Sashe 173
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tayi shiru tana girgiza kai alamun takaici ya isheta."sam yarinyar nan bata da mutunci wallahi, ka duba fa Aliyu ka gani an fi ƙarfin awa guda da watsar da ni da tayi a ƙasan tiles ɗin nan, amma kalmar haƙuri ta gagara fitowa daga bakinta. alhalin tun duku dukun safiya aka baro gidan uba aka taho gidan ɗana cin arziƙi, to da yake ma dai ɗan Adam butulu ne, amma babu komai akwai Allah ai".
Maama tace,"kiyi haƙuri Inna Wuro".
"a'a wallahi ba zai yiwu ki cuce ni ba ki bani haƙuri, ke dai je ki kawai da mugun halinki".
Maama ta fice daga É—akin tana dariya.
Aliyu yazo ya kama Inna Wuro don ɗagata, ta miƙe tana faɗin,"ba abin nace zan bawa Zainabu shawara ba tace zata ƙullace ni, ko kuma ta zage ni, amma da sai in ce ku kai yarinyar nan gidan ruƙiya zance na domin Allah kenan".
Aliyu yay guntun tsoki,"zancenki kenan aljanu".
"to kaji ba, ina kuma ga uwarka na faÉ—awa. yanzu in ace jikar Falmata ce wallahi kaina tsaye zanje in bata shawarar nan. yanzu kai Aliyu ban da kai ma dai halin uwarka ka yo na rashin son gaskiya tsakani da Allah ai ka san wannan Æ´a dai tana da iskokai".
yay mata wani kallo yana nufar kujera ya zauna,"babu wani zancen gaskiya tun da ba gani kika yi ta tayar ba".
"to Aliyu har sai ta tayar za'a san tana da aljanu, ina batun watsota da suke yi a guje fa?, Kullum fa haka zaka ganta fuuuu kamar guguwa, haba a duba lamarin nan dai. ni ko da kaji na faÉ—i haka ba wai sonta ne bana yi ba wallahi".
Aliyu ya ɗauki remote yana dannawa yace,"to ba wasu aljanu, kije ki duba ɓarna tayi miki".
yana yin shiru tai hanyar É—akinta cikin hanzari tana maganganu. kuma tana shiga É—akin ta tarar da plastic bucket É—inta yashe a tsakiyar É—akin, murfinsa a tsakiyar gado yayin da aka yashe rabin dubulan da alkakin da ke cikin botikin.
ta É—ora hannu a saman ka kafin ta zube a gefen gado ta zabga salati.
"Jikar Zainabu ko masifa, to wallahi ba zai yiwu ba dole ma ƴar nan ta bar gidan nan yanzu babu ɓata lokaci, tun da dai gida Ɗana ya gina shi ba Zainabu ba, ina dalili jarabar sata har cikin ɗakina".
Aliyu na tsaye bakin ƙofa ta kalle shi tace,"ashe kasan hali shiyasa kace in zo in duba dukiyata, to kuwa dai ban yafe ba ka faɗawa Zainabu da shi uban yarinyar".
bai kulata ba ya sauke wayar kunnensa ya nufi gadon don tashin Farha, wacca ke ta bacci bama ta san wainar da ake toyawa ba. yasa hannu ya shiga tashinta, ta buɗe ido a hankali, ganinsa yasa ta miƙe zaune babu shiri tana murza idanuwa.
Inna Wuro da ke gyara bokitinta tana lissafa dubulan da alkakin da ke ciki tace,"da yake kai ne ai kaga ta tashi, ni kuwa da nake ƴar iska idan na tasheta ai sai dai ta yarfo min zagi. ba abin na bawa iyayenta shawara ba su ƙullace ni, amma wannan ƴa ai da gani ta narki ruwan mahaifa, ya kamata kuma a fita da ita ƙasar waje su fasa kanta su kwashe shi, shi Yusufun da ike karatun likitancin banza da wofi yay ai ya kasa gane ƴarsa ta kwankwaɗi ruwan mahaifa".
