← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 176

Sashe 60

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turaki ya shigo ciki yana mayar da ƙofar ya rufe tare da ƙara saka key, zaton Fillo bai saka key bane, hakan yasa ta miƙe da azama cikin dabarar data tsara cewar zata bige shi ta buɗe ƙofar ta fice da gudu, irin gudun da ba zai iya kamota ba. kuma ba zata ƙara yardar ma tazo ɓangarensu aiki ba sai dai in Ɗausiyya.
Turaki ya tsaya yana kallonta da mamakin yanda ta wani taso a sukwane kamar wacca taga mugun abu, ya É—an matsa zai bata hanya gudun karta bigesa daidai nan É—akin ya gauraye da uban duhu sakamakon É—auke wuta da akayi.

babu shiri Fillo ta cakumo Turaki ba tare da sanin inda ta nufa ba tana kurma uban ihu tare da ƙanƙame shi.
"wayyo Allah nah, na shiga uku, Kakata". ihun take yi tana ƙara ƙanƙameshi kafin kuma ta shiga roƙonsa,"dan Allah ka kunna fitilar, wallahi ba zan ƙara ba, na bi Allah na tuba insha'Allahu ba zan ƙara yi maka ta'adi ba, kuma zan biyaka turarenka amma kaima Allah ka kunna hasken bana son duhu".

maganar take tana ƙara cikwikwiye shi, Turaki yasa hannu ɗaya ya riƙeta sosai ajikinsa, ya duƙa ya ajiye ledar hannunsa sannan yasa ɗayan hannun a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kunna tourch. idanuwanta a rumtse suke gam hakan yasa ba zata shaida hasken fitalar wayar ba, kuma har lokacin bata bar roƙonsa ba akan ya kunna fitilar tana ƙara shigewa jikinsa. ya leƙa fuskarta ya kalla yanda duk take a tsorace, sai haɗa uwar zufa take, ya girgiza kai kawai yana mamakin bala'in tsoro irin nata.

yayi ajiyar zuciya a daidai lokacin da wutar É—akin ta dawo, yay guntun tsaki na É—an jinkirin da aka samu before a kunna generator. shi kansa baya son wannan É—auke wutar duk da ba kasafe aka cika É—aukewar ba, dalilin da yasa ya dami Baffa kenan akan kawai a haÉ—a transformer a gidan a huta.

cikin sheƙar kuka Fillo ta ƙara cusa kanta cikin ƙirjinsa wanda tuni maɓallin wajen ya cire. karan hancinta na gogar fatar ƙirjinsa tace,"dan darajan Allah Turaki kayi haƙuri, idan na kuma yi maka ta'adi kayi min duk abinda kaga dama, ni ba da gangan na fasa maka turare ba suɓuce min yayi a hannu. kai ma Allah da ma'akinsa ka kunna hasken zan biyaka".

"kinyi alƙawarin zaki biyani?". da sauri ta ɗaga kanta,"ehh zan biyaka amma ba irin naka ba".
guntun murmushi ya sauka akan leɓensa yana bin tsakiyar kanta da ɗankwali ya zame da kallo. kansa ya ranƙwafo saitin kunnenta yace,"to ki sakeni sai na kunna hasken". da sauri ta girgiza masa kai,"a'a ka kunna a haka, idan na sakeka wani abun zai kamani".
yace,"wanne abu ne zai kamaki?". Fillo taji kamar tasa masa duka, sai kawai ta daÉ—a sa kuka tana cewa,"ni dai ka kunna don Allah, duhu tsorata ni yake wallah".

ya kai hannu kamar zai shafi gefen fuskarta sai kuma ya fasa yace,"to idan na kunna ta ina zaki sani bayan kin rumtse ido. ki buÉ—e idonki tuni aka dawo da light".

