← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 176

Sashe 165

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya riga ya sani, faɗar ubangiji ce kullu nafsin zaa’iƙatul maut, Allah ya faɗi hakan har sau biyu a littafinsa me girma, duk wani bawa mutuwa tana kansa, duk wani me rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa, yaro ko yarinya, babba ko ƙarami, sabo ko tsoho.
ya sani Mutuwa dole ce, ya san mutuwa akan kowa ta ke, ka aikata sharri ko akasin haka zaka mutu, kana kan aikata daidai ne ko akasin haka, baka san a wani hali za'a ɗauki ranka ba, za mu mutu a yau, ko gobe  ko jibi, ko anjima ko yanzu, sai dai dukkanin mu babu wanda yasan a wanne hali zata riske shi, kai dai bawa baka sani ba! baki sani ba!

ya sani yin mutuwa ko ambatonta bai da daɗi, amma dole ne sai mun mutu, dole za mu koma ga wanda ya halicce mu, wajibi ne mu amsa kiran ubangijin mu mai son mu, mai ƙaunar mu, mai jiran tuban mu a ko yaushe, dole ne zamu bar duniyar da aka ara mana, haka dole zamu tafi mu bar duk abin da muke so, haka dole zamu kwanta a ƙabari.

kana tsaka da jin daɗin rayuwa mutuwa na iya zuwar maka, wani tazo mishi fuj’an, wani ta zo mishi idan yay fama da rashin lafiya, wani tari kawai zai yi, wani atishawa kawai zai yi, kuma da zarar ya furta Alhmadulillah sai Kaga a wannan lokacin an ɗauki ransa, wani yana sallah za'a zare masa rai, wani daga bacci shikenan za'a zare ran, sai dai ya farka ya gansa a ƙabari, gidan da yake na gaskiya, gidan kowa.

duk irin son mu da duniya wallahil azim sai mun barta, duk irin so da ƙaunar da muke yiwa juna wallahil azim mutuwa sai ta raba mu, Ya Qadeer kai mana kyakkyawan ƙarshe, Ya Rabbi kasa mu dace duniya da lahira Ya'ilahi! Ya Hayyu Ya ƙayyum, kasa mu mutu muna matsayin mutanen kirki, ba waɗanda zamu mutu duniya da mutanen cikinta na tirr da mu ba, ya Rahmanu kasa kar mu mutu da hakkin kowanne bawa akan mu, don mun san cewa baka yafe hakkin wani akan wani, ya jama'atul musulim mu yafi juna!, mu yafewa junan mu!, kar mu dinga ƙullar junanmu domin ba mu san lokacin da zamu yi tafiya me gaba ɗaya ba.

"ta mutu".
Khalil yay ƙarfin halin furtawa sauran ƴan uwansa da kowannen su ke tsaye yana so ya fahimci abin da ke faruwa.

"Kamar ya ya wai? Mecece mutuwa kuma?".
Sameer yay tambayar a rikice.

"da ma haka ake mutuwar?, ɗa zu fa muka gama hira da ita ko awa ɗaya ba'a yi ba, haba this is insane, wallahi Dr ɗin nan ƙarya yake, ya za'ai ma Maama ta mutu, me tayi?, laifin me ta aikata?, don Allah Mum a kira wani likitan ya dubata, don Allah a kira wani likitan ya zo ya tasheta".

idan ace ba kallon fuskar Nihal suke yi ba, za su rantse da Allah cewa ba ita tayi wannan maganar ba, don kwatakwata muryar ba tayi kama da tata ba, ta fito ne cikin wani amon sauti na ƙololuwar tashin hankali, tana rawa tamkar iska na kaɗata.
haka rayuwar take dama, hanya ɗaya ce da ita, ko kabi tafarkin gaskiya ko ka kauce duk dai ƙarshe waje guda kowa yake nufa, alkhairi ko sharrin da kayi kafin ka ƙarasa, shi zai zama shimfiɗa mai kyau ko mai muni a yayin da ka isa, sai dai fatan dacewa kawai.

