← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 176

Sashe 87

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana yin shiru yay wani guntun murmushi na tayata jimami sannan yace,"ban labarin yanda aka yi bayan barinta gida".
jikinta na rawa tace,"lokacin da ta bar gida can ƙasar china ta nufa kamar yanda ka faɗa, bayan wata uku na bi sahunta zuwa dajin da kace anan aka jefa kurciyar domin na tabbatar da taje can ɗin. kuma ko da naje na ganta ɗin a gefen wata bishiya tana cin ganye, itama kuma ta ganni dan har ta dinƙa roƙona akan in taimaka mata bata san ta yanda akayi tazo wurin ba, ta bar Muhammad da Zaytun acikin ɗaki wuta tana ci bata san ba ko Madina ta kula kar yaran su cutu. sai nayi mata dariya nake faɗa mata cewar ni ce silar zuwanta wurin kuma ita da ƙara komawa wajen ƴaƴanta har abada. to muna cikin haka da ita ne sai ga wasu turawa sun zo, suna zuwa suke tambayata cewar nasan wannan mahaukaciyar ne?, da farko har zance musu a'a sai kuma nace ehh, sai ɗaya daga cikinsu yace min to suna da buƙatar siyanta idan zan siyar musu zasu yi tsafi da jininta, ni kuma jin hakan yasa ba tare da wani tunani ba na amince musu dan har inda suke da zama ma muka je tare suka min bayanin cewar zasu ajiyeta aɗakin tsafi tsawon shekara ashirin da shida cif kafin nan sai su zuƙe jinin jikinta suyi tsafin da zasu yi da shi, kuma tare da ni suka sakata a wani ƙaton ɗaki ko taga babu suka kulle suka ce za'a ke bata abinci ne kawai tana ci, don har sarƙoƙi suka saka suka ɗaureta saboda kar ɓacin rana yasa ta gudu, kaji abinda ya faru Boka, ko ɗaya ban saɓa ƙa'idar aikinka ba wallahi".

Boka ya ƙara murmushi sannan yace,"Azima aikinki ya lalace, domin kuwa maganar da nake miki yanzu asirin da yake kan Ramla ya barta kuma ba da jimawa ba za ki karɓi sakamakonki saboda aljanin da yay wannan aikin ba me yafiya ba ne".

Fulani Azima ta dafe ƙirji cikin bayyanuwar tashin hankali a tare da ita tace,"kamar ya Boka ban gane ba, me kake so kace min?, ta ya hakan zata faru?".
yana ɗago matacciyar kurciyar da jan ƙyallen yace,"waɗannan sune asirin da ke kan Ramla, wannan kurciyar da kike ganinta tun ranar da ta ɗauki Ramla bata ƙara zuwa nan ba sai yanzu, wanda ke tabbatar da cewa Ramla ta baro inda ta ke ta dawo cikin garin nan, kuma mutuwar kurciyar nan shine zahirin cewa babu wani abu da ya sami Ramla".
sai ya jefar da kurciyar sannan ya ɗauko ƙyallen yaci gaba da cewa,"wannan kuma shine ƙyallen da muka ƙulle ƙwaƙwalwar kifaye acikinsa saboda Ramla ta manta komai, dan haka faɗowar wannan da kuma warwarewarsa ya shaida mana Ramla ta dawo cikin tunaninta".

ya jefar da ƙyallen ma sannan ya juya bayansa yana kallon akuyar dake tahowa tana kuka yace,"idan za ki iya tunawa wannan itace akuyar da kika kawo muka ɗaurewa baki saboda rufe bakin Ramla, tsawon wannan shekarun tana nan tare da ni bata taɓa kuka ba sai yau kuma ayanzu, hakan ke tabbatar da cewa bakin Ramla ya buɗe duk inda ta ke yanzu tana can tana magana".

