk laifin da nayi miki, don Allah Fulani Nah, ki ce ina gaida Maama".
Bello da Khalil suka kama shi ya miƙe. suka riƙe shi suka fara tafiya domin barin cikin maƙabartar, sai da suka zo bakin ƙofar fita ya juyo yana daɗa hango kabarin, yana faɗin,"zan dinga zuwa kullum ina gaishe ki, zan dinga zuwa kullum ina yi miki adu'a, idan Aayan ya girma zan dinƙa kawo miki shi kina saka masa albarka, na gode Fulani Nah, sai anjima kinji ƴar aljannah".
komawar su gida suka tarar da ɗumin dandazon jama'a acikin rumfunan tanfol ɗin da aka yi kusan guda biyar, kai tsaye cikin gidan ya wuce bai tsaya a waje ba, yana shiga ya fara karɓar gaisuwar ta'aziyya daga mutane, ba wani ganin su yake yi ba, don ba ya gani da kyau.
ya ratsa ta cikin falon Mum ya haye sama, daga ƙofar ɗakin nata ya tsaya yana kallon Nihal da Ilham da ke goye da marayun jariransa, sai ya shiga ciki ya kunto yaran daga bayansu da kansa, ya fito ya bar ɗakin, ya kuma ratsa mutanen dake parlon ƙasa ya fice daga sashin gaba ɗaya.
kai tsaye ɓangarensa ya nufa, ya buɗe ɗakinsa ya shiga, ya zauna akan gado tare da jinginar da kansa jikin gadon, ya kwantar da macen a ƙirjinsa, namijin kuma ya ɗora shi a kan ƙafafunsa.
"your mum is no longer with us, she is gone and she is never coming back, death have separated us, she wants us to pray often for her, tun kafin ta haife ku tace Allah yaywa rayuwarku albarka, kuma na san ta biku, Allah ya raya min ku. Allah ya bamu haƙurin rashin da muka yi, ina yi mana ta'aziyya".
ya faɗa ya ƙara maimaitawa kamar yaran suna fahimtar me yake cewa, kafin a hankali ya rufe idonsa. in da a wannan lokacin Ilham ta shigo hannunta riƙe da tea flask, jikinta duk a sanyaye sai idanuwanta da suka yi jawur.
ta ƙarasa ta zauna a bedside drower tana kallonsa, tana kallon yanda hawaye ke fitowa daga idonsa yana bin kumatunsa, yayin da bakinsa ke motsi yana furta abun da bata san menene ba.
ta jima kafin ta iya saka hannu ta taɓo shi tayi masa magana, ya buɗe idonsa ya kalleta bai ce komai ba, Baby ɗin dake saman ƙirjinsa ta motsa, yay saurin gyara zama yana ɗagota daga ƙirjinta ya kalleta.
"sorry little...". sai ya rasa da sunan da zai kirata, da Aina'u(Hajiya Madina) ko kuma Halima(mahaifiyarta)?
cikin wata murya me mugun rauni ya ce,"yanzu baza ki iya samun ruwan nono ba?".
ya jefa tambayar ga Ilham, kafin ta ba shi amsa sai ya ƙara cewa,"ki taimaka musu don Allah, tun jiya babu abin da suka ci, Mum tace min sun ƙi shan madarar, na san su na jin yunwa, don basu da bakin magana ne kawai amma da sun faɗa".
kuka ya taho mata tace,"idan akwai yacca za'ai nonon ya zuba sai ayi, duk nayi nayi su kama nonon ko zai zuba sun ƙi. amma ɗazu da ku ka tafi kaita Fauziyya ta ba su sun sha".
"wacece Fauziyya?".