Farha ta sakko akan gadon tana ƙunƙuni ta fita daga ɗakin. direct part ɗin Ammi ta wuce, tana shiga parlo ta tarar da Ammi na cewa da Maama.
"wa ya faɗa miki ana taɓa kayan Inna Wuro, salon dai kija min jarfa. yanzu idan ta fara mita ta dinƙa yi kenan har sai an biyata kayanta, duk abin da kika ga tsohuwar nan ta ajiye a lissafe kayanta yake".
Maama ta turo ɗan ƙaramin bakinta, ta warware mayafin jikinta tana fito da uban dublan da alkakin da ta kwaso, ta buɗe leda tana zubawa aciki tana faɗin,"Ammi to ba ita bace nace ta bani sai ta ɗau guda ɗaya tal ta ban, ni kuwa tana fita na ɗauki rabona".
Ammi ta girgiza kanta,"to ai kuwa sai kiyi ki zuba a ledar ki ɓoye kafin ta biyo bayanki, don wallahi tazo wajen nan sai dai ku yi asararsa".
cikin sauri kuwa ta juye shi cikin leda ta saka a jaka. kuma kamar jira sai ga Inna Wuro ta faÉ—o É—akin tana faÉ—in,"to ina Zainabun?".
su ka haɗa ido da Ammi da ke kan kujera tana danna remote wurin sauya channel. Inna Wuro ta banka ma ta harara kafin tace,"ban ce fa lallai sai kin gaishe ni ba. saƙon Amadu nazo isar miki, yace wannan aljanar jikar taki ta tattara komatsanta ta bar masa gida kafin ya dawo, idan kuma kika yi kuskuren da yazo ya sameta acikin gidansa to sai dai kotu ta raba shi da iyayenta, saboda shi dai bakin uwa bai bishi ba da za'azo har gida aci mutuncin uwassa".
Ammi tace,"ai dama ba kwana zata yi ba, anjima kaÉ—an za'a zo a É—auketa".
"to shi yafi dai, yauwa ta bar gidan nan tun ba'a ƙure haƙurin ɗana ba, yo me ma na haɗa da ita da zata zo ɓangare na tayi min sata?, da ike ma dai ina da bala'in haƙuri shiyasa, don ma ban faɗa miki ba ne Zainabu, amma ƴar nan ƙafafuna biyu duk ta karya min, ban da Allah ya kawo Aliyu akan lokaci da ban san wa zai jona ni ba in samu in miƙe, amma dai na dai barwa Allah kawai".
Ammi tace,"kiyi haƙuri Inna".
"yo haƙuri ai dole tunda ni ba fitinanniya ba ce, kawai dai kija mata kunne kar ta ƙara zuwa gidan nan tunda batta da gado".
Ammi tace,"to".
"yauwa to sai anjima, zamu je wurin sarkin É—ori da Aliyu ne".
"Allah ya sauƙe".
"to amin Zainabu, na gode. amma ke ma dai sai kin rinƙa kulawa, in ba haka ba wataran tsaf zata jeho ki daga saman bene, tun naga aljanunta masu wurgi ne".
zata fita a ɗakin Maama ta buɗe baki, cikin ƴar ƙaramar muryarta tace,"a dawo lafiya Inna, Allah ya bada lafiya".
"amin in ma ba har zuci kika faɗa ba. ƴar banza da wofi me suffar ƴaƴan aljanu, kina fama da ƙaramar murya sai kace kukan mage, Allah ɗaya ma yasan manufar da yasa yayo ki a makauniya, sanyin tafiyar da aka ba ki ai ba'a banza ba, idan kin cuceni kin tsira kika cuci wani kafin kiyi taku biyu ai ya danƙo ki yaci ubanki. Allah dai ya jiƙan Uwarki ya gafarta mata, amma wannan halin dai ba nata ba ne sam".
ta fita tana ta zazzaga masifa, Maama da Farha kuwa sai dariya suke yi, bayan fitarta sai ga Ayan ya shigo, ya zauna kan kujera, bayan sun gaisa da Ammi take ce masa,"ni ai fushi nake da kai, yaushe rabon da kazo ka gaida ni?".
yana murmushinsa me kyau yace,"Ammi tare da Abie muke zuwa office shiyasa, kuma yau É—in mun makara wajen zuwa gun Ummi ne shiyasa ban shigo ba a lokacin".
sai ya kalli Maama yace,"ki taso mu tafi".