Fulani Azima ta É—ora hannu akanta tare da kurma ihu tace,"na shiga ukuna".
Boka yace,"ba ki shiga uku ba tukunna sai kinga yanda reshe zai juye da mujiya".
ya faɗa yana sa hannu ya daki ƙasar dake gabansa sannan yace,"kar hankalinki ya tashi sosai, ke ko garin da kike ba za ki bari ba, amma sai dai za ki kwanta baƙar jinyar da za ki ji gwara ace haukacewa kika yi ko kuma ɓatan kika yi da wannan ciwon da zai kamaki. domin za'a zo har kan gaɓar da hatta ƴarki ba zata iya zuwa kusa da ke ba".

Fulani Azima ta fashe da kuka sosai tana cewa da boka yay mata rai. cikin wata razananniyar tsawa yace da ita,"Azima ta shi ki bar mana wuri". ya faÉ—a yana nuna mata hanya.
suka miƙe tare ita da Jakadiya jikinsu sai rawa yake suka fita daga wajen tana ta uban kuka. suna fitowa tayi wani kukan kura ta shaƙi wuyan Jakadiya tana girgizata tana faɗin,"wallahi ba ki isa kin tona min asiri ba, ba zan kwanta cuta ba kibi ta bayan fage kije ki fallasa ni, zan kasheki sannan zan je in kashe Ramlar ma".

haka ta dinƙa sambatun magana bata saki wuyan jakadiya ba har sai da ta tabbatar ta mutu tukunna ta jefar da ita a wayen, ta bar wajen kamar ana tankaɗata har ta fito daga cikin jejin, tana zuwa ta buɗe mota ta shiga Driver yaja su, sai da suka shigo cikin gari sannan tasa ɗankwalinta ta shaƙo wuyan driver shima tana faɗar,"ba zan barka a raye ba kaima ka tona min asiri, ba zan barka kaga ciwona baka tona min asiri".
bata sake shi ba sai da ta tabbatar ya mutu, kuma kamin Fulani Azima tayi wani ƙoƙari na karɓar kan motar, motar ta gangara ta faɗa gefe, nan ta-ke glass ɗin motar ya tarwatse da yawa suka soki cikin kanta, ta kurma ihu tana neman ɗauki tana ƙoƙarin fitowa a motar, bata ankara ba ta kai fuskarta saitin wani glass da yay kamar kibiya ƙwayar idonta ɗaya ta soki glass nan take ruwan idon ya shiga tsiyayewa.

*A dai-dai wannan lokacin.*
*Yanda Abin ya kasance da kuma yanda abin ke faruwa.*

sanda Turaki ya ƙaraso wurin da kidnappers suka buƙaci da ya ajiye kuɗin, yay parking motarsa ya fito ɗauke da dumin jakar kuɗin.
ya tsallako side É—in da suka ce yay tafiya me nisa sannan ya ajiye jakar a wajen, ya É—auko wayar Maama dake aljihunsa ya É—aga calling É—insu dake shigowa.

daga can ɓangaren yaji ance,"kai ne kasa coffee yadi?".
yace,"ehh ni ne". ya faɗa yana duddubawa ko zai ga ta inda mutumin yake. sai yaji mutumin na dariya yace,"ai ba zaka taɓa ganinmu ba ka bar wahalar da kanka da waige-waige, ka juya ka bar wajen ka koma bakin motarka ka jira yaronka zai zo ya sameka".

jin haka yasa Turaki saurin juyawa ya bar wajen, for the next 5minutes sai ga mutumin yazo ya ɗauki jakar shi kaɗai, cikin sauri yake tafiya don barin wajen, a lokacin Turaki ya fito daga jikin wata rila da ya laɓe.
yasa hannu a bayan wandonsa ya zaro bindigar da bai taɓa riƙeta ba sai a yau, ya saita ƙafafun mutumin ƙwayar idonsa na hasko masa yacca ake harbi acikin film, bai taɓa ganin bindiga ido da ido ba sai a yau da ya shiga office ɗin DSP ya ɗauko ba tare da sanin kowa ba, kazalika bai taɓa riƙe bindiga ba balle har yay attempt na harbi, but today bindiga tazo hannunsa, and zai gwada amfani da ita ko da ace wannan itace dama ta ƙarshe da yake da ita a duniya.

