Sashe 119
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta ƙara kallon Baffa da kyau tace,"dan Allah ka samawa yaron nan lafiya haka nan, iyakar biyayya yai maka, wadda tun da ka haife shi yake yi maka har kawo yau bai taɓa bijirewa umarninka ba".
Baffa ya É—aga muryarsa,"shutup Ramla".
ya juya yana kallon Turaki yace,"ban goyi bayan ka rabu da kowacce acikin su ba, amma ka mayar da matarka yanzu anan, idan ba haka ba nayi mugun saɓa maka".
still kan Turaki na ƙasa bai ɗago ba, Mum tace,"wallahi tallahi sai dai idan bana numfashi amma ba zai mayar da ita a yanzu ba, yanda kake bin umarnin mahaifiyarka saboda ka gama da duniya lafiya, shima ka barsa ya bi umarnin tasa mahaifiyar saboda ya gama da duniya lafiya, yanda kake gudun fushin taka mahaifiyar haka shima, yanda kake so ka haɗu da ubangijinka lafiya shima haka yake so, haba Alƙali ka bar yaro ya huta mana ko so kake sai kasa masa ciwon zuciya duk saboda kai baka so ka ɓatawa taka mahaifiyar".
ta mayar da idonta kan Turaki da tsananin tausayinsa tace,"Babana ta shi kaje".
ya miƙe jiki ba ƙwari zai wuce Baffa yace,"daga yau na haramta maka shigowa gidana, kar in sake ganin ƙafarka a ƙofar gidan idan kuma ba haka zaka sha mamakin abin da zan maka, fitaaa a gabana". ya ƙarasa maganar a tsawace wadda har sai da ta tsorata su Maama.
Turaki yay saurin É—ago kai yana dubansa, zai yi magana Mum ta tari numfashinsa da cewa,"je ka Babana, Allah yayi maka albarka".
Turaki ya fice yana jan ƙafafunsa da yake jin kamar ba zasu ɗauke shi ba.
yana fita Hajiya Ramla ta dubi Boejo tace,"ina ƙara baki haƙuri, Allah ya huci zuciyarki".
Sannan ta kalli Baffa tace da shi,"kayi haƙuri your highness".
bai ko kalleta ba ya durƙusa gaban mahaifiyarsa yana bata haƙuri tare da lallashi.
Hajiya Madina ta É—auki wayarta ta bar wajen ranta fess, tayi upstairs tana danna kiran lambar Ummi, tana yin picking bayan sun gaisa take shaida mata cewa,"Ummin Fillo insha'Allahu ranar litinin zamu kawo lefe".
Ummi ta amsa da,"Allah ya kaimu".
daga haka suka yi sallama.
ɓangaren Turaki kuwa yana zuwa compound kiran wayar Dada ya shigo wayarsa, kamar ba zai yi picking ba sai kuma ya ɗaga, abinda ya tsammata shi ɗin ne ya faru, dan yana sakawa a dodon kunnensa ya ji tana da masifa tana cewa,"ka sakar min jika ko kuwa?, ka san Allah kar ka bari in muku ɗanyen kai".
muryarsa ta fito kamar ta mara lafiya da cewa,"Dada in tana kusa ki bani ita sai na faÉ—a mata".
a harzuƙe tace,"ka faɗa mata me?".
yace,"shi abunda kika ce".
tace,"wai sakin?".
yace,"ehh".
tace,"haba yaro aini ba Æ´ar yau ba ce, kaje ka tambayi tarihina na fi son komai za'ai ayisa da hujja, dan haka furtawa da baki kaÉ—ai ba zai gamsar da ni ba, ba kuma shi tabbatarwa da jama'a kayi ba, saki a rubuce nake so kayi shi cikin farar takarda ka yo min aikensa".
a hankali yace,"shikenan Dada, ina kan hanya yanzu zuwa gida, idan naje zan rubuta insha'Allahu".
tace,"ya dai fi, a sakar min jika dan bazan kawota gidan da za'a ke ma ta kallon banza ba"
ta kashe wayarta tana ta jaraba akan Fillo dake kwance kan gado tana aikin kuka tun É—azu.
Ilham na kwance a ɗaki hadimanta na matsa mata ƙafa Turaki ya shigo kamar an hankaɗo shi, ɗaya bayan ɗaya hadiman suka miƙe suka fita da azama. yay tsaye bakin ƙofa yana kallon Ilham wacce ganinsa yasa ta ɗauke idonta gefe tamkar bata ga shigowar tasa ba, shiru ya ratsa ɗakin na ƴan sakanni sannan muryarsa na shaida ɓacin rai yace da ita,"ki fito waje ki same ni".
har yay bakin ƙofa zai fita sai yaga kamar bata ji me yace ba, hakan yasa ya maimaita mata amma da mamakinsa sai yaji tace,"in fito in yi maka me?".
yay ƙyam yana ta kallonta from head to toe da son gano wani abu, sai dai hakan ya gagara, ba ya son wata sabuwar damuwar dan haka bai ƙara cewa da ita komai ba ya juya zai fita sai yaji tana cewa,"na faɗa maka zan kuma ƙara nanata maka Turaki, ba damuwata ba ne ka auro duk wacca ka ga dama, but ka san da abu guda ɗaya shine ba zan zauna da kishiya a cikin gida ɗaya ba, in har kuma ka aikata wannan kuskuren to ina mai tabbatar maka da cewa kayi bankwana da zaman lafiya da kwanciyar hankali kenan, sonka da nake ba shi yake nufin ka ɗebo duk yayin da ka ga dama ka watsa min ba, wallahi! wallahi! wallahi! muddin wata tare acikin gidan nan sai dai ko ni ko kuma ita".
