Sashe 88
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"raise your hands up".
su shidan da suka rage ba'a harba ba suka É—aga hannayensu sama time É—in da Dsp yay arresting É—insu.
Turaki kuwa tun shigowarsu babu ta kan wanda yabi sai laluben inda zai ga Fillo, haka ya koma kamar wani zautacce ya shiga can ya fito ya faɗa can ya leƙa can, kaf babu inda bai duba acikin gidan nan bai ganta ba, sai ga shi ya faɗo parlon kamar an jefo shi yana zazzare ido ko zai ganta anan duk da perlon ya fara dubawa.
jiri ya ɗebe shi ya tafi ya faɗa kan wata kujera dake wurin, yasa hannu ya dafe kansa da yake jin yana barazanar tsage masa, ya rumtse idonsa sosai yana rasa me ke masa daɗi a duniyarsa, wucewar daƙiƙa ɗaya ya ɗago kai ya buɗe idonsa wacca ƙwayar ta kaɗa tayi jawurr ya sauke kallonsa akan Dsp yace,"yallaɓai banfa ganta ba, bata cikin gidan nan yallaɓai".
muryarsa ta fito cikin bala'in rauni kamar zai yi kuka.
Dsp na tsaye daga gefe yana kallonsa bai ce masa komai ba, har sai lokacin da wasu Æ´an sanda guda uku zo, waÉ—anda sune aka saka su nemo Fillo a sanda suka shigo gidan.
"yallaɓai babu wurin da bamu duba ba acikin gidan nan kaf babu yarinyar".
Dsp ya kalli tawagar su Amir da suke tsaye hannaye a sama idanu duk sun raina fata, ya sakar musu wata uwar tsawa yace,"ku faɗa min ina ku ka ɓoye yarinyar?".
da farko duk shiru suka yi sai da ya ƙara doka musu tsawar da tafi ta farko tukunna ɗaya acikinsu yana karkarwa yace,"mu ma bamu san inda ta ke ba".
yana rufe baki yana jin saukar harbi a gwiwarsa, ba shiri ya saki ƙara ta azaba yana duƙe a wajen, tuni zufa ta shiga haɗo masa yana faɗin,"wallahi bamu san inda tayi ba ta gudu tun ɗazu, muna cikin nemanta ne ma ku ka zo".
furucin nasa yasa Turaki miƙewa daga kan kujerar da yake a kiɗime yana faɗin,"what!, ta gudu?, baku san ina tayi ba?".
ya furta yana jin kamar zuciyarsa zata buga.
Dsp ya ƙara harbin ƙafar wanda yay maganar, azaba ta ƙara ratsa shi ya kuma ihu wajen faɗin,"dan Allah kayi haƙuri". Dsp ya ƙara sakar masa wani a hannu, a wannan karon ko motsawa bai yi ba don tsabar azaba, maganarsa ta fito a hankali yana cewa,"na rantse da Allah ta gudu tun ɗazu".
Turaki yana shirin sauke ƙwayar idonsa kan mutumin kawai sai Allah ya kai idonsa kan Amir, yay saurin maida kallonsa kan Amir gaba ɗaya yana ƙare masa kallo da son tabbatar da abinda ƙwayar idonsa ke gani.
cikin kansa ya haska da hoton lokacin da yake tsaye gaban Fillo har yana riƙe ma ta hannu har zuwa lokacin da ya juya ya bar wajen.
"You!". Turaki ya faÉ—a in shock. sai kuma ya nufi wurin Amir gadan gadan kamar zakin dake cikin yunwa ya ga abinci.
yana zuwa yasa hannu ya shaƙi wuyan Amir, ya dinga tura shi da baya har sai da ya kaisa bango ya gwara kansa a jiki. "waye kai?". Turaki ya tambaya .
tun Amir bai basa amsa ba ya dunƙule hannunsa ya bawa fuskarsa wani mahaukacin naushi wanda yay sanadiyar ɗaukewar ji da ganin Amir na wucin gadin, hakama haƙorinsa ɗaya ya tsinke ya fara lilo.
