← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 176

Sashe 169

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Fulani Nah daure mu fita".
ta kalle shi cikin hasken da zata ce a matsayin mutum uku take ganinsa, ta tattaro dukkan sauran ƙarfinta da ya rage mata ta daure, ya kamata ta yunƙura ta miƙe tana dafa kafaɗarsa, zafin ciwon da ya ƙaru yasa duhu ya wanzu a cikin idonta, ta daina ganin komai, tabbas bata iya ganin komai harta mijinta da yake riƙe da ita, sai dai kunnenta na iya jiyo mata sautin muryarsa dake fita cikin tsananin tashin hankali.

Allah ya taimaka musu a bedroom ɗin ƙasa ne, da basu san ta yanda za'ai su sauko daga saman ba.
Turaki yaji tayi masa wata muguwar damƙar da zai rantse ba ita ba ce, domin ba ƙarfinta ba ne, bata da wannan ƙarfin ya sani.

"ka É—auko riyon Babies mu wuce asibiti".

"ba zan iya tafiya na barki ba a haka".

"zan iya Jannaty, zan iya daurewa, zan daure har ka dawo".
nan da nan Turaki ya haye sama ya tattaro duk wasu abubuwa da za'a buƙata a asibiti, ya kira Ilham a waya ta taho part ɗin, tana shigowa parlon ta tarar da Fillo durƙushe a ƙasa tana ambaton Ya salamu, Ya Salamu ka kawo min da sauƙi, idan na kasa ubangiji ka bani dauriyar da zan iya.

tayi kanta da sauri, Turaki ya sauko ya dire kayan hannunsa.

"kira yaran nan su kai mota sai ki zo mu kamata".
hankalin Ilham a tashe ta shiga ƙwalawa su Sakina kira, bata ma iya yi musu magana da baki ba sai nuni da tayi musu da hannu.

fitowarsu compound BoÉ—ejo ta iso gidan ita ma duk a ruÉ—e, tana ganin yanda suke tafiya da Fillon a hankali ta É—aga murya wajen ce musu,"kai ai zuwa zaka yi ka kawo motar nan kusa, sai mun hanzarta kar ta haihu a mota".
tsabar ruÉ—ewa Turaki ya manta da tunanin hakan, don haka ya sakarwa Ilham ita ya wuce cikin sassarfa yana haÉ—awa da gudu.

asibiti mafi kusa suka isa, su na zuwa aka karɓe su saboda ganin yacca Fillo ta gama galabaita cikin mintunan da gaba ɗaya ba zasu kai rabin awa ba, ƙari kuma da uban kuɗin da suka ji an sakar musu duk da cewa dama asibitin private ne. wucewar wasu mintuna da ba zasu wuce goma ba Dr ya fito yana shaida musu cewar ba zata iya haihuwa da kanta ba sai dai ayi mata CS.

"in har zata haihu lafiya ku yi mata koma menene, ina da buƙatar matata don Allah".

furucin ya fito daga bakin Turaki murya a kakkarye.

Dr ya ba su takardar da za su yi signing akai, Turaki yay signing É—in a san da hannunsa da jikinsa duka ke rawa.
kafin Dr Yusuf ma ya karɓa yay sigining a ɓangaren signature na mahaifinta.
cikin wasu ƙalilan ɗin mintuna aka shiga preparation ɗin yiwa Fillo tiyata.

lokacin duk ƴan gidan su Turaki sun iso asibitin, da Ammi mahaifiyar Yusuf, da wasu ƙannen Hayyo mutum biyu da suke anan garin gombe Safna da Alawiyya.
duk ɗinsu su na zaune a ƙofar labour room ɗin da aka shiga da ita tun ɗazu, kowa yay jugum jiki duk a sanyaye, babu wanda zaka kalla kaga kwanciyar hankali a tare da shi, mahaifiyarta sai kiran waya take yi ana faɗa mata ko tiyatar ma ba'a shiga ba har yanzu.
Turaki kuwa zama da tsayuwarma sun gagare shi sai zarya yake tayi, time to time sai yasa hannu ya sharce zufar da ke saman goshinsa.

motsin buɗe ƙofar labour ɗin da aka yi yasa duk suka tattara hankalin su gun, Dr ya fito cikin sauri ya nufi side ɗin operation thiater, a san da nurses biyu ke turo gadon da Fillo ke kwance akai, tana sanye cikin uniform ɗin da ake sawa na CS, nurses ɗin suka tsayar da gadon a san da suka ƙaraso saitin family ɗin nata.

Mum ta fara duba tace,"Mum kun zo?".

kallo ɗaya zaka yi mata ƙwalla ta cika idanunka, duk suka taso suka iso wajenta, ɗayan hannunta da babu canular shi ta dinƙa miƙa musu su na gaisawa tana amsa tarin adu'oin da suke tayi mata.

tana duban Ammi ta ce,"Ammi Ummi bata zo ba?".

"bata zo ba Fillo, muna dai tayin waya da ita, tana ta yi miki adu'a, tace kar ki yawaita raki kiyi ta adu'a".

"Ammi ina ta daurewa amma na kasa yin nishin da suka ce, kamar dai ko ba zan haihu É—in ba ne".

"za ki haihu kar ki damu, insha'Allahu Æ´aÆ´anki za su fito".

