← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 176

Sashe 98

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaka tace,"bafa zance ake na ki dawo da shi hannunki ba, kije ya ganki yasan kina raye kuma kina cikin ƙoshin lafiya shine maganar da nake yi miki".
Ummi tace,"ba yanzu ba Dada".
Kaka ta gyaɗa kai tace,"ai shikenan ban san lissafin da kike yi ba. ni Allah yasa ma ta hanyar arziƙi Hayyo yayi kuɗin da aka ce  yayi".
Ummi tace,"ni banma yarda da yaron da ya faÉ—a ba".
Fillo tace,"Ummi da gaske ne fa, ai sanda ku ka tafi gidan Inna Azimi munje ni da su Badariyya, da muka shiga matan gidan suka ce ai kusan wata huÉ—u kenan da suka sayi gidan, masu gidan sunyi kuÉ—i sun tashi, to ni naso ma na tambayi inda suka koma kawai na fasa".

Ummi dai bata ce komai ba tayi shiru, ita ai banda ma dai bata son musawa maganar mahaifiyarta ai bata ga me zai sa su ƙara komawa Taraba ba a rayuwarsu, tunda Allah baisa sunyi dacen dangi ba, ita bata yi dacen miji ba, ƴan'uwan Kaka kaf ba wani kula suke da ita ba, kamar ma ba ciki ɗaya suka fito ba ayanda suke nuna mata, kansu da matansu kawai suka sani, dalilin da ya dawo da Kaka nan gombe kenan ta samarwa kanta mafita na neman aiki a gidan sarki, daga nan kuma ta koma gidan Dikko ga kuma matsayin da Allah ya kawo su ayau.

Maijidda ta shigo parlon bakinta ɗauke da sallama, su Kaka suka amsa mata ta nemi wuri ta zauna tana kallon Fillo dake jikin Ummi tana hararta da cewa,"Ummi dan Allah ki daina ɗora wannan ƙatuwar abar a jikinki".
Ummi na murmushi tace,"autar guda?".
Maijidda ta taso ta taho tazo itama ta É—ora kanta a kafaÉ—ar Ummi tana cewa,"Ummi to nima ai autar ce".
Fillo tasa hannu ta tureta tana faɗin,"dilla ɗaga min uwa, da wani ƙaton kanki anan zaki ce zaki kwanta jikinta salon kija kafaɗarta tayi ciwo".

Maijidda ta harareta tana mayar da kanta wurin Kaka tace,"Kaka Yami tana gaisheki, wai ki bada wannan saƙon da za'a kawai Baba Huraira zata je gidan gobe".
Kaka tace,"aiko gwara da Allah yasa ta tuna min, jeki ɗakina ɗauko wannan baƙar jakar tawa ta gado ki kawo min".
Maijidda ta shiga ta ɗauko jakar ta dawo, Kaka ta ɗauko saƙon ta bata tana yi mata bayani. sannan ta ɗora da ce mata,"yauwa kuma ki faɗa mata jiya fa an karɓo kuɗaɗenmu na wajen matsiyacin yaron can, an karɓo miliyan shidan duka wallahi".

Maijidda tace,"shege ai ni naso jefe ɗan iska akayi kowa ya huta da annoba". sai kuma cikin tsokana tace,"umm in iya bakina kar Fillo ta ƙullace ni".
Fillo ta miƙe a jikin Ummi tana hararta tace,"banza kawai". ta faɗa tana tashi ta wuce ɗaki.
Ummi tace da Maijidda,"kin fara zuwa yiwa su Hajiya Madina aikin?".
tace,"ehh Ummi tun washe garin ma da ku ka taho ai".
Kaka tace,"to Maijidda sai ki kula da Allah, na san ki kema hankali da natsuwa ba daga nan ba, dan haka ki iya zamanki da mutanen nan, ki zama me gaskiya da amana da kula da aikinki, kina ganin dai ta dalilin iya zama da su da Fillo tayi alkhairin da suka yi mana, bacin haka wa zai ɗauki gida sukutun guda ya bamu kyauta?, waye zai tsaya tsayin daka akan a karɓar mana hakkinmu wajen wancan azzalumin bawan?, aini babu abinda zance da Hajiya Madina sai dai ubangiji yayi mata sakayya da gidan aljannah, mutuncin matar nan ya wuce duk mutum yake zato wallahi".

