Sashe 27
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ƙasa ta duƙa ta tattara takardun ta mayar cikin file ɗin da suka faɗo, sannan ta mayar cikin wata drower daban da wadda suke ciki da.
ta fita daga ɗakin jiki a saɓule, da ƙyar ma take yin tafiyar tamkar me ƙarancin jini a jiki, tana saukowa daga upstairs ɗinne cikin tsautsayi ta gurɗe ƙafa.
bakinta ya furta bismillah kafin ƴar ƙarar da ta saki ta biyo baya. cikin jin zafi da raɗaɗi na lokaci guda ta riƙe ƙafar tana cije fuska.
gurɗewar ba ƙarama bace, dalilin da yasa idanuwanta suka cika da tarin hawaye kenan, wani sabon kukan ya ƙaru akan wanda zuciyarta bata gama yinsa ba, sai da ta ɗauki kusan 4minutes sannan ta tashi ta sauko da ƙyar sai ɗingisa ƙafar takeyi, sai da ta kashe light na parlon tukunna ta bar side ɗin.
a ƙofar ɗakin me gadi ta tarar da mutumin, baƙi ne kamar yanda Hajiya Madina ta sanar mata, yana da curar ƙasumba, fuskarsa kuma sam babu fara'a. me gadi dake jin radio ganinta yasa shi yin murmushi, ta rissina ta gaishe shi ya amsa mata yana tambayarta ya aiki, ta amsa masa da lafiya.
sannan ta tsuguna a gaban mutumin da ko inda take bai kalla ba tun zuwanta, bata sani ba ko haka yake ko kuma ita yakewa hakan dan ta ɓata masa lokaci oho. "ina yini".
ya kalleta ta wutsiyar ido, kamar ba zai amsa ba can kuma yace,"lafiya".
ta fito da hannunta daga cikin hijab wanda ke ɗauke da file ta miƙa masa tace,"ga shi wannan tace a baka".
sai da yayi mata wani kallo kafin ya warta, dan ba zata kira hakan da karɓa ba sai dai warcewar, hakan kuma ya ɓata mata rai, ta miƙe cikin ɗaurewar fuska.
tafiyarta zata yi, ba zata ƙara ko da ɗigon minti anan ba, cewar ita ƴar aiki ce hakan ba yana nufin a dinga wulaƙantata ba. ta sani ita ba wata bace, ba ƴar wani bace, amma wallahi tafi ƙarfin wulaƙantawar kowanne kalar mahaluƙi, talauci ai ba hauka bane, dan haka yanda bata wulaƙanci haka ba zata yarda a wulaƙanta matsayinta ba ko da wasa, ita ƴar mutunci ce kuma da darajarta, aiki suke ake biyansu ba wai roƙo suke ba.
saboda haka yanda ya warce bai karɓa da arziƙi ba, haka itama zata bar wajen ba tare da ta jira nasa saƙon ba inma yana da shi, ai dama ce akai kawai ta ba shi, to idan ma yana da wani abin faɗa sai ya jira Hajiyar ta dawo ya bata, amma ba dai ita Fillo ta jira saƙonsa ba.
abunda bata sa ni ba a wannan lokacin shine, tun yunƙurawar da tayi zata tashi shi kuma ya bar wajen, saboda haka ko da ta kalli inda ya zauna taga babu shi bata yi wani mamaki ba, tayi tsammanin faruwar hakan.
tace da me gadi,"Baba kayi haƙuri dan Allah ban miƙo maka abincinka ba, wallahi ina cikin aiki ne sai yanzu na samu sarari amma bari naje na kawo maka yanzu".
