← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 176

Sashe 70

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kiran wayar Bello da ya shigo a karo na kusan huÉ—u yasa shi sakinta yana waiga yana daÉ—a kallon Fillo. ji yake kamar kar ya tafi, ya kama hannun Zaytun suka fita yana faÉ—a mata,"idan kinje wurin Kaka ki É—auko cream É—in da ta ke shafawa ki jefar, i don't think wanda kika saya ranar nan take shafawa".

Zaytuna tace,"tayi haske sosai ko?, nayi zaton ma wanda na sayo mata ne so after na tambayeta tace min bata fara using da shi ba, tana shafa wani da aka kawo musu, Kaka ta hanata buÉ—e sabon wai almubazzaranci, but zanje É—in sai na É—auke".

suka fito compound ɗin Bello dai na tsaye sai hararsa yake, Turaki ma ya hararesa ya ƙarasa wurin Maama, sallama dai kamar kar ai tafiyar, kuma kamar wannan ne karo na farko da zai fara tafiya, Nihal ma ta dage cewar ita dai zata bisa, yace sunyi late ai da tun jiya ta faɗa masa sai a anso tictiket har ita, Samha ma ta riƙesa tana faɗin kawai ba sai ya tafi ba ita bata so yana nisa da su, Hajiya Madina ta zabga mata harara tana me jin wani ɗaci da baƙin ciki na kasancewar Samha ƴarta.

Ilham kam da ta kwana a gidan tana riƙe da hannun Boɗejo tana goge hawaye. Boɗejo tace,"ni wallahi duk kun saka jikina yayi sanyi, tafiya sai kace yau zai fara, ko saboda kawai ya jima bai yi nesa daku ba?. fisabilillahi irin wannan sallamar da kuke yi ai ta masu bankwana da juna ce, irin fa wannan sallamar akeyi idan mutum zai mutu. to ni dai gaskiya idan tafiyar nan bata zama dole ba ke Madina sai kisa shi ya haƙura".

ta kalla Hajiya Madina taga tana goge hawaye tace,"ka ga wani ƙarin tsinkar da zuciya kuma".

Turaki dai yana tsaye jikinsa duk yay sanyi, shima ji yake kamar idan ya tafi ba zai dawo ba, sai kallon side ɗinsu yake yi, kamar zai ga Fillo ta leƙo ta window, kamar zata leƙo suyi sallama. ya sauke ajiyar zuciya ya kira sunan Ilham, ta ɗago tana goge hawaye ta tafi zuwa gabansa, ya ɗauke hannunta daga fuskarta yana sa handky ɗinsa ya goge mata fuskar, a hankali yace,"kukan mene?".

tace,"nace zan bika tun jiya". yay murmushi yace,"4days fa kawai zanyi na dawo". ya faÉ—a yana É—ago kai ya kalla Nihal yace,"auta zo". tazo itama nata hawayen na sauka a lokacin.
yace,"ku shiga kuyi min rakiya to".
BoÉ—ejo tace,"kaga in É—aukowa Ilham mayafinta ku tafi tare kawai, ni bana son kuka yana É—aga min hankali".

Khalil wanda zai driving nasu yace,"Allah babu da wadda zan tafi da ita, ina sauke su nima da inda zanje".

BoÉ—ejo na hararsa tace,"kana kama da mutanen kirki amma ba haka kake ba, in motar kai ka saya sai ka hanasu shiga ai".

Khalil dai ya tubure babu me binsa, har sai da Hajiya Madina tasa baki, amma hakan bai sa ya yarda sun tafi da kowa ba.

ƙarfe tara Fillo ta tashi, ta tashi a firgice tana bin ɗakin da kallo, ta sauko daga kan gadon da sauri tana rarrabawa idanuwa. har yanzu babu alamar ya shigo, to ta ya zata fita daga ɗakin alhalin yasa key?.
tana ta ɓata rai ta shiga gyara ɗakin, tana gyaran gado taci karo da farar takarda a ninke, ta ɗauke ta aje kan side drower sai kuma taji tana buƙatar buɗewa, bata san ba ko yana da alaƙa da mugwayen mutanencen.

ta zauna gefen gadon ta warware takardan, farkon abin da ya fara burgeta handwritting É—in jiki, sai kuma zanen heart da peppern ke É—auke da shi. sannan tabi rubutun da kallo tana karantawa acikin yaran fulatancin da aka rubuta.