ya saita ƙafar mutumin ba don yana tunanin dai-dai ya saita ba, kuma babu ɓata lokaci kai tsaye ya saki bullet, kuma cikin sa'a bulle ɗin ya shige ƙafar mutumin, hakan kuma bai sa Turaki ya haƙura ba ƙara sakin bullet ɗin wanda a yanzu kai tsaye ya wuce zuwa kaɗar mutumin daidai sanda ƙafafunsa ke durƙushewa a ƙasa yana sakin jakar kuɗin ya riƙe kafarsa dake zubar da jini.

abinka da wanda bai san kan lamarin ba kawai sai ya jefar da bindigar a wajen ya kwasa a guje ya ƙarasa gaban mutumin, ta baya ya damƙi kwalar rigarsa ya ɗago da kansa, ya zagayo ta gabansa yasa gwiwar ƙafarsa ya daki haɓarsa, ta-ke jini da ƙwaƙwalwarsa suka haɗu waje ɗaya, ƙwayar idonsa ta firfito waje yana buɗe su da ƙyar saboda azabar harbin da ya shige shi ya kalli Turaki, cikin zafin nama Turaki yasa hannu ya fizge facemask ɗin dake fuskarsa.

yana faman huci kamar mayunwaci za ki yace,"ina yarinyar ta ke?". ya faÉ—a cikin É—aga murya sosai.
sai kuma ya sassauta muryarsa yace,"zaka tsira da ranka, kuma zan kai ka asibiti sannan zan barka da wannan jakar kuÉ—in ka tafi safely, but first tell me ina yarinyar ta ke?".

shirunsa ya haɗe da ƙarasowar ƴan sanda wajen, suna zuwa ɗaya daga cikin ƴan sanda yasa ƙafa ya daki gabansa atake ya ƙwalla wata razananniyar ƙara saboda yacca yaji kamar za'a zare masa rai, babu shiri ya ɗaga hannu yana yi musu nuni da katangar gidan dake can gabansu.
Turaki is the first one da ya bar wajen a cikin gudu, wasu cikin Æ´an sanda suka mara masa baya, yayinda wasu mutum biyu suka É—auke wannan wanda Turaki ya harba sukai mota da shi.

harbin farko da Turaki yayi su Amir sunji a lokacin suna laluben Fillo acikin gidan, kuma rashin tabbatar da cewar harbin bindigar suka ji da gaske yasa basu bi ta kai ba sai a harbi na biyu, anan hankalinsu ya tattaru wuri É—aya saboda haka duk sai suka dakata da batun nemanta suka koma ta yanda zasu tsira.
Amir yace,"duk yanda akayi shegun mutanen nan da police suka zo".
wani me kama da shi yace,"tabbas kuwa, but har ta ya mu kayi sakacin hakan ya faru?".
sai ya juya yana kallon mutumin da ya taimakawa Fillo yace,"hau katanga ka duba mana".

yana hawa katangar ya ƴan sanda daga can nesa kamar cinnaku sun baibaye faɗin wajen, hakan yasa da ƙarfi yace musu,"police ne mota har guda uku".
yana faÉ—ar hakan ya dirge ta baya dan ba ya tunanin zai iya bari a rutsa har da shi.
su kuma nan suka fara neman hanyar guduwa ta ƙofar baya da Fillo ta bi, sai dai cikin rashin sa'a suna buɗewar suga police tsaitsaye a wajen riƙe da bindigu, kuma babu wata-wata suka shiga sakar musu harbi ratata, harbin ya sami kusan mutum huɗu su kuma sauran suka koma ciki da gudu don tsira da ransu, sai dai ko a lokacin tuni wasu ƴan sandan ma sun cika gidan.
Chapter 87 · 0% Book details