Tsohon ya washe bakinsa da duk haƙoran da suka ɓaci da goro yace,"laa babu komai ƴar nan, karki damu".
juyowar da zata yi kawai taga mutum tsaye a bayanta ya harɗe hannaye a ƙirji, da tsananin mamaki ta ke kallonsa from head to toe, baki buɗe ta kasa rufewa, what would she call the situation she got into ?, tasan dai gefe ɗaya farin ciki ne ya lulluɓeta, to amma ɗaya yanayin fa?.
idan tace ba ta kewarsa tayi ƙarya, idan tace bata yi murnar ganinsa ba tayi ƙarya, idan tace bata son ganinsa ta yaudari kanta.
cikin wani irin emotions da ta ke jin kanta tayi saurin saka tafukan hannunta ta rufe fuskarta, murmushi kawai take yi, irin murmushkin nan me faÉ—i dake fallasa kyawun fuska, wani daÉ—i ne kawai ke ziyartarta, ji take yi tamkar an mata albishir da kujerar makka.
tana son ganinsa, tana ta so ta kasance da shi amma babu dama, lokaci yayi mata ƙaranci tunda ta fara wannan aikin, rabon da ta saka shi a ido tafi sati uku, har Kaka ta gama ciwonta ta gama basu haɗu ba duk da cewar kullum sai yazo dubiya, sai dai idan ta koma Kaka ta bata sallahun saƙon gaisuwarsa daya bar mata.
Allah ya sa ni sai yanzu da ta gansa take jin tamkar ta É—auki shekaru bata gansa ba, kuma Allah ya sa ni a yanzu ji take yi kamar ta rungume shi don tsananin farin ciki, ta ya ya?, ta ya ya zata nuna masa irin jin daÉ—in da ta yi na ganinsa?.
ta ramin yatsunta take hango fuskarsa da gaba É—aya babu walwala, lokaci guda tasha jinin jikinta, wanne irin bayani zata yi masa ya fahimta?, ko me zata ce ba lallai ya gane ba, abu É—aya kawai tasan yana ransa shine yanzu ta fifita aiki akansa.
sai kawai jikinta yay sanyi, still hannunta na rufe da fuskarta tayi ƙasa da kanta tana jin kamar tayi kuka. bata yi aune ba taji faruwar al'amarin da bai taɓa faruwa ba a tsakaninsu ita da shi, hannunta ya ruƙo, wannan hannun nata da bai taɓa riƙewa ba tsawon lokacin da suka ɗauka tare, me zata yi yanzu?, zata sakar masa hannun ne ya sauke kamar yanda taga yana ƙoƙarin yi ko kuwa zata hana hakan?, domin gani ta ke kamar ba zata iya haɗa ido da shi ba, kunyarsa ta ke ji sosai, kunyar riƙe ma ta hannu da yayi, tana ganin tamkar sun aikata wani babban alfasha ne.
idanuwanta suka ciko da ruwa, ta shiga ƙiftasu a hankali, dai-dai lokacin kuma da ya sauke hannun nata daga kan fuskarta, kallonta yake har yanzu, ya kasa ko da ƙiftawa, ji yake kamar ya ɗauketa, ji yake kamar ya sureta ya kaita duniyar da babu kowa aciki daga shi sai ita.
a ƙoƙarinta na zame hannunta daga nasa ta ɗago ido tana kallonsa, kamar ruwa ta ke gani anasa idon shima?, kamar yana so yay kuka ne?, kamar rauni ne take gani a ƙwayar idon nasa?, kenan shima yayi kewarta har irin haka?.
shi kuwa kallon da take yi masa gani yake kamar tana masa kallon tuhuma ne, me yasa yazo nan?, me yasa ya biyota?, me yasa bai tambayi izininta ba?, ai tun kamin yazo É—in sai daya shiryawa amsa waÉ—annan tambayoyin, ya kuma san zata yi masa rangwame ko da zata hukuntasa.
ya rumtse idanuwansa tare da ƙara riƙe hannunta sosai yana murzawa sannan yace,"kiyi haƙuri, na kasa ci gaba da jurewa shi yasa na biyo ki".
cikin sanyayyar murya tace,"hannuna".
sai taji yace,"ba kuma zan iya sa ki ba Halimatu, wallahi ba zan iya ba. dan Allah ki barni".
ba tare da ta É—ago kanta daga sunkuyen ba ta raba hannayen nasu, sannan tace,"me yasa to baka tambayeni ba kafin...".