_Nisa tsakanin zuƙata biyu ba ya nufin shinge fa ce tuna kyakykyawar alaƙa da ke tsakani...ƙwarai akwai wanda yake ƙaunarki kwatankwacin yadda makaho ke buƙatar ido, fiye da yadda kurma ke buƙatar ji, fiye da yadda gurgu ke buƙatar ƙafa, Dai-dai da yadda mara lafiya ke buƙatar lafiya, cikin ƙanƙanen lokaci yana jin kin zama rayuwarsa gaba ɗaya, kula da kanki shi ne mafi abin da yafi so daga gareki kiyi masa a san da yay nisa da ke, amana!, amana!, amanar kanki a tafin hannunki daga gare shi._

haka siddan Ilham ta faɗo cikin zuciyarta a sanda ta gama karantawa, ba wai don ta santa ba ko tasan matsayinta, tana hasko hoton yanda ta same su jiya a ɗakin Boɗejo. ta taɓe baki ta miƙe tana jefar da takardar a ƙasa, tabi ta kanta ta wuce ta gyara kan table ɗin dake hargitse da takardunsa, tana gyaran ɗakin tana kumbura ba tare da sanin dalili ba, kuma har ta gama gyaran bata bi ta kan gadon da ta soma gyarawa ba, saboda haka ɗaya taji gyarasa baida wani amfani duk da ita ta kwanta akai.

tana riƙe da kwanukan abinci a hannunta taji an turo ƙofar ɗakin an shigo, idonta ya manne akan Ilham dake shigowa kamar wacca ƙwai ya fashe mata a ciki, fuskarta duk hawaye, ta shigo ba ko sallama ta wuce ta gaban Fillo ta faɗa kan gado tana ɗauko pillow ta rungume a ƙirjinta.

wani abu da Fullo bata san ko menene ba ya tokare mata a maƙoshi, tasa kai ta fice a ɗakin da sauri.