Ammi tace,"da wuri haka?, ba zai bar min ku sai dare ba?".
"Ammi zamu je dubo Maman su Antynmu ne".
Ammi tace,"Allah sarki wannan mata dai tana shan wuya, Allah ya kawo mata sauƙi".
"amin".
Ammi ta rako su har bakin gate, Farha kuwa sai da ta raka su har bakin motarsu, har sai da suka gaisa da Turaki sannan ta juya ta koma gida, suna yiwa juna bye bye ita da Maama.
"Abie kun gaisar min da Ummin?".
Maama ta tambayi mahaifin nata a lokacin da motar su ke hawa kan titi.
Turaki ya dubeta ta cikin mirror yace,"mun faÉ—a mata Maama".
sai kuma yace,"Maama ko dai muje asibiti?".
ta bar abinda take yi ta kai dubanta gare shi tace,"saboda me Abie?".
yay ɗan jim kafin yace,"ina ga kamar ayi miki aiki a maƙogoronki, Maama muryarki tayi ƙanƙanta da yawa, wanda ya saba da ke ne fa kaɗai yake iya jin me kike cewa farat ɗaya".
tayi knodding kanta tare da cewa,"Abie idan hakan yana damunka ayi min duk abin da kake so".
ya numfasa kafin yace,"ba komai zamu ci gaba da zuwa gaban ka'aba muna roƙon Allah".
tafiyar tasu tayi nisa acikin motar, yayin da suke hira jefi jefi, har sanda Turaki ya tambaye su,"ina da ina zan kai ku?".
da yake duk friday haka yake kai su gidan ƴan uwa da abokan arziƙi ziyara, ko kuma wani lokacin su yini shi da Ayan a maƙabarta wajen Fullo da Maama, sai in yamma yayi yaje gidan su Yusuf wajen Ammi ya ɗauko Maama da suke sauketa acan tun safe.
Ayan yace,"Abie muje gidan Anty Maijidda, kwana biyu bamu je ba, kuma last zuwa da muka yi mun barota bata da lafiya".
Turaki ya amsa masa da to, sai da suka fara tsayawa a hanya suka yiwa Æ´aÆ´an Maijidda siyayya kafin suka É—auki hanyar gidanta.
Turaki ya ba su kuÉ—i masu yawa su kaiwa Maijidda kamar yanda ya saba duk sanda ya kawo su. sai da yaran suka shafe kusan rabin awa kafin su fito tare da Maijidda wacca ta rako su.
hangota yasa Turaki fitowa daga mota, ya ƙarasa ƙofar gidan suka shiga gaisawa da ita, tana ta yi masa godiya akan irin aiken da yake bayarwa akawo mata ita da yara.
Maama na kama hannunsa ta riƙe yake tambayar Maijidda yaranta, ganin yau bai ga ko muutum guda ya rako su Ayan ba, da kuma ɗan ƙaramin ɗanta da ya zama kamar abokinsa, kasancewarsa irin yaran nanne masu saurin sabo.
Maijidda tace,"wallahi kaga wata tahfeez aka buÉ—e a bayan layin nan, shine aka kaisu can".
"har friday suke zuwa kenan?". Turaki ya tambaya.
tace,"ehh juma'a zuwa lahadi, tun safe sai yamma".
"masha'Allahu, Allah ya bada ilimi me albarka".
ta amsa da,"amin amin".
"to bari mu wuce, a gaida min da abokina".
tayi Æ´ar dariya tana faÉ—in,"Musaddiq sarkin magana, zai ji insha'Allahu, da sun samu hutu ai zan kawo muku su, sai su yini".
sai ta saka hannu tana share ƙwallar fuskarta tace,"Allah ya jiƙan Fillo".
Turaki da Ƴaƴansa jiki a sanyaye suka amsa da,"amin ya Rahman".