"ka kira Baffan ku ka sanar da shi, sai ka kira min Samha da Zaytun, amma ban ce ka faÉ—a musu ba".

Mum tayi furucin ga Khaleel, wanda yake tsaye har yanzu hawaye sun gaza sauko masa.

a wannan lokacin kuwa Nihal na kan gawar Hajiya Madina, tana girgizata akan sai ta tashi, tana roƙon su akan su kira likita me hankali ya tashi mahaifiyarta, ai hirar da suka kwana jiya su na yi baya nufin wasiyya ta bar mata, ita dai azo a tashi Maama, don tace mata a ƙarshen watan nan zata fara yi mata order ɗin kayan kitchen ɗinta.

a wannan lokacin kuma Turaki ya iya ɗago da kansa, ya kalli Nihal ɗin sannan ya kuma kallon fuskar gawar, sannan ya ƙara kallon zanin da aka rufe gawar hannun Fullo ke damƙe da shi, sannan ya kai ƙwayar idonsa kan Mum da ke zaune kanta a ƙasa, hawaye na saukowa suna zuba akan kayan da ke jikinta, sannan ya kalli Sameer da ke duƙe ya rufe fuskarsa da dukkan tafukan hannunsa da alama kukansa yake so ya tsayar tukunna ya ɗago ya ƙaryata mutuwar, sannan ya kalli Khalil wanda ke jingine a jikin wadrobe waya riƙe a hannunsa ya ƙurawa gawar ido, gashin idonsa ba ya ko ƙiftawa.

a wannan lokacin ne kuma hankalinsa ya fara gaya masa wataƙila zai sauya ma'anar rabuwa ta mutuwa a yau, don baya tunanin akwai abin da zai raba shi da gawar nan da yake riƙe da hannunta, Maamansa ba, babu me raba shi da ita.

*BAYAN AWA BIYU.*
a cikin wannan awannin, labarin rasuwar Hajiya Madina ya karaÉ—e cikin garin gombe, da sauran Æ´an'uwa da suke na kusa da na nesa.
lokaci guda tarin al'umma suka shiga ɓulɓulowa su na sauka a gidan Alƙali Dikko domin yin ta'aziyya, mutuwar da ta taɓa manya da ƙanan yara.

cikin gidan ya ɗauki shiru, a zazzaune ake wasu na kukan fili yayin da wasu ke kukan zuciya, domin tabbas anyi rashi, an yi rashin mace mai tsanani son mutane da kyautata musu, mai kirki da sauƙin kai, macen da ke da tsananin kyautatawa marayu, macen da ba'a faɗa da ita acikin mutane in har ba ƴaƴanta aka taɓa mata ba, macen da a tsawon rayuwarta babu wanda ya taɓa buɗa baki yayi kuka da ita, ya kuma ya faɗi aibunta.

a wannan lokaci ubangijin da ke da iko da zuciyar kowanne bawansa, shi kaɗai ya san adadin alhinin da ke cikin zuciyoyin ahalin gidan Alƙali Dikko, musamman yaran, waɗanda suka ruɗe da koke-koke, banda Samha da ke ta aikin suma tana farfaɗowa ta ƙara komawa.

"an gama yi mata wankan, ku faÉ—a musu za'a shigo da gawar ciki su yi mata adu'a".

"ina Hajiya Ramlan take?".

"yanzu ta tashi, Samha ce jini ya yanke mata, ana tunanin ko ɓari tayi".

a lokacin wani tsoho ya leƙo parlon yace,"to ina yaran su ke ne?".

"Baba Musa gasu nan fa, ku shigo da ita É—in".

ya juya fuskarsa daga waje yana kallon mutanen dake tsaye yace,"sai kun É—ago makarar da kyau fa, yawwa kai É—an karkata ta can".

mutanen maza su huÉ—u suka shigo parlon da gawar, da yake acan part É—in nata wasu Kakanninta mata da su BoÉ—ejo suka yi mata wanka.
su ka ƙarasa da gawar suka ajiyeta a tsakiyar yaran da ke zaune a ƙasan carpet, wacca Zaytuna ce kawai babu sai Samha da aka yi asibiti da ita yanzu.

