← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 176

Sashe 72

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fillo ta amshi kayan tana ta zuba godiya ta fita, fuskarta kawai ta É—auraye ta É—auki turaren ÆŠausiyya ta fesa, sosai tayi kyau acikin kayan kamar dama dan ita aka siyo.
haka kawai sai take jin sam bata ƙaunar zuwa wurin Amir, alhalin tun randa aka kawo kayan sa rana ta ke ta so ta gansa, kwana 5 tasan tayi kewarsa sosai da soyayyarsa, tunda in sunyi waya ma faɗa suke, bata saka mayafin kayan ba tasa hijab saboda yanda ta jita uncormfortable a riga da wandon.
ta tafi tana ta ɓata fuska, ji take kamar har yanzu bata huce daga haushin Amir ba, kamar ranar nan da ta kulasa ba ita bace, kamar yau idan taje zata yi masa wulanci ne wanda zai sa ba zai ƙara dawowa ba.

sanda ta shigo parlon ya miƙe a zuciye zai tafi, ganinta kuma yasa ya tsaya yana sauke ajiyar zuciya cike da farin cikin ganin nata.
tun daga kan yatsun ƙafarta yake kallonta har zuwa kan fuskarta, last da yazo ta fita da mayafi bata yi masa kyau irin yau ba da take acikin hijab. ta tsaya daga bayan kujerar da yake tana cin magani bata ce masa komai ba.

ya harɗe hannayensa a ƙirji yace,"nai zaton ai ba za'a barki ki fito ba dan naga wani iko ake nunawa da ke a gidan nan, ko basu san tawa bace?". tai masa shiru tana ƙara ɗaure fuska tana jin kamar ta juya ta koma.
sai taji yay ƙasa da murya cikin amo na shauƙin so yace,"fushi ake dani har haka da ba za'a min ma smiling ɗin nan dake melting heart ena ba?, zunubin me na aikata wanda ban sa ni ba gimbiya?".
sai kuma ya kama kunnensa yace,"am sorry, ba zan ƙara ba insha'Allah, kar a kuma yi min horon da zuciyata ba zata iya ɗauka ba this time around".

ba tare da ta kalle shi ba tace,"tunda nace maka ka bari zan saka maka ranar zuwa ai sai ka bari ko, ba wai ka ɗauko ƙafa ka taho ba notice ba".
yay murmushi yana zagayowa inda take tsaye, ji yake kamar ya rungumeta a duk sanda yake tare da ita.
yace,"kiyi haƙuri nayi kuskure, kasa haƙuri nayi wallahi, 5days ɗin nan ji nai kaman an shekara 5".

ta daɗa ɓata rai tace,"to ni aiki nake yi yanzu, Baffa ne zai yi baƙi anjima kaɗan muna aiki".
ta faɗa tana ƙoƙarin barin wajen, zai riƙo hannunta tayi saurin janyewa tana cewa,"bafa kyau ka daina min irin haka, ni ban ma san yaushe ka lalace irin haka ba na taɓani".

yay dariya sose yace,"tsabar ƙauna ce, amma ba zan ƙara ba daga yau, zan jure zuwa ranar da za a kai min ke...yanzu dai kafin ki tafi dan Allah kiyi min murmushi ko zan sami sauƙi".
ta ƙara cin magani tace,"ba zaka samu ba kam, kaga tafiyata".

ta faÉ—a tana wucewa sai ya daÉ—a dakatar da ita da cewa,"sorry na manta. Kaka tayi min magana akan siyar da filayenki guda biyu saboda hidimar biki da zata yi da su, to na faÉ—a mata cewar za'a bada takardu tace suna wurinki ke kika adana su, yanzu ya za'ai?, saboda an sami wanda zai siya da tsoka dan kowanne zai iya siyansa 1Ml".