ƙarar wayar Kaka ta katse maganartata, ta ɗaga tasa a kunne ba tare da ta san waye me kiran ba dan bata iya karanta sunan ba. sai bayan kuma ta ɗaga ɗin ta ɗau muryar Dr Yusuf daga can ɓangarensa da yay sallama, bayan gama gaisawa ta tambayesa iyalin da mutanen gidan sannan yace ta bawa Ummi.
Ummi na murmushi ta amsa sallamarsa tace,"Shikenan kuma sai É—ana ya manta da ni".
Dr Yusuf ya sosa ƙeyarsa yace,"na isa na manta dake Mommi, wallahi kullum sai munyi kewarki, Mommi ban san me yasa kika ƙi yarda kici gaba da zama a wurinmu ba, ko mun miki laifi ne Mommi?".
Ummi tace,"kul Yusuf naji ka ƙara ambatar kun min laifi, ni dai kawai abinda nake so ku sani shine har duniya ta naɗe ba zan manta daku ba da alkhairin da ku kai min,  ina nan zan ƙara zuwa na musamman in ƙara godiya, ina jikata Farha?".

Dr Yusuf yace,"tana lafiya Mommi, jiya ma Nuratu ke cewa tana so tazo ta gaida ke, to kuma sai naji kamar Maijidda tace kun bar can gidan Alƙali".
Ummi tace,"ehh wallahi, ai sun sallami Kaka daga aikin da sha tara ta arziƙi, sunce taje ta huta haka, wallah kam sun bamu gida anan Dubai Quaters, baka gida ba Yusuf so masha'Allah, dama nace sai munyi waya tukunna sai in sanar muku insha'Allahu, to ashe ma Maijidda ta rigani".
yace,"masha'Allahu, Allah ya saka musu da alkhairi".
"ameen Yusuf, dan Allah ka gaidar min da su Nuratu da Ammi da Umma, kai da kowa ma musamman Inna Wuro, gaisuwarta tafi ta kowa yawa".
yace,"insha'Allah Ummi duk zasu ji, sai munzo gaisuwa".
"to Allah ya kawo ku, ina nan ina zuba ido".
daga haka suka yi sallama, Maijidda na murmushi tayi tafi tace,"mu dai abinmu sharr".
ta faɗa tana kallon Fillo data fito cikin complete shirinta na tafiya makaranta, ta gimtse dariyarta Fillo ƙuma ta galla mata harara tana cewa da Ummi,"na fito Ummi". ta zauna Ummi ta dafa kanta tayi mata adu'a sosai, tana ƙara ce mata ta kula.

Kaka da zolaya itama tace,"ke kuma sai da angon naki ya kashe wayar sannan za ki fito, wannan kiran dai ai nasan ba namu bane, naki ne ake wani wayance da Ummi ake nema".
Fillo ta turo baki tace,"angon wata dai amma bani ba, me zanyi da wannan". ta faÉ—a da duk gaskiyarta.
Ummi ta waro ido waje tace,"iye! Auta ɗan nawa kike cewa me zaki yi da shi?, ban da shi Auta kin isa yanzu ki ƙara saka ni a idonki?, ah lallai, wato babu ko kunya a gabana kike faɗin me zaki da ɗana, ba ki san nafi sonsa ba akanki".
cike da shagwaɓa kamar zata yi kuka tace,"Ummi ni to ba zan auri me mata ba, dan Allah ku daina haɗa ni da shi".
Ummi na ƴar dariya tace,"idan kin kwantar da hankalinki ma nima ba zan yarda ayiwa ƴata Nuratu kishiya ba, ah tou can ki yanka kije ki samo daidai dake ɗin, nima ɗana yafi ƙarfinki dan ba abinda zai yi da ƙwaila irinki".