sai kuma tayi shiru tana fashewa da kuka tana miƙewa zaune ta kifa kanta da gwiwa, sosai take kuka tana faɗin,"me nayi maka a rayuwa kayi min wannan tsanar, ka rasa da me zaka ƙuntata min sai da kishiya, kishiyar ma aure ko wata biyar ba'ai da yi ba, waɗanna kalar maganganu kake tsammanin kunnuwana zasu dinƙa ji daga bakin mutane, kamata, tsakani da Allah kayi min adalci kenan?, kai ko tausayina ma baka ji, ina cikin tashin hankali na irin mawuyacin halin da mahaifiyata ke ciki, kai baka zauna ka rarrasheni ba kuma kace wai ka auri wata tun kafin ni, wanna kalar rainin hankali ne wannan?, to wallahi duk wacce ta shigo gidan nan sai naga bayanta ka rubuta ka ajiye".
Turaki yay murmushin takaici ya fice ya bar ɗakin, ba tare da yace da ita ƙala ba, bedroom ɗinsa ya wuce kai tsaye, yana shiga yay kiran lambar Bello.
Bello na ɗagawa yace da shi,"kai MT you should have call me ka faɗa min bama baman da suke tashi a gida, kawai kasa na ɗau ƙafa na tafi zance Boss yace kar in ƙara zuwar masa gida in ba haka ba sai ya ɓalla ni, Boɗejo kuwa kamar zata bankawa motata wuta, to ni dai yace in ƙara jadadda maka inuwarka ma kar ya sake gani. you thank God kana da gidanka har da mata, ni yanzu fisabilillah ta ya zan jure rashin ganin Zaytun har tsawon lokacin da zai sauko daga dokin fushinsa?, MT please ban shawara dan wallah jin zuciyata nake kamar ana ɗinketa da zare da allura, AC ce fa a motata amma uban gumi kawai nake haɗawa".
a sanda Turaki ke ɗaura towel a ƙugunsa yace,"kana jina?".
Bello yace,"yo MT ko ban da kunnen jinka ai ya zama dole ma na aro na saurareka, balle kuma akwai, ma za ka faÉ—i duk wata kalar shawara da kake ganin zata zama way out".
Turaki ya cika bakinsa da iska ya fesar yana kama ƙugu sannan yace da Bello,"plss kar ka min hauka, i want ask you something and be serious ka bani amsa, ta ya ake gane mace na da ciki?".
Bello ya lailayo wata ashar yace,"dan ubanka dama har haka kayi babban aiki?, shege wooo kace baka sonta?, to da kake tambayata ya ake gane mace na da ciki waka taɓa gani na yiwa?, ni ba ɗan iska ba MT karka ƙara min wannan tambayar, ka ɗauketa kuje asibiti ka tambayi waɗanda suka karanci abun, ka ban shawarar kawai da na tambayeka ta ya zanke ganin Zaytun?".
Turaki yaja tsaki da cewa,"useless".
sannan ya kashe wayar. ya ƙara lalubo lambar Dr Hasheer, sai da kiran ya yanke sannan Dr Hasheer ya kira shi, bayan sun gaisa yake ce masa.
"Dr kana gida please?".
Dr Hasheer yace da shi,"ehh lafiya dai?".
Turaki yace,"in ba damuwa don Allah ka leƙo gidana".
Dr Hasheer yace,"ok babu damuwa, on my way right now".
ya dire wayar yana shiga toilet ya sakarwa kansa shower, bai jima ba aciki ya fito yazo ya tayar da sallar azahar don ba ya jin zai iya fita masallaci, duk da already ma an riga an idar. idarwarsa kenan Dr Hasheer ya kira shi yake shaida masa yana ƙofar gida, yace da shi alright ga shi nan fitowa.
jallabiya ya zura ya sauka ya fita ya shigo da Dr Hasheer, suka É—an zanta a parlo na Æ´an mituna sannan Dr Hasheer ya ba shi urine container.
sanda ya shiga É—akin Ilham tana toilet, har zai tsaya jiranta kuma sai kawai ya isa bakin toilet É—in yay knocking.
ta kashe shower É—in tana tambayar waye, yace,"ni ne, are you coming out now?".
tai masa shiru bata yi magana ba har tsawon minti uku, bai ji ta amsa mishi ba kuma bai ji ta kunna shower É—in ba.
ransa ya ɓaci kawai ya murɗa handle ɗin ya faɗa ciki, ya ɗaure fuska ya haɗe girar sama da ƙasa ya miƙa mata robar,"yi fitsari ki ban".
"ban gane ba". ta faɗa tana kallonsa nata ran itama a ɓace tana ɗaure tata fuskar.
da yay mata jan ido ya sakar mata tsawa bata san lokacin da ta miƙa hannu ta karɓa roban ba, zuciyarta kamar zata fito waje dan baƙin ciki ta durƙusa tayi fitsarin ta miƙa masa.
ya karɓa yana ƙare mata kallo tsab a naked ɗin da take don gano wasu alamomi da Dr Hasheer ya faɗa masa, ya watsa mata banzan kallo sanda zai fice, ko ƙofar bai rufe ba ya bar ɗakin kamar iskar guguwa.
Dr Hasheer ya miƙe ganin ya fito, Turaki ya bashi container ɗin da yake riƙe da ita kamar ya riƙe kashi, yace,"please Dr kar ya wuce yau".
Dr Hasheer yace,"you just give me 1hour, shima saboda ba hospital zan wuce direct ba, amma da zarar mun kammala gwajin i will call you and tell you the result".
Turaki ya basa hannu su kai shaking yana faÉ—in,"thank you so much".