Baffa ya ƙaraso wajen ya zauna shima, zaman nasa babu wuya kira ya shigo wayarsa, daga can ɓangaren Zaytuna da ke ta kuka tace,"Baffa don Allah kar akaita sai na zo, ya tafi ya nema mana ticket yanzu zamu taso Baffa".

"Zaytun kiyi haƙuri kinji ko, ki tayi mata adu'a kawai, idan aka ce za'a jira ku lokaci zai ƙure, kinga magariba na gabatowa".

bayan gama wayar ya ɗaga kai yana cewa da Yayar Hajiya Madina,"Asiya kirawo Ramla don Allah, tazo su yi sallamar ƙarshe".

"Baffa don Allah ku bar mana ita a haka ba sai an kaita wani wajen ba, mu zauna da ita a haka don Allah".

Yayan Hajiya Madina Baba Nafi'u yace,"tun É—a zu kake ta surutai Sameer, ya isa haka, kai musulmi ne ya kamata ka yarda da wannan mutuwar, batun a bar muku ita babu shi domin binne gawa wajibi ne".

"don Allah Baba ku bar ta ko zuwa da safe ne, ƙila fa baccin ne yay mata nauyi da yawa, ko kuma shi likitan ne bai bincika da kyau ba, amma ɗazu mu ka gama hira da ita wallahi, wallahi lafiyarta ƙalau bacci kawai tayi tace idan Saamirawo(sirika Fillo) tazo to a tasheta".

Nihal ke maganar duk a gigice.

Baba Nafi'u ya ƙara cewa,"ku yi haƙuri kin ji Nihal, duk wani abu da ya ke faruwa tsarin ubangiji ne, namu tawwakali ne da addu'a, don haka ku yiwa mahaifiyarku adu'a".

Baffa ya numfasa a hankali ya shiga kiran sunan yaran nasa da sirikan nasa É—aya bayan É—aya.

"Khalil, Samir, Nihal, Halima, Ilham". sannan ya kalli Turaki daga ƙarshe yace,"Muhammad ku daure zuciyoyin ku, kuyi tawwakali ga Allah, wannan ita ce mutuwar, haka take, haka kowa yake haƙura da ita, haka take riskar kowanne bawa ba sai an shirya mata ba, mu ma nan duk jiranta muke yi. yanzu lokaci na tafiya, mutane na can a waje su na jiran a fita da ita, na san abin da kowannenku yake ji, na san raɗaɗin da zuciyarku ke yi muku. ku yi mata adu'a, wannan kukan da ku ke yi da musawar da ku ke yi ba gata bane a wurinta, zallar soyayyar da za ku nuna mata shi ne kuyi mata adu'a, wannan jinkirin kaita ɗin da ake ba alkhairi bane agareta".

Maganar ta Baffa ta doki kunnuwan kowannen su, furucin da yay akan soyayya, sai kawai suka ji su na shuÉ—awa zuwa duniyar baya, wani lokaci me tsayi da ya shuÉ—e, kamar haka ne, kamar wannan lokacin su na zaune da ita take faÉ—a musu...
_"ku nuna min soyayyar ku ko bayan raina Ƴaƴana, ina nufin kar kuyi kuka da rashina, adu'a za ku yawaita yi min"._

Turaki ya matsa kusa da makarar, Baffa ya kalle shi, zuwa yanzu idanuwansa ƙamas babu alamun danshi na hawaye, haka fuskarsa tayi fayau babu wani abu da zaka tsinta a ciki illa tsananin tashin hankalin da yake ciki. haka shi ma Khaleel, wanda tun ɗa zu sai ayanzu da ya ɗora hannunsa akan makarar sannan hawaye yay nasarar gangaro masa, sai dai yay saurin saka gefen rigarsa ya goge.
Chapter 165 · 0% Book details