Amir ya ɗago kansa a galabaice sai dai tun bai gama buɗe idonsa ba Turaki ya ƙara sakar ma fuskarsa mugun naushin da yafi na farko, kan Amir yayi ƙasa jini na zuba ta hancinsa. Turaki ya ƙara yin kukan kura ya ɗago da fuskar tasa ya kuma naushin fuskarsa a gefen ido, take jini ya taru cikin idon Amir, haka ma jini ya shiga fita ta hanci ta baki.
Amir yay yunƙurin ƙwatar kansa amma inaa lokaci ɗaya Turaki ya damƙi hannu da wani irin ƙarfin da bai san yana da shi ba barƙala hannun har sai da hannun Amir ya ɓalle.
a taƙaice dai Turaki sai ya koma kamar mahaukaci wajen dukan Amir, ya koma tamkar zakin da ya shekara ba abinci ya kuma samu abinci a daidai lokacin da yake so, naushi yake ta kaiwa fuskar Amir hagu da dama cikin ƙaraji yana tambayarsa,"who are you?".
sai da fuskar Amir ta kumbura tayi suntum babu kyan gani, ko'ina ya farfashe banda uban jini dake zuba ta gefen idonsa, tukunna Turaki ya bar fuskar tasa ya kai shi ƙasa yana tattaka ruwan cikinsa, yasa ƙafa ya dako shi ta can ya doko shi ta can, yay fatali da shi ta can, ya jefa shi ta can ya gwaru da bango, haka Turaki yayta ball da shi kamar wanda ya samu ball ɗin gaske.
tun Amir na iya ihu har yazo ya daina, tun yana buÉ—e baki yana uban nishi da son yin magana har ya kasa, shi kansa so yake yace da Turaki who is he, dan wannan dukan da yake masa ko uwarsa ya kashe sai haka.
da Dsp yaga dai Turaki na ƙoƙarin yin kisan kai yace da ƴan sanda dake tsaye,"ku dakatar da shi".
amma me ƴan sanda uku akansa sun kasa ƙwace shi daga kan Amir, suma ɗin duk sai da ya watsa su gefe yana miƙewa cikin huci da cewar duk wanda ya ƙara zuwa kusa da shi sai ya haɗa da shi.
bai ma san sanda yasa bayan hannu ya kwaɗe police ɗin dake ƙara yowa kansa ba, ya fizgo shi gabansa ya zare bindigar dake gaban wandonsa ya koma ya haye ruwan cikin Amir, ya cije fuska yana ɗaga bindigar ya bugawa Amir a kansa, ta-ke jini da ƙwaƙwalwar Amir suka haɗe wuri guda yaji kamar kansa babu komai, tukunna Turaki ya saita ƙirjinsa da bindigar yana bala'in huci yace,"for the last time i will ask you, tell me who are you?, in ba haka ba wallahi sai na sakar maka harbi a zuciyarka".
in ace da damar magana Amir zai yi, to amma ankai stage ɗin da yatansa ɗaya ma ba zai iya motsawa ba, balle kuma ya buɗe bakinsa da uban jini ya taru aciki yana tsiyayowa ta waje, shi da wannan mahaukacin dukan da Turaki ke yi masa ma da harbe shi ɗin yayi da ya huta, kuma baya jin ba zai mutu ba muddin Turaki ya ƙara dukansa, azzakarinsa kansa jini yake saboda Turaki ya daki wajen ya kuma ya daka yasa hannu ya kama ya murɗa, to ko da iyaka haka aka barsa ai yana jin sun gama ɗaukarwa Fillo fansa dan yasan ko ace ya tsira da ransa to tabbas a hoto zai tashi dan yana da yaƙinin Turaki ya gama kashe masa gaba, bai da burin da ya wuci a yanzu irin ya buɗe baki ya bawa Turaki haƙuri, kuma yaga Fillo ya nemi yafiyarta.