ta miƙe cike kunya tana barin kusa da Ummi tace,"ni bama yanzu ba ai, sai na zama barrister tukunna in zaɓa in dirje, by then Abba nah ya shiryu ya gane gaskiya sai yazo ya ɗaukemu, mu koma can inda muka fito sai mu bar tsohon ɗan naki anan da shi da gwalagwajin matar tasa".
ta faɗa tana ƴar dariya, Ummi ta ɗau hula ta jefa mata. "kin ci ƙaniyarki naji kin ƙara kiran Nuratu da wannan sunan, ki kiyayeni wallahi".
tana dariya sosai saboda yanda Ummin tayi tace,"nima to a faÉ—awa mijinta ya kiyayeni ya fita a sabgata, ya bar ganin ya taimakawa Ummina hakan ba zai sa ya kafa gwamnatinsa a zuciyata ba".
sai kuma ta harari Maijidda tace,"ke kuma baƙar munafuka kici gaba da min abinda kike, Allah idan baki wasa ba naje na faɗawa Hamisu me gadi kince kin amince ya turo iyayen nasa. kuma wallah ki faɗawa Dr'n da yake wahalar dake kan yi masa campeign, Fillo ba zata auri me mata saboda haka ya kama gabansa".

Maijidda tace,"wallah ba zan faÉ—a ba, insha'Allahu sai kin zama amaryar Dr".
Fillo bata ce mata komai ba taiwa su Kaka sallama ta fita tana sai ta dawo.
tun satin da suka dawo wannan sabon gidan da Hajiya Madina ta basu kyautarsa ta fara zuwa islamiyya wacca ƴaƴan maƙotansu suke zuwa, makaranta ce me kyau da tsada acan wajen gidan sarki, itama Hajiya Madina ce ta sakata dan har gida tazo ta sameta tana ƙara tambayarta,"Fillo ina sonki, ina tsananin sonki Fillo, gani nake har yanzu ban kyautata miki da rabin alkhairin da kika min ba, dan haka ki faɗa min me kike so na kuma yi miki yanzu?".

Fillon na kukan farin ciki tace mata,"Maama ni makarantar Islamiyya nake so in koma, ina so na haddace alƙur'ani". kuma take a wurin Hajiya Madina ta kira Khalil ya gama yi mata komai a washegari kuma ta fara zuwa.
yanzu haka kuma ana ma ta processing na zana private wa'ec ne, dan Hajiya Madina na gab da tafiya wani course kuma tana so idan zata tafi su tafi tare da ita kamar yanda tayi mata alƙawari.

tana tsaye bakin titi tana jiran abin hawa wata jar mota tayi parking a gabanta, gabanta ya faɗi sanda aka zuge glass ɗin motar, ta ɗan ƙaƙalo murmushi tace,"Adda Samha ina yini".
tace,"lafiya lau Fillo, makaranta zaki wuce?".
tace,"ehh". "to shigo sai in ajeki a hanya".
Fillo kamar ba zata shiga ba, saboda ita har ga Allah tana tsoron mutumin da ko da sau ɗaya ne ya taɓa cutar da wani a rayuwa, balle kuma wanda ya jima yana haddasa abubuwan za zai sa yaga bayan wani duk da Allah ba ya ba shi nasara, gani take tamkar su Samha ba akan Turaki bane kawai suke da wannan mugun hali, wataƙila sun cutar da mutane da yawa ma ba tun yanzu ba.
ɗayan ɓari na zuciyarta yace mata,"ki kyautata musu zato a yanzu, ki ɗauki komai da ya faru a matsayin abinda ya jima da wucewa".

Fillo ta sauke numfashi ta buÉ—e motar ta shiga, daga yanda ta kalla Samha na driving É—in ta san tana cikin nishaÉ—i sosai. dan kamar ba wannan azababbiyar Samhan da ta sani ba a baya ba, kamar ba wannan Samhan da taji suna haÉ—a plan É—in yanda zasu kashe É—an'uwansu ba, ta saki baki sai labari take yi mata, hirar da ita dai bata cewa komai.
Chapter 98 · 0% Book details