jin hakan yasa a hankali ta shiga buɗe idonta, sai da ta tabbatar idan ta buɗe duka idonta zata ga haske sannan ta buɗe, ta buɗe idonta duka tana saukewa ajikinsa. take ta zabura ta sake shi tana fita a jikinsa tare da ja da baya, sai aikin rarraba idanuwa take yi. sai kuma tayi saurin dafe kanta da taji yayi mugun sara mata a lokaci ɗaya, jiri ya nemi ya ɗebeta ya yasar, Turaki daya lura da hakan yay saurin kamo hannunta ya janyota ta dawo gabansa, ƙarar bugun ƙirjinta tarr a kunnensa.

yana riƙe da hannunta da take son ƙwacewa ya sunkuya ya ɗauki ledar, ya jata suka zagaya zuwa ɗaya side na gadon. cikin fargaba da tsoron matakin da zai ɗauka akanta na yadda tasa rigarsa ta cikwiwiye kamar an ƙwato a bakin jaki.
idanuwanta sukai rau-rau tasa hannu tana ture nasa tana cewa,"kayi haƙuri dan Allah, ba zan sake ba".

bai ko kalleta ba fuskar nan a haɗe ya zaunar da ita a gefen gadon. sannan shima ya zauna kusa da ita yana janyo table gabansa, ya buɗe coolern abincin dake kai yaga dambu ne na cous-cous da yaji hanta acikinsa sai ƙamshi yake. daga buɗewa duka wajen ya baɗe da ƙamshi.

ya juyo da kansa kaÉ—an ya kalleta tana ta matsar ido, ya tamke murya yace,"when did you wake up?".
taja majinar hancinta cikin muryar kukan da bai barta ba tace,"kayi haƙuri dan Allah". Turaki ya daki gefen gadon yayo kanta gaba ɗaya yana sakar mata tsawa,"nace when did you wakeup?".

da bala'in tsoro tasa hannu ta kare kanta jikinta sai kyarma yake yi, cikin rawar murya tace,"ban jima ba".
bai ƙara bi ta kanta ba ya tashi ya fita, after few minutes sai gashi ya dawo riƙe da wani ledan daban. ya ajiye akan gadon ba tare da ya kalleta ba yace,"ci abinci".

tsananin tsoron yanayinsa da ya rikiÉ—e bata tunanin zata yi masa musu, don haka da azama ta sauka a gefen gadon, hannu na rawa ta É—auki plate ta buÉ—e coolern ta zuba abincin ta ajiye a gabanta.
tunda ta zuba taji idanunsa akanta, hakan yasa ta kasa sakewa, kuma ta kasa ɗagowa ta kallesa balle ta nemi izininsa taje ta wanke hannu, shi kuwa ciwon hannunta kawai yake kallo da Zaytuna ta ƙara dressing.

sai da ta ga ya yunƙura zai tashi sannan tayi saurin cewa,"zan wanke bakina". yay gaba abinsa bayan yace,"karki je ki wanke kici a haka".

yana fita a ɗakin ta miƙe ta shiga toilet, bakinta ta wanke da macline sannan ta ƙara wanke toilet ɗin tukunna ta fito. har lokacin kuma hawaye bai bar sauka a fuskarta ba, ita tsoron da take yi kar Maama ta nemeta, duk da tasan zuwa yanzu Kaka na can tana jiran dawowarta.

ba zata iya cewa ba zata ci abincin ba don tana jin yunwa sosai, ga shi kuma girkin ya burgeta, ƙamshinsa kawai taji tasan girkin Adda Zaytuna ne. tana cikin ci taji ƙarar buɗe ƙofa, tun da ta hangosa ta wutsiyar ido tayi mugun tsorata da sauri ta ajiye spoon ɗin ta kama jan yatsunta.
ya dawo ya zauna a inda ya tashi, ya kalla plate É—in abincin tukunna ya kalleta yaga yanda take ta raba idanu, yaja tsaki cike da takaici. zai É—aga murya sai kuma yay controlling kansa, calmly yace,"du ka za ki cinye, ke kika zuba ai ba wani ya zuba miki ba...finish eating and take your drugs".
ya faÉ—a yana jefata mata ledan magungunan.

ta É—an kallesa taga baya kallonta tace,"idan na cinye to zaka barni na tafi?".
yace,"idan kin biyani abinda kika fasa min ba. ko an faÉ—a miki da kuÉ—in banza aka saya". tace,"insha'Allahu zan biyaka amma ba irin wancan ba, sai dai wani daban, Kaka bata da kuÉ—in wancan".