Turaki na ƙoƙarin sakin bullet a ƙirjin Amir Dsp ya taho da sauri ya bige hannunsa bullet ɗin ya sauka a kafaɗar Amir, Amir ya saki wata gigitacciyar ƙarar da shi kaɗai yaji kayarsa babu wanda yaji, don hatta wurin fitar sautin muryarsa Turaki ya gama kashe shi.
Dsp ya fizge Turaki daga kansa yay gefe da shi yana faÉ—in,"wa ya baka izinin yin harbi?, are you a police?, to ko mu ba'a bamu umarnin yin harbi kai tsaye ba".
Turaki da duk ya gama ficewa a hayyacinsa yana ta uban huci yace,"yallaɓai na taɓa ganinsa a ƙofar gidanmu tare da ita, yafi ƙarfin rabin awa awajen kafin ya ƙyaleta ya tafi, and am sure shine ya ɓoyeta ma a yanzu, ka tambayesa inda ya ɓoyeta tun ban ƙarasa shi ba wallahi".
Dsp ya dafa kafaÉ—arsa yana faÉ—in,"calm down mana, yanzu idan muka kashe shi waye zai faÉ—a mana inda ta ke?, to dole mu bi komai a hankali ba wai mu É—auki mataki mai gaba É—aya ba".
Turaki ya dunƙule hannayensa duka biyun yaja da baya yana zaunawa kan kujera tare da fesar da zazzafar iska daga bakinsa.
ya rumtse idonsa sosai yana É—aga kansa sama, ba komai yake hangowa ba sai sanda Amir ke tare da Fillo, muryarsa na fita a hankali yace,"Fulani where are?, bana ce miki zan zo ba yanzu, why did you leave?".
sai ya rumtse idonsa yana tunawa da maganar da ta faɗa masa,_"wai sai sunyi amfani da ni"._ bai san lokacin da daki hannun kujerar ba har sai da ƙashin hannunsa yayi ƙara.
ya kifa kansa a hannun kujerar yana faÉ—in,"ina kika tafi?, Fulanii why?, why Fulani?, how do you think i will survive without you by my side?, please tell me where you are zan zo na É—auke ki ko da ace daga na ganki zan mutu".
ya faɗa a sanda wannan jarumtar tasa ta karye, raunaninsa ya wanzu, kukan dake can ƙasan zuciyarsa ya ɓalle, hawaye ya sauko masa ƙwayar idonsa na haska masa hotunan faruwar abubuwa kala-kala a tare da Fillo.
"idan kika tafi da wa zanyi rayuwar farin cikin gidan aure irin wadda na tsara mana ni da ke kaɗai?, wa ye zai tayani nemo Mum idan ba kya nan?, dan Allah karki min nisan da ba zan saka miki da ceton rayuwata da kika dinƙa yi ba".
sai kawai ya cije leɓensa na ƙasa ya kuma yin kukan kura yay kan Amir a fusace, da hanzari police suka ruƙo shi akai waje da shi.
*A dai-dai wannan lokacin.*
gudu suke sosai babu waige babu tsayawa har sai da suka ga cewar sun shigo cikin gari, kuma a lokacin ne Fillo ta faÉ—i tana kuka tace,"Mum ba zan iya ba na gaji".
tausayin kansu ya kawo zubar sabon hawaye saman fuskar Hajiya Ramla, ta duƙa ta kamo Fillo tace,"ki daure mu ƙara yin gaba, kinga nan wajen ma ba kowa zasu iya kama mu anan".
Fillo tace,"Mum ki barni ke ki tafi, su Adda Zaytuna suna can suna jiran dawowarki, Turaki kullum sai yayi kuka akan rashinki, dan Allah ki tafi Mum ƴaƴanki na buƙatar ganinki a raye".
Hajiya Ramla ta dafe kanta da ta-ke jin wani abu na mata yawo aciki, so ta-ke ta ɗauki magangun yarinyar ta saka su a ɓangaren tunaninta ko Allah zai sa ta gane abinda ta-ke cewa.