ta juyo ta kallesa tace,"Kakan tace maka za'a sayar min da fili saboda hidiman biki?".
ya É—aga kafaÉ—arsa,"yes, in kin koma zata daÉ—a miki bayanin hakan. ko na kira Yami sai kiji daga bakinta?".
tace,"tabɗijam, ashe gwarama da Allah yasa na ɓoye takarduna, to aiko babu me sayar min da fili ko guda ballantana har filaye 2. ayi haƙuri kamin lokacin Allah zai bada yanda za'ayi duk wata hidima...ka gaida su Inna sai anjima".
ta faÉ—i hakan tana ficewa daga parlon ta bar Amir da sakin baki yana binta da kallo fuskarsa na nuna damuwa da rashin jin daÉ—i.

in ya lura kamar yanzu bata son auren nasu dan ƙarara yaga hakan a fuskarta, me ke shirin faruwa ne?, wani ne ya hure mata kunne a lokacin da sukai faɗa da shi?, waye shi?, aina yake?.
sai yaji wani bala'in kishi ya tokare masa zuciya, a fusace yabi bayanta dan jin amsar tambayoyinsa sai dai yana fitowa compound ɗin ya tarar babu ita, haka ya bar gidan zuciyarsa na masa ƙunci.

da daddare Fillo na kwance a ɗakinsu wajen 9 na dare, time ɗin sun gama karatu ita da Ɗausiyya, suna hirar duniya Fillo kuma cikin ranta tana ƙudurcewar gobe zata cire tsoro taje ɓangarensu, ta kuma bawa Kaka shawaran kar a sayar da fili ko ɗaya gwarama a sayar da dabbobinsu.
wayar ɗakin tayi ƙara Ɗausiyya ta miƙe tana mita tai picking call ɗin.

daga ɓangaren Zaytuna tace,"Ɗausiyya Fillo tayi bacci ne?". tace,"a'a". "to ce mata tazo da sauri please". tace,"tom Adda".
ta ajiye wayar tana kallon Fillo da har ta rufa bacci ya fara É—aukarta, tace,"kije Adda Zaytuna na kiranki".
ta sakko daga kan gadon tana yamutse fuska saboda baccin dake cinta, veil É—in da ke É—aure akanta ta warware ta yafa ta fita.

cike da tsoro ta fito compound, tana tafe tana dube-dube har ta ƙarasa sashen su  Zaytuna, ta buɗe ƙofar ɗakin Zaytuna ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ganin Zaytuna bata ɗakin ta tsaya gefe tana jan yatsun hannunta, bacci sai daɗa fusgarta yake, Zaytuna kuma na toilet tana wanka, jin sallamar fillo yasa ta ƙwanƙwasa ƙofar toilet ɗin, wannan yasa Fillo neman kujera ta zauna tana ta jera hamma.

wayar Zaytuna da ke kan gadonta tayi ringing har sau biyu, ana ukun ta leƙo a toilet ɗin tace da Fillo,"ɗaga please ko waye kice bana kusa".
Fillo ta miƙe tana layin bacci taje ta ɗau wayan, dai-dai lokacin kiran ya katse, sai kuma ya ƙara shigowa, sai da zata yi picking tayi noticing vedio call ne, ta ɗaga murya wajen faɗawa Zaytuna cewar Vedio call ne.

Zaytuna tace mata,"wanne suna ne jiki?".
tace,"DH".
tace,"just pick".
Fullo ta gyara zaman gyalenta tai picking call É—in tana kauda fuskarta daga kan screen É—in wayar, call É—in nayin connecting tace,"bata kusa, idan ta dawo zata kira".

daga hotel É—in da Turaki yake zauna kan gado ya lumshe idonsa sannan ya buÉ—e yace da ita,"ke kuma kina ina?". tace,"ina É—akinta ita kuma ta fita".