"Allah yasa Ammi. don Allah a ki kira min Ummina".

ta furta hakan ƙwayar idonta na mannewa akan fuskar Turaki da yake tsaye yana kallonta ya kasa tahowa wajenta.

bayan sun gama wayar da Ummi, nurses É—in su ka cigaba da tura gadon, suka tsayar da shi a gaban Turaki.
duk sun kasa ɗauke ido daga na juna, ita da take cikin ciwo ita ce me ƙarfin halin yi masa murmushi, don a wannan lokacin Turaki baya iya jin ko murmushin menene zai iya yi, ko da ace kuwa haihuwar tayi, har sai ya ga ta koma asalin Fulaninsa da ya sani, ba wannan Fulanin da yake gani ba me ƙarfin hali.

ta miƙa masa hannunta ya kama ya riƙe, ya zubar da gwiwoyinsa a gaban gadon yana ce mata,"sannu Fulani Nah, sannu ƴar aljannah".

sai fuskarta ta juye zuwa tsantsar damuwa tace da shi,"kayi haƙuri Jannaty ba zan iya ba, nayi duk iya ƙoƙarina amma na kasa, Dr ɗin yace ƙugun maza gare ni ba zan iya haihuwa da kaina ba sai dai suyi min aiki".

Turaki ya kasa ce mata komai, ya kifa goshinsa a gefen hannunta, ta ɗago ɗayan hannun dake da canular da ƙyar ta ɗora a kansa.

"Ka kwantar da hankalinka don Allah Jannaty, babu abun da zai faru kaji?, lafiya lau za'ayi aikin nan da izinin ubangiji, kuma lafiya lau za'a fito maka da ni da Æ´aÆ´anka".

Turaki ya É—ago kansa ya kalleta, a san da yake amsawa da Allahumma amin.
Fillo ta dinƙa kallonsa tamkar yaune ta soma ganinsa, mamaki take yi sosai, bata taɓa yi masa murmushi ba yaƙi mayar mata da martanin hakan, haka zalika bai taɓa kallon fuskarta ba, ba tare da tasa fuskar ta washe da kyakykyawan murmushi ba, a yau kuma a wannan lokacin fuskarsa na looking so hard, babu wani emotion da za ta ce ta tsinta a ciki, zatonta ranar yau ita ce ranar da yake ta jira, wan nan lokacin shi ne yake tsimayin jiransa saboda ƴaƴansa guda biyu za su fito duniya, don haka a wannan lokacin ya kamata ace taga yana farin ciki ko ya ya ne.

amma tun a gida data fara ce masa ciwo, yay É—an guntun murmushi yana tsokanarta da Lukutar gombe zata haihu zata sace a koma gidan jiya, zata dawo kamar muciya da zani.
ta san tayi dariya a lokacin da yay wannan maganar, but ita a lokacin data tsokane shi da cewa haka aka gani a muciya da zanin aka nace sai da aka ɗauka, bata ga wani kuzari na martanin dariya daga gare shi ba, kawai dai ya miƙe ya ɗauko jarkar rubutu ya bata ta tasha cikin mutuwar jiki.

ta lumshe idonta ta buɗe kafin tace,"ƙarfe nawa Jannaty?".
zai iya cewa da ƙyar ya iya karantar agogon kafin yace mata,"takwas da rabi Fulani nah".

ta sauke numfashi ta ce,"sun ce sai ƙarfe tara da rabi zamu shiga, da za su bani dama da na kalli gabas nayi adu'a".

sai kuma tace,"ka ci abinci Jannaty?".
bai iya magana ba illa girgiza mata kai da yay.

"me yasa to?, kana so Aayan ya taso ya fika ƙiba ko?, mutane suke tsokanarka su na cewa ɗanka yafi ka ƙiba".

sai ya daɗa riƙe hannunta kamar wanda za'a ƙwace masa ita yace,"ta ya zan iya saka wani abu a cikina alhalin kina cikin mawuyacin hali?".

"Jannaty na faÉ—a maka ka kwantar da hankalin ka, lafiya lau za'ayi komai babu abin da zai faru".

"zan ci abinci amma sai an fito da ke, wataƙila ma yau ba zan ci irin abincin da za kici ba, wan da zanci zai fi wanda zaki ci daɗi, ko don saboda nayi ƙiba a daina yi min gori".

tayi murmushi,"to me zaka ci?".

sai ya kai hannunsa ɗaya saman breast ɗinta ya taɓa yace,"madaran yarana zan sha, mu uku za kiyi feeding yau".

"baka da damuwa guda É—aya ma za'a bar maka, sai suyi shairing guda É—aya".

ta ƙara cewa,"ka yi min waƙar da kake yi min Jannaty".

ya girgiza mata kai,"ban da waƙa sai dai adu'a".

"to kayi min karatu cikin ƙira'arka me daɗi".

a hankali kuma ya shiga biyo mata suratul shu'araa.
har san da yazo kan aya ta ashirin da takwas,_wa'izaa maridhtu fahuwa yashfeeeen_.

sai ta ji wani abu na bi ta ƙasan zuciyarta, ta kira sunansa da irin amon sautin da zai ce bai taɓa jinta da shi ba, ya kalleta idanuwansu suka sarƙe waje ɗaya, ya haɗiye wani abu da bai san menene ba kafin yace,"menene Fulani Nah?, me kike so?, ciwon yana raguwa?".

ta mayar da murfin idon ta rufe ta ce,"hold me Jannaty, i want to talk to you". ta faÉ—i hakan tare da buÉ—e idanuwanta.

"Jannaty duk da halin da nake ciki ina yi maka murmushi, please kayi min wannan kyakykyawan murmushin naka atleast ko da sau É—aya ne, ko da bai yi faÉ—i da yawa ba, ka daure kayi min ko ya ya ne".

shirunta ya haɗe da bayyanar haƙoran Turaki duka a waje, maimakon murmushin da tace tana so sai kawai ya sakar mata dariyarsa me daɗin sauti, dariyar da har ita ma sai da tayi irin tasa ɗin, dariyar da ta ratsa jijiyoyin Turaki ta zarce har cikin zuciyarsa ta huda wani waje.
Chapter 169 · 0% Book details