yay mata shiru, tana ɓata rai tace,"kuma ni lafiyata lau ai". ta faɗa tana ture ledan maganin daga kusa da ita.

sai da ta cinye abincin da ta zuba tass sannan ta miƙe ta wuce toilet ta wanko baki ta dawo, ta ɗauke plate ɗin ta ɗora akan table. kamar bada ita yake ba yace,"ba da kuɗin banza na sayo su ba, ɗauki kisha".
ba don komai ba sai saboda gudun kar ya sakar mata tsawa ko kuma yay mata wannan kallon da bata so tayi saurin ɗaukan maganin tasha, tana sha tana hawaye, bata miƙe ba sai da taci kukanta duk yana jinta amma bai ko kalli inda take ba.

bayan ta gama kukan ta zagayo ta gabansa ta zube duka gwiwanta biyu a ƙasa, ta haɗa hannayenta waje ɗaya alamar roƙo tace,"dan darajan Allah kayi haƙuri, kaga dare yayi Kaka na can tana jirana. kuma nasan Maama zata neme ni".

ta faÉ—a sabon kuka na taho mata, amma sai ta danne shi. Turaki yaci gaba da kallon wayarsa, kamar ba zai yi magana ba can sai taji yace,"thank you for saving my life which you have done so many times. but i want to ask you something and please you tell me truth".
furucinsa ya bata mamaki matuƙa, how does he knows that?, zuciyarta ta ambatar mata sunan Maijidda, ita kaɗai tasan wannan sirrin nasu.
to amma!...sai ta ɗago kai don kallonsa ƙirjinta na bugawa, gani take kamar maganar da yay ba da ita da yayi ba, ganin waya ce kare a kunnensa yasa ta sauke dogon numfashi, hakan ya shaida mata ba da ita yake magana ba.

cikin wayar da Turaki yake da Bello ta faki idonsa ta ƙarasa zaro key ɗin da ya leƙo ta aljihunsa ta yanda ba zai ji ba, ga mamakinta harta miƙe sai taji ya riƙe hannunta gam.

ta rumtse ido kamar zata yi kuka, ganin za tai magana yay saurin ɗora yatsansa saman lips ɗinsa alamar tai shiru. hakan yasa tai gum tana bo ne fuska. bayan ya gama wayar ya dubeta, tai tsaye ta rufe idanuwanta gam ko motsi taƙi yi tunda ya riƙetan. tsoronta Allah tsoronta kar yaga key ɗin motarsa da ta ɗauke, dan a second fitarsa ta ɗauke tasa acikin rigarta.

taji yace,"ni zan shanye sauran maganin?". ta buɗe ido ta ɗauki ledan da yay mata nuni da shi, cike da ƙaguwar ya sakar mata hannu.
tace,"wa zan kaima?". yana sakin hannunta yace,"ki wuce da shi". tace,"ina?". yace,"duk inda kika ga dama".
tana hararsa ta ƙasan ido tace,"ƙofan a rufe yake".
ta faɗa tana yamutsa fuska. ya miƙe yaje ya buɗe ita kuma ta fice da gudu, wannan gudun nata kuma yasa shi sakin gajeran murmushi yana girgiza kansa.
cikin sanɗa ta fita daga side ɗin nasu gaba ɗaya, ko tsayawa ba tayi ba a compound tayi ɓangarensu dan bama taso su haɗu da Maama a yanzu, sai safiya kuma.

sai after take jin wani mugun ƙamshi me shegen daɗi na binta, ta dinƙa jan hanci tana so taji daga ina ne, sai da ta shinshina jikinta taji ƙamshin a jikinta yake. tsabar daɗin ƙamshin nunfashinta har kusan sarƙewa yayi, tana tafe tana lumshe ido har ta kusa zuwa ɗakin Yami. aina ta samo wannan ƙamshin to?, ƙamshin da zata iya ce duk duniya babu ƙamshin da ya kaisa daɗi.
Chapter 60 · 0% Book details