Turaki dai so yake ta haska fuskan nata gaba ɗaya amma taƙi, sai side face ɗinta da yake kallo, ita ba ta ɗauki muryarsa ba ma, ya san halinta zata iya tayi droping wayar ko kuma ta bar wayar a haka taƙi haska fuskan ba tare da ta ƙara cewa komi ba har sai Zaytuna ɗin tazo.

ya miƙe daga kishingiɗen da yake ajikin pillow ya zauna sosai sannan yace,"bata ɗakinta ta fita, ke kuma kika shigo har kike ɗaga mata waya. what those that means?, stealing or snatching or what?".

ai furucinsa na ƙarshe yasa Fillo bata san ma sanda ta haska screen ɗin wayar gaba ɗaya ba a fuskanta, ta cune tana ɗaga gira duka biyun sama tace,"banyi kama da ɓarauniya ba balle in tsaya ɓata lokacina kan snatching, kuma ai ita me wayan da kanta tace in an kira na ɗaga, if not ba zan taɓa picking ba ko za'a dawwama ana kira".

tai maganar tana murguɗa ƙaramin bakinta, dan ko waye ya bata haushi ya ɓata mata rai, duk da ba'a son ranta ta faɗi hakan ba, stealing fa!, ya san mene ma'anar danganta wani da sata?

Turaki yay murmushi sai kuma ya ɗaure fuska yace,"ni kike faɗawa haka?, sa'anki ne ni?". sai a lokacin ta ɗauki muryarsa, a tsorace ta murza idanuwanta tana ƙifƙifta su, ta shiga uku ita ce kalmar da ta ambata cikin ranta. sai taji ƙirjinta na duka a lokaci ɗaya, ta marairace fuska tana yin kamar zata yi kuka tace,"kayi haƙuri ban san kai bane".

ya ƙara tamke murya yace,"ɗago kanki ki kalle ni". ya faɗa muryarsa a ɗage. ta ɗago kanta tana dab da fashewa da kukan dake ƙasan ranta, ta tsana, ta tsani wannan ɗaga muryar da yake mata. kuma a yau babu abinda zai hanata faɗa masa kar ya ƙara raising mata wannan voice ɗin nasa.
so tayi itama ta É—aga murya wajen faÉ—a masa ta yanda zai shaida gargaÉ—inta garesa, amma sai taji muryarta tayi sanyi tana ce masa,"bana so kake É—aga murya haka dan Allah".

Turaki ya shafo wuyansa yace,"are you commanding me?".
Ta girgiza kai ba tare da tace komai ba tana sa hannu ta goge hawayen da ya sakko mata. sannan tace,"Adda Zaytuna É—in wanka take yi, zan faÉ—a mata idan ta fito".

ta faɗa tana ƙoƙarin kashe wayar yay saurin dakatar da ita, shin bata san tun randa ya taho ba ya rasa natsuwarsa saboda tunaninta, tunanin halin da take ciki, bata san tun ranar da ya taho ba yake jin fargaba akanta ba, kuma tun da ya sauka a kowanne bugar sakan na agogo so yake ya ganta, yaga motsinta, yaga yacca lafiyarta ke ciki, bata san a daren yau ya rufe ido yafi sau 5 ba amma ya kasa baccin duk saboda yana so ya ganta, ko ya samu hankalinsa ya kwanta, ko wannan faɗuwar gaban ta bar shi.

ya tausasa muryarsa yace mata,"ce nayi ki É—ago ido ki kalle ni bawai ki kashe wayar ba".

da ƙyar ta iya samun courage ta ɗaga ido ta kallesa tana jin ƙirjinta na ta duka, sai dai kallo ɗaya da tayi masa sai ta kasa ɗauke idon nata gaba ɗaya, wannan tsoron ganinsa ɗin da take ji sai taji ya yaye, taji tana so ta kalle shi tai ta kallonsa.

kallonsa take yi ta kasa ɗauke idonta a kansa, zata iya cewa kamar ya rame, kamar yana cikin damuwa, kamar yana buƙatar wani abu.
ya katse tunaninta da faÉ—in,"kina da matsala ne?".

har yanzu idonta na kansa tace,"me ka gani?".
yace,"me ya sami idonki?".
ta lumshesu tukunna tace,"bacci nake ji".

muryarsa na ƙara yin ƙasa yace,"bayan bacci fa?".
tace,"ba komai".
yace,"are you sure?".
tace,"yes".
ya ƙara kallonta sosai sannan yace,"daga tuesday zuwa yau faɗa min kalar fitinar da kika yi".
ta waro ido waje taje,"fitina kuma?, ai ni bana fitina, da hankalina".
Chapter 72 · 0% Book details