*vote, comment and share.*
[8/29, 20:48] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

```DAGA MARUBUCIYAR```

1-Sirrin Ɓoye
2-Al'amari
3-Hidaya Noor
4-Alhussain
5-Sanadin Talauci
6-Ƙaddarar So
7-Prince Khaleed
Da sauran su.....

*31*
wani abu da Fillo ke ji akan Ilham ya tsaya mata a ƙirji kamar ƙurji, har ta baro upstairs ɗin wani irin ɗaci take ji a tare da ita da bata san dalilinsa ba.
lokacin da ta fito compound zata wuce ɓangarensu ta tarar ana rage flowers ɗin gidan, wajen duk yay kaca-kaca, tausayin masu aikin cirewar da gyara wurin ya kamata, neman halal da wuya, kuma a haka namiji ke fita yasha wahala ya kawo macen da bata arziƙi ba tayi masa ɗiban albarka, ta girgiza kai tana me jin tausayin kowanne namiji acikin ranta amma banda Hayyo mahaifinta.

sai da taje gab da shiga gate ɗin nasu kawai maganar macijin jiya ta dawo sabuwa acikin kanta, take kuma tsananin tsoro ya rufeta ganin wani reshe na flower da aka sare wada yay kama da jikin macijin, ba shiri ta kurma uban ihu tana duƙewa a wajen sai kururuwa take, da sauri masu aikin suka yo kanta suna tambayar lafiya, dai-dai nan Khalil ya ƙaraso wajen shima yana duƙawa gabanta da tambayar lafiya.

cikin kukan da take tace,"maciji ne". with suprise kowa ya ƙara maimaita abinda tace,"maciji kuma?". ta ɗaga kanta jikinta sai rawa yake yi. nan da nan masu aikin suka shiga laluben wajen, Khalil kuma yace ta tashi sai ta girgiza masa kanta tace,"ba zan iya ba".
yace,"kin gurɗe ne?". ta ƙara girgiza masa kai ba tare da tace komai ba.
yana murmushi yace,"daure ki tashi babu komai anan, macijin ai ya tafi ga shi can sun kashe shi".

tun ɗazu da ta duƙe sai a yanzu ta ɗago da kanta tana rarraba idanuwa, yacca take yi ɗin ba ƙaramin bawa Khalil dariya tayi ba. bai kasa riƙe dariyarsa ba ya saki yana ce mata,"tashi na raka ki". ya faɗa saboda yanda yaga duk ta firgice, firgicewar da ba zata iya tafiya ita ɗaya ba.
ta miƙe da ƙyar sai ƙanƙame ƙafarta da jikinta takeyi, ya wuce gaba yana cewa,"muje".

idonta ya sauka cikin compound ɗin nasu, maganar Turaki ta cewar ai wadda ma macijin ya maƙale mata mutuwa tayi, sai taji inaa ba zata taɓa iya shiga ɓangarensu ba, tana jin ma kamar sai dai Kaka ta dawo nan itama. ba shiri taja da baya tace da Khalil,"Hammah Khalil ba nan zani ba ɗakinmu zan wuce".

tana tafe tana ɗage ƙafafu haka ya rakata har ƙofar ɗakinsu, zaune ta sami Ɗausiyya na gyaran zogale, ganin Fillo yasa Ɗausiyyan ƙyalƙyalewa da dariya tace,"matsoraciyar kawai". Fillo na hararta tace,"tsoro ai halal ne, kuma tsoron me kika kalla nayi".
ÆŠausiyya tace,"ai ina kallonki sanda kika zube, har nayo wajen naji ana batun maciji babu shiri nayo reverse".

Fillo na ƙara harararta sanda take zama kan gadonsu tace,"ashe kema matsoraciyar ce".
ÆŠausiyya tayi dariya tukunna tace,"2days kina makarar shigowa".
Fillo na kwanciya kan gadon tace,"wani lalataccen barci nake fama da shi 2days É—in, in kuma kina da magani sammani".
tai maganar tana jin jikinta a saɓule, yanayinta duk babu daɗi kamar wani abu na shirin faruwa mara kyau.
ÆŠausiyya tace,"aiko dai ki nemi magani. É—azu da Hammah Babba zai wuce yana cewa da Adda Zaytuna wai in yaje can wurin da zai je zai sayo mata maganin daina bacci, da kina nan kema da kin faÉ—a masa tunda naga yana da kirki, kawai dai baida sakin fuska, jiya ma 2k ya ban".

lokaci ɗaya Fillo taji allon ƙirjinta ya girgiza, Turaki ya tafi?, when is he coming back?, tare da Bello suka tafi, ta ya zai iya kula da kansa?, ya tafi da maganinsa?.
tarin tambayoyin da suka zowa cikin kanta kenan a lokacin, ga shi babu ɗaya da take da amsarta, dan haka ido kawai ta lumshe kamar me bacci, tana jin Ɗausiyya nata magana amma bata jin zata iya buɗe baki ta amsa mata saboda faɗuwar gaban da take ji, wani irin yanayi da bata taɓa jin kanta aciki ba, like kamar dai something bad will happen soon.

bayan kwana biyu aka kawo akwatin sa ranar auren Fillo daga gidan su Amir, Innarsa da wasu Anties nasa guda biyu na ɓangaren mahaifi su ne suka kawo, akwaiti guda ɗaya da atamfa 4 aciki sai less da zai kai 6k guda biyu, shadda ɗaya da material guda ɗaya, da fashion na yari da sarƙa guda biyu sai takalmi da jaka duk guda ɗaya, sai kuma hijabs har ƙasa guda biyar da 5k a haɗe, akasa ranar aure wata biyu masu zuwa.
kaya dai masha'Allah sunyi kyau sosai gwanin san barka, kowa ya gani sai ya yaba, haka akaita zuwa ana gani ana tafiya da masha'Allah, su Yami kam baki har kunne jikarsu tayi goshi.
Chapter 70 · 0% Book details