bata ƙarasa ba ya katseta,"naga zan mutu shi yasa, kuma bana so na mutu ban mallakeki ba, ba kuma na so na mutu ba muyi sallama ba...ina ta son ganinki, ina ta so nayi magana dake, amma wannan aikin yabi ya toshe kowacce ƙofa, ita kuma zuciyata sai zafi take tana kukan rashinki, shisa yau nace babu abinda zai min shamaki da ganinki ko da ace fadar sarkin gombe kike aiki yau sai na shigeta na ganki, daga nan kuma nima sai na nemi taimakon a ɗaukeni aikin muke yi tare ina rage miki, ta yanda zanke samun ganinki ko da yaushe...nazo da complete takarduna, please kiyi min iso ko Allah zai sa a dace".
ta kalleshi tana murmushi, da gaske yake babu wasa a maganarsa neman aikin yazo. ta kalli takardun ta ƙara kallonsa tukunna tace,"ni babu takardun komai aka ɗauke ni".
yace,"arziƙin Kaka kika ci shine dalili".
ta juya idanu sannan tace,"ko da babu Kaka ni banga ana É—aukan me wanke-wanke da shara da takardu ba".
yace,"kuma dama na iya wanke-wanke sosai ba".
ta saki dariya sosai tana ɗora bayan yatsunta akan bakinta. yana kallonta har yanzu fuskarsa bata gama saki ba yace,"dariya na baki?, Allah da gaske na iya wanke-wanke, kuma ki tambayi Inna kiji, idan na wanke kwano har ƙyalli yake ya dawo kamar sabo, kuma na tabbata na fiki iyawa...saboda haka nasan idan suka ɗaukeni a kwana ɗaya zasu bani ɗaki a gidan nan, wataƙila ma ke su kore ki, kuma dama haka nake so dan wallahi bana ƙaunar wannan aikin".
tayi wani murmushin tace,"kaga ni kuma ina sonsa, tunda da kuɗin muke rufawa kanmu asiri...yanzu haka ma Kaka ta kusa siya min ƙaramin fili da kuɗin da ake ajiyewa".
ya ɗan kauda kai gefe sannan ya dawo yana ƙara fuskantarta. "sau nawa kike aikin ruwa?". ta juya idanu sannan tace,"ummm ya danganta, ina wanke kwanuka kuma zanyi girki idan Adda Zaytuna bata yi ba, sannan kuma in wanke banɗaki 6, shikenan".
"shikenan!, wannan yawan aikin shi zaki kira da shikenan Halimatu?". ya maimaita kalmar da mamaki.
ta É—aga gira,"eh, ai babu wahala tunda ba É—auda suke yi ba, nan da nan nake kammalawa na tafi É—aki na huta...saboda haka ka bar damuwa watarana sai labari".
yace,"balle ma kin kusa ki daina, very soon insha'Allahu...nayi mafarki na zama É—angote".
ta waro ido tana kallonsa, ya ɗaga kai yace,"da gaske, wai na koma Ɗangoten Gombe, na aureki mun bar ƙasar gaba ɗaya, muka ajiye Inna da Kaka a saudia mu kuma muka wuce London Honeymoon".
tayi far da ido ta maimaita kalmar, "Honeymoon, kamar na taɓa jin wannan kalmar amma na manta aina".
"zaki ma santa ne lokacin da mukayi aure, Allah Halimatu na aureki da Uwar kuɗina a yawon shaƙatawa kawai zamu ƙare rayuwarmu, wani banzan aikin gida duk ba za kike yi ba".
tasa hannu cike da kunya ta rufe fuska,"ni fa yarinya ce nace ka daina faÉ—a min kalmar aure".
yay mata harar wasa yace,"kin manta É—azu kika zo duniyar...ai na tabbata a karatun aure babu wanda ba ki sani ba sai dai ki raina min wayo, sai kace ba aminiyar Maijidda ba".
ta danne dariya tace,"me kake nufi da Maijiddan?". yace,"oho".