"ƙanwar Bello".
sai ya ɗago da sauri ya kalleta yace,"don Allah kirawota tazo ta ƙara ba su, kinga Maama ta tashi, bana so tayi kuka".
cikin sauri Ilham ta tashi ta fita, tana fita ya ɗauke Aayan daga kan ƙafarsa ya kwantar akan gadon, ya sauko yana jijjiga Maama a saman kafaɗarsa.
idanunsa na ƙara cika da ruwan hawaye, ya tuna jiya kamar yanzu ya na tare da mahaifiyar su, yana hasko san da Fillo ta ɗauko kayan da ke jikin yaran a yanzu, yana tuna sunan lukutar gombe, yana tuna irin dariya me faɗin da take yi a duk sanda ya faɗa mata hakan, yana tuna ranar da tayi fushi da shi ta kalle shi ta murguɗa masa baki, har tana cewa ko ta haihu yaranta da sunanta za su bearing ba nasa ba, sai dai ace Muhammad Halima da Aina'u Halima, duk ba zasu saka Turaki ba, tana faɗin ai ita ta haifa, shi kuma yana faɗin ai dai shi ya bayar.
yanzu bata raye, komai nata ya zama tarihi, ta tafi ta barshi da memories masu matse zuciya, yaji hawaye masu zafi sun sauko masa, tashin hankalinsa ɗaya ne, damuwarsa ɗaya ce, tunaninsa ɗaya ne, nonon wa yaran zasu dinƙa sha?.
*BAYAN SHEKARA GOMA SHA SHIDA.*
[9/7, 03:37] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*GAMJI WRITER'S ASSOCIATION*
  _Home of exceptional writers._
*61*
Da gudu ta fito daga cikin ɗakin, isowarta falo suka yi karo da Inna Wuro ta faɗi a ƙasa, ita ma medical glass ɗin idonta ya faɗi, nan da nan ta shiga kokawar ɗauko shi daga ƙasan.
idanun sai ƙiftawa suke yi kamar an tsokane su, sai da ta saka glass ɗin sannan suka daina ƙiftawar, kuma kallo ɗaya zaka yiwa ƙwayar idon nata ta cikin glasses ɗin ka san ba lafiyayyu ba ne.
yanda jikinta ke rawa zaka ce ko bata da lafiya ne, nan kuwa zallar rashin gaskiya ne a tare da ita.
ta kalli Inna Wuro ta gefen ido, dariya ta taho mata tayi saurin sa hannu ta toshe bakinta.
"huhuhu, la'ila ha'ilallahu, waiwaiwai. to ni dai sai dai in ce Allah ya isa kawai".
ta buÉ—e baki zata yi magana Inna Wuro tayi saurin É—aga mata hannu tana girgiza kai.
"a'a fa ni ba sai kin ce min komai ba, ai na riga na kaiwa Allah ƙara, zai yi min sakayya da kansa, cuta ce dai kin gama yi min ita".
Aliyu ya shigo a lokacin, Inna Wuro ta ɗaga kai ta dube shi tana aikin rumtse ido, ta yarfar da hannu ta ce,"gwara da Allah ya shigo da kai Aliyu, hanzarta ɗauko mota ka kawo bakin ƙofar ɗakin nan nawa, gidan sarkin ɗori zamu tafi tun ban gama shiga uku ba, ta ɓalla min duk ƙafafun nawa biyu, kai baka ji irin azabar da ke ratsa ni ba. waiwaiwai, huhuhu Allah dai ya saka min".
Aliyu ya kai dubansa ga Maama wacca ke tsaye tana gyara zaman glass ɗin idonta, fuskarta ɗauke da siririn murmushin ƙeta, a yayin da dogwayen lashes ɗin sama da na ƙasa suka haɗe, kafin ta buɗe su kyawawan chocolate eye balls ɗinta masu ɗauke da ruwa su bayyana.
suna haɗa ido da ita tayi ƙasa da kanta tana haɗe pink lips nata, still tana ƙunshe dariyarta.
sim sim ta bar bayan Inna Wuro ta nufi hanyar fita Aliyu ya dakatar da ita, ta tsaya tana rumtse idanu kafin ta juyo ta kalle shi.
cikin siririyar muryarta me bala'in zaƙi tace,"Uncle ba na sane fa".
sai ya kalli Inna Wuro da har yanzu take dirshen a ƙasa, sai matsa ƙafafu take yi a lallai sun karye.
"Inna to kinji bata sane".
"to dama tsoron Allah take yi da zata faɗa maka gaskiya, ni dai tun da ta riga ta cuceni kaje ka ɗauko mota kawai mu tafi gidan sarkin ɗori tun ban koma amfani da sanda ba, dan ƙarshe dai asibiti su yanke ƙafafun, ni kuwa ina zan so naga ana tura ni a keken guragu".